Showing 21001 words to 24000 words out of 48142 words

Chapter 8 - DIJEN KAUYE COMPLETE

29 Aug 2026

12

zatayiwa kawai domin tasami gamsassiyar amsa.

Ta shiga kirga kwanakinta a gidan ta shiga fushi da quncin rai na rashin ganin Abdu

lhakim domin shi da kansa yayi mata alqawarin cewa zai rinƙa shigowa yana dubata.

Saida tayi sati biyu sai gashi kwatsam da yamma aranar dama mubina bata zoba.

Ranar lahadi ranar takama babu aiki don haka a ranar yasami sararin zuwa gidan kuma Abdall

ah baya nan duk da ya sanar masa zaizo ta waya.

Taji farin cikin ganinsa amma farko fushi tayi ta cika tayi fam taki kulashi saida yace mata, "To tunda ba'ayi maraba dani ba bari nakoma inda nafito."

Ta

ɗ

auka da gaske yake ganin har ya juya. Da sau

ri ta taso ta riko hannunsa kamar zatayi kuka tana fadin, "Na huce zo ka zauna abokin birni."

Yayi saurin kwace hannunsa jin wani yanayi daya hudashi ya ziyarci kwakwalwarsa.

Yanemi guri yazauna taje kusa dashi daf ta zauna ya dan matsa nesa yace mat

a, "Me yasa kike fushi da

ɗ

an uwanki haka?"

Tayi dariya, "To ai naga ka mance dani ne yau kwana sha hudufa," ta fa

ɗ

a tana hada yatsunta alamar kirge

Yace, "Ina sane dake khadija nabar kune kusha amarci kafin...."

Ta toshe masa baki da sauri, "Alla

h yakiyaye min inyi amarci da wancen me mugun halin kasan Allah yau kwana sha hudu kenam rabona dashi, tunda kuka kawoshi ban sake sakashi a idanu ba."

Yakama baki yace, "Haba khadija ai kece da laifi, mijinki ne, ya kamata ko bai zoba ke kije ai shi za

man Aure sai anyi hakuri za'a sami dacewa a cikinsa."

Taja tsaki tace, "Amma dai kasan bana sonshi ko?"

Ya daga kansa yace, "Na asani amma inaso ki koyi sonsa daga yau."

Ta makale kafada, "A'a walh ba zan iyaba kasan so kuwa?"

Ya girgiza kansa,

"Ban saniba sai khadija ta fa

ɗ

a min," ya karashe zancen da zolaya.

Ta gyara zama tana fa

ɗ

in, "Kaga shi so in kayi shimfida ka kwantar da wanda kake so agun to babu yadda za'ayi katasheshi cikin sauki ka kwantar da wani ya maye gurbin..."

Ya tafa h

annayensa yana dariya har da tuntsurawa, "Ahhhh, lallai khadija kinsan So tabdijan ashe ke bata wasa bace? Daga yau kin zama malamata a fagen sanin sirrikan So."

Ta washe baki tace, "To na yarda na zama kaima kayi min karin bayani akan so."

Ya girgix

a kansa yace, "Ban san komiba khadija saidai kuma kaina ya kulle inaso kiyi min karin haske akan yanda kike nuna cewar kinyi shimfida kin kwantar da wani dan Allah inaso inji wanene wannan??

Ta kalleshi da wani irin kallo me kashe guiwa da diga digi ta

langwabe kai ta bude baki da nufin cewa shine sai sukaji sallama a kofa. Abdallah ne ………

_Muje xuwa fans_

[23/02, 7:17 pm] _DIJEN ƘAUYE_

🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True Life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)

PG 40-45

Kwata-kwata hankalinsa bai kai akan Abdulhakim dake a falon tareda ita ba, ita ka

ɗ

ai ya hango.

Yadda yake kallonta kamar wani kashi mai

ɗ

oyi ya fusata ba ka

ɗ

an ba, ya tsaya cak yana watsa mata wani irin kallo mai cike da raini da takama kamar yana so ya nuna mata shi ne mai iko, shi ne mai fa

ɗ

a aji kuma koma miye yayi bata isa ta kawo mashi wargi ba.

Ita kuwa ta

ɗ

aga kanta a hankali, zuciyarta na tafarfasa.

