Showing 24001 words to 27000 words out of 145961 words
sannan suka bada kayan akai sai nan da sati d'aya za'a amshi wasu
daga baya sai a zo a amshi sauran.
_A gida_
Ashraf ya dad'e yana bacci kafin ya tashi, wanka yai sannan ya ci abinci, ya gama kenan Amra ta shigo tace Mumy na nemansa hakan yasa ya mike yai waje.
Yana ganinsu Asim da kannensa
a zaune d'auke kai yai kamar bai gansu ba yai gaba, yana wucewa kuwa sukaja tsakin takaici.
Sun gaisa da Mumy sannan ya gaida Kawu, shiru ne ya biyo baya kafin kawu yace " Ashraf dama maganar auranka ne da Aneesa. "
Kallan Kawu yai sai dai ba
ice komai ba, Kawu ya cigaba "saura wata biyu a d'aura auren shine nakesan jin ra'ayinka akan abubuwa guda biyu."
Ganin Ashraf bai da niyyar magana yasa yace " Da farko inda zaku zauna, anan kake so ko kuwa a d'aya daga cikin gidajen mahaifinka zaka
duba d'aya? "
Ashraf kam tambayar ta d'an b'atamai rai sai dai bai nuna ba kawai cewa yai "A tsarin mahaifina yafisan inzauna anan cikin 'yan uwana. "
kawu yai murmushi yace " yauwa haka ake so dams banasan tauyema hakki ne, tambaya ta biyu mag
anar aiki fa? "
Ashraf ya kalli Kawu ga mamakinsu murmushi sukaga ya saki, Mumy ta daure tace "Ashraf me kenan? "
Kallan Kawu yai yace "Kawu so kake in fara aiki? "
Gabab Kawu yad'an fad'i badai yaron nan yasan basaso ya fara aiki ba?
Mum
y ce tace "wani irin zance kakeyi haka? "
Bai amsa mata ba sai maganar sa ta d'azu daya maimai ta "Kawu so kake na fara aiki? "
kawu ya saki murmushi yace "in banda abinka Ashraf tun yaushe nake cema ka fara aiki? Ga mahaifiyar ka nan duk ta dam
u akan rashin aikin ka."
Bai kara magana ba kawai kansa ya maida gefe, Mumy kam abin nan na damunta ganin zata sake magana yasa Ashraf yai saurin cewa "Kawu zan shiga ciki akwai abinda zanyi. "
Kawu ya kalleshi sannan ya kalli Mumy wanda jikinta ya
i sanyi, bai jira amsarsu ba yai waje, Umma dake tsaye a kofa tanajin me ake cewa sam batasan Ashraf zai fito ba tana ganinshi ta shiga borin kunya, ko kallan ta baiyi ba yai gaba, duk ransa na dadi.
D'akinsa ya wuce ya d'au waya ya kira Little
, nan ta sanar dashi sun dawo gasunan shigowa, yace "kuzo keda Nafeesa. "abinda ya fada kenan ya kashe wayar.
Little ta girgiza kai tare da kwaikwayan abinda yace, Nafi tace "to me kikeso yace? "
Little tace "Inkun iso to kuzo ke da Nafisa in
a nemanku. "
Nafi ta juya kai tace "meye marabar hakan da yanda ya fada? "
Little ta harareta tace "Lalai nafi na kula bakyasan indinga kushe yayan nan nawa."
Nafi ta kalleta kawai batace komai ba, Little tai murmushi tace "ko da yake dole
ne ganin yanda ya taimakeki. "
Sun isa ko bangarensu basuje ba suka wuce bangaren Yaya, a zaune sukaga su Ya Asim hakan yasa suka rusuna suka gaidasu, harsun yi gaba Asim yace "Ke yar kauye? "
Nafi ta juyo cikin tsoro alama ya mata da hannu ka
n ta matso, a tsorace ta matsa inda suke.
Asim cikin izgilanci yace "Nemanki yake ne? "
A tsorace tace wa?
Dariya yasa irinta rashin mutuncin nan ya kalli kannensa yace "kun yadda Ashraf haka kawai ya kawo ta nan ba da dalili ba? "
Nafi
cikin mamaki ta kalleshi dan bata fahimci inda ya nufa ba.
Dariya suka kara mata d'aya daga cikin su yace "amma wannan kwailar? Kalli fa kirjin? "
Dariya suka kara sawq hrda tafawa, Nafi kam yanzu tafara ganewa, kasa tai da kanta a hankali haw
aye suka zubo mata.
Little ce ta matso wacce batasan me suke cewa ba sai dai ganin suna dariya ya nuna mata iskanci suke mata.
Tana karasowa tace "Ya Asim yanzu Ya Ashraf ya kira muje ko ince mai ka tsaida ita? "
Hararar Little din yai san
nan ya kalli Nafi yace dalla bani guri.
Nan Little ta kamata sukai gaba, tambayarta tai meya faru? Kai kawai Nafi ta girgiza alamar ba komai, haushi ya kama Little tace "to na fadama ya Ashraf inyaso sai ki fadamai. "
Da sauri Nafi ta rike ha
nnun Little tace "Maryam karki fad'amai dan Allah. "
Da mamaki Little ta kalleta, Nafi ta goge hawayenta tace "dan Allah mubar maganan nan in yaji ransa ne zai b'aci. "
Little tai shiru sai dai tana jinjina hakuri irin na Nafi.
Sun kwankwa
sa sai dai jin muryar mace sukai tace ku shigo, ba sai an fada ba sun san wacce.
Fuskar Nafi ce ta canza, a falo suka ganta ta baje a kasa tana cin abinci shi kuma yana gefenta amma a saman kujera yana kallo.
