Showing 117001 words to 120000 words out of 145961 words
yaron da suka taso tun suna kanana har yafi san wata wacce basu dade da haduwa ba."
Nafi kam jitai wani abu ya tok
are mata makoshi, kallansu kawai take tama kasa ko motsi.
Asim ma mamakin Ashraf ne ya kamashi.
Gogar kuwa duk jikinta ya gama sanyi kallan Ashraf kawai take kamar yanda ya umarceta, Ashraf yace " Nisa!"
A hankali tace " Naam."
Yai murm
ushi yace " Yauwa ko kefa."
Kallansa ta tsaya tanayi, ya saketa tare da juyawa ba tare da ya kalli Nafi ba zai wuce.
Da sauri Anisa ta riko hannunsa tace " yaya nidai wlh ka zaba ko ni ko waccen, banaji zan iya ganin tana zama kusa dakai zuciyata
bata fashe ba."
Ba tare da ya juyo ba ya had'iyi wani abu sannan yace " Karkisata a ranki u r so dear to me."
Yana kaiwa nan ya ja hannunsa yai gaba.
Nafi kam bata san sanda taji hawaye ya zubo mata ba tana kokarin mai magana taga ko kallan
ta baiyi ba yai gaba.
Yana tafiya Umma ta matso gunta tana dariya tace " ah ah su Amarsu yanzu kin tabbatar da matsayinki?"
Kallansu tai ba tare da ta tanka ba, mamaki take mai ya samu Yaya daga shigowa?
Umma tai dariyar mugunta tace " ah to
da an fada miki barno gabas take? Shi dama namiji kan ya samu abinda yake so ne zai ta lallabaki amma da ya samu shikenan kin zama kashi."
Wani irin kallo Nafi ta kafe Umma dashi, Umma ta wanka mata mari tace " A da in mun barki kinyi iskanci saboda
mijinki ya baki matsayine bawai yanzu da kike kamar bola ba."
Anisa ta matso tace " ke harkin isa dama kice zaki kwace min miji? Yar kauye dake? Mutumin da na taso dashi tun muna yara ke kuwa yar karo?"
Nafi wacce ke rike da kuncinta ta daure tac
e " wannan kuma tunaninku ne ba na yaya ba."
Tana kaiwa nan ta fara dingisa kafa tana gaba.
Anisa ta matsa ta fizgota da karfi tace " ni kika fadama magana d'azu ko?"
Nafi ta kalleta tare da fincike jikinta ta cigaba da tafiya, Anisa tasa da
riya tace " yi maza ki je ki shiya yan kayan da kika samu anan kafin insa a baki takardarki."
Nafi bata juyo ba tai bangarensu.
Tana shiga ta zauna akan kujera a falo, meke faruwa? Tayaya ya Ashraf zai canza mata lokaci d'aya? Da sauri ta girgiza
kai alamar a'a tace " Yanada reason dinsa ni na sani, zanje anjima in ma laifi na masa in bashi hakuri."
Da wannan shawara taji hankalinta ya kwanta.
Anisa kam tana ganin tafiyar Nafi suka kwashe da dariya, Asim ya matso yace " Anisa ina mamaki
fa ya akai hakan?"
Anisa ta dan yi fari da ido tace " yaya na sona ni nasani kawai abinda ya faru ne yasa ya shareni."
Asim yace " to yanzu kije ki lallabashi ki samu kisan yawan dukiyayonsa da kuma inda takardun suke, karki bari ya gane komai."
Kai Anisa ta jinjina alamar gamsuwa tace " karka damu yaya ni nasan ya Ashraf a tafin hannuna yake."
Dariya sukai dukansu, Anisa ta wuce bangaren Umma da sauri tai wanka ganin magrib tayi tai sallah sannan ta saka wasu riga da siket 'yan kanti sun
bi jikinta sosai.
Mayafi ta yafa sannan ta fito tace "Umma ya kika ganni?"
Umma ta shiga tafa mata tace " yauwa 'yata sai da safe."
Nan Anisa ta fito cikin tsantar farin ciki.
Bangarensu ta nufa tare da bud'e kofa.
Ashraf na zaune
ya baza wasu takardu yana dubawa, jin motsi yasa ya d'ago.
Ganin Anisa yasa ya sakar mata sansanyan murmushi.
Cikin rangwada ta karaso gunsa tace " yaya shine bakazo biko ba ko?"
Kallanta yai bayan ta zauna daf dashi yace " sry Nisa kunya c
e ta hanani zuwa."
Kankameshi tai tace " yaya nagode da ka nunamin kana sona."
Zareta yai daga jikinsa yace " Amma kin dawo kenan ko?"
Cikin shagwaba tace " anya kuwa?" tafada tana karema takardun kallo, tace " wad'an nan fa?"
Tataresu
ya farayi yace " ba komai." ya fada tare da mikewa da sauri Ya nufi d'akinsa."
Kallan bayansa tai tace "da alama takardune masu amfani ganin yanda ya kwashesu da sauri, sannan da tana dubawa taga kamar takardun fili."
Mikewa tai da sauri tabi bay
ansa, kofar dama bai rufe taba.
Yana kokarin sawa a drawer ta jikin madubi sai ga Anisa.
Da sauri ya tura yasa key, ta matso gunsa tare da rungumeshi ta baya tace " ka gama?"
Makullin ya bari a jiki ya juyo ya kalleta yace " eh muje falo."
Nan ta kara kallan gun sannan sukai falo.
zama sukai ta zauna akan cinyarsa tare da rungumeshi ta fara sambatarsa, sam hankalinta ya gama tashi saboda rashinsa datai kwana biyu bataji buga kofar da ake ba.
Ashraf ya d'an zareta kadan yana ko
karin sauketa Nafi ta turo kofa, tunaninta jin tanata bugawa ba'a bud'e ba mayb yana masallaci sai tai tunanin ajiye masa abinci tai gaba.
Cak ta tsaya daga jikin kofa tana kallansu.
Anisa kam ganin Nafi ce yasa tai wani dariyar mugunta sannan ta k
ara kai bakinta cikin na Ashraf tana mai wani saban salo.
Nafi kam jitai jikinta yana kakkarwa anan bakin kofar ta ajiye abincin tai waje da sauri.
Tafiya kawai take batasan inda take sa kafarta ba sam kuma bata kallan gabanta.
Saura kiris
ta buge da bango taji an jawota, kallan wanda ya jawota tai, jitai yace " Gimbiya me kike tunani haka?"
Kallansa take kamar bata cikin hayyacinta ta kwace hannunta tana kokarin ci gaba da tafiya.
Gabanta yasha yace "Gimbiya menene? Baki kula da
ni bane?"
Kallansa tai sannan ta kewayeshi tai gaba.
Bin bayanta ya farayi yana mata magana sai dai da alama batama san yanayi ba.
Sunje shiga bamgarensu, Little kuma na shirin fitowa.
Ganin Nafi yasa ta karaso da sari tace " Ni harzan gudu
gun Mumy muyi hira dan nasan ke kuma sai gobe ni da na ganki."
Nafi ta kalleta sai dai batace komai ba, muryar Habib taji yace " Princess kece?"
Da sauri ta matsa daga gun Nafi ta karasa gun Habib, itakam Nafi ciki ta shiga kawai ta zauna a baki
n gado.
Hoton yanayin datagansu sam ya ki barin kwayar idanunta, ta sani matarsa ce ba kuma ta da hakki akan hanashi yin abinda yaga dama da matarsa sai dai me yasa takeji kamar Ashraf yayi betraying dinta??????
Nikaina bansan me zance ba Feena
h
����
��
Yes mâ
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*70*
Little ta kalli Habin tace " Yaya sai yau fa naganka!" cikin shagwaba tai maganar, ya k
alli kofar da Nafi ta shiga yace " Princess nazo ai bamu hadu bane ba kawai."
Ta dan turo baki tace "na kiraka ma baka dauka ba."
Ya hada hannayensa biyu yace " sry mayb ban kula bane."
Ta kalleshi tace " naga sako na gode."
Kallan mama
ki ya mata yace " sako?"
Kai ta daga alamar eh tace " eh mana wanda kaba Feenah ta bani."
Shiru yai a ransa yace " au kayan dana bata ma Little taba?"
Bai dawo daga tunaninsa ba Little tace " yaya, bari inje inga Feenah da alama yaya ne ya b
'ata mata rai, nayi mamakin ganin ta haka."
Sannan ta karasa maganar a hankali " Naga they get along with eachother very well, da alama fadan masoya sukai."
Ya kalleta yace " Ai Asharaf sai a slow, amma...."
Little ta kalleshi jin yayi shi
ru, kallan mamaki ya mata yace " me kikace daga karshe?"
Cikin rashin damuwa ta maimaitamai tace " Allah naga tunda mukasan tsakaninsu kullum suke tare da juna."
Cikin tsananin mamaki yace " me kikace?"
Yanda yai maganar yasa jikinta yadan
yi sanyi tace " oh bakasan fa ashe matar yaya bace fa ko?"
Gani tai yadan yi baya tare da rike kansa, cikin wani irin yanayi yake kallan Little wanda yasa tasha jinin jikinta, yace " matar wa?"
Kasa maimaitawa tai sai kallansa kawai datakeyi, gan
in tayi shiru yasa ya juya jiki a sanyaye yai gaba batare da ya kara cewa komai ba.
Little tabi bayansa da kallo me kenan? Ko dai shock ne irin wanda sukaji da suma suka samu labarin?"
Ciki ta shiga ta samu Nafi ta sauko daga kan gado ta zauna a k
asa tare da d'aura kansa a kan jikin gadon.
Little ta matsa kusa da ita tace "matar yaya da alama fada kukai ko?"
Nafi ta kalli Little sai dai batace komai ba, Little tai dariya tace " karma ki fadamin nima ba san ji nake ba, na kuma san goben na
n zaku shirya."
Ta karasa maganar tare da mikewa.
Nafi da kyar ta tashi ta watsa ruwa kawai tai sallah ta kwanta, sam ta kasa bacci ita ba wai ganin yanayin da suke ciki da Anisa bane yafi daga mata hankali, kiss din da sukai a gabanta shine ya t
saya mata a kwakwalwarta, ai karama wani abun ce, ta tuna sanda yake ce mata su zauna a shagari su biyu.
Wani dogon tsaki taja tace " kamar irin da gaske ya manta da matarsa din nan."
Sam kasa barci tai sai juyi kawai take, da kyar baccin ya d'auk
eta.
A b'angaren Ashraf kuwa sun zuba love shida nisa sai dai sam yaki yadda ya kusanceta, ganin ta matso da hakan yasa ya d'an matsa kadan, haushi ya kamata tace " Hubby meye hakan?"
Kallanta yai tare da rike hannunta yace " sry Nisa."
Ta
fizge hannunta cikin fushi tace " me? Kana tunanin matarka Nafisa ne ko me?ko kuwa so kake kace baka sha'awar yi dani bayan kayi da yarinya?"
Jawota ta yai jikinsa ya rasa me zaice, baisan sanda yace mata" ba haka bane, banajin dadi ne wanda likita ya
hanani saduwa amma inani ina kin matata?"
Nisa ta kalleshi cikin zargi tace " me ya sameka? Sannan naji Umma tace ka kwana da Nafi fa!"
Kara jawota yai yace " zargin Umma ne kawai karki wani sashi a ranki."
Da wannan yasa ta saki ranta, shik
uma ya kwanta yai bacci.
Tana gani yayi bacci ta mike a hankali ta bud'e drawer din nan a hankali ta zaro takardun nan tai falo.
Karantasu tai taga tabbas kuwa takardun filayene da wani babban gona.
Tai dariya tace " da alama zan gano komai
wannan karan."
Nan ta dau hotunan a waya ta turama Asim, sadi ya kara kamashi tace " yaya in sato su?"
Yace " a'a ki maidasu sai mungama ganin ragowar tukunna karya gane."
Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta maidasu a hankali ta koma ta k
wanta.
Hankalin Ashraf a kwance ya tashi yai asuba, duk yanda yaso ta tashi tai sallah taki, dama inda sabo ta saba dan bata sallah sai rana ta fito.
Sai daya gama shirinsa na gun aiki sannan ta farka ta kalleshi yana fesa turare.
Mikewa tai
tazo ta bayansa ta rungume shi, yai murmushi yace " kun tashi My Neesa?"
Wani irin sanyi ne ya ratsata tace " eh hubby."
Ya juyo da ita gabansa yace " da fatan kinyi bacci mai dadi."
Kai ta daga tace " sosau ma, na dade rabon danai bacci ma
i dadin haka."
Yai murmushi yace " gud, ni zan fita."
Kiss ta mannamai a kuncinsa tace " sai kadawo."
Kai ya d'aga mata baice komai ba.
Yana fita waje yasa hannu ya goge inda tamai kiss din sannan yai waje.
A waje yaga Asim da kan
sa ya karasa ya mikamai hannu suka gaisa wanda hakan yai bala'in ba Asim mamaki, Ashraf yai murmushi yace " Asim dama inasan magana dakai."
Asim yace " inaji."
Ashraf yace " kamar ya kamata muwa Kawu magana ya karama matsayi inaganin kamar inda a
ka maidakai yanzu is too low for someone like u."
Cikin tsananin mamaki Asim ya kalli Ashraf yama kasa magana, Ashraf ya dan dafa kafadarsa da hannu daya yace " barshi in baka so."
Yana kai wa nan yai gaba, da sauri Asim yasha gabansa yace " da g
aske kake?"
Fuskar Ashraf a maze kamar yanda yake kullum yace " wasa nakeyi to da?"
Asim ya sa dariya yace " mamaki nake yi ai bantaba tunanin za ka taimaken bane ba ai naga tun muna yara bama wani shiri."
Ashraf yace " ko ba ma shiri ai kai
dan uwanane."
Yai gaba abinsa daga fadar haka, Asim yai dariya yace " wai yau me nakeji haka?"
Bangaren Kawu ya nufa cikin zumud'i ko sallama baiyi ba ya tura kofar d'akin, kawu na gaban wannan akwatin, jin Asim yasa yai saurin rufewa tare da tu
rashi karkashin gado da sauri, ya kalli Asim cikin fada yace '" kai wai sai yaushe zakai hankali ne?"
Asim yabi akwatin da kallo sannan ya basar yace " Abba anya kan Ashraf d'aya kuwa?"
Kawu yamai kallan mamaki yace " ban gane ba."
Asim ya m
atso yace " yanzu wai yacemin ya kamata muma magana ka karamin matsayi wannan matsayin nawa na yanzu is too low for me."
Kawu yai wata dariyar rainin hankali yace " amma ba kada hankali ko?"
Asim cikin mamaki yace " bangane ba."
Kawu yai dan
tsaki tare da mikewa yace " Kanaso kacemin Ashraf ne yace ma haka?"
Da sauri Asim ya daga kai, Kawu ya hade rai yace " ba ka cikin hayyacinka da alama mafarki kai."
Asim zai sake magana Kawu yace " mu fita ni."
Haushi ya turnuke Asim yai wa
je a zuciye, har yayi nisa ya dawo gun Kawu yace " Abba me kake nufi dani?"
Kawu ya kalleshi cikin mamaki ba tare da ya amsa ba, Asim ya cigaba " menene baka yarda dashi ba game da ni? Ni din ne baka yarda Ashraf yayi acknowledging din aiki na ba ko k
uwa baka yarda da zan iya wani abun bane?"
Kawu ya kalleshi cikin kulluwa da wannan halin nashi, yace " duka, u always disappoint me."
Yana kai nan yai gaba yabar Asim a tsaye a gun.
Asim yabi Kawu da kallo cikin tsananin takaici da ha
ushin yanda Kawu yake mai.
Kawu kam mota ya shiga cikin takaici.
***********
Nafi kam bayan tayi wanka tana zaune a d'aki ita kadai duk abin duniya ya isheta ta kira Ferry a waya nan sukai ta hira har Ferry ta sanar da ita jarabawarsu t
a fito.
Nafi tace " haba?kin dubo?"
Ferry tace " a'a amma ya Nabil yau zai dubo min."
Naf tace " kice ya dubo da nawa "
Ferry tace " to, amma Nafi karfa ki yaudaren kije ki cike wata makarantar ba BUK ba."
Nafi tai dariya tace " ka
rki damu duk inda kike nima ina nan, sai dai in samu ne banyi ba amma ina zani?"
Sun dade suna hira kafin suyi sallama bayab sun gama tsara bikin Jibiya da za'a fara nan da 2wks, Nafi tace " Zata kawu mata kudin ankon inyaso sai a musu gaba d'aya koma
i iri d'aya."
Tana kashe wayar tai shiru, a ranta tace " Ferry fa batasan ni matar aure bace fa ko? Ya kamata in sanar da ita kar taji daga baya ta d'auka ko yaudararta nai."
**********
Ashraf na zaune a office ya dukufa sosai gun a
iki yaji an banko mai kofa, Secretary dinsa yana biye da wanda ya bud'e kofar yana cewa " malan meye hakan?"
Ashraf ya kalli Habib yama Secretary din alama da hannu akan yaje.
Nan yai gaba, Ashraf ya kalli Habib yace " Habib lafiya naganka haka?"
Habib cikin fada yace " Ashraf me ake nufi akan kai mijin Nafi ne?"
Ashraf yamai kallan mamaki yace " ban gane ba?"
Habib yace " baka gane ba kamar ya? Little tace kai mijin Nafisa ne, ni kuma banaj na taba