Ba ta gushe ba daga kallonsa ba hakazalika ba ta sunkuyar da kanta ba. Ta kafeshi da na mujiyarta tana maida masa kallon da ya watsa mata. Kallon nata ya fi na shi kaifi, irin kallon da ke cewa back to the sender. Idan yana tunanin zai tsoratar da ita, to

ya yi kuskure, Dijeh take walki daidai kugunsa har kafafu.

Abyn ya fusata ta matuƙa na yadda yake nuna mata raini da takama kamar shi ka

ɗ

ai ne ba ya son auren. Yadda yake jin an tursasashi ita ba da son ranta bane ba. Ita ma tana da nata burin na wanda

take matuƙar so.

A zuciyarta ta riga ta gama yanke shawarar ko dai ya sauko daga wannan takamar, ya shiga taitayinsa ya mu’amalanceta da hankali da girmamawa ko

kuma ta nuna masa cewa ita ba irin wacce za a raina a zauna lafiya bace ba. Idan har ya zab

i takama da wulakanci, to ita ma za ta koma masa chali-chali, ta koya masa hankali ta hanyar da zai fahimta.

Tsulum idanunsa suka sauka akan Abdulhakim, da sauri ya gyara yanayin fuskarsa yayi sallama.

Abdulhakim ya amsa sallamar tareda miƙewa ya tares

hi yana mika masa hannu suka gaisa.

Abdallah ya hau fara'ar dole shi a dole kada Abdulhakim ya fahimci halin da ake ciki, da raha yace, "An zo tsegumin ne? To idan ma kunyi gulmata ba yafewa nayi ba ato."

Dijeh tayi sagalailai da bakin tana kallon ab

un da yafi karfin tunaninta, yanzu-yanzu ya gama yi mata kallon raini amma daga ganin Abdulhakim har ya sauya alkibla yana mata magana kamar wani sun saba.

Abdulhakim yace, "In har kayi abin gulmar ai dole ayi magana akai don haka gwara ka gyara tun kaf

in kaji kira daga wajen dady."

Abdallah yaja tsaki yawuce yana fa

ɗ

in, "Wanda duk bai kai karata wajen dady bai cika dan halak ba, ga fili ga mai doki kuma zama dai indai danni akeyi to za'a ci takaici a koshi domin ni mutum in baya gabana ko kallo bai

isheni ba, idan an gaji da zaman gadin da ake sai ayi magana in bada shedar tafiya."

Fahimtar da ita yake ta murmusa tace, "Ita fa Dijeh idan ta raina kasuwa ko sauto bata bayarwa cikinta, kai nifa idan na raina kasuwa ko abun da ya biyota ta cikinta b

ana kallo."

Yace, "Ohh to yayi."

Yana gama fadin haka ya shige bedroom dinsa.

Ta bishi da kallon takaici tana ji kamar ta kurma ihu, har ita wannan

ɗ

an talahikin zai ya

ɓ

awa magana a kaikace, ashe kuwa ba za'a zauna lafiya ba.

Wani takaici ya ts

aya mata a makoshi, wato ita yake jira ta nemi saki idan ta gaji da zama lallai wannan bai san ta ba, aikuwa zatayi maganinsa ta inda zaiyi zato ba, asalin

ɓ

ullo masa ta bayan gida zatayi, da ita yake magana, sai ta nuna masa zallar maganar sunan DIJEN ƘAU

YE, sai tayi amfani da kauyanci da gidadanci ta nuna masa iyakarsa a cikin ruwan sanyi.

Abdulhakim daya kame a tsaye hannunsa a harde da juna ya hau jinjina kansa yana fadin, "Eh babu shakka, Lallai Abdallah wuyansa ya isa yanka, a gabana yake fadin hak

a wato inje in gayawa dady ba ya shakka? Tabbas ina tunanin akwai abokan da suke hure masa kunne aiko walh baxan taba bari ya wulakantaki ba."

Cikin ranta tace, "Kayyah wulakanci ya wuce wanda buga min a yanzu."

"Khadija ka da ki bari wannan abun da

ya fa

ɗ

a ya dameka a rai, ina mai tabbatar maki da cewa ko yana so ko baya so sai yayi zaman Aure dake cikin kwanciyar hankali da lumana."

