Showing 15001 words to 18000 words out of 145961 words

Chapter 6 - ZUCIYA COMPLETE

ganin bataci abinci baiyi mamaki ba, ta ina zata iya cin abinci a cikin mutane?

Bayan kowa ya gama ne Kawu yai Ham

dalla sannan ya fara magana "Alhamdulila Allah ya taimakemu d'an mu ya dawo da ransa da kuma

lafiyarsa wannan ba karamin abin farinciki da alfahari bane, lalai Muna godiya ga Allah wanda yasa muke zaune yau da Ashraf kamar yanda muka saba. "

Kowa ya

jinjina kai alamar jin dad'i, akace Ashraf yai magana.

Shiru yadanyi nawasu dakika kafin yace " Nagode da kulawarku, Sai dai inaso in nuna muku Nafeesa wacce itace sanadiyar zamana anan gurin haka, Itace wacce ta taimakeni a lokacin da nake tuna

nin yanke alaka da duniya, Allah ya kawomin ita ta taimakeni ta ceci rayuwata. "

Jin haka yasa kowa ya kara kallan Nafi wacce kanta ke kasa, sai gabanta daya tsananta fad'uwa.

Wani daga cikin mazan gun yace "Lalai Ashraf to dan ta taimakeka

shine ka taho da ita nan ko me? Iyayene batadaso ko me? "

Ashraf ya bugamai wani kallo baice komai ba, Umma mahaifiyar Aneesa tace "Ashraf ina ganin gaskiya Nuhu ya fada in ta taimakeka sai a bata kud'i ban gane dalilin tahowarka da ita ba. "



Ashraf ya dan kalleta kadan nan ma bai tanka ba, Mumy tai murmushi tace " tunda ya taho da ita akwai dalilinsa nayin hakan nasan halin Ashraf sarai. "

Kansa ya juya sai dai fuskarnan a had'e take tamau, nan aka dan fara musu wasu suce ya kamata was

u suce bai dace ba, Anisa kam kallan kyana kawai takema Nafi.

Cikin wata kakkausar murya mai zafi Ashraf ya mike yace " Me? Dan na taho da yarinya shine ake cece kuce? A kan wani na ajiye ta ko me? Ko kuwa anaso ace ni Ashraf ban isa in kawo w

anda na ga dama cikin gidan nan bane? "

Wannan kalamai dayai ya gigita kowa itakam Nafi idanunta ne suka ciciko tsoro ya kara kamata, Kawu ya kalli Ashraf yace " Kada ka manta Ashrac akwai iyayenka anan, taya dan ranka ya baci zaka hada da kowa ka

fara fad'a? "

Ashraf ya kalli Asim sannan ya kalli inda Nafi take yace "Duk wanda yake ganin hukunci na bai mai ba sai ya tareni muyi magana. "

Yana kai nan yai waje, Umma tabishi da kallo, Mumy kam da sauri ta mike ta bishi.

Nan aka ci

gaba da 'yan maganganu, little ta kama hannun Nafi tace "Nafi mu bar nan ko? "

Suna kokarin mikewa sai ga Ashraf ya dawo daga bakin kofa kawai ya kalli Nafi sannan ya kalli Aneesa yace " Neesah inasan ganinki. "

To fa gani nai Nafi ta mike itam

a Aneesa ta mike, Umna ta kalli Nafi tace " ke yake kira? "

Nafi wanda itakam jitai kamar yace "Nafeesa"tai tsuru tana kallan Umma.

Aneesa wani haushi ya kamata, a zuciye ta bangaje Nafi tai gaba.

Nafi ta tsaya cak kamar gunki sai hawaye,

Kawu ya mike shima da zuwanta bai wani burgeshi ba yai waje.

Little ta taso ta kama hannunta Asim yasa dariya yace "ko dai akwai wata manufa ne a tahowa da wannan kwailar? "

Yai maganar yana kallan Nafi aka kwashe da dariya, sudai sukai wa

je.

Suna fita Nafi tasa kuka.

