Showing 6001 words to 9000 words out of 48142 words

Chapter 3 - DIJEN KAUYE COMPLETE

29 Aug 2026

8

gashi kuma zasu za

ma matan sa wai yaya kenan ………???

_Muje zuwa_

[23/02, 7:17 pm] _Dijen K'auye_



🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 15-20

Kwana dai yakama dady a kauyen Rogo domin bada shirin kwana yazoba,dayake acikin gdn gonar akwai building agefe guda da aka tsarashi ya hadu sosai Dan karamin bene ne duk Wani kayan alatu an tanadar ga kayan cima a kicin da firji tamkar macece acikin gi

dan Inkana ciki Dan Yana Samun gyara part din daga ma,aikatan Dake kula da gdn

Daddy Dole saida yaga mahaifin Dije wato marikinta knn mijin addaji awashe gari.

Baffa yawale mutumin kirki Yatarbi Dady cikin karamci da murnar ganinsa domin duk cik

in kauyen ansan dady da irin taimakonsa ga wanda bayadashi gashi da son shiga ckn dattijan kauyen inyazo shiyasa kowa yasanshi

Baffa yawale yai masa shimfida azaure suka gaisa a mutumce tareda gabatar da juna

Dady yace "Nasan kasanni amma ni ba

nsan kaba saigashi Neman Aure yakawoni gidanka yara sun hadamu.

Baffa yace "to!to madallah naji dadin hakan.

Dady yagyara xama yace "wato dama d'an wajena ne yake son "yarka nikuma Shine nabiyo baya domin atsaida maganar Aure kuma banason aja kwana

ki dayawa.

Baffa yace "waye kenan yake sonta ? Yasunansa ? Ko wancan na wajen danaga kunzo tare? Yana nufin Abdulhakim da sukazo tare yatsaya awaje

Ddy yace "Yana birni bamuzo dashi ba yayi tafiya dafatan za.a bamu auran khadijan domin so nake nan

da sati mudawo adaura auran kuma bana bukatar asiya mata komi na cikin gida,zanyi mata kayan daki da duk abinda yakamata .

Baffa yaji dadi sosai har ransa take kuma yai amanna da wannan daddad'an batu yacewa dadyn '"Naji dadin wannan magana takaruwa d

a farin ck dakaxomin da ita nidai anawa bangaren na amince saidai kuma akwai wanda yake tamkar jigo gareta da zan gayawa kafin atsaida ranar daurin auren duk da nasan shima baxai ki ba kanin mahaifin tane don ni daka ganni kanwar mahaifinta nake aure yarin

yar marainiyace rikonta nakeyi kawai.

Dady yagyada kansa yace "Allah sarki A ina kanin mahaifin nata yake domin inaso inje dakaina nasameshi muyi mgnr sbd agobe sassafe zankoma

Da baffa yaga Alh mustafhan amatse yake da zancen saikawai yatashi da

kansa yarakashi har gidan kawu Amadu din

To shima kawun nata mutumin ne me saukin kai kuma yaji dadin wannan magana taneman Auren dije da murnarsa yakalli baffa yace "to inbanda abinka baffa yawale kaida diyarka meye naka nasaikaxo guna neman yardata A

lhalin duk dayane kuma "ya dai takace kyauta aka baka komi kayi daidaine tunda baxaka cutar da itaba

Baffa yace "wannan ai dole ne inga nabaka hakkinka kada kuma nayi abu nikadai

Kawu yace "to hakane amma saidai naji kuna batun ayi biki kwananna

n aikyanta abamu lokaci sbd musamu damar yin kayan daki tunda birni zata xauna balle muyi mata "yan tagajan tagajan

Nan baffa yai ms bayanin da dadyn yai masa kan cewar su zasuyi mata komi basai sun wahalar da kansuba

Ai dajin haka kawu ya amint

a da batun tunda Allah yahutarsu

Kafin dady yatafi saida yadire sadaki dubu dari biyar komi da komi gaisuwar iyaye nagani inaso toshi, sannan yadire wata dubu dari da hamsin yace abaiwa amarya tayi siyayyar kayan da zatayi fitar biki da sauran hidima

Sosai sukaita mamakin wadannan dubban kudaden don basu taba ganin ankawo su haka a auren kauyenba