"Ta wacce hanyar!?" Ta fada a ranta amma a fili sai tace dashi, "Ai walh Abokin birni bari kaji abun da baka sani b

a, nifa sbd kai da kuma daddy nike zaune a gidan nan domin idan har aka ce yau na nemi saki na koma kauye to abin zai zame muku magana, ace kun kasa rikeni ko ayi muku wata fassarar ta daban, idan hakan kuma ya faru duk lokacin da kukaje kauyen nunaku za'a

rinkayi ina gukmarku, in banda hakan da tuni na kashe auren na kagawa bujena iska tunda ba tareda aka haifo ba ballantana yace idan babu shi bazan rayu ba."

Ya hau gyada kansa yana fadin, "That is true khadija.!"

Ta yatsine fuska, "Kai nifa ba gane wa

nnan yaren bokon nikeyi ba, kawai ka fa

ɗ

a min abun da kace da Hausa, nifa a wancen yaren na boko ko zagina kayi ba ganewa zanyi ba."

Dariya ta bashi, ya saki dariya har da kyakyatawa, "Khadija," ya kira sunanta sannan ya

ɗ

ora da fa

ɗ

in, "Wannan gaskiya n

e shine abun da na fada domin duk maganarki gaskiya ce kuma naji dadi da kk kasance mai hangen nesa shiyasa kike burgeni. Khadija ina son kiyi min alqawarin zaki zauna da dan uwana da zuciya daya zaman Aure babu gazawa."

Wai ita Mi yasa yake mata haka n

e? Tana tunanin hanyar da zata koya mashi hankali shine yake nema ya

ɗ

aureta da jijiyoyin wuyanta akan wannan mutumin da yake nuna bata da daraja a idonsa.

Tayi jim tana nazarin wani abun kafin daga bisani tace, "To shikenan amma nima sai kayimin Alqawa

rin wani abun tukunna."

Ya gyara tsayuwarsa yace, "Fadi naki ni kuma nayi maki alqawarin zanyi maki kowane irin abune Dijeh."

Ta lumshe idanu tana jin dadin sunanta daya ambata tamkar a bakinsa aka halicci sunan.

Ta bude idanu a hankali ta watsasu

a kanshi a take yaji wata kasala na neman rufeshi.

Ji yayi tace, "ina so kayi min Alqawari akan kullum zaka rinƙa zuwa muyi hira."

Yayi jim kafin daga bisani ya murmusa yace, "Wannan ba mai wahala bane ba, nayi maki alqawari zan rinƙa zuwa saidai ki

nsan jiki da jini zan iya tashi daga aiki inji gajiya kinga dole in zauna a gida in huta ko?"

Ta gyada kanta.

Yace, "Da fatan kema zaki cika alqawarinki?"

Ta jinjina kai tace, "Tunda har nayi alqawari zan cika."

Yace, "To ina so a kullum ya kas

ance kina gaida mijinki sannan ki rinƙa yi masa sannu da zuwa tunda gashi yanzu da ya dawo banga kinyi masa ba."

Cikin ranta tace, "Ai kaima bakaga kallon da yayi min bane, banda na kai zuciyata nesa da tsaf zan dauki dutse in rotsa kansa saidai ayita w

allahi dani, yoh da fitinar ciki gwara ta waje, kuma dai fitinar duniya da mai ake yinta."

Amma a zahiri sai ta maƙe kafa

ɗ

a tace, "Tabdijan nikam ba zan shigar masa daki ba, yadda yake neman hanyar wulakatani idan naje kamar na siyawa kaina wulakancin n

e da kaina, idan na kai kaina duk abinda yayi min ni na janyowa kaina, kana ganifa yanzun maganganun da ya jefa min masu zafi. Gaskiya ba zanyi ƙarya ba, kawai dai zan haƙura in rinƙa gaidashi a nan shima idan ya kwana ukku bai amsa ba watsar dashi zanyi t

unda babu dole."

Abdulhakim ya murmusa kadan yace, "Kina da kafiya khadija amma hakan ma is fine."

Ta kama baki tana dariya, "Niko don Allah ina son in koyi wannan yaren naku mai dadin ji."

Ya tintsire da dariya yace, "turancine fa ba yarenmu b

a, ni da kike ganina bahaushene usul kuma turanci baida wahalar koyo indai mutum yasa kansa, dagewa kawai zakiyi wajen koyon."

