Showing 42001 words to 45000 words out of 145961 words
hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa " Zaki tafi ki barni ni kad'ai. "
Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun.
Little ta dafata tace " Muje Ya Habib na jiranmu. "
Nafi ta kalleta sannan ta d'anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace " Maryam bazanje inma yaya sallama ba? "
Little ta d'anyi dariya sannan tace " kije mana, amma bada ni zaki ba, n
i zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had'u. "
Nafi ta d'aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance " ke dan kut**** baki iy
a gaisuwa ba? Ko dan zaki tafi wata kucakar makaranta kike tunanin kinfi kowa? "
Nafi wacce tsoro ya rufeta ta kalleshi a tsorace tace " yahkuri Ya Asim wlh ban kula bane. "
Ya girgiza kai sannan yace " da alama ma kayan sa miki akai. "
Nafi
tai kasa da kanta kawai batace komai ba, ya tab'e baki sannan ya juya kai tare da cewa " sai aje ayi sallama da dadiron ki. "
Nafi kam bata fahimci me yake nufi sam da dadiro ba shiyasa ma bata damuba, ta juya ta cigaba da tafiyarta a ranta tana mam
akin irin zuciya ta wannan mutumin.
B'angaren Ashraf tanufa, a hankali ta kwankwasa kofar, daga ciki Ashraf ya amsa da ashigo.
A hankali Nafi ta murd'a kofar sannan ta shiga ciki, yana zaune akan kujera rike da laptop da alama aiki yakeyi, bai d'ag
o ya kalleta ba bare tasa ran zai tanka mata.
A hankali take d'agowa tana kallansa sai dai ganin har yanzu hankalinsa nakan laptop d'in ga lokaci na tafiya yasa ta d'aure tace " Yaya zamu tafi. "
"To Nafisa Allah ya kiyaye. " abinda ya fada mat
a kenan har yanzu hankalinsa nakan abinda yakeyi, Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye,
makullin d'akinsa ta ciro sannan a hankali ta fara takawa har zuwa inda yake, mikamai makullan tai tace " gashi yaya."
D'agowa yai ya kalleta, idanunsu ne suka had
'u gabanta yai wani irin fad'uwa da sauri tai kasa da ido, shikam har yanzu idanunsa na kanta bai kuma amshi makullin ba sai cewa yai "Sanda na baki cewa nai ki dawon da shi in zaki wani gun? "
Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, idanunsa na kanta
hakan yasa ta karayin kasa dakai tare da cewa " kafin in dawo kayi aure nasan kuma a lokacin baka bukatar aikina. "
Bai san sanda ya saki murmushi ba sannan ya maida kansa kan aikinsa tare da sa hannu ba tare da ya kalleta ba dan ya amsa, hannunsu ne
suka had'u da juna, sai dai abin mamaki ya kasa d'auke hannunsa haka itama.
Ganin yanda take mutsu mutsu da baki yasa ya rike hannunta tare da makullin.
Yanaji sanda ta d'an zabura kad'an shi dariya ma taso bashi, ta d'ago tare da kafeshi d
a ido, mamaki ne ya kamata ganin hankalinsa ma baya kanta.
Idanunta na kansa sam ta kasa d'aukewa, jitai yace " kallan bai isa ba? "
Da sauri tai kasa da kanta, yace " ba jiranki ake ba? "
Kallansa tai da mamaki taya za'ai ta tafi bayan y
a rike hannunta?
Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " So kike kuyi dare ko da wani abin da zaki fad'amin? "
Nafi ta d'an yi rau rau da ido tace " Yaya Hanuna fa? "
Yanda tai maganar ita kanta batasan ta iya ba, ya kalleta sannan ya kalli h
annun, sakin hannun ta yai tare da zare makullin, ya kalleta yace "zan ajiye in ko in dawo sai kizo ki amsa. "
Ta kalleshi da mamakin kalamansa, ta daure kawaj sai cewa tai " Yaya nagode insha Allah bazan baka kunya ba. "
Ya mata wani kallo san
nan yace " kada dai kije ki biyewa kawayen banza, sannan kar ki kuskura kiyi kuka da sunan wai kinyi rashin mahaifinki ko nan. "
Nafi ta d'aga kai jiki a sanyaye, nan tamai sallama ta juya a hankali take tafiya har ta fita daga kofar.
