Showing 114001 words to 117000 words out of 145961 words

Chapter 39 - ZUCIYA COMPLETE

ba."

Rigarsa ta rike, ya juyo ya kalleta tadan karkatar dakai cikin shagwaba tace " in nai kuka fa?"

Kallanta yai batare da ya bata

amsa ba, tace " Allah zanyi kuka, bakasan zafin da nakeji ba."

Murmushi ya karayi sannan ya d'agata, d'aki ya kaita ya ajiyeta a kan gado sannan ya zauna a gefenta yana kallan yanda take murmushi kasa kasa, ya kura mata ido yace " me kike saka wa?"

Mazewa tai ta kalleshi sannan cikin sanyin murya kalar tausayi tace " ruwa nakesan sha kuma bansan ya zan ba."

Kallanta yai yace " ruwa?"

Kai ta daga da sauri, ya mike yai waje, tabi bayansa da kallo, yana fita tadanyi dariya.

Bai dadeb

a sai gashi da ruwa ya bata ta amsa ta sha, yace " ni danazo dan karamin honeymoon kin maidani mai kula da mara lafiya."

Kasa tai dakai tace " ya hkuri yaya nima ba asan raina naji ciwon ba."

Ajiyar zuciya yai sannan ya matso kusa da ita, cinyart

a ta nunamai tace " kwanta anan."

Harararta yai yace " salan anjima kizo kice na sagar miki da kafa?"

Baki ta turo tace " tayaya zan fadi haka?"

Kwanciya yai akan cinyarta tasa hannu tana shafa kan sumarsa.

Idanunsa ya lumshe ba tare da

ya bud'e idanunsa ba yace " Mu gudu mubar garin nan gaba d'aya?"

Kallan mamaki tamai tace " Yaya."

Idanunsa a lumshe yai murmushi yace " mu bar komai a yanda yake in daukeki mu bar garin nan?"

Kanta ta sunkuyo ta daura fuskarta kan goshins

a tace " duk inda kake so muje in dai har da kaine bana shakka sai dai ka tabbatar zaka iya hakura da komai? Iyayenka? Kannenka? Company din da mahaifinka ya gina da guminsa?"

A hankali ya bud'e idansa ya kalleta yace " Nafisa i am really scared."

D'agowa tai cikin mamaki ta kalleshi tace " Yaya!" cikin raunanniyar murya.

Idanu ya dan runtse kadan yace " Ina tsoron abinda zan binciko, bansan wani abu mai rikitarwa zan kara cin karo dashi ba."

Hannunta tasa cikin tafin hannunsa idanunt

a suka ciciko tace " bayan kawu akwai wasu ne?"

Cikin mamaki ya kalleta yace " ya akai kikasan....."

Murmushi tai tace " yaya kenan, da alama da a birni na taso lawyer zan zama ko inzama Agent."

Yai murmushi tare da maida kansa saitin cikinta

yace " i am always impressed yanda kwakwalwarki ke saurin daukan abu."

Murmushi tai tace " naji ance Abba kasheshi akai, to abun ai ba mai wuya bane, waye yafi amfanuwa da mutuwarsa? Duk ta inda aka duba kawu ne, kaga kuwa wannan binciken mai sauki n

e na gaske."

Dagowa yai kadan ya kalleta yace " whoa! Lalai na yarda matar nan tawa tana ja."

Idanu ta rufe yai murmushi sannan ya maida kansa saitin cikin ta, yace " mai kike tunani gama da Mumy?"

Cikin mamaki ta kalleshi, tare da tsayawa d

aga shafamai kan da take, tace " yaya ni fa har yanzu......."

Kasa karasawa tai jin bakinsa akan cibiyarta, numfashinta ne taji ya dan dauke, a hankali ya shiga sarrafa ta cikin salon soyayya wanda itama ba'a barta a baya ba............

Ganin

yanda suka fita hayyacinsu yasa na jawo kofar ina dariya nace " ko ina ciwon

🤔

???"

************

Dakyar aka samu kan Datti sai dai tun da ya fara magana zancenshi daya " Mairo Allah ya isa."

Abinda yake ta fada kenan, ganin haka yasa yay

ansa ya taimakamai suka tafi rigarsu dashi.

Duk yan uwansa ba wanda ya tausayamai da jin abinda ya faru, kowa Allah ya kara yakeyi wasu kuwa suce dama ai ance in bakai sharar masallaci ba kayi ta kasuwa, bai har matarsa? Yarsa?iyayensa da yan uwansa s

unci arzikinsa ba ai gashinan wata katuwa can ta yasheshi."