Kudin agun kawunta yk domin baffa yace shiyafi cancanta yarike bashiba dukda saida akai tirjiya kafin yakarba shima

Koda baffa yaxowa da Addaji

batun tayi murna sosai tasawa abin Albarka

A al,adar kauyen kuma ba.a taba zanta Auren budurwa Agabanta balle agaya mata inhar antsaida mk da miji saidai kawai kiji anayi

Hakama in ita takawo mijin to idone nata kawai

To wannan ce tafaru ga dije d

omin kuwa kwata kwata batasan bidirin da akeyiba na Auren da za.ai mata

Itadai akullum tana tunanin Abokin birni tana jin zugin sonsa aranta tana tunanin ta yaya zata gaya masa tana sonsa tunda yaki ganewa

Shiko Abdulhakim ransa qal yai na mugun qu

lli tsakanin dijen da Abdallah dama can yasha aiyana cewar inama yaga Allah yakaddara auren Abdallan da dijen yaga shin yaxaiyi yaga yanda zaiyi da rayuwarsa tunda yazama mijin wacce yafi tsana aduniya.

Murmushi kawai yakeyi inya hanga yahango irin xa

man tabbas yasan akwai daru da tirka tirka

Saiyaringa jin kuma tausayin kawar tasa yasan tabbas zata shiga wani hali tunda itanma ba son Abdallah takeyiba tatsaneshi shine shaida to amma

zaici damarar taimaka mata azaman da zatayi da Abdallah ganin bai

cutar taba zai ringa kai kafa akoda yaushe domin debe mata kewa can wata xcyr tace dashi shin kodai akwai son khadija aranka? Dasauri yahau girgixa kansa yana fadin "ko kusa ko alama babu kaunace ta tsakani da Allah da haduwar jini kawai. Yabaiwa kansa ams

a

Abangaren dady kuwa dayajewa da momy wannan labari ba karamin dadin hakan tajiba itanma domin tanada labarin dijen kauye tun tuni tunda Abdallah naxuwar mata da furarta da nonon

Saigashi xata xama surukarta koda yake dama ita momy ba sawa ba ci

rewa indai akan dadyne tana son duk abinda zai nuna yanaso baitaba nuna baki yace farine shi tace masa a.a ba fari bane ina aikomi yace e, hakane shine amsarta

Baikarajin dadi ba sai Aunty maryam tazo taji itanma ta amince da hakan domin taji ance ank

ai kudin komi kuma baxa.a fasa na Ni,imaba itanma tanason abinda duk iyayanta keso to balle yarinyar da suke yabo kuma aikin gama yagama tunda antsaida ranar aure ai dole itanma taso ko taki ko taso

Dady ya aika wakilansa suka kai kudin aure gidansu Ni,

ima baban Safna mijin Aunty maryam ne yakarbi kudin shine waliyyinta amatsayinsa na babban yayanta

Nan ma dai antsaida magana akan cewa nan da sati biyu daurin Aure dai dai dana dijen kauye rana daya za.a daura knn

Nan ma dadyn yacake makudan kud

ade Ata bangaren nasu

Daddy Gida babba yasaiwa ango wanda ke unguwar ladanai babban gidane flat house me part 2

Ango dan gata knn wasuma itasa suke nema basu samuba

😅

Amma shi Yana kakkaucewa wanga Aure.

Babu wanda yagaya masa koda ta wayane amm

afa jikinsa nabashi akwai abinda ke shirin faruwa dashi yakikkira Abdulhakim yafi biyar aranar amma bai daga kiran saba kuma bai biyoba to ko daganan yasan ba qalau ba gashi aranar Uncle din nasa yake sanarsa cewa yashirya agobe zasuje kano gidansu Zasuyi

muhimmin wani abu.

