Showing 30001 words to 33000 words out of 48142 words
ya amsa da kulawa yana tambayarta lafiyarta
.
Dije bata tabbatar da irin kaunar da dady yake mata ba saida taji yayi waya da Abdallah yace ya taho masa da waya karama mai kyau sabuwa keypard da layin mtn.
Lokacin da Abdallah ya dawo yana baiwa dady wayar, dady ya miko mata yana mai fa
ɗ
in, "Kha
dijatu ga tukuicin furar da nake sha a kauye, yanda kika faranta min nima ina son na zama mai faranta maki sannan inaso in tambayeki- Shin kinada ra,ayin karatu a nema miki ki fara daga farko ko kuwa ba kyaso a bari?
Khadija data kankame waya tana fam
an farin ciki tahau naxari anya kuwa zatayi karatu kuwa? Ita bokokon nan ba wani burgeta yake ba duk da dai tana son ace yau gatanan itama tana jin yaren turanci, saidai tasan zatasha wahala sosai kafin ta iya wasu abubuwan ta kalli wayar hannunta tasan it
a kadai darasine akan rashin ilimi domin idan baka da ilimi hatta ita kanta waya gagararka amfani takeyi sai kaga lamba wannan sai mutum ya bada an duba masa saboda bazai iya gane sunayen ba.
Bugu da ƙari tana so ace itama tazama wayayyiya kodan yan isk
an mata yan rainin hankali irinsu Zannura.
Dady ya katseta mata tunani, "Khadija idan kinga baki da ra,ayin karatu bazan takura maki kiyi adoleba dama ra,ayinki nake son inji tunda kokin aminta sai idan mijinki ya amince sannan zansa ya nema miki."
D
ije ta dago kanta asukawane takalli Abdallah dayake ta danne danne awayarsa kamar bayajin abinda dadyn yake cewa.
Yadda ya nuna halin ko in kula akan maganar ya bata haushi, bai nuna wata damuwa ba kan ko ta yi ilimi ko ba ta yi ba. Yana nuna kamar abu
ne mara muhimmanci, kenan bai damu ba koda rayuwarta za ta ci gaba haka nan ba tare da canji ba. Wannan halin da ya nuna ya ƙona mata rai matuƙa gaya, domin ita a zuciyarta ta san darajar ilimi da tasirinsa a rayuwar mutum.
A ganinta wannan ba maganar z
uwa makaranta kawai bace, maganar ce akan makomarta. Ta fahimci cewa idan tana son ta waye ta fita daga duhun jahilci zuwa hasken sani to kuwa sai ta amince an sakata a makaranta.
Idan ta samu dama ta yi karatu, za ta koyi rubutu da karatu yadda ya kama
ta, ta goge, ta iya Turanci, ta fahimci yadda duniya take tafiya da yadda karyar Zunnura da Na'ima su kirata da bakauya.
Amma rashin nuna damuwarsa ya sa ta kara jin haushi da takaici. Domin abin da take gani a matsayin haske, shi yana ganinsa a matsayi
n abu marar amfani. Duk da haka, burinta bai gushe ba. A ranta ta ƙuduri aniyar cewa wata rana za ta samu wannan damar, ta waye, ta goge, ta kuma nuna mashi cewa itama mai daraja ce.
Da wannan tunanin ta juya ta kalli dady tace, "na amince dady inaso."
Dady ya gyada kansa yace, "That is good, yayi kyau to Kai Abdallah kaji khadija tana son tayi karatu ta amince a nema mata makaranta ta fara zuwa, Shin kaima ka aminta?"
Kansa akasa yana amfani da waya yace, "Wannan ba matsala bane na amince tayi kar
atunta."
Dady yace, "To shikenan sai ka nema mata makaranta mai kyau a kusa da gidanka ta fara daga farko, dama daga primary yakamata ta fara."
Abdallah yakarkace kai yakalli dije yace, "yanzu dady wannan godeden ce zatayi primary a cikin yara? Lal
lai amma zata zama maman yara kenan."