Tayiwa Mu
my sallama nan Mumy ta bata dubu biyar wai kudin kashewa, itakam Nafi kin amsa tai sai da taga ran mumy ya b'aci tukunna, nan tai godiya suka fito, b'angaren Umma sukaje.
Tana zaune a falo, Aneesa na gefe itada kawarta suna kallan wasu kaya, d
a kyar aka amsa sallamar ta, jiki a sanyaye ta shiga sannan ta tsuguna tagaida Umma sannan tagaida Aneesa da kyar suka amsa suna mata kallan uku saura kwata, Umma tace " ai anyi dabara da aka saki boarding dan na gaji da ganin yar rigar fulani tana yawo a
gidan nan. "
Nafi batace komai ba, Aneesa ta harareta tace " Allah ya raka taki gona. "
Jiki a sanyaye Nafi ta fito daga b'angaren nan ta karasa kitchen tama su Goggo sallama.
A mota ta taradda Little zaune a gaban Mota kusa da Habib suna
hira, tasa hannu ta goge fuskarta sannan ta karasa cikin mota.
Habib ya juyo ya kalleta yace " Gimbiya Nafeesa irin wannan jira da aka sani haka? "
Murmushi ta d'anyi sannan tace " Tuba nake, amma gimbiya ai Maryam ce bani ba. "
Habib ya
kalli Little wacce taji dadin kalaman Nafi, yace " to me kike so indinga ce miki? "
"sunana mana. "
Habib yai dariya yace " ai ni bana fadan sunan mutum, kowa da sunan da nake cemai. "
Nafi ta kalli little tace " Little ki zabarmin to. "
Su d
ukansu dariya sukai, nan Habib ya tada mota, Nafi dama tana baya, ita kuna Little na gaba.
Sun fara tafiya Little ta juyo tace " Kinje kunyi sallama da yayan? "
Nafi tai murmushi tare da dg mata kai, Habib ya kalli Nafi yace " me yakeyi?
"
Tace " na daiga yana danna abu irin na Little a falo. "
Suka sa mata dariya sannan Habib yace " Ashraf kenan, yanada kwakwalwa ga iya aiki amma har yanzu na rasa me yake hanashi yin aikinsa. "
Nafi ta kalli Habib da mamaki sai dai batasan me
zata tambaya ba, jitai Little tace " anya ba abin da bane yake damunsa? "
Habib yai ajiyar zuciya yace " nima ina tunanin wannan, ai ko waye dole ne abin ya zamarmai Karma. "
Kai Little ta jinjina tace " Shiyasa bana ganin laifinsa in yana fada,
itama Mumyn ai.... "
Sai kuma tai shiru.
Nafi kam ta kasa shiru ta kalli Little tace " Me ya sameshi dan Allah. "
Little tai ajiyan zuciya tace " Nafi ki bari sai kin dawo zan sanar dake."
Habib ya kalli Little baice komai ba.
Har su
ka isa makaranta zuciyar Nafi fal take da tunani kala kala menene ya faru da Ashraf? Ita kanta tana mamakin Mumy da ta auri kanin babansa kuma harda 'ya a tsakaninsu.
Sun shiga makaranta nan Principal ta hadata da wata Copper wacce zata dinga nata
extra lessons, sunyi sallama Little ta shiga mota duk tausayin Nafi ya kamata.
Nafi kam sai data b'oye hawayenta, Habib ya mata alkawarin zuwa d'aukota shida Little in biki yazo, itakam batace komai ba dan bata wani damu taje bikin ba.
Tana na
n a tsaye har suka shiga mota suka tafi, ta goge hawayenta sannan ta karasa gun House Captain dinsu da aka kira, nan ta kira yara yan Js 1 suka kwashi kayan Nafi.
¤¤¤¤¤
A gida kam har yanzu Ashraf bai sakema Aneesa kamar da ba, sai dai yanzu
tana iya kokarinta wurin ganin ta farantamai rai, sosai take kula dashi, sai dai wannan ba damuwarsa bace in fact gani yakema ta takura mai bayan shi mutum ne dayakesan ya zauna shi kad'ai.