Nanma yasha jinin jikinsa saiyashiga tunanika barkatai damuwarsa ma rashin daga wayarsa da Abdul yayi

Yarasa waxai kira yaji news gashi sunbabe da Aunty maryam yai mata laifi ga ta gidansa Zannura tayi fushi dashi duk dayasan shi

yayi mata laifi ya disgata gaban kanwarta

To amma dai ahakan yakirata awaya kuma akai sa.a tadaga masa kamar ma wani abun bai faru tsakaninsuba

Duk yadda yaso yaji ko akwai wani abu dake faruwa agidan bata yarda tasanar ms ba domin ankwabesu sosai i

tada Mubina sbd ansan zasu iya kiransa su tsurkunta ms duk da Zannun ce suke very close

Abu daya tagaya masa cewa "Eh to nikam bansan ko meke tafiya ba nidai naji anata zancen za.aje biki kauyen Rogo amma iya maxane zasuje.

Yatambayeta "bikin waye ha

kan? Ta tabe baki tace masa "oho walh ban saniba may be ckn familyn dadyne na can zasu Aurar da "ya"yansu

Yace "anya kuwa? Ai familyn dady a rogo duk sun kare damafa kakannine acan kuma babusu wataqila dai ko ackn abokansane zasuyi wata hidimar kinsansh

i da kara shine harda yin gayyarsa shima.

Ta daga kafada tana murmushi tace "inajin dai hakanne ma amma yaya yakamata kadawo aje dakai kaima tunda aiduk xumuncine.

Yace "Eh zanzo nima aje dani tunda uncle yamatsa wai dole tare dashi zamuje.

Nan

sukai sallama tana ms dariyar mugunta tabbas banda tana qule dashi na abinda yai mata da babu abinda zaisa taki gaya masa yanda suke ai babu batun ta iya boye masa wani abun balle damuwarsa tatace to amma yajawa kansa

*****A can bangaren Amarya dij

en kauye kuwa batasan wainar da ake toyawaba har ana gobe daurin Aure itadai taga iyayanta maxa sai shige da fice suke ackn gidan sunayin kus kus da Addaji.

Taga kuma yan garinsu Addaji da wasu yan uwan sunxoxxo gidan wai biki sukaxo har ana ce mata am

arya! Nan tahau tuhumar kanta wacece amaryar?! To bikin wa akeyi haka da batada masaniya abu har ckin gidansu akeyi?

Da dare ta tisa Addaji a daki ita kadai ta sata agaba da tambaya

"Addaji wai bikin wa akeyi ackn gidan nan dahar ban saniba? Waye ad

angi ake bikinsa kuma ackn gidanmu?

Addaji takalleta da tausayi tace "Dije Aurenki ne mana kina nufin baki ganeba? Ko bake kk kawo mijin ba??

Da sauri dije ta ja baya tare dafe kirji idanu awaje ckn rawar jiki tahau fadin "Aurena kuma Addaji!? Dawa z

a.ai min Aure ban saniba?? Yaushe nakawo mijin?walh bansan wani mijiba nikam bansan zancenba dan Allah kiyi min bayanin daxan fahimta.

Nan Addaji ta warware mata magana tace mata Alh mustafha me gidan gonane yaxo dakansa gidan yanemi Aurenta ga dansa k

uma iyayanta maza suka amince sannan kuma ai naji ance kina son yaron Ko Abdul waye ma sunansa na dai manta.

Dije ta tsaya cak tunaninta yahau zagaye,ta dawo nutsuwarta can tahau tunanin wani abu tayi shiru domin tunaninta bata yayi wato dady yaxo yanem

awa Abdulhakim Auranta knn har An bashi amma bata saniba to meyasa Abdul yai mata hakan meyasa baizo yasanarta ba har suka tafin. Ita ai dama shi takeso wannan ai abin farin cikin tane.

Ta mike asanyaye tafuta taje dakinta takwanta tana tunanin Abdul

MurmuShi tahau zabgawa tana farin cikin wannan lamari

Wai gobe iwar haka taxama mata agun Abdulhakim tabbas dole tayi godiya ga Allah daya cika mata burinta yabata Abdul A salin Alin batareda tasha wahala wajen bayyana tana sonsa ba.

Takai cikin dar

e tana juyi tana tunano kyakkayawar fuskar Abokinka burni,me yawan fara,a da wasa da dariya.