Momy ta katseshi da fadin, "To Abdallah idan banda abunka nawa khadijan take da baxata shiga ckn yara ba, ko sha bakwai batayiba sannan kuma ai tanada fuskar yara girman jikin ne kawai kaidai kawai kayi mata fatan A
lheri."
Dady yace, "Koma dai meye banaso a samu matsala, na bar maka komai a hannunka, tunda private ce zasu karbeta ko aji nawa ne tunda kudi za.a
kashe don haka banaso a samu matsala ka tabbatar kai zaka rinƙa kaita makaranta, is that clear?"
Ran A
bdallah a bace ya amsa da, "Torh," kawai ba dan ransa yaso ba.
Abu daya ne ya faranta masa rai shine da yaga har zuwa wani lokaci iyayen nasa basuyi masa magana akan ko dijen takawo kararsa ba sai hankalinsa ya dan kwanta don ya zaci ko yanda tace masa
zata fada din ko ta fada.
Duk yanda ta wakana afalo akan zancen saka dije makaranta Abdulhakim yaji tas dayazo saukowa amatatttakalar benen ransa bai masa dadi ba sbd bayaso ace khadija tana futa kullum sbd yasan idan har aka ce yau khadija ta waye ta b
ude idonta to za.a sami matsala yatabbatar baxata zauna da dan,uwan saba shi kuma a rayuwa yana son zamanta da Abdallah ya
ɗ
aure.
Ya juya ya koma daki ya zauna akan gado tareda dafe kansa ya hau tunanin mafita.
Abdalla yashigo dakin nasu yana fadin,
"Dan uwa wai dama kana cikin gidan Amma banji motsinka ba?"
Abdulhakim yadago kansa tareda kakaro murmushi yace, "Ina nan ban fita ba, banajin ddi ne."
Abdallah yabashi hannu suka gaisa, "Sannu friend ko akwai damuwa ne?"
"Babu wata damuwa kawai d
ai baccine da bai isheni ba, jiya nakai dare sosai ina ciccike files dinnan da za.a fita dasu gobe."
Abdallah yace, "ok sannu dan,uwa Allah yasauwake."
"Amin."
Harya juya zai futa Abdulhakim yakirashi yawaigo yace, "akwai wani abunne?"
Abdulh
akim yace, "Kwarai xoka zauna muyi wata magana mai muhimmanci."
Abdallah ya dawo ya xauna kusa dashi.
Abdulhakim yagyara zama yace, "uhhmm akan maganar Khadija ne dama."
Gaban Abdallah saida yafadi domin yasha ko zancen da sukayi na shan giyar d
ayai ne da ita ko dama Abdul din tagayawa, yana shakkar Abdulhakim yaji wannan maganar domin baya masa ta dadi zai iya juya masa baya su
ɓ
ata.
Abdulhakim yace, "Naji maganganunku dasu dady dazu akan batun saka khadija makaranta da za.ayi nikam banso h
akan ba banso kuma naji ka aminta ba sbd khadija bata san kowa ba a kano saimu inajiye maka halin matan birni da mazuga, kada tazo ta shiga sch tahadu da muggan kawaye su
canxa mata ra.ayi akanka taxo tafi karfinka dan haka ina mai shawartarka da babbar mu
rya akan kadakatar da wannan batun tun wuri sbd...."
Abdallah ya daga masa hannu, "Dakata Abdulhakim! Enough! Idan na fahimta so kake kace min nan gaba zata iya fin karfina kenan?"
Gyada kai kawai Abdulhakim yayi.
Abdallah ya nuna kanta, "Ni wacce
n ƴar kauyen zatafi karfina, to bari kaji lalacewata ba kai nan ba."
Ransa a matuƙar
ɓ
ace yace, '"Ta dade batafi karfin nawa ba, walh ni da hakan zata kasance zanfi kowa son hakan sbd kai shaidane na tsani yarinyar nan bana sonta, wannan zaman ma adole
nike yinsa da ita, to meye nawa don tashiga sch aini fatanama Allah yakawo ranar rabuwarmu cikin sauki ko Allah yasa nasamu na Auri burin raina lowerst."
