Showing 18001 words to 21000 words out of 48142 words
/>
oye. Yadda ta sunkuyar da kanta, tana murza yatsunta, ya motsa masa zuciya. Wani
ɓ
angare na zuciyarsa na son ya matsa kusa ya ce ma
ta ta daina wannan damuwar, amma wani
ɓ
angaren kuma na tunasar da shi cewa girman kai da tsana sun riga sun shiga tsakaninsu.
Abdulhakim ya ce, "To, Amarya, mu za mu tafi. Allah Ya sanya alkhairi."
Sai ya dubi ango ya ce, "Abokina, ka zama mai riƙe
min amanar kanwata. Ka kuma ji tsoron Allah a cikin zamantakewarku, sannan ka yi adalci a tsakanin matanka. Ka sani cewa ba zan zuba maka idanu kana kuntata wa Khadija in yi shiru ba, domin yarinya ce kuma ba ta da kowa a garin nan sai mu. Ka fi kowa sani
n yadda muke da ita na amintaka. Dole zan rinƙa zagayowa gidan nan domin ganin yadda zamanku yake tafiya, idan kuma na ga abin da bai yi min ba daga gare ka, to wallahi da gaske da daddy zan rinƙa, atorh."
Wata harara Abdallah ya makawa Abdulhakim din.
Nura ya hau ƙyaƙyata dariya yana fadin, "Ai gaskiya ya fada gara ma ka kiyaye domin hakkin Aure wuyane dashi saika dage zaka tsallake."
Suka miƙe tsaye.
"Ka tashi muje murakaka dakin
ɗ
aya amaryar taka muyi muku nasihar zaman aure inyaso saika da
wo nan dakin uwar gida ka kwana," Abdulhakim ya fa
ɗ
a da raha cike da zolaya.
Abdallah ya murtuƙe fuska, "Ka da fa ku takura min don ba za ku rinka juyani kamar waina atanda ba, atorh."
Nura ya dafashi yace, "Kwantar da hankalinka
ɗ
an uwana, abun da
Abdul ya fa
ɗ
a daidai ne, tunda har muka kawoka nan to dolene can ma mu kaika don mu fita hakkinta itama."
A dole ba dan yaso ba ya miƙe yabi bayansu
Dije tabi bayan Abdulhakim da kallo, taji inama ta bishi, taji inama ace shine angon nata, taji
kamar tace masa 'yaushe zaka dawo?' Saidai bakinta yayi mata naushi, harshenta ya gagara motsawa.
Ranta yayi fari jin da tayi Abdul yace zai rinƙa zagayowa gidan domin tabbatar da lallai tana cikin farin ciki. Tayi addu'a a ranta Allah yasa Abdulhakim d
in yakamu da sonta shima kamar yadda zuciyarta ta kamu da sonsa
Kai jama'a
😅😅😅
Kujimu da shirme Fa na dije
😅
Amarya Na'ima na jin takon angwaye ta gyara zama akan three seater da take zaune a kai, ta yaye rufin kan da tayi idanunta akan kof
a.
Har suka shigo bata dauke ganinta akan angon nata ba.
Abdallah yasha mur yahade rai ganin irin kallon kurullan da Na'ima take masa kamar wata mayya, wannan lamarin ai babu aji, sai yaji wani karin tsanarta a ransa
Shi kansa Abdulhakim ba ta b
urgeshi ba domin duk amarya da aji aka santa kamar dai yadda khadija tayi ta nuna kunya da aji, ta kuma nuna ita din amaryace ba kamar Na'ima ba da ta hakimce a falo kuma tari ango da mayen kallon kamar ta cinyeshi a tsaye
🤣🤣🤣
Suka zazzauna tare da
zolayar amaryar.
"Amarya ansha kamshi ga angon naki mun kawo maki," cewar Nura ya fada yana dariya.
Shi ko Abdulhakim cewa yayi, "To agurguje nasiha zamuyi muku akan zaman Aure domin dai Aure dan haƙuri ne ballantana kuma ke na'ima da zaki zauna da k
ishiya kuma ma kishiyar me karancin shekaru don na tabbatar akalla zaki baiwa khadija fin shekara uku ko hudu don haka ina san ki rike girmanki, ka da ki bu
ɗ
e hanyar da raini zai shiga a tsakani duk da ba haduwa zaku rinƙa yi ba idan ba da dalili ba tunda
kowa na nasa bangaren daban."