Kwana tayi tana farin ciki tayi baccin dadi sosai harda makara wajen yin sallah

Allah Allah taringayi axo adaura tayita kasa kunne don taji ana daurin aure

amma har hantsi bataji anxo daurin Aurenba tace Allah yasadai bafasawa sukaiba

To acan birni kuwa saida "yan daurin Aure suka fara zuwa Aka dauro Auren Ni,ima sannan Aka rankayo kauyen rogo domin Daura aure na biyu

Ango dai yadawo gidansu Amma baisa

mi zuwa kowanne daurin Aurenba domin rashin lfyr karya yakwanta dasukazo da uncle wai duk don dadynsa yatausaya masa kada yai masa fadan barin gidan dayai hhhmmm shiko dady kallonsa kawai yai ba magana me tsayi sai Allah ya sawwaqe

;

Shiko babban Aboki

me Dalilin Aure Amininna hannun dama Abdallah tuni yabi ayari zuwa kauyen rogo daurin Aure Inka ganshi saika zata shine Angon yanata bazaza babbar Riga.



Sai shabiyu daidai suka isa

Ba b'ata lokaci aka daura Aure aka kawo musu fura taji nono da suka

ri suka hau sha suna yin santi harda masu qullawa zasuyi guxuri da ita

Kafin sukoma Abdulhakim yasamu kebewa da Amarya asoro

Taxo tasha kwalliya kanta lullube ruf da mayafi kowa yai xaton shine angon ackn gidan domin yasha babbar riga yai kyau ainu

n

Yarasa da wane lafazi zaiyi mata bayanin komi

Saida tadago idanunta takalleshi da wani kayataccen murmushinta take yaji wani yarrr!

Abinda bai tabaji atattare da itaba sai yau

Tagaidashi tace "Ango na ina wuni.

Jin hakan yasa yadaure yafar

a mata bayani " khadija ina me bakin cikin sanar miki cewa ba dani aka daura mk Aure ba nasan zakiyi tunanin ko nine mijin naki to bani bane da dan,uwana ne,Dady shi yayi sha,awar yahada auranki da jininsa sbd kyan halinki da yagani dan haka kiyi hkr kiyi

hkr khadija Abdalla ne mijinki baniba ……

Xumbur ta mike tsaye ta yaye gyalen ta jingina da bango jin zata fadi ta nunashi da yatsa tana kuka takasa ma maganar donta makale amakoshinta

Tuno fuskar Abdallah datayi yasa taji wani jiri tareda ganin wani

duhu aitake taxube agun

Suma tayi na awa biyu anata shafa mata ruwa don matane suka fito suka dauketa aka kaita dakin Addaji

Shiko duk yarikice yashiga damuwa sai alokacin yahau nadamar abinda yayi,inama Bai gaya Mata yanzun ba..

Wayyo khadija kad

a ki mutu baki yafenba.nayi nadamar wannan hadin domin ji yayi xcyrs na mata wani mugun tausayi fiye da yanda xai tausayawa kansa.

Yan taron daurin aure basusan komi daya faru da amaryaba suka hau shirin komawa abinsu cikin farin ciki.

dady yace sai

sati me yazagayowa za.a dawo daukar amarya kafin nan aun gama bikin al,adunsu suma na kauye

Jikin Abdulhakim Asanyaye yabisu suka koma birni ransa ba dadi.ba dan taso ba,taso ace akwai Wani Dan space da zai samu tsakaninsa da Dije Dan ya rarrasheta ya

samo kanta

Dije tafarka taganta ajikin Addaji jikinta sharkaf da ruwa da alamar shafa mata akai tayi don tafarfado

Subiyune adakin kawai.

Tana farkawa tahau kuka ckn harshen fillaci tahau fadin " *Wallahi mi yid'a mo Addaji mi wanyi ma lara yeso

mako* (walh banasonshi Addaji,natsaneshi bana qaunar inbude ido inganshi)

Addaji tahau bugun bayanta ahankali " *wadu munyal dije, Allah su'bine ko lati khairu* (kiyi hakuri dije kada kibujire Allah yasa hakkane mafi Alkairinki)

Dije tahau kuka ta

na share kwalla

Addaji tace "kada kinunawa jama.a cewar bamu isa dakeba tunda kuma anriga andaura hkr xakiyi kixama me biyayya don kiga dakyau arayuwa kiyi shiru kinji dijena kixama me bin iyaye da miji.