Da zakuwa tace, "To yaushe zamu fara da gaske nike fa."

"Alright sai mu fara gobe, idan nazo goben sai mu fara daga A,B,C,D

."

Jin zai koya mata ta hau murna tana buga tsallenta, ya bita da kallo yana girgixa kai tabbas akwai yarinta a tattare da khadijan.

Yace, "Dakata daina murnar hakan nikuma inaso inkoyi fillanci yaushe zamu fara kenan?"

Ta washe baki tace, "Ahab,

abu mai sauki ma, aini ko yanxu inkanaso saimu fara."

Ya girgixa kai yace, "A'a mubari goben idan nazo sai mukoya tare kiyi min fulatancin inyi maki turanci."

Ta amsa da, "To."

Ya mike yana shirin tafiya

Tayi narai narai da idanu saying, "Kai a

bokin birni har zaka tafiya?"

Yace, "ah!to inban tafiba kwana zanyi? Mijinkifa ya dawo, ya kamata ki bashi kulawa ko domin samun lada."

Hawayene suka zubo mata domin taki jinin taji ance Abdallah mijinta ne bugu da kari yadda ganin Abdulhakim ya saka

kaunarsa ta dawo mata sabuwa danya shakaf.

Ji yake kamar yasa hannu ya goge mata hawayen amma ba dama.

Sai ya hau girgixa kai yana mata alama da hannu cewar ta daina kukan harda yi mata dabara, "Banda yawan kuka khadija, ki zame mai

ɓ

oye damuwarki,

let me tell you something in har kika bari Abdallah yaga kina kuka dadi zaiji ya zaci shine yasaki a bakin ciki kuma kinga dadi zaiji dan haka ki kiyaye kinji."

Ta gyada kanta

Haka sukai sallama, jikinta a sanyaye ta koma bedroom ko kallon dakin Abd

allah ba tayi ba domin zuciyarta ta shiga jaxaba ta soyayya.

Shikansa Abdulhakim din da tunaninta ya kwanta ga wani tausayinta da ya mamaye masa zuciya; yana tunanin da yadda zai taimaketa? Anya kuwa zai iya jurar ganinta a cikin damuwa??

********

Washe gari tunda safe take zuba idanun zuwan Abdulhakim, kuma ya cika mata alqawari ya zo da yammaci kusan biyar da rabi.

Ranar mubina ta tafi da wuri ana la,asar ta tafi wai zasuje unguwa

Amma da intaxo mata sai magriba take tafiya tana koyar da it

a kalolin girke-girke da abubuwan da bata saniba.

Tatsalo wankanta cikin wata doguwar riga da aka kawo mata cikin kayan da akace angone yahado musu akwatina daddaya

Tayi kyau abunta.

Lokacin da Abdulhakim yayi arba da ita saura kiris ya yaba kwall

iyar sai kuma ya tuna matar aure ce bai dace ba hakan wannan ya saka yaja bakinsa ya tsuke.

Dijeh ta kawo masa ruwan gora mai sanyi tareda glass cup, ya zuba yasha ka

ɗ

an, "Ina Mijinki ko bai dawoba?" Ya tambaya.

Fuskarta babu yabo babu fallasa tace,

"Bana jin ya dawo don banga shigowarsa ba."

Yace, "hhhmmm yayi kyau ai."

Tace, "Abokin birni in tambayeka mana."

Yace, "Inajinki."

Tace, "Wai dan Allah ya kuke da Abdallah anya momyce ta haifeshi kuwa?"

Yayi dariya yace, "Itace ta haifeshi man

a, nine dai ba itace ta haifeniba don mahaifiyata ta rasu, na rasa mahaifana a hatsari, da daddy da mahaifina ƴan uwa ne, shine ya rikeni tun ina yaro."

Ji tayi jikinta yayi sanyi, ta jinjina kai tace, "Allah yajikansu da rahama." Ya amsa da, "Amin." Ya



ɗ

ora da fa

ɗ

in, "Yanxu dai mufara karatu ko?"

Tace, "Eh mana ashirye nake ai."

Yace "baki shiryaba tunda banganki da takarda da abun rubutu ba."