Na'ima ta shaka ba ka
ɗ
an ba, tuƙuƙin bakin ciki yana ragargazarta a zuci, ta murmusa cikin takaici tace, "Ba komai, Allah ya bamu xaman lafiya."
Abdallah ya amsa da, "Amin." Suka miƙe tsaye su duka.
Saida ya rakasu
har compound suka shiga motocinsu suka kama hanya sannan ya nufi sashen dije, direct dakinsa dake jikin nata ya shige.
Babban gado ne a dakin da yar drowarsa a jikin bango.
Ya rage kayan dake jikinsa ya
ɗ
aura towel ya shige bandaki ya watsa ruwa ya z
ura jallabiyar bacci yabi lafiyar gado tareda daukan wayarsa ya kira babynsa lowerst suka fara hirarsu ta masoya har na tsayin awa guda
ɗ
aya.
Da suka gama wayar ya dade bacci bai ziyarci idonsa ba yana ta tunanin yanda zai zauna da mata har biyu wanda k
wata-kwata baijin zai iya sonsu a ransa
Tabbas kowaccensu saita kwashi takaicinsa domin sai yayi musu Gashin Kuma sai sun gwammace rabuwa dashi akan zama dashi.
(Ni kuma nace to ai ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, ka da lamari yazo ya juye, re
she ya juye da mujiya, koda yake namu idanu idan kace zaka hadiye muciya sai mu dauko maka katuwa, kaci ka koshi kayi hani'an).
😅😅😅🤣🤣🤣
_muje zuwa a wannan labarin na Dijeh da Abdallanta_
[23/02, 7:17 pm] _DIJEN ƘAUYE_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
*Nabilancy Luv*
💘
{Auntyn S&S}
PG -35-40
Na'ima tasan ita ce uwar gida wannan kambun nata ne, kenan dai bangarent
a ya kamata ya kwana.
Dare ya yi nisa, shiru ya mamaye falon da take zaman jiran dakonsa. Ta tsaya tana sauraron takun sawunsa ko motsin ƙofar da zai nuna shigowarsa, amma shiru kakeji kamar loma ta tafi zagayar makoshi. Zuciyarta ta fara raya mata zarg
i.
A hankali ta nufi dakinsa dake bangaren, tana saka ran ko za ta sameshi a can. Saidai tana tura ƙofar ta tarar da dakin wayam. Gadon a shirye yake, komai tsaf-tsaf yake kamar ba a ta
ɓ
a kwanciya a ciki ba.
Wani irin takaici mai zafi ya tokare mata
maƙoshi. Ta tsaya cak, idanuwanta suna yawo a cikin
ɗ
akin tamkar wacce take ƙoƙarin hango wani
ɓ
oyayyen al'amari. Ita ce uwar gida, amma ga shi har ya iya wucewa bangarenta ya nufi wani wuri ba tare da wata sanarwa ba. Ashe kuwa za'ayi fitina a gidan amma
ba yau ba, ba gobe ba Amma dai gobe sai ta tayar da
ɓ
alli.
A bangaren Abdallah kuwa ya nufi bangaren Dijeh ne saboda yasan ba zata takura masa ba. Na'ima kuwa ba zata bashi sassaucin da zaiyi wannan wayar ba.
Washe gari tun da wuri Abdallah ya fice
ya bar gidan ya tafi gidan Abokinsa Anwar kasancewar Anwar bai ta
ɓ
a Aureba shiyasa yawancin abokansu nan suke taruwa suna badalarsu.
Dije ta tashi tayi sallah takoma kan lintsimemiyar katifarta ta koma bacci, bacci take har munshari, duniya tayi mata
da
ɗ
i.
A barcin ta rinƙa mafarkai masu dadi wai gata nan a gona ita da Abdulhakim suna tadi na masoya har yana ce mata I love you
Yana gaya mata irin son da yake mata
Kamar yadda takeyi masa murmushi a mafarkin kamar haka ne ta tashi da murmushi
akan fuskarta saidai inda aka samu akasin shine yadda cikinta ya
kulle na yunwar da takeji, ta gumtse fuska tana hamma tareda shafa
ɗ
amammen cikinta.