Jin sun shigo yasa ya kallesu itam
a kallansu take ganin Nafi yasa tace "me take anan?"
Ashraf yace "d'akinki ne? "
Cikin shagwab'a tace "Amma ai ya kusa zama nawa. "
Idanunsa akan Tv yace "sai kijira inya zama naki sai ki fad'i haka. "
Mamaki ne ya cika Nafi wai hak
a itakam saurayi yake ma budurwa magana? Jiya da suka dawo sai taga kamar bada wannan zafin yake mata magana ba to ko abin zuwa yake?
Ashraf ne ya katsesu da cewa "so kuke inta d'aga murya? "
Nafi kam bata fahimceshi ba, Little tace " mu shiga.
"
Sun karasa Little ta zauna kusa da Aneesa tace "Yaya Neesa nan kika gudu cin abincin? "
Ta kalli Ashraf tace "nafisan inci abinci a plate din dayaci tunda bayasan muci tare. "
Kasa Nafi tai da kanta da sauri, Ashraf ya kalli Aneesa sai d
ai bai ce komai ba.
Little ta kalleshi tace "Yaya munkai."
Gud kawai yace, Little ta kara cewa "Gamu to. "
Nafi ya kalla yace "Nafeesa so nake gobe ki gyaramin b'angare na. "
Murmushi tai sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Toh. "
Li
ttle tai kwafa aranta tace "kiyi murmushi da kyau. "
Aneesa ce ta harareta hakan yasa tai saurin maida kanta kasa, kanta ta maida kan Ashraf tace "Ya Ashraf yanzu me wannan zata maka? "
Cikin rashin damuwa yace "to ko zakiyi? "
Da sauri tai
shiru dan ba abinda ta tsana irin aiki, Ashraf ya kallesu yace "Little kuje."
Little wacce dariya ta kusa kamata da yaba Aneesa amsa ta mike itama Nafi ta mike, har sun fara tafiya Nafi ta juyo tanasan tambayarsa.
Kallanta yai yace "d'azu yaus
he kika tafi? "
Aneesa ta kalla cikin tsoro tace " ban dade ba ai. "
Kai ya d'aga kawai, ta daure tace "Goben karfe nawa zanzo? "
"Sanda kika gama abinda kike.
"
Juyawa tai bayan ta amsa da to.
Aneesa ta rakata da hararar tsana...
.
Suna fita ta shagwab'e ma Ashraf wai ya dizgata a gaban nafi.
Murmushi yai yace "kinsan banasan irin tambayoyin nan ai amma naga in bakimin ba bakyajin dad'i.
*THE INNOCENT TEAM*[5/5, 1:06 AM]
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Sry jiya nayi mistake zansa 16 nakara sa 15.*
*Nagode kwarai da tunatar dani.... LYSM*
1
⃣
7
⃣
Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayaw
a sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga
Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin.
Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta
gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya f
ita, me zata gani?
Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa, hucin da yake fitowa daga bak
insa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba, a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani, itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun, ya
kara daurewa ya bud'e ido, yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon."
Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube, hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake, da sauri ta d'auko ta mikamai, nun
a mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. "
Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara, ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'a
ngaren sa na haggu.
Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun, mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura, da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i, kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji
ba, yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta, a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa, sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke, tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai.
Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? "
A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. "
Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai, sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba, Ashraf k
am ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi, meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi.
Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta ta
na mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. "
Kai ya girgiza mata alamar a'a, idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah, in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. "
Idanu ya bud'e
a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?"
Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. "
Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki, xaka iya ci? "
Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh"
D
a sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate, tazo kusa dashi, kallanta yai baice komai ba.
Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba.
Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi, kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biy
u kenan Ina tsaye. "
Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. "
Falo ta fito ta maida abincin sannan ta shiga gyara, har ta gama bai farka ba, itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sa
i dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa, ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba.
Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta fita tabarshi shi kad'ai, kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso.
Haka t
anaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin.
_Kauye_
Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba.
Sun fito suka tarar da D'
an Litti a inda sukai zai jirasu, Kowa ya kalli D'an litti sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha, riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa, ya kawo hula irin tamu ta
hausa ya saka, sannan ya kwama glass dinsa, gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka.
Tsayawa yai ya wani karkace, su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi, wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su
fura ne, kayan mata ne, gayayyaki na magani, su daddawa ne, kub'ewa busassa da sauransu.
Datti ya kalli D'an litti yace " kai amma wannan yaron kana burgeni, ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. "
Dan Litti ya juyo cikin gayu
nsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. "
Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. "
Sun isa Gwaram suka s
amu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige, Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya."
Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. "
Ta kalleshi tace " Dan boko b
anajin turanci. "
Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba "
Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. "
Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba ta
re da ka sanmana ba? "
Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima."
Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya hakura.
Nan mota ta tashi suka fara tafiya..........
_Gida_
Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa, yace "Hajiya lafiya kuwa? "
Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? "
Kawu ya mike zaune
tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan, ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura, sai mu bari sai anyi auren kenan ko? "
Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai s
hi daya tafi. "
Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. "
Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menen
e wannan abun......
To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina, Wacece matar Ashraf ta farko??????
*
🗣🗣🗣🗣🗣🗣
My Beely Badaru, duk Amarcin ne
🙈
?*
*THE INNOCENT TEAM*
[5/5, 1:06 AM]
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Where are u my Cwt Nafeesa? Ur page is here!!! Hope banyi late ba? Happie Birthday dear wish u long life and prosperity.....*
1
⃣
8
⃣
Duk
yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan