Showing 12001 words to 15000 words out of 48142 words
🏕
*Nabilancy Luv*
💘
{Auntyn S&S}
PG -35-40
Washe garin Abdallah da wuri yafuce yabar gidan yatafi gidan Abokinsa Anwar sbd shi Anwar din baitaba Aureba yawancin abokansu nan gidan suke taruwa suna badalarsu
Dije ta t
ashi tayi sallah takoma kan lintsimemiyar katifarta ta koma bacci
Taringa mafarkai masu dadi wai gata nan a gona itada Abdulhakim suna tadi na masoya
Yana gaya mata irin son da yake mata
Yanda taringa masa murmushi haka ta tashi da murmushin ak
an fuskarta saidai kuma da cikinta ya kulle najin yunwa tuni ta gimtse fuska tana hamma tareda shafa d'akalallen cikinta
Ta sauko daga kan gadon tana dibi dibin neman kicin ko zata sami madafi tayi girki
Tashiga kicin din saidai tsayawa tayi turus
tana kallon gas din dake girke akan ma.ajiyarsa
Ta waiga koina taga ga kayan abinci nan hardasu indomie akwali ga mai nan fari da ja gasu magi nan da duk abinda xa.a bukata saidai baxata iya kunna gas dinba
Falo ta dawo tana tunanin mafita
Taka
lli dakin dake jikin nata ta raya aranta ko nan ne dakinsa
Ta tafi ahankali ta murda kofar taji ta bude
Ta kusa kai tashigo don tayi tsammanin ko yana ciki ta tasoshi ya kunna mata duk da tasan zata fuskanci wulakanci da toxarci amma ciki ba.a masa
wasa xata shanye komi indai zata sami abin kari
Taga wayam bayanan amma da alamar ankwana acknsa ga zanin gado nan ya yamutse ga toilet a bude anshigeshi
Ta juya da tsaki takoma falon
Taxauna akan doguwar kujera ta takure guri guda
Kusan
mintina goma daxamanta tajiyo sallama abakin kofa
Ta amsa ahankali
Yammata tagani su biyu sun shigo da kuloli ahannunsu
Babbar sai yatsina takeyi takalli dije shekeke tace "Hhhmmm Amaryar kauye sannu ko.
Dije ta amsa fuska ba fara.a don
ta fahimci dame taxo
Karamar datake fara.a takalli dijen tace "Matar yaya Ina kwana.
Dije tace "lfy qalau.
"Sunana Mubina wannan kuma yaya tace Zunnura uwarmu daya ubanmu daya da yaya Abdallah momy ce ta aikomu mukawo muku abin kari.
Cewar mu
bina knn
Zannurat tace "kinga ni xan wuce gun Amaryar mu Ni,ima ke ki ajiye mata na hannunki ni bari nakai mata nata daidai cimarta sbd ita yar birnice nasan tasaba da dankalin turawa da kwai ita ajiye mata kunun gyadar da kosan nasan tafi sabo da kos
ai...mubina tace "amma dai yaya Zannura baikyautu ba hakan gaskiya wannan ai cin fuskane.
Zannura ta harari mubina tace "to uwar shishshigi gaya min gaskiya.
Taja tsaki ta juya "nikinga tafiyata ma gun Aunty Amaryarmu.
Da gayya tafadi hakan dan
dije taji haushi
Aiko dai dijen ta shaqa saidai bata nuna ba
Mubina ta zauna tana fara,a tace "matar yaya zoki dauka ki karya kinji.
Murmushi dije tayi tace "to nagode ki mikan gaisuwata da godiya gun momyn.
Ta mike taje ta dauko flet da cuf a
kicin taxo ta diba tafara zirawa
Mubina tana kallonta tana murmusawa itakam taji qaunar dije Kuma ta burgeta
Dije takalleta tace "ke baxakici bane ?
Mubina tace "nakoshi matar yaya naci nawa daxu.
Dije ta gyada kai tace "Amma kinsan sunana
kuwa?
Mubina ta gyada kai tace "nasani mana.
Dije da dariyarta tace "to ainaji kinata cewa matar yaya, inhar kinsan sunana to fadi inji.