Maganganun addaji sunshigeta nan tayi lakwas

ajikinta tana faman matse kwalla tana fidda numfarfashi

Addaji taci gaba da bata baki cikin fillanci " *jedu accu vojji, d'o on jarabu ma ambo* (kiyi shiru kidaina kuka jarabawarki kenan)

dije ckn sanyin murya tace " to *Addaji wannam do'a, Allah wad

u hanjum on khairu me* (addaji kiyimin Addu,a Allah yasa hakan yaxamar min Alkairi Arayuwata)

"Allah yasa dijena.Allah hokkumo sa.a.

Itakanta Addaji saida tayi mata kuka abayan idonta don ta bata tausayi data nuna hkr lokaci guda

Tunani yaiwa di

je yawa yaya zatayi da son da takewa Abdulhakim knn?bazata iya cireshi arai ba

Ta wani bangaren kuma ai burinta yacika naxuwa birni

To amma wane irin rayuwa zatayi a birni da wanda bataso baya sonta ????? ………

_muje zuwa_[9/26, 6:08 PM] Itz B

Y ebrerheem:

🙆🏼

🐄

*Dijen kauye...



🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True life story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 20-25

Cikin kwan

a guda da yin daurin Aure Dije ta rame ta futa hayyacinta danma tanada garin jiki dama batayo jikin siraran fulanin rugaba

Addaji taringa matsa mata akan saitaci abinci dole ga "yan taron biki basu watseba domin sai anyi sati ana biki ana shad'i dayin

bikin mard'on na fulanin kauyen wanda "yammata ke hadawa a dandali da daddare

Bikin mard'on bikine nashan damammen gero dafaffe yasha nono da sugari

Kwarya kwarya ake hadoshi daga gidan amare akawo "yammata susha suda samarinsu ana hira ana nishad

i me kida nayin kidansa afili wasu na rawa a na liki

To ita dije dama bawani kawaye take dasu wararruba

Kawayen kara dai sunzo mata "yan unguwa da sa,o,inta "yan uwa ancika anyi bidi,a ta al,ada

Ba laifi ta saki jikinta ackn yan biki wanda ba kow

anema yafuskanci tanada damuwa ba

Akwai "yar gidan kawunta sa,ar tace wato indo itace ma tasan abinda ke wakana atare da ita insun kebe takan tausheta da bata baki harda ce mata "aike ki godewa Allah ma da zakiyi rayuwar Aure a birni don wasu hakan suke

nema ma kuma mijinki dan gayu ga kudi dan Allah kicire damuwa aranki kiyita Addu,a Allah yasaka mk sonshi kawai.

Dije dai bata iya ce mata komi saidai tace mata "hhhhmmmm. (Ba baka sai kunne)

Ita kadai tasan me takeji aranta mekuma take hange

agaba don ko tayi addu.a Allah yasa mata sonshi aranta to shikumafa yazatayi da tsanar dayai mata, itakam har Abada zuciyarta Abdulhakim take kauna kuma baxata dainaba abinda ma yasa taji hankalinta yadan kwanta tuno kalaman Abdul din datayi nayanda ya bat

a hkr da kuma nuna mata cewar akullum acan zai kasance tare da ita xaikuma taimaka mata baxai bari Abdallah yacuce taba.

To wadannan kalami inta tuno takanji sanyi aranta.

**** *****

Daga can bangaren ango Abdallah kuwa baitashi saniba sai dare

yaji Abokansa ta koina suna masa waya ana masa Allah yasanya Alkairi wasuma harda nuna fushinsu akan bai gaya musu ba sai gani sukai da Jin Yai Aure.

Mamaki yamamaye shi farko yaringa musu dry don yazaci ko zolayace to inbanda tsokanarsa suka shiryi y

i yama xa.ai ace yai aure arana guda ya auri mata har biyu kuma daya a kauye daya abirni duk shi kadai

Bai gaskatasu ba saida Uncle dinsa yatashi tfy yakirashi daki agaban mahaifinsa ya shiryasu yai masa fadan gudu yabar gidan dayayi yakumace masa shima

yatabbatar yabar maganar Lowerst domin ayanzu shi din me Aure ne akansa Aure ma harna mata biyu.

Ya zabura arikice yace da uncle "Aure kuma uncle?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login