Showing 105001 words to 108000 words out of 145961 words
Kasan komai ko kuwa kaima bincike kakeyi??"
Isma'il yai murmushi yace " Bansan komai ba sai dan abinda ba'a rasa ba."
Ashraf yai dan huci kadan yace " Auw
al Max a ina zan sameshi??"
Kai ya girgiza yace " bansan inda yake ba, tun wannan ranar, in fact banmasan ko yana raye ba ko ya mutu, sai dai nasan abu d'aya tabbas shine wanda yaja Alhaji a wannan ranar sai dai abin zargi shine sun fita daga gida tar
e amma daga baya danai bincike sai naji Alhaji ne kawai a cikin motar sannan a bincike nane na gano Auwal Max mai gadi yana kallansa sanda ya shiga kasan mota, hasashe na ne yasa nasan yayi wani abu bawai proof gareni ba."
Ashraf ya matse hannunsa da
karfi, tare da runtse ido yace " Shi Abban a ina ya san Auwal max din?"
Isma'il ya kara girgiza kai yace " bansani ba, sai dai tun da nasanshi tare nake ganinsu, sai dai a koda yaushe inaji kamar bawai zuciya daya yake zaune da Abbas ba ganin duk wan
i plan indai mukai kafin mu aiwatar sai muji shi a gari ance Muktar yayi, shi kuma Abbas ba ya kara tada zancen."
Ashraf yace " Daga bangaren mahaifiyata akwai wani abu da kasani na gaba ko wani abun a tsakaninsu??"
Isma'il ya dan shafi goshinsa
sannan yace " akwai case daya faru wanda ya jawo asarar dukiya mai yawa daga bangaren matar Abbas."
Idanu Ashraf ya zaro yace " case?? Wani iri kenan?"
Isma'il ya girgiza kai yace " i can't tell u, sai dai kai ka nemo menene."
Ashraf yai sh
iru yana tunani, sun danyi shiru kafin daga bisani Ashraf yamai sallama.
Yana fita ya shiga mota tare da sa kansa a sitiyari wani irin zafi yakeji zuciyarsa namai.
Ya dade kafin ya daure ya tada mota yai gida.
**********
Nafi kam
yau sam bata fita ba tana kwance a d'aki gani take kamar in ta fita za'a gane abinda ya faru daren jiya.
Bayan magrib tai sallah tana zaune ita da Little sukaji ana knocking.
Little ta tashi ta bud'e, Mumy ce ta shigo fuskarnan tata a b'ace.
Little tace " Mumy ya akai?"
Bata kulata ba ta karasa gun Nafi wacce cikinta har ya duri ruwa, Mumy tace " Ki shirya gobe zansa a maidake garinku."
Nafi ta zaro ido cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy, Little ta matso tace "Mumy wai meyasa kike h
aka ne? Matar yaya ce fa....."
Tsawa mumy ta mata tace " fita."
Little mamaki ya kamata ta fita da sauri, bangaren Ashraf ta nufa tana zuwa tahau bugawa, shiru da alama bai dawo ba gashi ta bar wayarta, jiki a sanyaye ta dawo nan ta hangoshi daga
nesa.
Da gudunta ta karasa gunsa, Ashraf ya kalleta yace " Little!"
Cikin haki tace " Yaya Mumy ce."
Yace "Mumy?"
Ta daga kai tace "Nafisa...."
Ai bai jira ta gama ba yai bangarensu da saurinsa.
Yana zuwa bakin kofar dayake a
bud'e yake yaji Mumy na cewa " Me zaki iyama Ashraf da har kike tunanin zamq matarsa? Ban yarda da wannan auren ba dan haka dole ne gobe ki koma kauyenku."
Nafi kam hawaye ne kawai ke zubo mata.
Muryar Ashraf ce ta daki kunnuwansu yace " Inji w
a kenan?"
Mumy ta juyo har zuciyarta sai dataji dan tsoro sai dai ta dake tace " injini ni mahaifiyarka."
Ashraf ya karaso ciki yace " Do you hate us that much? Ni da Mahaifina nake nufi?"
Idanu Mumy ta zaro cikin mamaki tace " me kake fada
haka?"
Yai murmushi yace " me? Ba tsantsar tsana bace yasa kike bakin cikin ganin farinciki na? Na sanar dake matatace, na dauka uwa mai san danta zataso farin cikinsa."
Ya girgiza kai cikin takaici yace " sai dai me? Ban taba gani kinso abinda n
akeso ba tun da na mallaki hankali na, in har nace gabas nake san yi to burinki kice kekuma yamma kikeso nai."
Cikin murya mai zafi ya karasa maganar da cewa " inkinsan da haka meyasa kika auri Abba har kika haifine??"