Yayansa yaje kauyen su Mairo sai dai iyeyenta sun sanar dashi suma basu ganta ba yanzu haka 'yayanta ma ake nema.

Nam yayam ya gane dama can sun gama tsarawa.

Amma Datti yana me?

Ala fitar da dabbobi haka masu uban yawa???



*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡



*68*

Kwance yake akan gado ita ku

ma tana kan cikinsa ya kalli agoggon bangon d'akin azahar tayi yace " tashi muyi wanka muyi sallah."

D'agowa tai ta kalleshi tace " yaya sai dai ka kaini toilet kasan kafata ciwo take."

Baisan sanda dariya ta kamashi ba yace " au dama haryanzu ka

far tana ciwo? Sai naga d'azu kamar kin ma manta da ita."

Fuska ta had'e tace " bafa mantawa nai ba kawai daurewa nai."

Murgina wa yai daga inda yake ya koma gefen gado yace " hmm na fahimta yanzu."

Nan ya sauka tare da d'aura towel sannan

ya d'agata sukai toilet.

Sunyi wanka sukai sallah, yana zaune kan sallaya yaji wayarsa nata neman agaji.

Nan ya mike yai falo, ganin Dan litti ne yasa ya d'aga da sauri yace " mutumin ya an dubo?"

Dan litti yace " Yallabai munje makarantar d

a yake da ita ni da officer din sai dai a can mukaji makarantar shekararta 30 da ginawa."

Ashraf yace " 30?"

Dan litti yace eh, sannan karamin asibiti din dayake dashi shima haka.

Ashraf yace "gidajen hayansa fa?"

Dan litti yace " su din n

e bamu gama nemo su ba."

Ashraf yai shiru can yace " is ok ma hakan, nagode, sannan ina shagari quaters ka kawomin mota please, zan turoma address."

Yace " okay."

Yana kashe wayar ya zauna tare da kurama wani guri ido yana tunani, wato tun A

bba nada rai kenan makarantar take da asibitin.

Kan kujera ya kwantar da kansa ya d'aura hannunsa akan goshinsa tunani yakeyi sosai, so yake ya hada puzzle din da yake a rarrabe a kwakwalwarsa.

Nafi jin shiru bai dawo ba yasa ta mike tare da ding

isa kafa ta fito falo.

Ganin yanayin da yake ciki yasa tasan tunani yakeyi, a hankali ta taho kusa da shi ta zauna batace komai ba.

Ashraf kam can cikin kwakwalwarsa abu d'aya ke saka masa, wato dady sun hada baki da kawu sun salwantar da rayuwa

r Abbansa saboda dukiya kenan.

Shi kawu yana san dukiyarsa da kuma matarsa, shikuma Dady wato saboda kin taimaka masa da Abba yai da wuri shiyasa yake ganin shine sanadiyar talaucewarsu da kuma rasuwar iyayensa.

Wannan dalilin ne yasa suka salwant

ar da Abba shima dan ya samu nasa kason na dukiyar Abba? Ko kuwa kafin Abban ya rasu ya mallaki dukiyar?

Ajiyar zuciya yai tare da sauke hannunsa daga kan goshin sa, jin alamun mutum yasa ya juyar da kansa ba tare da ya d'ago ba.

Kallan Nafi yai

wacce itama kallansa take.

Idanu ya lumshe sannan ya bud'e su a hankali yace " Yaushe kikazo?"

Itama kanta ta kwantar a saman kujerar tana kallansa a hankali itana tace " tun dazu."

Ya dan murmusa kadan sannan yace " banji motsinki ba."



Tai murmushi tace " na kula kana bukatar kasancewa kai kadai ne, ni kuma banasan barinka shiyasa na zauna anan ba tare da saninka ba."

Murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan ta matso, a hankali ta matsa kusa dashi yasa hannu a kugunta

tare da kwantar da kanta akan kafadarsa yace " mu dawo nan da zama?"

Kai ta girgiza alamar a'a tace " yaya meyasa kaketa fadan magana irin haka."

Kansa ya dan kwantar akanta yace " yanzu dai kawai jinai inasan inganni daga ni sai ke a gidanmu mu

biyu."

Tace " mu biyu? Ko uku?"

Kallanta yai cikin mamaki zai ce mu uku kuma? Sai ya tuna da Anisa, hakan yasa yai shiru.

Kallanshi tai tace " ya kamata in daura mana abinci sai dai naga ba komai a gidan na girki."

Yace " hmm kaya

n abinci ba matsala bane sai dai da alama kin warke, kar anjima azo acemin baza'a iya abincin ba bayan an siyo, a nemi sani a kitchen."

