Showing 54001 words to 57000 words out of 145961 words

Chapter 19 - ZUCIYA COMPLETE

shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. "

Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. "

Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai, jiki a sanyaye ta fito, sai dai dankar ka

wayenta su gane ta saki fuska.

Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo, ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa?

Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai, bai dade b

a bacci ya d'aukeshi.

Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi, da saurinsa yai alwala ya fito masallaci.

Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki, saboda kawar Little ce sosai

, sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki.

Anko suka saka, light purple d'in wani yadi ne, shiba lace bane sannan ba material bane, riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai,

balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta, Nafi tace " amma ankon yayi kyau. "

Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. "

Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? "

Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. "

Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? "

Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. "

Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani

mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. "

Little tace " to. "

Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne, sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi, kamar yanda nace Nafi ba fara bace can

sai dai tana da kyau gashi batada jiki.

Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud'in liki inji Little.

A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta, yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya

bud'e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba.

Ganin d'an wake yasa ya gane dalilin kiran, zubawa yai yafara ci kenan, Little tai sallama, amsawa yai saidai bai d'ago ba, lokacin Mumy ta tashi daga falon, wata sallama ya sakeji bayan ta l

ittle sai dai wannan muryar cikin sanyi take.

Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d'auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba.

Little ta karaso cikin murna tace " Yaya kaine anan? "

Nafi ta kalleshi ta baya

gabanta yai wani fad'uwa yaushe rabon data ganshi, Ashraf ya kalli Little yace " ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had'u a wani gun. "

Ta rike hab'a tace ina na isa yaya? Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai mun

a takura muku nikuwa ina zaka ganni? "

Baiyi magana ba, tace"Mumy fa? "

Ya ce tana ciki, da sauri Little tai ciki.

Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace " Yaya ina wuni? "

Juyowa yai dan ganin mai magana, kallan

mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa.... She can't be.

Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata, tai hanyar waje, dasauri yace " Ke! "

Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace " ke!

"

Nafi dai tana tsaye bata juyo ba, a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad'a yace " ba dake nake ba? "

Nafi ta juyo fuska a had'e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace " ganinai ba sunana kenan ba."

"mene? "

Nafi tad'an burtso bak

i, kallan mamaki ya mata yace " Ba Nafisa bace? "

Ta kara had'e rai ta kalleshi tace " au kama mantani? Ka d'aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? "

Ta juya cikin takaici zata wuce, da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tama

i, tace " Yaya mai kake yi? "

Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad'a a ransa, a fili yace " ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. "

Ta d'ago ta kalleshi sai dai batai magana ba, yace " wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? "



Tace " menai kuma? "yanda tai maganar yasa yace "Lalai yarinyar nan. "

Kokarin kwace jikinta tai tace " ni ba yarinya bace. "

Ya saketa tare da cewa " ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. "

Ta juya kanta gefe tace " nemana akeyi?"

Ya koma

ya zauna yace " ina zaku haka? "

Biki zamuje.

Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan.

Mama ne ya kamashi yace " lalai yarinyar nan, yaushe ta girma haka? Gaba d'aya tama canza kamar ba Nafin riga ba."

Itakam tana

fita tai d'akinsu, a falo ta zauna ta matse hannayenta, jikinta sai rawa yakeyi, meyasa suka had'u?

*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *HWA*

*na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMo

hd*

{ *33*}

A can Little ta ganta falo zaune ta kifa kanta, ajiyar zuciya Little tai tace " Feena meye hakan? Mun taho tare shine zaki taho nan ki barni. "

Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tace " Sry My Little wlh jinai kaina na d'an saraw

a. "

Cikin damuwa Little tace " ayya! Sannu, ko zaki hakura da zuwa? "

Kai Nafi ta girgiza tace " Muje nima ina san zuwa ai, kuma kan yama daina. "

Nan suka mike Nafi ta kara gyara fuskarta sannan suka fito, sunzo shiga mota shikuma ya fito

daga b'angaren Mumy, yana kallansu har suka shiga ya d'an yi wani smiling yace " lalai yara sun girma." abinda ya fada kawai kenan yai gaba.

Su kuma suka shiga motar Little 'yar karama wanda Kawu ya sai mata wai murnar gama secondary.

¤¤¤¤¤¤¤

Umma na zaune kusa da Asim acan kuryar d'aki, Asim ya nisa yace " Umma tanashan maganin nan kuwa?"

Umma tai murmushi tace " Ai tunda muka bata magani tai b'arin nan na tsoratar da ita akan in har ta haihu yanzu da Ashraf to fa lalai wulakantata xa

iyi dan kuwa maza basasan mace mai saurin haihuwa."