Abdulhakim yaja wani mugun tsaki yace "A kullum kana bani mamaki domin kana kawo abinda bazai taba
yiyuwa bane kuma baxaka gane gatan dasu Daddy sukayi maka ba sai nan gaba."
"Aini walh ba gata aka yi min ba, kawai dai an cuceni an tauyeni kuma nasan cewa da saka hannunka akan komai, da ace ka hana dady da hakan batayiwu ba sbd yanajin maganarka yana
kuma bin abinda ka kawo to amma dayake kashuka min mugunta sai ka boyemin; idan ba haka bane ba Me yasa tunda anjona min Na,ima kai baka karbi yar kauyen tunda dama kuna shiri? Kawai dai bansan nufinka nayin hakanba sbd dakai ta dace sannan sai ka gujeta
saidai nima baxata taba samun farin ciki aguna ba sai zallar bakin ciki da takaicin da zai saka ta gudu da ƙafafunta."
Abdulhakim yace, "Ni kuma inhar ina raye baxan taba barin khadija ta kasance a cikin bakin cikiba..."
A hasale Abdallah ya katses
hi da fadin, "To ko insaketa ka Aureta don ta samu farin cikin?"
Abdulhakim yace "Wannan kuma kai ya shafa, gaka ga khadija ga dady nan amma ina san ka tuna irin hukuncin da ya tanadar maka idan ka saki daya daga cikinsu don haka koma miye zakayi bai sh
afeni ba, saidai ince ga fili ga mai doki."
Abdallah ya buga tsaki ya miƙe ya fuce fuu.
Koda yasauka kasa falon bai tadda kowa ba su dady sun tashi hakanan mubina da dije suma sun kule a dakin mubinar.
Kai tsaye gidan abokinsa Anwar yawuce domin
kwakwalwarsa tadau caji dayawa saida ya watsa ruwa sannan ya koma falo ya baje akan doguwar kujera yana shan sigari hankali kwance yana waya da babynsa lowerst.
Sai faman zuba masa shagwaba takeyi harda kukanta wai itakam _she miss him over_ gaskiya
zata diro nigeria a karshen wata koya shirya tararta ko bai shirya xuwantaba dole zatazo itakam.
Babu yanda zaiyi da ita a dole ya amsa mata ba dan yaso ba.
**********
Zannura da Na'ima kuwa wani kauye suka je me suna kaburma dake yankin dawanau
, basu wajen ba saidai aka yi masu kwatance aiko sunsha wahala kafin su gano gidan malamin me suna mallam matawalle wanda ake masa layi sai mutum yayi kusan awa guda kafin aganshi saboda cikowa.
Sunyi budu-budu dasu nakurar jar kasa a hakan ma don a
achaba suka karasa gidan ne.
Suma layin suka hau don mutane sunkai 20
😱
suka tarar
Dakyar dai da hkr da juriya suka samu suka shiga dakin da mallam yake
Mallam matawalle yaji bayanin da Na'ima ta koro na yanda take zaune da mijinta amma ba
ya sonta
Mallam yace, "Yanzu me kike so ayi masa?"
Ta gyara zama tace, "Malam so nike a saka masa azababben sona a zcyrsa ta yadda zaizamo dukkanin abun da nace shi zaibi ya zame min tamkar rakumi da akala sannan kuma ina so ya rabu da kowacce mace
ya tsaya a kaina kawai."
Ya hau gyada kai sannan yayi rubutu a jikin kasa ya bukaci jin sunanta da na mijin nata ta fa
ɗ
a masa.
Yayi surkullensa yagama sannan yahada mata magunguna na wanka da zatayi da kuma na turarawa da wani rubutu da zata rinƙa
yayyafawa sau ukku a filon da yake barci.
Ta zaro dubu 20 ta bashi tana godiya suka tafi ckn farin ciki.
Koda suka fito daga kauyen saida suka siyi ruwa suka wanke kafafunsu gudun kada a ganosu a gida.
*****
"Yanzu matar yaya har kin ga
ji daga dan wannan aikin da kikayi?"
Mubina ta tambayi dije tana mai jan babbar silbar fulawar da suka buga gabanta.
Dije tahau dariya tana fadin, "Ke walh bakida tausayi, yanzu duk irin wannan Dukan da naiwa fulawar bai saka kin yabamin ba saima
mita xakiyimin Allah zangudu wajen momy in barki da aikinki," ta karasa maganar tana dariya.
Mubina tace, "haba matar yaya ke yanzu saiki tafi kibarni da uban aikin nan me yawa kinga fa cake kawai mukayi ko cincin din bamu fara ba, gashi bamuyi su samo
sa ba balle azo kan meet pie."
Dijeh ta ware idanu tana fa
ɗ
in, "Kai yau naga ta kaina, daga zuwa taya aiki gashi za.a wahalar da ni akan za.a burge sirika"
Mubina tahau dry tace, "to amma dai naga kema zaki amfana tunda ko banza zaki gwanance a wan
nan fagen?"
"Eh kumafa hakane," Dije ta fada tana janyo silbar gabanta, "Kinga bani wannan aikin kama wani kawai."
Haka sukaita hira har suka gama abubuwan da suka tsara zasuyiwa saurayin mubina faisal wanda zaitafarwa mamansa dashi, maman nasa tan
a son mubina tana mata aike sosai shiyasa itama yau ta shiryata wa
ɗ
annan kayan makulashen.
Koda Su Na'ima suka dawo ba subi ta kansu Dijeh ba suka kule a daki.
A cikin leda mubina taba dije snaks din ta tafi dashi don magriba nayi Abdallah yaxo D
aukarsu don komawa gida
Sbd Ya qular da dije saiyace da Na'ima yace, "ke shiga gaba dan kinfi kalar gaban mota."
Aiko ta shige tana wani yauki da yatsina annuna mata so.
Allah Sarki dije ko ajikinta don hankalinta kwance tashiga baya ko afuska
bata nuna jin haushin hakanba.
Cikin ranta tace, "A banza, gwara in zauna a bayan kun zame min direbobi dama direbobi ke zama gaba masu mota su hakince a baya."
Ta kwantar da bayanta akan kujerar tana buga game da wayarta keypad da Dady ya bata.
_muje zuwa_
[28/02, 10:16 pm] : *DIJEN ƘAUYE.*
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
*True Life Story*
*Nabilancy Luv*
💘
(Auntyn S&S)
PG 60-65
Tunda Aka fara tafiya Dije batayi ba koda tariba tana baya abinta ta hakimce tana buga game daga baya ta ajiye wayar tana kalle kallen gari tanajin wani nishadi yana nashigarta.
Allah yayita da son ganin dogayen g
ine gine na bene musamman irin hawa biyu zuwa saman nan abin saiyaita bata sha.awa don tana gani a kalanda acan kauyensu, a kullum dama fatanta shine taga taxo birni taga abubuwan da take gani a kalanda ko a hoton wani abun dai.
Shiyasa a yanzun da take
zaune da take ganin da idanunta tayi tsuru abunta babu komi aranta na damuwa sai zallar farin ciki tana kitsa yadda zata cusawa Na'ima takaici kamar yadda suke cusa mata da aka hanata shiga
gaban mota aka yi mata gogar zana akan ita ba macen sakawa a gaba
n mota bace ba.
Dole sai ta saki Bomb ya ragargaji zuciya, walki take daidai duwawunsu.
Lokacin da ta tuno Abdulhakim saitaji wani iri aranta sbd taso taganshi kafin tafito amma Allah bai nufa zasuyi sallama ba.
Na'ima uwar iyayi ta fiddo waya dag
a handbag ta kanga a kunne tana waya da wata cousin dinta suna hira tana zuba turanci duk don ta cusawa Dijeh takaici shi kuma gogan tana yi ne domin ta burgesa.
