Showing 123001 words to 126000 words out of 145961 words

Chapter 42 - ZUCIYA COMPLETE

hannu ya goge inda tamai kiss din sannan yai waje.

A waje yaga Asim da kansa ya karasa ya mikamai hannu suka gaisa wanda hakan yai bala'in ba Asim mamaki, Ashraf yai murmushi yace " Asim dama inas

an magana dakai."

Asim yace " inaji."

Ashraf yace " kamar ya kamata muwa Kawu magana ya karama matsayi inaganin kamar inda aka maidakai yanzu is too low for someone like u."

Cikin tsananin mamaki Asim ya kalli Ashraf yama kasa magana, Ashraf

ya dan dafa kafadarsa da hannu daya yace " barshi in baka so."

Yana kai wa nan yai gaba, da sauri Asim yasha gabansa yace " da gaske kake?"

Fuskar Ashraf a maze kamar yanda yake kullum yace " wasa nakeyi to da?"

Asim ya sa dariya yace " mam

aki nake yi ai bantaba tunanin za ka taimaken bane ba ai naga tun muna yara bama wani shiri."

Ashraf yace " ko ba ma shiri ai kai dan uwanane."

Yai gaba abinsa daga fadar haka, Asim yai dariya yace " wai yau me nakeji haka?"

Bangaren Kawu ya

nufa cikin zumud'i ko sallama baiyi ba ya tura kofar d'akin, kawu na gaban wannan akwatin, jin Asim yasa yai saurin rufewa tare da turashi karkashin gado da sauri, ya kalli Asim cikin fada yace '" kai wai sai yaushe zakai hankali ne?"

Asim yabi akwat

in da kallo sannan ya basar yace " Abba anya kan Ashraf d'aya kuwa?"

Kawu yamai kallan mamaki yace " ban gane ba."

Asim ya matso yace " yanzu wai yacemin ya kamata muma magana ka karamin matsayi wannan matsayin nawa na yanzu is too low for me."

Kawu yai wata dariyar rainin hankali yace " amma ba kada hankali ko?"

Asim cikin mamaki yace " bangane ba."

Kawu yai dan tsaki tare da mikewa yace " Kanaso kacemin Ashraf ne yace ma haka?"

Da sauri Asim ya daga kai, Kawu ya hade rai yace

" ba ka cikin hayyacinka da alama mafarki kai."

Asim zai sake magana Kawu yace " mu fita ni."

Haushi ya turnuke Asim yai waje a zuciye, har yayi nisa ya dawo gun Kawu yace " Abba me kake nufi dani?"

Kawu ya kalleshi cikin mamaki ba tare da

ya amsa ba, Asim ya cigaba " menene baka yarda dashi ba game da ni? Ni din ne baka yarda Ashraf yayi acknowledging din aiki na ba ko kuwa baka yarda da zan iya wani abun bane?"

Kawu ya kalleshi cikin kulluwa da wannan halin nashi, yace " duka, u alway

s disappoint me."



Yana kai nan yai gaba yabar Asim a tsaye a gun.

Asim yabi Kawu da kallo cikin tsananin takaici da haushin yanda Kawu yake mai.

Kawu kam mota ya shiga cikin takaici.

***********

Nafi kam bayan tayi wanka

tana zaune a d'aki ita kadai duk abin duniya ya isheta ta kira Ferry a waya nan sukai ta hira har Ferry ta sanar da ita jarabawarsu ta fito.

Nafi tace " haba?kin dubo?"

Ferry tace " a'a amma ya Nabil yau zai dubo min."

Naf tace " kice ya d

ubo da nawa "

Ferry tace " to, amma Nafi karfa ki yaudaren kije ki cike wata makarantar ba BUK ba."

Nafi tai dariya tace " karki damu duk inda kike nima ina nan, sai dai in samu ne banyi ba amma ina zani?"

Sun dade suna hira kafin suyi sallam

a bayab sun gama tsara bikin Jibiya da za'a fara nan da 2wks, Nafi tace " Zata kawu mata kudin ankon inyaso sai a musu gaba d'aya komai iri d'aya."

Tana kashe wayar tai shiru, a ranta tace " Ferry fa batasan ni matar aure bace fa ko? Ya kamata in sana

r da ita kar taji daga baya ta d'auka ko yaudararta nai."

**********

Ashraf na zaune a office ya dukufa sosai gun aiki yaji an banko mai kofa, Secretary dinsa yana biye da wanda ya bud'e kofar yana cewa " malan meye hakan?"