Asim yace " to kidai tabbatar tanasha dan kuwa in har ta haihu da Ashraf to fa komai bazai yiwu ba, bazata taba bamu hadin kai ba, sannan muma in muka halaka Ashraf bayan mun amshe company d'insa d

a sauran dukiyarsa in har abinda aka haifa ya girma ya gano nan ma kinga akwai matsala. "

Umma ta jinjina kai tace "karka damu da wannan amma nikam har yanzu fa hankalina bai kwanta da wannan wasiyar da ya bata ba. "

Asim ya kurawa kasa ido, sann

an can yace " karya yakeyi ai ni da farko na yarda sai da naga wani murmushi da Kawu yai bayan ta kawomai haka kawai jikina yaban ba haka bane, sai daga baya nai tunani ta ina mutumin da zai mutu zai bar wasiyar kud'i kawai???? "

Umma ta jinjina kai

tace " nima yanda naga babanka nayi ne yasa nasan ba haka bane sannan nasan halin Yaya sarai bazai bada kudi kawai haka ba. "

Nan suka cigaba da kule kulensu....Nikam nace Allah ya kyauta dama ita zuciya kowa da irin tasa.

¤¤¤¤¤¤¤¤

Su

Little kam an d'auko Amarya suka wuce inda za'ai event d'in, suna tafe ana hira saboda duk kawayene, Nafi ma yanzu bata kunyar shiga hira, har suka isa.

Guri yayi kyau bayan Amarya tazo ne aka fara gudanar da shagalin biki, Nafi tana zaune daga g

efe ganin yanda 'yan mata keta rawa su Little ma an zake sosai, Nafi dai tana gefe rike da wayar Little tana dadanawa, tunanin kiran Ferry ne yazo mata, nan ta mike ta d'an matsa kadan daga inda ake shagalin.

Daga can ferry ta d'auka nan suka shig

a hira, tana nan a tsaye suna waya sai dai suk sanda ta kalli gun idanunsa na kanta, hakan yasa ta fara tsarguwa, daga gani shima gun bikin yazo yana zaune akan motarsa.

Ganin kallan ya fara isarta yasa ta matsa daga gun, bayan sun gama waya Nafi

ta juya da shirin komawa.

Ganin mutum tai kawai a bayanta tana juyawa suka hada ido, Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace " Malam lafiya? "

Wani lalausan Murmushi ya sakar mata sannan yace " Aminci Allah su tabbata a gareki. "

Ta kalleshi ci

kin mamaki sannan ta d'an motsa baki a hankali tace "tare da naka, amma..... "

" Shiiii dan Allah karki koreni kar kuma ki nuna bakya sona daga gani na yau d'aya."

Nafi cikin mamaki ta kalleshi, sai dai har kasan ranta yaso sata dariya yanda yai,

ya cigaba da cewa " Sunana Al-Amin masoyin wannan yarinyar. "

Juyawa tai bayanta dan ganin wace yarinyar, ya sakar mata murmushi yace " ina kike dubawa bayan gatanan a tsaye. "

Nafi ta harareshi yanzu kam ta gane da ita yake, ya d'an rike kunn

uwansa yace " Tuba nake ranki ya dade da alama na b'ata miki rai. "

Nafi batasan sanda tai murmushi ba tace " ba wani b'ata rai sai dai kayi hakuri ni matar aurece. "

Gani tai ya hau dariya, ya kalleta yace " matar aure? Wow na gode da alama da

wuri zamuyi aure in killeceki a d'aki."

Nafi ta makamai harara, da sauri ya kara rike kunne, yace " Taya zakice min ke matar aurece? Ina mijin? "

Shiru Nafi tai a ranta ta ce " inafa yake? Yana can gun matarsa. "

Al-Amin yai murmushi yace "

please ki amince dani, zan kula dake yanda bakya tunani, ni d'an Katsina ne, sannan kanwar maman yarinyar da ake aurenta ne. "

Nafi ta kalleshi sannan tace " lalai yayi kyau."

Hannunsa ya had'e guri d'aya yace " Dan Allah sunanki?????? "

*

FEENAH* abinda ta fada kenan, yace "wow nice name, a ina kike? "

Ta juya kai tace " zan koma ciki. "

Bata jira amsarsa ba ta fara tafiya, Biyota ya fara yi sai data juyo tace " dan Allah Al-Amin ka kyaleni. "

Kansa ya shafa yace " kai!!! Naji

dadi dan sake ki kiran sunana." ta kara harararsa sannan ta juya.

Taji dad'i sosai dataga bai biyota ba, haka kawai taji ta saki murmushi.

Sai da aka gama, wajen isha'i sannan suka fito zasu tafi, suna fitowa ya taso ya karaso gunsu tare d

a musu sallama, Little ta amsa tana mai kallan sani sai dai ta rasa a inane, yace " Little manya, can na ganki ai kinata rawa ana bikin Aminiya. "

Little ta nunashi da yatsa tace " Ya Al-Amin."

"Bingo!" ya fad'a yana murmushi, itama murmush

in tai tace " Ya Al-Amin ace kaine, nifa ince na rasaka sam ashe ka zama babba ko a hanya na ganka zanyi wahalar ganeka. "

Ya harareta yace " Haba Little a gaban Swt Feenah kike fadar hakan? "

Ta kalleshi sannan ta kalli Nafi data juya kanta, t

ace " yaushe ka ganta?"