Mumy da ita da mahaifiyar Habib suka shiga kasuwan ni
kala kala mall da sauransu, suka had'a lefe na gani na fad'a, sunso suje Dubai sai dai Ashraf ya hanasu, yace " shi baiga wani abu da za'a siya da har za'a rasashi anan kasar ba. "
Kaya kam anyishi, naira ta gurzu, sai dai wannan ba komai bane a ka
n irin dumbin kud'in da Ashraf yake dasu.
¤¤¤¤¤¤
An ba Nafi d'aki cikin 'yan ajinsu, gaishesu ta shiga yi dan ita a gunta hakan shine daidai.
Dariya sosai suka mata, jin hausarta yasa suka san bafulatana ce, d'aya daga cikinsu wacce kan
a ganinta kaga wayayyiya tana kwance saman up na gado, sanye da vest da wando ta zuro kai tace " lalai da alama mun sami yar kwana. "
Dariya suka kara kwashewa dashi wata tace " Ferry ashe kin gano? Da alama kan ba komai sai iyaye suka sami kud'in go
mnati. " tafad'a tana kallan tulin kayan provision din Nafi.
Dariya suka kara sawa, Nafi tana nan tsaye idanunta suka fara neman kawo ruwa, watace ta dafata tace " ki shiga da kayanki, sai ki zauna a up gadan dake kallan na Ferry. "
Nafi ta d'a
ga kai alamar to, sannan ta shiga da kayan, daga ganin yanda suke mata kallan wulakanci yasa tasan bazataji dadin wannan zaman ba.
Sai dai ya zatai?????
Tana gama jera kayanta aka turo wata yarinya akan ta fito karatu karfe 2 tayi, Nafi tayi
mamaki ganin ai yau tazo, sai dai ba yanda zatai sallah kawai tai tafita waje tanaji suna gulmar ta.
*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Gaisuwa da jinjinar ban girma
gareku masoyan arziki, soyayyarku daban take 'yan group d'ina na The Queen Bee da Ayusher Fan Club..... ILYSM
💋
*
{ *27*}
Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata, sai karfe
5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa.
A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta, ba kowa a d'akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had'a ta zauna tasha, jin cikinta ya d'auka yasa ta fito tai a
lwala tai sallar la'asar.
Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi 'yan d'akin sun dawo.
Nan suka mata wani kallo Ferry tace " ke kina nan wato mu muna can an samu wankin toilet ko? "
Nafi ta kalleta tace " wlh ba
m sani ba. "
Wacce ta dafata d'azu yanzun ma ita tace " haba Ferry taya za'ayi yarinya tazo yau d'in nan amma kice tai aiki? "
Ferryn ta kalleta cikin kuluwa tace " Ke Jibiya banasan salon iskanci, meye naki a ciki? Ko dake nake magana? "
Wa
cce aka kira da Jibiya itama cikin fad'a tace " badani kike ba amma hakki nane in fada miki gaskiya sannan ko yanzu kika kara abinda bai dace ba dole ne in fada miki gaskiya koda kuwa zakiji haushina."
Ta ja tsaki a karshen maganarta sannan tai waje a zu
ciye, Ferry ta bita da harara tace " Yarinyar nan ta gama rainani wlh. "
Itakam Nafi tana zaune duk jikinta yai sanyi,ba abinda ta tsana irin taga anyi fad'a a kanta.
Mik'ewa tai ta kalli Ferry tace " D'an Allah kiyi hakuri." sannan tai waje in
da taga waccan ta fita.
Ga mamakinta a zaune taganta cikin mutane suna ta hira da dariya.
Nafi ta karasa inda take tare da musu sallama, Jibiya ta d'ago ta kalleta sannan tace " new comer ya akai? "
Nafi ta d'an motsa baki alamar tana san
magana, ganin haka yasa ta mike taso kusa da ita, Nafi ta kalleta tace " Banji dadi ba daga zuwana kuna fada akaina, d'an Allah kiyi hakuri. "
Jibiya tasa dariya sannan ta kama hannun Nafi suka zauna tace " Karki damu da wannan, Ferry yayatace, u
banmu d'aya, indai fad'a ne irin wannan mun saba. "
Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " Ayya bansani ba. "
Hannu ta mika mata alamar suyi musabaha tare da cewa " Sunana Aisha Isma'il. "
Nafi tai murmushi sannan ta mika mata hannu itama tace
" Sunana Nafisa Abubakar. "
Murmushi sukama juna, Jibiya ta kalleta tace " a kano kike? "
Nafi ta d'aga kai alamar eh, fara'arta ce ta kara bayyana tace nima haka. "
Nafi tai murmushi, jibiya tace " Karki damu da Farida ko ince Ferry kamar
yanda ake cemata, a ido ne take haka amma a zuciyarta sam mace ce mai saukin kai. "
Nafi kam murmushi kawai tai, suna nan a zaune Jibiya na janta da hira sama sama har magrib tayi.