Ashraf y

a kalli Habib yama Secretary din alama da hannu akan yaje.

Nan yai gaba, Ashraf ya kalli Habib yace " Habib lafiya naganka haka?"

Habib cikin fada yace " Ashraf me ake nufi akan kai mijin Nafi ne?"

Ashraf yamai kallan mamaki yace " ban gane

ba?"

Habib yace " baka gane ba kamar ya? Little tace kai mijin Nafisa ne, ni kuma banaj na taba jin wannan labarin."

Ashraf ya koma ya zauna fuskarnan a hade yace " yanzu ai kaji."

Habib ya matso cikin tsananin kishi ya kamo wuv yan Ashraf y

ace " how can u do this to me? Kasan kuwa yada nake da burin auren yarinyar nan? Taya za'ai kac......."

Ture hannunshi Ashraf yai da karfi yace " kai ko kunyata ma bakayi? Taya za'ayi kazo kanamin zancen wai so bayan kasan kanwata yanda take sanka?"

Habib ya kalleshi, Ashraf yai wani murmushin yace " badai cemin zakai baka sani ba? Zan iya aminta inka fadi wani abu amma ba wannan kalmar ba."

A hankali Habib yadanyi baya, Ashraf ya sake murmushi yace " mubar wannan maganar, ina Dady?"

Jik

i a sanyaye Habib yace " yana gida."

Ashraf yace " Allah sarki Dady baka gani ya kamata a dan ko karamai girman asibitin nan ko kuma a bud'e mai wani babba?"

Habib yai dariya yace " tab lalai, dady din?"

Wani irin kallo kasa kasa Ashraf yamai

, Habib yacigaba " kabar Dady kawai sani ne bayasan ayi amma yanada kudi sosai inaj fa yanada gidajen haya manya kusan guda goma."

Ashraf yai murmushi yace " amma wannan ai mayb daga baya ya saisu."

Habib ya girgiza kai yace " a'a wlh, ni fa rann

an inajinsa da Mumy yana zancen da gidajen lokacin duniya na kwance basa kawo kudi sosai amma yanzu dayake komai ya tashi kudi suke kawowa sosai."

Ashraf yai murmushi, kafin daga baya Habib ya tafi.

Ashraf ya d'au waya da sauri ya kira Uncle baya

n sun gaisa yace " Uncle nikam kasan komai ma dukiyar Abba kuwa?" yai maganar cikin bugar ciki.

Uncle yai dariya yace " a iya sanina nasan komai nashi."

Ashraf yai shiru jikinsa ya fara sanyi, can ya daure yace " kasan komai nashi tun kafin ya ra

su?"

Salim ya sake dariya yace " gaskiya nidai a iya sanina nasan komai."

Ashraf yai shiru can yace " shikenan na gode."

Yana kashe wayar ya mike tare da zuge glass din window yana kallan titi, a ransa addu'a kawai yake Allah yasa ba haka ba

ne......"



*[truncated by WhatsApp]

*Ina mika ta'aziyata zuwa Feedoh Deedoh Allah ya jikanta da rahama yasa Aljanna ce makomarta, ku kuma Allah ya baku hakurin rashin ta.* Ameen suma Ameen.

*May her gentle soul rest in peace*

Amee

n

*#ASHRAFEENAH*

��

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*77*

Ana azahar Dan Litti yazo suka fita shida Ashraf, gidan Salim suka wuce.

Fa

lo suka nufa inda Salim yace musu Auwal max na ciki, Ashraf ya kalli Dan Litti yace " dole ne ka hade rai ka maida abu serious."

Dan litti ya jinjina kai sannan suka shiga.

Ashraf da sauri ya isa gun Auwal ya kama hannunsa cikin nuna tsananin kul

awa yace " Uncle kana lafiya? Badai abinda ya sameka ko?"

Auwal cikin tsananin mamaki ya ke kallan Ashraf.

Ashraf yace " ko ba Auwal bane?"

Yace " nine Auwal Max"

Ashraf ya zaunar dashi sannan ya zauna a gefensa ya kama hannunsa yace "

nine Asim, babban d'an gidan Mansir."

Sai a lokacin Auwal ya saki fuska, Ashraf ya kara rike hannun sa Yace " Abba ne yace in tabbata na samoka kafin Ashraf ya fara samunka."

Auwal yace "Ashraf D'an....?"

Ashraf ya karasamai " dan Abbas mari

gayi."

Idanu Auwal ya zaro cikin tsananin tsoro yace " ya akai ya sanni?"

Ashraf ya dan saki fuska cikin yanayin damuwa, Dan litti yace " bincike yake akan abinda ya faru a baya."

Auwal cikin tsananin rud'ewa yace " inalilahi ya zanyi? Nika

m na shiga uku, banda masifun da suke afkuwa akaina yanzu kuma wannan?"

Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Abba yace inkula dakai sannan yace in tambayeka ranar meya faru? Har dakai akai hatsarin ko yaya?"

Auwal ya kalli Ashraf yace " mantawa y

ai? Ai na sanar dashi komai."

Shiru Ashraf yai yana tunani, sai jin Auwal yai yace " bayan mun shiga mota ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, aikuwa tana kira yace inje shi bari yaja

motar, da alama dai Mansir ya manta da hakan."

Ashraf yai dariya yace " da alama kasan yanzu abubuwa sunmai yawa dole ne mantuwa ta dinga shiga."

Auwal ya jinjina kai, Ashraf yace " amma ai ba wata hanya da Ashraf zai gane kaine ka lalata birkin

ko?"

Auwal yai shiru yana tunani kafin daga bisani yace " kai, babu sai dai in mahaifiyarka."

Cikin mamaki Ashrad yace " Umma?"

Auwal ya jinjina kai yace " ita kadai ce ta ganni lokacin da nake aikin, bayan ita gaskiya ba kowa."

Ashraf

yai murmushi yace " ai bakomai indai Umma ce, amma Dady fa?"

Auwal yace "Dady?"

"Hisham nake nufi."

Auwal yai dariya yace " shi ai bashi ya sani ba shine dai ya bani kudin aikina."

Ashraf yace " nasan wannan wai nufina baku kara haduwa

ba?"

Auwal yace " ina zanganshi nida na koma garinmu?"

Ashraf ya kara rike hannunsa yace "karka damu Abba yace inkula dakai ba abinda zai faru."

Auwal yai ajiyar zuciya sannan yace "tunda na taho gabana ke faduwa sai yanzu hankalina ya kwant

a."

Ashraf yamai murmushi.

Auwal ya kalli Ashraf yace " Amma kafi kama da Abbas, sam baka kama da mansir."

Ashraf ya shafi fuskarsa yace " duk ba jini d'aya bane su? Kowa haka yake cemin wai nafi kama da Marigayi, shikuma Ashraf din inka ga

nshi abin mamaki kamarsu d'aya da Abbana."

Auwal yace " ikon Allah, ai nikam bazan taba mantawa da Abbas ba, naci amanarsa na yaudaresa shiyasa nake ganin ishara kala kala."

Ashraf yace " karka damu ka kwantar da hankalinka."

Auwal ya daga k

ai.

Ashraf ya kalli Dan litti yace " ka maidashi gidana na Darmanawa."

Dan litti ya amsa da to, sannan ya kalli Auwal yace muje ko?

Ashraf ya mikamai kudi yace kasai mai abinda zai bukata na nan da sati d'aya.

Kallansa Auwal yai yace "har sa

ti zanyi anan?"

Ashraf yace " tsoro nake kar mu maidaka Ashraf ya sa a kamaka."

Jin zancen kamawa yasa yace "to ai ba laifi satin ma."

Nan sukai waje Ashraf ya bishi da wani kallo na takaici, sannan ya zaro wayarsa dayai recording ya sa a co

mputer ya yanke maganar daga inda yace " _Nine Auwal Max_"

Ya tura ma Kawu da d'aya wayarsa.

Kawu wanda ya fito daga meeting kenan ya ga anturo mai email yana bud'ewa yaji muryar Auwal da abinda yace.

Mamaki ya kamashi, meye hakan kuma?

???

Bai kawo komai ba yai gaba.

Salim ya kalli Ashraf yace " amma kana tunanin zaiji wani abu dan yaji suna kawai?"

Ashraf yai wani murmushi yace " it won't be fun in na turamai komai a lokaci d'aya, so nake naga yanda hankalinsa zai fita

daga jikinsa a kowace rana, yana wannan case din ga kuma na d'ansa."

Salim ya dafa Ashraf yace " U are very smart Ashraf sai dai please kayi a hankali dan ina tsoron wannan kawun naka."

Ashraf yace " karka damu Uncle, sannan ina tunanin Mumy ne,

in barta anan ko inkaita wata kasar, kar ya hanani komai saboda ita."

Salim yai shiru sannan yace " tabbas kayi tunani dan kuwa zai iya cewa zai mata illa inkaki bin umarninsa."

Ashraf yace " shi nake tsoro."

Uncle yace " ka sata kawai ta ta

fi umara, taje ma ta nemi yafiya tai ibada ko ta samu rangwame."

Ashraf yace " nagode Uncle."

Nan ya fito.

**********

Su Asim an mallaki company murna a wannan rana ba'a magana, dashi da Anisa da Umma da sauran kannansa sunje sunga

guri kowa ya yaba sannan ya kira mahaifinsa ya sanar dashi.

Mamaki ya kama Kawu a ina Asim ya samu kudin siyan Company? Sai dai haka ya karasa company din dan tabbatarma idanunsa.

Mamaki sosai yakeyi ganin wannan katon guri wai mallakin d'ansa ne

, ya kalli Asim cikin zargi yace " ina ka samu kud'i?"

Asim yai shiru yana tunanin karyar da zaiyi, sai dai kafin ya furta komai sai ga wasu mutane ne nan su hud'u sanye da kayan 'yan sanda sunzo kusa da Asim.

Nan fa kowa ya matso ana san ganin

menene.

Na gabansu ya zaro id card dinsa yace " I am Sergeant Kabir."

Asim ya mai kallan banza yace " me ya damen da sunan ka?"

Ankwa ya ciro yace " u are under arrest."

Asim ya kalli Kawu sannan ya kallesu yace " ban gane ba, me nai?"

Kabir ya cafki hannunsa ya fara kokarin sa mai ankwa Asim na turgewa.

Kawu ya rike hannun Kabir yace " me yai?"

Kabir yace " an kai kararsa akan d'eban kudin company dayai "

Kallan mamaki Kawu yama Asim yace " me kenan?"

Asim ya shi

ga jijiga kai yana cewa " Abba ba Company dinmu bane, ai ba wani abun bane in na ranci kudi a ciki."

Hankalin kawu ya tashi yace " ku tsaya ayi magana."

Kabir yace " i am sry sir, bayan wannan yana dauke da laifin satar kayan da ba nashi ba."

. Asim cikin rud'ewa yace " mena sata kuma?"

Kabir yace " filayen daka saida takardun ba na gaskiya bane bayan kuma ka riga ka amshi kudin mutane."

Asim ya rikice ya kalli Kawu yace " Abba."

Kawu wanda gaba d'aya yama rasa abinyi yace " yan

zu me kuke bukata?"

Kabir ya karasa datsamai ankwa yace " am sry sir dole ne ya biyomu."

Yana kai nan yaja hannun Asim.

Umma wacce ta saki wani ihu tare da bin bayansu tana kira sai dai ina.....Sunyi gaba, Anisa ma kuka take sosai, Umma ta

matso gun Kawu ta rikemai kwallar riga tace " malam ka wuce ka amsomin d'ana."

Kawu ga runtse ido cikin takaici, Umma ta kara rikicewa tana masifa.

Kawu ya fizge jikinsa yace " me yasa kwatakwata kwakwalwar yaron nan kamar ta kifi take? Bashida h

ankali ne ko me? Ke ma kina ina da kika kasa bashi shawara,?in har bazaki iya dashi ba ai sai ki sanar min, yanzu wani irin abune wannan?"

Ya fada cikin tsananin takaici.

Nikam nace

🤷🏻

‍♀ ko a jikina.

Lol masoyan Asim amin afuwa, duk da

banaji yanada masoya.....Lol

[17:32, 05/09/2017] hm: *ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

��



*78*

Asim kam duk ya gama rikicewa sai rokon Kawu yakeyi,

Umma kam kuka kawai takeyi tana itadai a anso mata d'anta.

Sun isa police station akasa Asim a wani dan karamin d'aki dan yin bincike kafin a rufeshi.

Kawu ya karaso a tasa motar ya umarci a barshi ya fara magana da Asim, ba musu kuwa suka barshi

.

D'akin ya shiga ya kalli Asim yace " ina kasamo filayen gidaje da gonaki haka?"

Gabansa ne ya fadi, ta ina zai iya cewa satarsu yai? Cikin rawar murya yace " siya nai."

Kawu ya bugamai wani kallo yace " Asim kana wasa dani, wlh akan kai ka

dai bazan yi asarar abinda na tara da kyar ba, zan iya yanke tsakanina dakai in har naga kana neman zubarmin da kemata."

Asim ya kara rikicewa yana rokon Kawu akan yai hakuri, kawu yace " kasan nawa kaci kudin company kuwa? Banda zubarmin da mutunci

dakai, dole haka nan nizan yi kashin wad'an nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login