Dariya tai sannan tace " ko na saka a kitchen din ai bana tunanin akwai abinda zaka iya dafawa."

Yace " akwai

abinda zan iya dafawa mana."

Cikin zumudi tace " haba? Mene? Fadamin dan Allah."

Dariya yai sannan yace " matso in rada miki."

Da sauri ta kai kunnenta saitin bakinsa, ya jawo kunnen da hannun harsai da tadanji zafi sannan yace " kinasan ji?

"

Kai ta daga alamar eh, yace " ruwan zafi."

Yana fada ya mike yana dariya.

Leb'enta ta ciza tace " YaYa."

Ta fada cikin fushi.

Dariya yasa mata tare da yimata gwalo.

Mikewa tai dasauri tana dingisawa ta bishi kafarta ya nuna

yana mata dariya.

Nan ta kara sauri dan kamoshi.

Dariya sosai yake mata ya shige d'aki, itama ta bishi nan suka fara zagaye gado yana tsokanarta wai Nafisa Cogal, ganin ba yanda zatai ta kamashi gashi ta gama kuluwa yasa tace " wayyo kafata."

Ta fada tare da durkusawa.

Da sauri ya matso yace " Nafisa menene?"

Cafkeshi tai tace " wacce Cogal din?"

Dariya yai ya jata suka fada kan gadon, dariya suke sosai dukansu kafin daga bisani su tsagaita.

Matsowa tai ta daura hannunta k

an kirjinsa tana kallansa tace " yaya inaji farin ciki zaimin yawa, ina tsoro kar ya yankemin lokaci guda."

Kallanta yai cikin kauna yace " Baby tun da nake, bandai san kafin Abba ya rasu ba sai dai a iya tarihin rayuwata yanzu ne nasan me ake nufi da

farinciki, me ake nufi da dariya, me ake nufi da tsokana, me kuma ake nufi da so, Nafisa ban taba tunanin zan yi experiencing wad'annan emotions din ba, sai dai yanzu jina nake kamar yaro dan sha takwas, akanki gani nake zan iya komai."

Idanunta ne

suka ciciko da kwalla, ya harareta yace " karki soma min kuka please dan banasan kuka ko kadan balle daga wacce nake tsananin kauna."

Batasan sanda hawaye ya zubo mata ba, ba shakka bata taba tunanin akwai ranar da zatazo wanda Ashraf zai sota haka

ba, kallanta yai tare da kankance ido yace "na dauka nace banasan kukan nan?"

Ta share hawayen da hannunta tace " yaya akwai hawayen da suke zubowa in har farinciki ya musu yawa, in har kaga nayi kuka to yanzu akan abu biyo ne, ko dai farin ciki yamin

yawa ko kuma kai nakema kukan da zuciyarka ta kasa."

Kallanta ya keyi cikin tsananin kauna, kanta ta kwantar akan kirjinsa tace " in har zuciyarka na maka radadi akan wasu al'amuran ni zan ma kukan da zai sanyayata, dan nasan kai bakasan kuka ko k

adan."

Idanu ya rufe batare da yace komai ba.

Tai murmushi itama.

Ya bud'e ido a hankali sakamakon wani idea data fado mai, kallanta yai yace " Nafisa duk abinda zan aikata a wadannan lokacin inaso ki kauda kanki, ki kuma yafemin a hankali

zan sanar dake dalilin da yasa nai komai, sai dai inaso ki sa a ranki ni Muhammad Ashraf mai san Nafisa ne."

D'agowa tai ta kalleshi ba tare da dogon nazarin kalamansa ba ta matso ta sumbaci goshinsa tace " nima inaso kasa a ranka ni Nafisa mai tsana

nin kaunar Ashraf ce a koda yaushe."

Rungumeta yai wani sanyi na ratsa zugakan mutane biyun, sai dai Ashraf yana saka plan dinsa da zai fara gudanar wa.

Nace hmmmmmm

************

A b'angaren Mumy kuwa tun bayan tafiyar Nafisa data sh

iga daki ta dade tana kuka kafin daga bisani ta kwanta.

Juyi kawai takeyi san tunani sun taru sun mata yawa akanta.

Tana nan a d'aki har yamma kawu ya shigo d'akin ganin bata falo.

Kusa da ita ya karaso yana tsaye yace " Hajiya me ya sameki?

Naga na dawo bakyanan sannan na shigo banga kin mun sannu da zuwa ba."

Ba tare da ta kalleshi ba tace " kaina ke min ciwo."

Cikin rud'ewa ya matso tare da cewa kinsha magani? Ko zamuje asibiti?"