Mubina tayi dariya tace "Khadija sunanki
Dije ta girgixa kai tace "a.a babu me cemin wani khadija a ka
uye Kawai kice min Dijen kauye yafi don kada sunan nawa ya bace
🤔😂
Mubina ta tintsire da dariya tace "dije ai ba sunane me dadi ba kuma kema kince ta kauye kinga kuwa ai khadija shi sai yaxama na birni tunda abirnin kk ko?
Dije ta dire kofin ta
dawo kusa da mubina tace "to kuma in dijen ya bace fa.
Mubina tace "ai gara ya bace tunda ko Nana khadija matar manzon Allah S.A.W ba dije akece mataba kuma kema ai yafi miki aji ace mk khadija ko?
Dije ckn sokonci ta kama hab'a tace "ni dijen g
ala ina naga wani aji,angaya mk nayi makarantane da zaki kiramin aji, tab!
Mubina ta sheke da dariya tace "ke ajin da nake nufi bafa na ajin da ake shiga ayi karatu ba aji na haduwa da kamun kai
Dije tayi dry tace "au na fahimta
Mubina t
ace "Aunty khadija kinada kyau fa dan Walh kinfi Aunty Ni,ima kyau.
Dije tace "wacece Ni,ima kuma.?
Mubina tace "Kishiyarki mana matar yayan namu Ai gunta Zannura ta tafi yanzu.
Dije tace "kada kiji haushina mubina yayarki batayi minba sbd nag
a kamar yar wulakancice naga wani gani gani takemin amma dai ba momy ce ta haifetaba ko?
Mubina tayi dry tace "momy ce ta haifeta mana kawai dai ita halinta ne haka injinin ku bai haduba to bata nunawa mutum kauna karara dan haka saikinyi hkr da ita sbd
kada ma kiga ta nuna tafison Aunty Ni,ima kiji haushi dama kawar tace kuma jininsu ya hadu da Yaya Abdallah zasu iya nuna miki kishinsu afili dan haka kada ki damu da wannan kinga ni ina sonki momy da dady suna sonki gakuma Yaya Abdulhakim ko? Tafadi tan
a karyar dakai tana kallon Dije datayi sakato tanajinta
Dije tace mata "nasani mubina nakuma ji dadi, Yanzu ina yaya Abdulhakim din yake ?
Mubina tace "sunfita da dady kafin mufito sbd zasuje can wani kamfanin dadyn daya bude musu.
Dije ta gyada
kanta tace "to inkinje ki gaidamin shi
Mubina tace "zaiji insha Allahu.
Dije takwashe kayan takai kicin ta dawo ta zauna kusa da mubina tana fadin "Amma dai ba yanzu zaki tafiba ko.
Mubina tace "a.a ba yanzu ba muna hirarmu me dadi ina zantafi
momy ma tace intsaya muyi girkin rana da dare nidake in nunnuna mk abinda baki ganeba na electric.(Kayan wuta na gas)
Dije taji dadin hakan sosai
Nan ta sake da mubina sukaita hira abinsu
Dama sa,annine baifi shekara daya ko biyu Mubinan ta
baiwa dije ba
********
Sati guda da dije tayi agidan kusan kullum mubina saitazo tayata hira kuma tun zuwanta bata saka idonta akan ango Abdallah ba hakan bai dame taba bama taso taganshi hatta Ni,ima babu abinda ya hadasu kowacce na part d'inta
Sha
kuwa sukai sosai da mubina da dije domin kullum intazo hirarsu suke tamkar yan,uwan juna ita mubina tayita bata labarirrikan birni na ban al,ajab ita kuma dije labarukan kauye na ban dariya take bata bayama labarinsu na fulani aiko mubina nashan dariya
Sau dayawa dije na tambayar mubina shin Ina Abdulhakim anya kuwa sakon gaisuwarta na isar masa?
Takan gaya mata cewar tana gaya masa mana yana dai busy ne sai uxuri don yafara xuwa kamfani shida Abdallahn
A bangaren Ni,ima akullum neman samun shiga t
akeyi agun Abdallah dataji yashigo part dinta zatayi saurin fitowa dg dakinta tayi masa sannu da zuwa wani zubin ma harda binsa da ruwa da lemo ckn dakinsa amma bata taba ganin fuskaba ahakan dai bata gajiya tasawa ranta cewar baxata taba gajiyawa ba harsa
i hakanta yacimma ruwa domin ita kama yanxu Abdallah ne agabanta ba dije ba don ta dije me saukine tunda tanada labarin abin duk dayane ma ashe itada da itan babu wacce yakeso Zannurace ta gaya mata hakan dayake zannun itace abokiyar hirar Abdallan
Itak
o mubina ta hannun daman Abdulhakim kullum tazo gun Dije saitayi mata tambayar cewa "Shin wai wacece budurwar Yaya Abdul hakim ne?yaushe shima zaiyi auren?
Mubina takan tabe baki tace mata "wuuuu!tabdijan ai yaya Abdulhakim baida budurwa bansan kuma ran
ar aurenba tunda bai tsayar ba baikuma kawo mana wacce zai Aureba kinga dai nice abokiyar hirarsa da da akwai zansani nidai nasan cewar Yaya Zannurat tana sonsa sosai Amma shi baya sonta yaki kulata suyi soyayyar
Ran dije yakara baci dajin hakan saita
ji ta kara tsanar Zannuran aranta Amma kuma Abu dayane yatsaye mata arai shin tayaya Abdulhakim da Zannura zasuyi soyayya ta yayama cikinsu daya zatace tana sonsa?toko dai zannurar batada sanine a addinance yahamta ka Auri yayanka ciki daya? Lallai ta yard
a zannu batada hankali bawan Allah yasan abin bame yiyuwa bane shiyasa yaki knn.
Tabbas tashiga duhu alamarin saidai ta kasa tambayar mubina komi wannan tambayar Abdulhakim zatayiwa kawai domin tasami gamsassiyar amsa.
Taringa kirga kwanakinta agidan
ta shiga fushi da quncin rai narashin ganin Abdulhakim domin shifa yai mata alqawarin cewa zai ringa shigowa yadubata
Saida tayi sati biyu sai gashi kwatsam da yamma aranar dama mubina bata zoba
Ranar lahadi ranar takama babu aiki don haka aranar y
asami sararin zuwa gidan kuma Abdallah baya nan amma yasanar masa zaizo ta waya.
Taji farin cikin ganinsa amma farko fushi tayi ta cika tayi fam taki kulashi saida yace mata "to tunda ba.ayi maraba dani ba bari nakoma inda nafito …… ta dauka da gaske
yake ganin yajuya din ai dasauri ta taso ta riko hannunsa kamar zatayi kuka tana fadin "na huce zoka zauna abokin birni.
Yai saurin kwace hannunsa jin wani yanayi daya hudashi yaziyarci kwakwalwarsa
Yanemi guri yazauna taje kusa dashi daf ta zauna ya
dan matsa nesa yace mata "meyasa kkai fushi da dan.uwanki haka?
Tayi dariya tace "to ainaga kamance dani ne yau kwana sha hudufa.tafada tana hada yatsunta alamar kirge
Yace mata "ina sane dake khadija nabar kune kusha amarci kafin....
Ta toshe ma
sa baki da sauri "Allah yakiyaye min inyi amarci da wancen me mugun halin kasan Allah yau kwana sha hudu tunda naxo gidannan da kuka kawoshi bansake sashi a idoba.
Yakama baki yace "haba khadija aikece da laifi mijinkine fa yakamata ko baixoba ke kije a
i shifa zaman Aure sai anyi hkr za.a sami dacewa ack.
Taja tsaki tace "amma dai kasan bana sonshi ko?
Ya daga kansa yace "nasani amma inaso ki koyi sonsa dg yau.
Ta makale kafada "a.a walh baxan iyaba kasan so kuwa?
Ya girgixa kansa "bansaniba
sai khadija tafadamin.
Tayi murmushi tana cewa "shifa so inkayi shinfida ka kwantar da wanda kake So agun to babu yadda za,ayi katasheshi ckn sauki ka kwantar da wani ya maye gurbin...
Yatafa hannayensa yana dry "ah,lallai khadija kinsan So tabdija
n ashe ke bata wasa bace? Daga yau kinxama malamata a fagen sanin So.
Tace "to nayarda nazama kaima kayimin karin bayani akan so.
Ya girgixa kansa yace "bansan komiba khadija saidai kuma kaina ya kulle inaso kiyimin karin haske akan yanda kk nuna cew
ar kinyi shimfida kin kwantar da wani dan Allah inaso inji wanene wannan??
Takalleshi da wani irin kallo me kashe guiwa da diga digi ta langwabe kai tabude baki da nufin cewa shine sai sukaji sallama akofa Abdallah ne ………
_Muje xuwa fans_
🐄
*YAR FILLO*
🐄
_Dijen k'auye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
*True Life Story*
*Nabilancy Luv*
💘
(Auntyn S&S)
PG 40-45
Abdulhakim ya Amsa
sallamar Abdallahn tareda saurin mikewa yatareshi yana mika masa hannu suka gaisa
Abdallah yahau fara.a yana fadin "Anxo tsegumin ne? To inma kunyi gulmata ba yafewa nayi ba ato.
Da raha yafadi dan haka sai Abdulhakim yace masa "inhar kayi abin g
ulmar ai dole ayi magana akai dan haka gara ma ka gyara kafin kaji kira gun dady.
Abdallah yaja tsaki yawuce yana cewa "wanda duk bai kai karata gun dady bai cika dan halak ba ga fili gamai doki kuma zama dai indai danni akeyi to za.a ci takaici akoshi
domin ni mutum inbaya gabana ko kallo bai isheniba kawai dai in anji angaji da zaman gadin da akene to ayi magana inbada shedar tafiya
Yana gama fadin haka yashige bedroom dinsa
Wani takaicine ya tsaya a makoshin Dije wato kenan ita yake jira ta ne
mi saki inta gaji da zama lallai wannan bai san taba zatayi maganinsa itama.
Abdulhakim daya kame atsaye hannunsa arike da Baki yahau gyada kansa yana fadin "lallai Abdallah wuyansa ya isa yanka agabana yake fadin haka wato inje ingayawa dady ma baya sh
akka? Tabbas ina tunanin akwai abokan da suke hure masa kunne aiko walh baxan taba barin yaringa wulakanta kiba khadija kada kisa wannan abin daya fada arai kinji wallahi ko yana so ko baya so sai yayi xaman Aure dake cikin kwanciyar hankali da lumana.
Ta wacce hanyar "!? Ta fada aranta amma afili saitace dashi "Aini walh Abokin birni bari kaji abinda baka saniba sbd kai nake zaune agidan nan da kuma dady domin inhar akace yau nanemi saki nakoma kauye to abin zaizame muku magana ace kun kasa rikeni ko ay
i muku fassara dayawa duk lokacin da kukaje nunaku za.a ringayi amma da ace bakwa xuwa garinmu to walh da baxan yarda naxauna bama balle har akai ga hakan.
Yahau gyada kansa yana fadin "that is true khadija.!
takama baki tana cewa "ikon Allah me haka
n kuma kenufi? Kasan niba jin wannan yaren nakeba bafa abokin birni dan Allah fassara min
Yayi dariya yace mata "wannan gaskiya ne shine abinda nafada khadija domin duk maganarki gaskiya ce kuma naji dadi da kk kasance me hangen nesa shiyasa kk burgeni
dan haka inaso daga yau kiyimin alqawarin zaki zauna da dan,uwana da zuciya daya zaman Aure babu gaxawa.
Tayi jim kana tace "nima saikayimin Alqawarin wani abu kana zan maka.
Yace "fadi naki nayi alqawarin zan mk kowane irin abune kinji Dijah.
Ta
lumshe idonta jin dadin sunanta daya fada
Ta bude idonta ahankali ta watsasu akanshi aiko dai take yaji wata kasala na neman rufeshi agun
Tace "inaso kaimin Alqawarin kullum zakazo gidana muyi hira.
Yayi jim kana yai murmushi yace "wannan bame wah
ala bane nayi mk alqawari saidai kinsan jiki da jini zan iya taashi daga aiki inji gajiya kinga dole inxauna agida inhuta ko?
Ta gyada kanta
Yaci gaba "to inkinmin Alqawarin dafatan zaki cika?
Ta daga kanta tana murmushi
Yace" to inaso akullum
ki kasance kina me gaida mijinki kiringa masa kuma sannu da zuwa tunda gashi naga bakiyi masaba.