Aneesa kam a gefe taga Ashraf ta karasa inda yake fuska a had'e tace " menene? "

Shima fuskarnan a had'e yace " ki fadama ummanki tadaina min abinda takemin menene nata dan na taho da Nafisa? Akan wani zata za

una? Ko kuwa yarinya ce ita daza'ace wanka ma yi mata za'ai? "

Aneesa ta kalleshi cikin bacin rai tace " Yaya dama saboda kamin fada ka kirani? Sannan yanzu kace Neesah amma dayake yarinyarcan yar rainin hankali ce ta d'auka wai ita kake kira. "

Ashraf ya kalli su Nafi dake tahowa ganin tana kuka ya kalli Aneesa yace " ki fadama Umma tadaina min haka sannan kema na dauka ko me na kawo gidan nan zakibi bayana in har kina sona, na gode da nunamin din dakikai abinda nake tunani ba haka bane. "yan

a kainan yai gaba.

Nafi tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Aneesa ta maida kanta kasa.

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*Kuyi hakuri jina shiru da kukai

jiya, na shiga tarone wlh kuma dana dawo na gaji.....na gode kwarai da kulawarku da kuma san da kukema littafin nan*

😍😍

1



0





Little ce rike da hannunta kawai tana tafiya amma idanunta nakan Ashraf dake tafiya, Aneesa kam har wuya

tazo ganin yanda Ashraf ya hauta

da fada akan wata banza kucaka, da saninta ta taho ta mangaje Nafi wanda har sai da ta kusa kai kasa, Little ta kalleta tace "Haba Yaya Neesa? "

Aneesa ta kalli Nafi tace "Sorry ban kula ba."tai gaba.

Little

ta kalli Nafi wanda ta kakaro murmushi tace "Maryam karki damu ai bata kula bane, kuma taban hakuri. "

Little tai karamin hucci tace" Nafi kiyi hakuri. "

D'aki suka shiga, Nafi ta zauna a kasa, little na shirin mata magana wayarta tai kara, d

a sauri ta d'aga tace "Naam Yaya. "

Daga can bangaren Ashraf yace " Little ki samarmata abinci dan banaji taci wani abinci. "

To, little ta fad'a tana kallan Nafi wacce itama hankalin ta ke kan Little tunda taji ance Yaya.

Little ta ka

she wayar sannan ta kalli Nafi tace "kinga Yaya ma ya kula bakici abinci ba."

Nafi tad'anyi murmushi, hakab yasa Little tai waje.

Ashraf kam yana shiga bangarensa ya kwanta a kan kujera doguwa dake falo, hannu yasa akan goshinsa, meyasa d

uk sanda akace za'ai meeting indai har saboda shine sai an b'ata masa rai? Yai dan karamin tsaki zai juya yaji sallama, muryar Mumy ce hakan yasa ya amsa sama sama.

Mumy ta shigo ciki, shi kuma ya mike daga kwanciyar da yai ya sauka kasa, mumy ta

karaso ta zauna akan kujera, kansa na kasa bai ce komai ba.



Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace "Ashraf kayi hakuri. "

Batare da ya d'ago ba yace " Ya wuce ai tunda dai ba wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan. "

Mumy ta jinjina kai s

annan tace" Ashraf a gaskiya nima hukuncinka bai min ba, bana ganin dan ta taimakeka ya kamata ka taho da ita, sai dai in akwai wani dalili bayan wannan. "

Bai kalleta ba haka kuma baice komai ba, Mumy ta cigaba " ba komai nasan tausayinta ne yasa

ka taho da ita insha Allah nikuma zan kula da ita. "

Yanzu kam ya d'ago ya kalli Mumyn sai dai baice komai ba, tai murmushi dan ta gane yaji dadin maganar ne tace "Ashraf zuwa nai muyi wata magana. "

Inaji kawai yace.

Tace " Baka ganin l

okaci yayi da zaka fara aiki a company d'in mahaifinka?? "

Kallanta yai cikin mamaki yace " Ba Kawu da Asim suna kula da company d'in ba? Meye kuma nawa na fara aiki acan?? "

Mumy cikin damuwa tace " Ash raf mai yasa kake abu kamar bakasan koma

i ba? Companin nan na mahaifinka ne fa? Kai kad'ai ne d'ansa sannan ya bar maka share d'in sa gaba d'aya kanada 50% na share d'in company d'in kafi kowa, akan me zakayi ta zama a gida bayan ka gama karatu? "

Ashraf ya mike tsaye yace " Mumy bana

san wannan maganar dan Allah. "

Jikinta a sanyaye tace " Ashraf? "

Ya d'an kalleta sai dai bai ce komai ba, mikewa tai a hankali tai waje, yabi bayanta da kallo tare da dafa kansa, meyasa kowa ba ya hango abinda shi yake hangowa?