"Da wannan don wannan, toni ina zan gansu ballantana har inzo karatun dasu, ai kai ya kamata ka taho

min dasu tunda ba fita zanyi in nemo ba ko?"

Yace, "To ai shikenan, ta tabbata dai yau karatuna ka

ɗ

ai za'ayi, ke naki ayi gobe idan na nafo maki da abun rubutun."

Ta gyara zama tace, "To, dame za.a fara maka?"

Yace "Da gaisuwa ko kirge nakeso muf

ara

Tace "to kaga dai *1-GO'O* *2-D'id'i* *3-Tati* *4- nayi* *5-Jowi* *6-joweego'o* *7-joweed'id'i* *8-jowee tati* *9-joweenayi* *10-Saffo*………yadaga mata hannu "Saurara haka *"yar fillo* atsaya iya nan gobe ma dora inyai yawa zan mance yanzunma saikin m

aimaito

Ta hau masa dariya, yadda take fada yana fada din harda zolayarsa "walh dai kunji dadinku da har baku dage kun koyi fulatancin ba, garin fa mahaifan kune."

Yace, "A'a ka da kiyi min gori ni uwata ka

ɗ

ai aka haifa a kauyenku."

Tace, "Naji ya

nxu dai muje wani abun idan ka shirya sai muci gaba."

Ya gyara zama yana dariya yace, "Na shirya muje zuwa na kwashe wancen."

Tace, "To koro tambaya mana ingaya maka da fulatancin."

"Yawwa idan zance kyakykyawa da fulatanci me zance?"

" *Bod'

d'um* tafada atakaice

"To mummuna fa?

Tace " *Yiddud'um*

Yahau tafa mata yana cewa " najinjina mk fillo

Tace, "Bajinjinar da tafin ba, karike karatun shine."

"Zan rike ai babbar kwakwalwa ce dani yarinya... To idan zance zantafi masallaci

fa?"

" *Mi dillay juulirde* _Zantafi masallaci_

"Ina rubutu fa?

Tace " *Mi d'on winnda.* _Ina rubutu_

"mun godewa Allah fa?

ta murmusa kafin tace," *yettoore Allah* shine mun godewa Allah, fatan ka fahimta?"

Ya jingina kansa tabbacin ya

gane. Yace, "To a barshi haka kinga magriba tasawo kai zuwa gobe maci gaba "

Ya mike zaitafi tace, "Amma daka tsaya kaci abincin dare anan ko."

Yagirgixa kai, "a'a nagode, gobe naci kinji Dijaa."

Nan sukai sallama tabi bayanshi da kallo kawai tan

a girgixa kanta

*****

Abdallah kuwa yana part din Na'ima kwance akan doguwar kujera yana kallon Ajent Ragab.

Ta kawo masa ruwa mai sanyi, tasha kananun kaya na sace zuciya don kusan ana ganin tsiraicinta.

Tana kwarkwasa da yauki ta dire masa ru

wan ag abansa tana masa sannu da hutawa kuma ba laifi yasaki fuskar tasa harda ce mata "yawwa.

Ta zauna akujerar kusa dashi

Wayarsa tahau tsuwwa

Yana dubawa yaga babyn sace lowerst yadaga da fara,arsa cikin yanga da karairaya Ni,ima ta mike tadau

ko remote akan reciever tarage volume tadawo da tafiyar yauki ta zauna kusa dashi

Hankalinsa baya kanta sai soyayya suke zubawa shida masoyiyarsa awaya abinsu, hankalinsa a tashe yake lallaba lowerst yana mata dabara na hanata zuwa Nigeria domin tasaka

ranar da zatazo shikuma bayaso tazo taga yayi Aure ta tashi hankalinta ko kuma tayi masa hauka sbd yasan kayansa tana matuqar kishi yanxu saita yanki mace akansa

Na'ima tayi mutuwar zaune tana sauraren wayar da yake, ranta yana mata Quna, ashe dama zanc

en da ake fadi na yana da budurwa a turai ashe gaske ne, kuma ma wacce ba musulmaba, lallai ta yarda yana sonta tunda gashi taga har wani lallabata yake akan tace zatazo gunsa bayaso taxo yanzu.

Ta shaka ba ka

ɗ

an ba, ta cika tayi famm jira kawai take ya

gama wayar ta tuhumeshi sai ya fa

ɗ

a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login