Ta make kafada tace "tabdijan nikam bazan shigar masa daki ba dan innakai kaina duk abinda yaimin ninajawo kana ganifa yanxun ma maganganu yagayamin masu z
afi saidai in inringa tsayawa inya futo zai futa ingaidashi afalon
Abdulhakim ya murmusa kadan yace "kina da kafiya khadija amma hakan ma is fine
Ta kama baki tana dariya "niko dan Allah inason inkoyi wannan yaren naku me dadin ji.
Ya tintsire
da dariya yace "turancine fa ba yaren muba nida kk ganina bahaushene usul kuma turanci baida wuyar koyo inmutum yasa kansa dagewa kawai zakiyi wajen koya din.
"To yaushe zamu fara da gaske nakefa Allah
Yace mata "daga gobe khadija, innazo gobe sai mu
fara tun daga A,B,C,D
Tahau murna tana dan buga tsallenta yabita da kallo yana girgixa kai tabbas akwai yarinta atattare da khadijan
Yace mata dakata daina murnar hakan nikuma inaso inkoyi fillanci yaushe zamu fara knn.
??
Tayi farat tace "aini
ko yanxu inkanaso saimu fara.
Ya girgixa kai yace "mubari goben innaxo saimukoya tare kiyimin nayi miki.
Tace to "
Ya mike yana shirin tafiya
Tayi narai narai tace "kai abokin birni har tafiya?
Yace "ah!to inban tafiba kwana zanyi? Mijinkifa
yadawo khadija yakamata kibashi kulawa ko domin samun lada.
Hawayene suka xubo mata domin taki jinin taji ance Abdallah mijinta gashi kuma yau kaunar datakewa Abdulhakim din tadawo sabuwa tadawo danya shakaf
Yaji kamar yasa hannu ya goge mata hawaye
n amma ba dama
Sai yahau girgixa mata kai yana mata alama da hannu cewar ta daina kukan harda yi mata dabara "kiyi saurin tsaida hawayenki khadija kiringa boye damuwarki domin inhar kika bari Abdallah yaga kina kuka dadi zaiji yaxaci shiyasaki a bakin c
iki kuma kinga murna zaiyi da haka plz ki kiyaye kinji.
Ta gyada kanta
Haka sukai sallama jikinta asanyaye takoma bedroom ko kallon dakin Abdallah batayiba don zuciyarta tashiga jaxaba ta soyayya
Shikansa Abdulhakim din da tunaninta ya kwanta ga
wani tausayinta daya mamaye masa zuciya to waishin ta yaya zai taimaki khadija ne? Zaikuwa iya jurar ganinta adamuwa??
********
Washe gari kuwa Abdulhakim yacika mata alqawari yaxo mata da yammaci kusan biyar da rabi
Ranar mubina ta tafi da wuri a
na la,asar ta tafi wai zasuje unguwa
Amma da intaxo mata sai magriba take tafiya tana koyarda Dije girki kal kala da abubuwan da bata saniba
Tatsalo wankanta cikin wata doguwar riga da aka kawo mata cikin kayan da akace angone yahado musu akwatina da
ddaya
Tayi kyau ainun
Dan Abdulhakim dayaxo sauran kiris ya yaba kwalliyar saikuma yatina bai daceba hakan saiyaja bakinsa ya tsuke
Ruwa me sanyi dije takawo masa a jug
Yasha kadan yadire yana fdin "ina Mijinki ko bai dawoba?
Fuskarta ba far
a.a tace "banajin yadawo don baishigoba
Yace ""hhhmmm yayi kyau ai.
Tace "abokin birni intambayeka mana.
" Inajinki " yafada yana kallonta
Tace "wai dan Allah ya kuke da Abdallah anya momyce ta haifeshi kuwa?
Yayi dariya yace "itace ta haife
shi mana nine dai ba itace ta haifeniba don mahaifiyata ta rasu itada mahaifina hatsari sukai dady dan,uwa ne gun mahaifi shike rike dani tun ina yaro
Ta gyada kai asanyaye tace "Allah yajikansu.
Yace "Amin. Yanxu dai mufara karatu ko?.
Tace "Eh m
ana ashirye nake ai
Yace "baki shiryaba tunda banganki da littafi da fensir ko biroba
Ta yarfar da hannu "toni ina xangansuma aikai yakamata katahon dasu tunda ba fita zanyi innemoba ko
Yace "to aishikenan kinga yau karatuna za.ayi knn,ke naki a
yi gobe innaxo da abin rubutu knn.
Ta gyara zama