Nam suka mike sukai alwala suka nufi massallaci.
Washegar
i bayan sun shirya da safe suka fito aji dukansu 'yan d'akin, Nafi an shiga cikin Uniform ba laifi tayi kyau dagwas da ita.
Sunshiga aji malamin Math ne ya fara shigowa, itakam Nafi kawai iya kacinta kallon duk malamin daya shigo dan ko kad'an bata fa
himtar kalma d'aya da take fahimta ba.
Sai dai ta kalli Malami ta kuma kalli alo, haka malamai sukai ta fita wasu na shiga har aka tashi, itadai tasan kawai dumama benci kawai takeyi.
¤¤¤¤¤¤¤¤
Wani mugun kallo Ashraf ya ma wata kawar
Aneesa da sauri ta kalli Aneesa a tsorace, Aneesa ta kalleshi tace " Hubby me kake nufi? Events d'in ne bakaso kome?"
Ashraf ya kalleta yace " Anie kanki d'aya kuwa? Biki kwaya d'aya shine kike neman yin event kusan guda 10? Sannan kina san ni in h
allarci guda 8? Akan me? "
Aneesa ta kalleshi tace " bangane akan me ba?"
Ya dan rufe ido kad'an sannan yace " tambayar ki ai nake akan me zanje? "
Kawar Aneesa ta daure tace " Ashraf amma..... "kallan daya mata yasa tajs bakinta tai dif, Aneesa
ta mike rai b'ace tace " Yaya meyasa kake min haka?"
Murmushi ya sakar mata sannan yace " me kuma nai yanzun? "
Aneesa ta kafeshi da ido ranta duk ya gama b'aci ta daure tace " Ka tab'a ganin mijin daya ce ma matar da zai aura akan me zaije gun
bikinsu? "
Ashraf ya d'an daga kafad'a tare da d'aukan wayarsa ya fara dannawa sannan can yace " kowa da irin zuciyarsa, sannan dama namiji aka sani dayin kyale kyalen biki ko mace? "
Aneesa idanunta ns kansa ranta yakau kololuwa gun tashi, ta
bud'e baki zatai magana tags ya d'au waya ya kira wata number sanan taga yaa mike yai cikin d'aki.
Idanu ta bishi da shi sannan tai waje fuuu, kawarta ta mike ta biyo bayanta.
D'akin Umma ta shiga da gudu ba ko sallama, Umma na zaune tanacin a
binci, Aneesa ta fad'o kanta sannan ta saki kuka.
Nan Umma duk ta rud'e ta shiga tambayarta abinda ke faruwa, kawarta ce ta sanar ma Umma komai, ran Umma ya b'aci sosaii ta kalli Aneesa rai a b'ace tace " Akan haka ne kike kuka? Ai nasha fad'a mi
ki ki cire san Ashraf aranki kiso kud'insa kawai ba wai shi ba amma nsga alama sam kin kasa fahimtata. "
Aneesa cikin kuka tace " Umma ya zanyi? Nafa fad'ama friends d'ina zancen events d'innnan. "
Umma ya shafa kanta tare da kama hannunta sukai
d'aki.
A bakin gado suka zauna, Umma ta kalleta tace" ki rage events d'in daga goma zuwa bakwai, a wannan lokacin kibar Ashraf ya sami duk abinda yakeso, karki kuskura ki b'ata masa rai har zuwa lokacin da zai aureki ki amshi wasiyyar mahaifinsa.
"
Aneesa ta kalli Umma sai dai batace komai ba, Umma ta cigaba "a sanda kika samu kansa kikasan ya