Idan

u ya runtse yana tuno sanda akace fatiha an d'aura auren Nafi da Ashraf, yai wani hucci sannan ya mike kawai ya zari makulli yai waje.

************

Sosai Nafi ta ci abinci, ji take wani dad'i na ziyartarta, tanaji tunda

take bata tab'acin abinci mai dadi irin wannan ba, tas ta cinye wanda little ta zubo mata, ta kwankwad'i lemon kankana mai sanyi da ke cikin jug, wata gyatsa tai sannan tasa dariya ita ka dai.

Ita kad'aice a d'akin dan little ta fita, tace " oh y

au banyi gyatsar nono ko madara ba."

Ta sake yin dariya tace " Kai abincin nan yayi dad'i, wannan kuma ko menene?" ta fada tana d'aga ragowar juice d'in kankanar data sha, tace " Tabdi lalai akwai abin dad'i a birni."

Sai dataji abincin ya tsir

ga mata saboda cin datai dayawa, tad'au tiren kamar yanda Little tace mata ta maida kitchen.

Ta fito ta kalli gabas inda little ta mata kwatance, ta fara tafiya, tafiya kawai take, gani tai ta b'ata nan ta shiga waige waige, jitai ance " Ke."



Juyowa tai cikin mamaki, Ganin umma uwar Aneesa yasa tai saurin yin kasa dakanta, Umma tace " Dan gidan ku uban me kike anan? "

Nafi cikin tsoro ta fara magana cikin in in na tace " Um kitchen nake nema. "

Umma ta kalli kwanon sannan tad'an

tabe baki tace " Kwarai dole ai, a can kauye ba'a sami damar zakewa aci abinci ba shiyasa ake neman bud'e mana ciki? "

Nafi wanda jikinta duk ya gama mutuwa ta kasa magana sai motsa baki kawai take.

Umma ta kalleta kallan banza tace " wuce mu

je kitchen d'in. "

Nafi ta kalleta da mamaki, Umma tace " To munafuka bakijini bane kike kif kif da ido? "

Nafi tai saurin yin kasa dakai, nan tai gaba Nafi ta bita.

Sun isa katon kitchen d'in inda masu aiki keta hidima Umma ta tafa han

nun ta hakan yasa duk suka taho, Umma ta kallesu tace " Yauwa dama so nake in sanar daku kun samu kari. "

Kallan juna sukai na mamaki, tasa hannu ta finciko Nafi tace " gatannan da safe zatazo ta tayaku aiki sannan da rana ma haka."

Nafi ta kar

a kasa da kanta, Umma tace "na umarceku ku sata aiki sosai, saboda ita ta fiku cin riba dan inda zata kwanta yafi naku haka abincinta da suturarta tafi taku. "

Suka amsa da to, ta kalli Nafi tace." Ke kuma dan gidanku kullum da sasaafe in ganki ana

n hakama da rana, bazaki dinga cin abinci a banza ba. "

Nafi ta d'aga kai, Umma taja kunenta tace " kuma wlh inji maganarnan abakin wani ko da Little ce bare Ashraf Allah sai kin gane kuranki. "

Tana kai nan tai gaba.

Nafi tai shiru, jit

ai ance ajiye kwanukan ki tafi gobe kya fara zuwa, Nafi ta kalli mai maganar wata babba ce a kalla zatai sa'ar Innarta, ta ajiye tiren sannan ta gaidasu tare da musu sallama.

**********

D'aki ta koma ta zauna a kasa tai shir

u, bacci ne yai gaba da ita.



Ashraf kam bayan ya fito daga d'aki Aneesa yama waya yace ta fito ta rakashi an guwa.