Nafi da sauri ta taso ta
zo kusa dashi ta dan turashi baya, idanunta na zubar da hawaye tace " Yaya me kakeyi hakan?"
Mumy kam gaba daya jikinta ya gama mutuwa kamar wacce aka kwarama ruwan sanyi, Nafi ta cigaba da turashi zuwa waje tanacewa " please Yaya ka bari, kar kai fad
a da Mumy saboda ni dan Allah."
Ashraf ya rike hannunta idanunsa suka kada sukai jajawur kamar jan gauta, ya kalli Mumy yace " na tabbata sanda mahaifina ya rasu kina daya daga cikin masu farin cikin faruwar hakan."
Nafi kai kawai take girgizawa
tana kuka, Ashraf na gama fadar haka ya fara jan hannun Nafi, har sunje bakin kofa ya juyo yace " in har baso kike nabar gidan nan ba kar ki kara shiga harkar matata."
Ya ja hannun Nafi sukai waje, zubewa Mumy tai a gun ta rike inda zuciyarta take jin
tana mata zafi ta saki wani irin kuka mai kuna.
Ashraf kam jan Nafi kawai yake sunje yin kwana sai ga Anisa ta sha gabansu, ya buga mata wani kalli dan yanda yakejin zuciyarsa tayi sa'a ka da bai mareta ba, itama harararsa tai tace "anji kunya wlh
kwartanci da ranar Allah, to wlh baku isa ba naga uban da zai maye min gurbina."
Ashraf ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace " gurbin inaji nine nake rike da ragamarsa ko? To mai zai faru in na sallami mai gurbin?"
Idanu Anisa ta zaro tace "m
ai kake nufi Yaya?"
Yace " zaki matsa ko sai na fahimtar dake abinda nake nufi??"
Da sauri ta matsa ya ja hannun Nafi sukai bangarensa, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsa ya kalleta cikin tausayi ya runtse idanunsa, ransa na kara soyuw
a, baya ya juya mata yana wani hucci da sauri da sauri.
Nafi da sauri ta matso ta rungumeshi ta baya, tasa kanta a bayansa tana kuka tace " Yaya please cool down, me yasa ranka zai baci akan abinda baikai ya kawo ba??"
Idanu ya runtse yanajin wan
i abu na tasomai a ransa yace " ina zaki gane bayan wani bangaren na sanar dani harda Mumy a salwantar da mahaifina, tunda nasan abu ya hadasu da danginta."
Nafi ta kara kankameshi ta baya tace " Yaya Mumy fa ba wai tsanar ka tai ba, ka taba ganin ind
a uwa taki danta? Ni inaji a jikina akwai dalilinta na yin haka."
Idanu ya sake runtsewa, Nafi ta zagayo ta gabansa ta rungumeshi tace "please yaya kadaina fadamata magana mai zafi haka tun balle in akainane."
Hannu yasa ya zareta daga jikinsa ya
ce " Nafisa, kinsan ya nakeji a raina? A duk lokacin da matar nan tamin haka? Tun da nake da ita bata taba san abinda nakeso ba, bata taba yarda da abinda nace ba, bare in nemi kulawarta ko shawararta."
Hawaye ne ya zubo mai, Nafi kam hawayenta sai
tsananta gudu suke yi, da sauri Ashraf ya juya dan bayasan taga hawayensa.
Kara rungumeshi tai tace " Yaya fitar da duk abinda ke ranka, inaji kamar abubuwan da kake hadiyewa sunyi yawa, shi hawaye rahama ne in kayishi yanasa bakin cikin mutum ya ragu
, sannan maganar Mumy ni dai inaganin da wani abu."
Ashraf ya hadiye hawayensa yabar idanunsa a runtse, Nafi ta dago a hankali ta danyi dage ta sumbaci bakinsa kadan, tace " i am here with u, ka daukeni a matsayin mutum mara ji mara magana, ka fadi du
k abinda kake boyewa a ranka ko ka samu sauki cikin ranka, Yaya na kula bacci ma bakayi yanda ya kamata, kuma ni nasan duk saboda abubuwan da kake hadiyewa ne kai kadai."
A hankali ya bud'e idanunsa ya jawota ya rungume tsam, yace " Nafisa I really Lu
v u."
Dagowa tai cikin mamaki, ya kara kankameta yace " kece mace ta farko ko ince mutum na farko da nake jin tabbas wannan itace, itace wacce takesona tsakani da Allah, itace wacce ta yarda dani, itace wacce zuciyata ta aminta da ita, itace nakeji in
har tana tare dani i can endure everything."
Ya dan yi ajiyar zuciya yace " ban taba tunanin zan taba jin mutum haka a raina ba, ban tabaji na aminta da mutum haka ba, Nafisa please don't ever betray me"
Wani hawayen dadi ne ya zubo mata kai kaw
au take girgizawa tace " How can I! How can I......."
Sam ta kasa karasawa ya dago a hankali ya kai bakinsa cikin nata......
_Ni kaina idanuna yau sun ciciko, tabbas Ashraf yaga rayuwa ko ince yana gani, babu abu mafi soyuwar zuciya da kunci
irin ka rasa wanda zaka aminta dashi, ka rasa wanda zakai shawara dashi, ka dinga ji kamar kowa na kusa dakai nemab ganin bayanka yakeyi_
Allah ya tsaremu daga sharrin mutum domin kuwa sharrinsa yafi na shedan.
Ameen
*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*64*
Kwance suke tare a kan gado tana makale a jikinsa sun shiga bargo, fitilar d'akin a kashe take sai
ta gefen gado da take a kunne, sunyi shiru sunajin dumin junansu.
Cikin sanyin murya Ashraf yace " Nafisa."
Tana kan kafadarsa tace " Naam."
Yacigaba " Abba hatsarin dayai a kwai hadin baki a ciki."
Da sauri tai nufin mikewa yasa hannu
ya maidata yanda take, shiru tai sai dai gabanta sai faduwa yakeyi, yacigaba " bansan takamaimai dalilin dayasa Abba ya tsole musu ido ba ko ince suka tsaneshi ba sai dai gobe nake sa ran tambayar Uncle Salim in har shima bai sani ba sai inyi bincike da k
aina."
Nafi tai shiru, Ashraf ya cigaba " tun dana mallaki hankalin kaina nakejin komai ba daidai ba a gidan nan, sam na kasa yarda da yanda al'amuran gidan nan ke tafiya."
Nafi ta makalo hannunta ta kwibinsa a hankali itama tace " Yaya ni kaina
bayan Little taban tarihin gidan nan na rasa dalilin dayasa na kasa fahimtar abubuwa guda uku."
Ashraf yace " me da me kenan?"
Ta gyara kwanciyarta tace " Mumy inaji a jikina akwai dalilinta na auren kawu cikin gaggawa."
Ashraf yai dan kara
min tsaki yace "ba wani dalili dama kila can shi takeso ta yaudari Abba."
Nafi ta girgiza kai tace " karka bari zuciyarka ta nemi boyema gaskiya."
Kai ya dan kawar gefe sannan yace " next."
Tace " Meyasa kafin Abba ya rasu yafi zama dakai, naj
i hatta aiki ba fita yake ba kullum kuna tare dashi, nasan zai iya yiwuwa jikinsa ne yake bashi hakan sai dai yanda baya zama da kowa sai kai yasa nake tunanin da wani abu, ko yasan akwai manakisar da akemai ko kuma akwai wani dalili da mu bamu sani ba."
Shiru Ashraf yai yana tunani, Nafi tacigaba " nakarshe karkace kishi ne ko wani abun sai dai inaganin tayaya Abba dayakesan ka auri yaya nisa zai bada wasiyya akan aba matarka ta farko? Indai har yaya nisa yake so ta zama matarka banaji sai yace matark
a ta farko sai dai kawai ya bada yace abawa Yaya nisa in aurenku ya tashi."
Shiru Ashraf yai yana tunani lalai wannan abun tambaya ne, Nafi tace " nayi mamaki danaji wasiyyar ta kudi ce ganin ba kudi kuka rasa ba,banaji akwai dalilin dazai sa Abba y
a bada wasiyyar kudi."
Ashraf yai shiru yana tunani, Nafi ta matso da kanta tace " yaya karka damu da abubuwan danace, zargi nane kawai ba wani abu serious ba." tafada tare da kara shiga jikinsa.
Ashraf yai shiru yana tunani, ganin haka yasa Na
fi tai bacci, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya jawo littafinsa ya zare jikinsa a hankali ya nufi falo.
Can tsakiya ya bud'e inda yaga Abba yasa " Baban burina bai wuce naga na hada zuri'a da Muktar ba."
Shiru Ashraf yai ya dade kafin ya daw
o ya kwanta.
Da sassafe kuwa bayan sunyi sallah sun kwanta sai daya jira tai bacci sannan ya zare jikinsa yai waje.
Mota ya fada yai waje.
Gidan Uncle ya nufa kafin ya karasa ya kirashi a waya yace " dan Allah ya fito waje zasuyi magana ne
."
Yana zuwa kofar gidan kuwa yaga Uncle a tsaye.
Ashraf ya karasa suka gaisa sannan yace " Uncle zaka iya tuna me ya faru tsakanin Abba da dangin Mumy kafin ya rasu."
Uncle ya kalleshi yace " Ashraf a ina....."
Hannu ya hade gu daya
alamar toko yace " dan Allah kafadamin Uncle, nasan ba yanda za'ai case ya hada su da Abba ace lawyer dinsa baisan komai ba."
Uncle yai ajiyar zuciya yace " mu shiga motarka."
Nan suka shiga, Uncle ya kalleshi yace " Ashraf mai nene dalilinka nas
an jin abinda ya riga ya wuce?"
Ashraf ya kalli Salim cikin zakuwa yaji yace " ba komai kawai so nake naji ne."
Salim ya jinjina kai sannan yace " Mahaifin Ruma ya fara kasuwanci bayan yayi retire, ko da yake ba wai fara wa yai ba dan dama Hashim
(mahaifin Habib) dan kasuwa ne, kasuwancinsu ya bunkasa alokacin da Abbas arzikinsa da matsayinsa yai fice a garin nan.
Bazan manta ba bayan ka gama nursery ka shiga primary 1 wannan mumunan al'amari ya faru.
Hisham da mahaifinsa sukayo dealer
din kaya mai uban yawa wanda ya kunshi kusan duk arzikinsu, sai dai kaya aka hanasu shigowa, Customs suka rike musu kaya gaba daya container's dinsu.
Ba karamin tashin hankalu suka shiga ba duk yanda sukai a barmusu kayansu su wuce amma ina... Sam ab
u yaki yiwuwa."
Ashraf ya kalli Salim cikin mamaki yace " sunyo order din abu mara kyau ne?"
Ajiyar zuciya Salim yai yace " Kwarai kuwa sai dai sun b'oye hakan, ganin ba yanda za'ai kayan su ya fito ga dukiyarsu duk tana ciki yasa mahaifin Ruma y
a yanke jiki ya fad'i, tashin hankali ya kara tsananta.
A wannan lokacin nan Hashim ya samu Abbas yace ya taimaka suyi cuwa cuwa a sakar musu kayansu, Abbas mutum ne mai tsaurin gaske jin Hashim ya zo mai da wannan uzuri yasa ya mai duban kurila yace
" Hashim mai kuka sako a cikin kayanku?"
Ran Hashim ya baci yace " ko ma me muka sako ai ya zamarma dole ka taimakemu ganin mune muka samar ma aiki har kakai matsayin da kake yanzu."
Abbas yace " bai zamar min dole ba dan kuwa in har abinda kuka
d'auko akwai abin cutarwa to wlh ko d'ana Ashraf ne bazan taimaka mai ba."
Nan dai suka rabu zuciya ba dadi, bayan Abbas yayi bincike nan ne ya gano mugayen abubuwan dake kasan kayayyakinsu, ciki kuwa har da hodar iblis da 'yan kanananan makamai."
Ba karamin tsorata Abbas yai ba ya samu Hashim cikin tsananin fushi yace " Hashim da hankalinka zaka saro wannan mugayen abubuwan?"
Hashin cikin zafin rai yace " ce maka akai nawa ne? Na wani abokin Abba ne dan majalisa ne yace mu taho mai da sakon
sa."
Ran Abbas ya sake b'aci yace " to meyasa shi baiyi magana an sakar muku kayan ba?"
Hashim ya dan shafi kansa yace " tun bayan faruwar abin nan yabar kasar ma gaba daya, ba yanda zamuyi mu sameshi."
Abbas yace " kanaso kacemin kaf mugayen
abubuwan nan ba naka ko na Abba ko daya a ciki?"
Hashim cikin hasala yace " akwai mana, bayan yace mu taho mai dashi nima nai tunanin sawa a dan samomin jin yanda suke da tsada sosai."
Abbas ya bud'e baki cikin mamaki yace "Hashim kanka daya kuw
a??"
Hashim ya mike rai a b'ace yace " me? Yanzu dan ka zama babban mutum kana tunanin zaka wulakantamu? To wlh kayi kadan dolene kaje kasan yanda zakai su sakar mana kaya."
Yana kai nan ya nufi hanyar waje, daidai nan Ruma na kawo kai, Abbas ya mik
e yace " ba dole a ciki, sannan tunda dai bakuji kunyar cutar da mutane ba banaji nima ya zamarmin dole na bi bayanku, kasan inka sai da hodar da makaman wadanda za'a cuta dasu? Kasan bayin Allahn daza'a halakar dasu?mai makon ma ka dauki laifinka akan kus
kuren dakai sai ma gani kake baka aikata komai ba?"
Hashim ya kalli Ruma yace " ke Ruma!"
Mumy ta kalli Yayanta cikin tsoro, yace " wuce mu tafi gida, da alama Abbas ba sanki yake ba