Yace " gatannan sai wulakantani take ashe kawarki ce."

Little ta kalli Naf tace " Feena d'an uwan namu kike wulakantawa? "

Nafi ta kalli Little kamar zatai kuka, yace " wlh ina zuwa na ajiye su Hajiya na dawo dan in

kaita gida "

Nafi ta harareshi tace "cewa nai zan bika? "

Ya kara had'e hannayensa yace " Little please."

Little ta juya da sauri ta shige motarta taja tai gaba tana dariyar mugunta.

Nafi ta saki baki tana kallan Little cikin mamaki, Al-Am

in ya kalleta yace " Cwt Feena da alama dai nid'in nan nine zan kaiki. "

Ta juya kai cikin takaici tace " da wayace kazo nan ma. "

Yace " Matata tana guri ba dole inzo ba?"

Nafi ta kalli agoggon hannunta karfe 8 ga gun duk ba mutane, katseta y

ai da cewa. " Please Cwt Feenah ki taimaka, ai indai gidansu Little ne na sani. "

Nafi ba dan ranta yaso ba ta karasa gun motar ta shiga rai a b'ace, tana shiga ya zuge glass tare da kunna mata AC, itakam kanta ta maida gefe tana kallan waje.



Sun fara tafiya shi kad'ai yake mata magana, ganin batada niyyar kulashi yasa yai shiru.

A daidai kofar gidan yai parking, a wannan lokacin kuma, Ashraf ya fito kenan zai fita, kallan motar yai cikin mamaki, har zai wuce sai yaga alamar mace ce

a ciki, badai Little bace? Abinda yazo mai kenan, hakan yasa ya ja motar yai parking a gefe.

Itakam Nafi tazo fita yasa lock cikin mamaki ta kalleshi ya kashe mata ido sannan yace " Cwt Feenah shikenan bako sallama?? "

Nafi ta d'an turo baki

tace" in na fita ai zan ma. "

Kai ya girgiza alamar a'a sannan ya mika mata wayarsa yace "a'a na yafe numberki kawai nakeso. "

Ta d'anyi murmushi tace " sry Al-Amin sai dai banida waya. "

Kallan mamaki ya mata yace " mene? Shikenan wato dan

bakyasan ki bani mumber ki shine zaki fad'i haka? "

Kai ta girgiza alamar a'a tace "wlh ba haka bane, banida itane. "

Kallan mamaki ya mata, shikam Ashraf ya cika fam, me Little take a cikin mota har yanzu? A zuciye ya fito yazo kofar da take s

hikuma daidai lokacin Al-Amin ya cire sim d'insa na Mtn ya bar glo ya mika mata wayar yace " ga tawa akwai sim a ciki ba wanda yasanni da sim d'in ni in na fita nasai wani..... "

Kallan mamaki takemai, zatai magana sukaji an kwankwasa glass d'in motar

, inda take, Al-Amin ya zuge cikin mamaki.



Cikin tsananin mama ki Ashraf ke kallan Nafi, ransa yakai kololuwa gun b'aci, itakam tunda ta ganshi gabanta ya shiga fad'uwa.

Al-Amin ne ya katse mugun kallon da yake mata yace " Yaya Ina wuni?

"

Wani kallo ya bugamai batare da ya amsamai ba, ya kalli Nafi cikin tsananin takaici yace " kin fito ko sai na karya ki? "

Motar ta bud'e zata fita Al-Amin ya sake cewa " Cwt Feenah gashi. "

Juyowa tai ta kalleshi haka kawai taji tanasan

ansar wayar yanzu a gaban Ashraf, hannu tasa ta amsa sannan tace " Nagode kawai tai waje. "

Ta gabansa ta rab'a ta wuce haryanzu gabanta fad'uwa yake, Ashraf ya bita rai a b'ace, hannu yasa ya riko ta da karfi yace " abinda aka koya miki kenan a

makarantar??? "

Idanunta ne suka dan ciciko ta daure tace " me nayi yaya? "

Yai wani murmushin takaici yace " me kikai? Ke harkin kai ki zauna a motar namiji ku zuge glass? Ku kuma dade a ciki? "

Nafi wacce hannunta ke mata rad'ad'in rikon

da ya mata tace " kawoni yai daga gun biki."

Xaiyi magana yaga hawaye sun zubo mata cikin rawar murya tace " Yaya hanuna. "

Kallan hannunyai sai a lokacin ya kula da yadda ya matse mata hannu sosai ga agogo agun, nan ya sake mata hannu, agoggo

n kuwa har ya ji mata ciwo, mamakin kansa ya shiga yi.

Ya juya da sauri ya shiga motarsa ba tare da ya kalli inda take ba, Nafi kam agoggon ta cire tabi ciwon da kallo lalai ta yarda Ashraf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login