Kallansa kawai takeyi ba tare da tace komai b

a, ya kalleta cikin mamaki yace " menene? Naga kin kuramin ido?"

Idanunta ta dauke daga kansa tare da girgiza kai tace "ba komai."

Ya karasa kan madubi ya d'auko magani sannan ya fita dan dauko ruwa.

Kalli ta bishi dashi wanda ni kaina ban f

ahimci kallan me take mai ba.

Bai dade ba sai gashi nan dauke da ruwa ya nemi d'agata nan tace zata iya tashi, ta mike ta amshi maganin tasha sannan ta kwanta.

Yace " bari in fita naga kamar kinasan hutu."

Kai ta daga kawai hakan yasa yai wa

je.

Yana fita ta share wasu kwalla da ni kaina ban fahimci kwallar ta menene ba.

***********

Datti kam sam ya kasa magana, banda Mairo Allah ya isa ba kalmar da take fitowa daga bakinsa, an kaishi gurin malamai harda yan duba sai dai h

aryanzu ba sa'a duk hayakin da akemai kuwa, abinci ma sam bayaci sai dai ai ta duramai kunu.

Yana zaune kamar gunki sai kalmar Mairo Allah ya isa kawai dayake fada.

'yan gidan ba wanda ya damu dashi banda yayansa guda d'aya.

Datti kam dun

iya ta juyamai baya..........

Mairo ko tana ina??? Abinda ya fado min kenan.*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

��



*Wannan shafin sadaukarwace ta musa

mman gareku 'yan Xahra Bukar Novel, nagode kwarai da gaske da kaunar da kukemin da littafaina.........ILYSM

��

*

*69*

Da yamma Dan litti ya kawo mai mota, bai bari ma sun gaisa ba makullin kawai yaba mai gadi ya juya yai gaba.

Suma waj

en karfe 6 suka fito daga gidan, hannunsu rike da juna, tana dan dingisa kafa kadan kadan.

Tuki yake zuciyarta nata sarka masa abubuwa kala kala, Nafi kam ganin haka yasa ta kwanta kawai batace komai ba.

Sunje shiga gida ya zaro Atm daga wallet d

insa ya mika mata.

Kallansa tai tace " Name nene?"

Yace " nasan akwai abinda kike bukata sai kuje ke da Little, sannan ki barshi a gunki incase in akwai abinda zaki bukata nan gaba."

Kallan mamaki tamai tace " nan gaba in zan nema ba sai na

fadama ba?"

Kansa yad'auke baice komai ba.

A karamar purse dinta ta saka suka shiga gida.

Sunje gun ajiye mota sukaga Anisa da su Umma a tsatsaye sai masifa akeyi, ga Asim nan ya rike kofar motar Anisa shima yana fada.

Tunda suka kula

da motar Ashraf sai duk suka zubama ma motar ido kowa fuskarnan a murtuke, Nafi kam yau ko a jikinta jitake yanzu bazata iya jurar wulakancin kowa ba.

Ashraf na tsayar da motae ya bud'e da sauri tare da kallansu, kafin yai magana Anisa ta matso a har

zuke ta cakumi wuyan rigar Ashraf kamar zata fashe saboda tsabar masifa tace " Wlh Yaya yau sai ka zaba ko ni ko wannan yar iskar, har ni zatacima mutunci d'azu? Sannan yanzu ka dauketa kun tafi yawan iskanci, wlh da so nai in ja mota duk inda kuke in neme

ku, nagaji da wannan dadirancin da kukeyi."

Umma ta matso itama tace " Kai Ashraf a wani matsayi Anisa take a gurinka? Ka maidata kamar ba matarka ba sam ka daina ko shiga harkarta, kana tunanin mu iyayenta zamu barka ne?"

Asim kam kallan Ashraf

kawai yake yana hucci.

Nafi ta bud'e motar ta fito tana kallan ikon Allah, Ashraf ya zare hannun Anisa daga jikinsa a hankali yace " Nisa calm down wannan fadan fa?"

Kallansa tai idanunta ya ciciko tace " yaya bazan iya ba, na san ba sona kake ba

, ni kuma wlh bazan iya zama da waccen tsinaniyar ba."

Ta fada tana nuna Nafi.

Ashraf ya dan kalli Nafi kadan sannan ya maida idansa kan Anisa mayafinta da ya fadi kasa saboda masifa ya tsugunna ya d'auko mata, ba wanda ya zata sai gani sukai ya

yafa mata mayafin ya kalleta cikin kulawa yace " Nisa kalleni nan."

Jikin kowa ne yai sanyi, Umma a ranta tace " dama ta ina za'ace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login