Jifatu ya wuce da ita, tanata murna ganin yau gata ga masoyinta, suna tafiya ne ta kalleshi tace " Yaya ya magana

r sa ranar da akai ai tana nan ko? "

Ya kalleta tare da murmushi yace " eh mana ko musa a kara matsowa da shi? "

Idanu ta rufe tace " Kai yaya wata biyu ai kamar yau ne. "

Aneesa ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace " Yaya wlh ni kad'ai

nasan missing dinka danai jiya. "



Titi kawai ya kalla baice komai ba sai murmushi da yai.

A bakin jifatu yai parking, nan ta fito shims ya fito suka shiga ciki, bangaren kaya na atamfofi lace da mayafai sukai, ce mata yai kawai ta zab'a, hak

an yasa tai tunanin nata ne, sosai ta jidi kaya shima yana tayata, suks wuce gun takalmi, nan ne dai yace banda takalmi sai dai jaka, saboda shikam yasan baisan size dinta ba.

Itakam Aneesa sai farin ciki take har suka gama zaben suka fito, sun s

higa mota ta kalleshi cikin kauna tace " Yaya na gode sosai. "

Ya kalleta cikin mamaki yace " name fa? "

Tace "na kaya mana. "

Murmushi yai yace "Aneesa ke kuma mai zakiyi da kaya? Duk yawan kayanki? "

Fuska ta had'e tace " na waye t

o? "



Ya kalli titi yace " Nafeesa. "

Gabanta ne ya fad'i cikin tsoro ta kalleshi sai dai gani tai shi ko a jikin sa, ranta yai mugun b'aci........

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυн

d*

ayushermohd.blogspot.com

1



1



Ashraf ne ya kalleta kadan yace "Aneesah tailorn ki kuwa yana nan? "

Fuska ta kara daurewa tamau tace " menene? "

"kayan Nafisa nake tunanin muje akai mai can naga ba laifi ya iya d'inki sosai.

"

Jitai zuciyarta na neman tsagewa saboda takaici, rasa ma mai zata cemai tai, kawai sai ido ta bishi dashi, ganin kamar bai ma fahimci ranta a b'ace yake ba yasa tace " Yaya d'anyi parking."

Cikin mamaki ya kalleta yace " parking kuma? "

Kai ta d'aga hakan yasa ya gangara gefen titi, ta bud'e kofar ta sannan ta kalleshi tace " randa zaka fita domin ni ka d'aukoni amma bazan zauna kusa da kai domin wata ba. " tana kai nan tai waje, ya bita da kallo cikin mamaki, me take nufi domin wata?



Yana kallanta ta tari adaidaita, ga magrib ta kawo kai,shima ya ja mota yai gaba.

Aneesa na shiga mota ta fara matsar kwalla dan tsabar takaici ita zai d'auka su zaboma wannan kucakar kaya?

Tana isa gida ta wuce gun ummanta da gudu na

n ta sanar da Ummanta duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa " Umma kinga lesukan dana zab'a kuwa? Na d'auka nawa ne? Ina wannan kucakar ina sa kayan dubu talatin? "

Umma ma da ranta yakai kololuwar tashi tace " kwantar da hankalinki ita d'in b

anza? Har ta isa tasaki kuka? Bare har ta had'aku fad'a da Ashraf?"

Aneesa ta goge kwallarta tace " Umma me Ashraf yake cemin? "

"Neesah mana, tun kina karama yake fad'a miki haka shi yasa wasu ma haka suke ce miki."

Aneesa tai kwafa t

ace " to Umma tunda na cemai wannan yarinyar ta d'auka ita ya kira d'azu bai sake cemin Neesah ba har yanzu. "

Umma ta kanne ido cikin b'acin rai tace " Aneesa kada ki kuskura ki kara yadda Ashraf yasan bakyasan yarinyar nan, sannan karki kara yim

ai musu akanta."

Aneesa ta mata kallan mamaki, Umma tace " tabayan gida zamu b'ulo mata, ni na fad'a miki bazata cika sati a gidan nan ba zata d'auki tsuman kafafuwanta tayi gaba. "

Aneesa ta jinjina kai alamar gasuwa tace " Umma ni ko gani

nta ma bana sanyi wlh. "

Umma tai murmushi tace " d'aure kinji 'yata, sati d'aya yayi yawa. "

Nan sukai murmushin mugunta su dukansu.



Nafi kam tana zaune a d'aki ita kad'ai mahaifinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login