Abdallah
ɗ
an wulakanci sai tsaki yake yi don wayar ta isheshi ba qaunar jin surutu yake yib
a ransa baya masa dadi sbd yana a cikin wani yanayi, duk lokacin da ya tuna cewar Gobe lowerst zatazo sai yaji gabansa na yawan faduwa yanaji a jikinsa za.a iya samun matsala daga bangarenta don tace itakam idan tazo sai Andaura musu Aure sannan zata koma
kuma yasan dole zata gane yanada mataye, yasanta da bakin kishi na tsiya shikam duk baisan yanda xaiyiba tunda iya kokari yayi don tsaidata Amma abin ya faskara taki aminta.
Yarasa mafita duk da dai Anwar yabashi shawarar ya kawota gidansa tunda shi
shikadaine agidan amma bai aminta da hakanba saidai idan tazo yanemi shawararta in tafi son hotel shikenan saiyakaita.
Ransa ne ya sake baci jin Na'ima tana shewa tana tafa hannuwa tsabar yadda wayar tayi mata da
ɗ
i.
Ya buga mata tsawa yana fadin, "
Ke! Wai wace irin wawiyace ke? Ko kin mance a inda kikene kike mana ihu da tsawa kamar wacce take a tsakiyar kasuwa, walh ko ki datse wayar nan ko kuma in saukeki a hanya kya taho a kafa."
Da sauri ta kashe wayar cikun kissa ta kalleshi da rage murya
tana cewa, "haba sweety me yayi zafi hakan, tuba nike ranka ya dade, da dai a jiyeni a hanya gwara in kashe wayar, indai wayace baxa.a sake dagawa bama ballantana ta bata maka rai."
Yaja mata tsaki kawai baice uffan ba
Itako Dije abin dariya yaba
ta taita darawa kasa kasa tana jin anyi ƴar gadarar tsawa da wulakanci maimakon taji haushi saima hakan ya sata tarayrayarsa allai wani abun sai a birni ai walh in itace saita gwaba masa magana akan kaikaice.
Ta dauko wayarta a yar pos dinta babu wanda
zai kirata, to waye ma yasan tanada wayar alhalin du-du-du yau aka bata ita, gwara-gwara mubina tadauki nambar itama tasa mata tata har tayi mata saving.
Tana juya wayar a hannunta, lallai wayar tayi mata kyau ta burgeta saitaji inama ta iyata inam
a ace tayi karatu.
Take ranta yayi fari tas data tuno wataran zata zama me ilimi tunda zata fara karatun nan gaba.
**********
Da isarsu gida Yai farking a gun daya saba ajiye motar tasa Na'ima tayi saurin futowa don tanada qudirin taje ta aikat
a abinda boka yasa tayi ayau
Itako Dije Ko motsi batayi ba hankalinta nakan wayar hannunta tanata dannawa dataga wani game mai muciji, game din ya tafi da hankalinta don baida wahala tana gwada iyawarta taga ta iya ta kware cikin sakanni aifa tuni tahau
kaftawa.
Abdallah yabuga mata wata tsawa da saida ta furgita don wayar saida takusa subucewa ahannunta ma
" _what Are you doing here_! Ko motar gidan tsohon kice ne da kk like kk ki futa?"
Ranta yabaci da wannan mugun kalamin nasa musamman da tag
a Na'ima ta juyo tana mata dariya.
Da tsiwa takalleshi ido ckn ido tana murguda baki tace, "Koma ta gidan waye kaita shafa bani ba kuma inkai hakuri aixan futa ack ba shekara zanyiba ato."
Kuma tayi zamanta domin so take ya bu
ɗ
e mata motar tayi wa N
a'ima gugar zana, a fusace ya bu
ɗ
e motar yace, "Fito."
Ta fito tana sakin wani shegen murmushi ta dubi Na'ima tace, "Ke Jimana, kina ta cika da batsewa saboda kin zauna a gaban mota, to ai gaban mota na direbobi ne, su masu matsayi a baya suke hakimcewa
kamar dai yadda na hakimce na bararraje a baya. Ke da kanki kika bu
ɗ
e mota sannan da yake ni mai matsayi ce kina gani da kansa ya bu
ɗ
e