Ta zuro kafufunta ta sauko daga kan gadon tana leke-leken neman madafa ko ta samu ta girka abun da zat
a sakawa cikinta.
Ta shiga kitchen ta tsaya turus tana kallon gas din dake girke akan ma'ajiyarsa, ta waiga taga kayan abinci gasu nan hardasu indomie akwali ga mai nan fari da ja gasu magi nan da duk abinda za'a bukata saidai inda gizo yake saƙar shine
ba ta iya amfani da gas ba.
Ga yunwa tana ji amma dole ta haƙura girkin ta dawo falo tana neman wata mafitar.
Takalli dakin dake jikin nata ta raya aranta ko nan ne dakinsa ta harari dakin kamar mai dakin ne a gabanta.
Ta tafi ahankali ta murda
kofar taji ta bude
Ta kusa kai ciki a tsammaninta yana ciki, a nufinta ta tasoshi ya kunna mata duk da tasan zata fuskanci wulakanci da toxarci amma ciki ba'a masa wasa xata shanye komi indai zata sami abin kari.
Amma saidai mi wayam ta tarar da daki
n babu shi babu alamarsa, amma da alamar an kwana a cikinsa ga zanin gado nan ya yamutse ga toilet a bude alamar an shigeshi.
Taja siririn tsaki ta koma parlour, ta zauna akan doguwar kujera ta takure guri guda.
Kusan mintina goma da zamanta ta j
iyo sallama a bakin kofa
Ta amsa a hankali.
Ƴ
an mata ta gani su biyu sun shigo da kuloli a hannunsu
Babbar sai yatsina fuska takeyi tana kallon dije shekeke irin kallon rainin nan wanda mutum yana gani yasan kallon rainin ne, "Hhhmmm Amaryar k
auye sannu ko," ta fa
ɗ
a da raini.
Dije ta amsa fuska babu fara'a don ta fahimci da wacce tazo kuma ita guguwa ce daidai kafafunta duk wanda ya nemi kawo mata wargi.
Karamar da take fara.a ta kalli dijen tace, "Matar yaya Ina kwana?"
Dije ta amsa
da, "Lafiya kalau."
"Sunana Mubina wannan kuma yayata ce Zunnura uwarmu daya ubanmu daya da yaya Abdallah momy ce ta aikomu mu kawo muku abin kari," Cewar Mubina kenan.
Zannurat ta ta
ɓ
e baki tace, "Kinga ni zan wuce wajen amaryar mu Ni'ima, ita
kuma wannan abar ki ajiye mata na hannunki ni kuma sai in kaiwo tamu amaryar
ɗ
ankalin turawa da kwai saboda ita ƴar birni ce ta saba dashi, ita kuma wannan miye sunanta ba Kande take ko miye ma, koma miye sunanta ki bata kunun gyadar da kosan domin shine d
aidai ita, shi ta saba gani, kada taci burodi da shayi ta
ɓ
ata mamu falo da zawayi."
Mubina tace, "Amma dai gaskiya yaya Zannura hakan bai kyautu ba, wannan ai cin fuskane."
Zannura ta harari mubina tace, "to uwar shishshigi gaya min gaskiya."
Taj
a tsaki ta juya, "Ni kinga tafiyata wajen Aunty Na'ima Amaryarmu ta birni."
Da gayya tafadi hakan dan dije taji haushi
Aiko dai dijen ta shaƙa ba ka
ɗ
an ba saidai bata nuna ta damu, ta nuna ko a jikinta wai an tsikari kakkaura.
Mubina ta zauna ta
na fara'a tace, "Matar yaya zoki dauka kiyi karin kumallo kinji."
Murmushi dije tayi tace, "To nagode ki mika gaisuwata da godiya wajen momyn."
Ta miƙe ta dauko plate da cup a kicin ta dawo ta zuba kunun da kosan tayi
ɗ
aya-
ɗ
aya tana ci tana more dad
insa, ita fa wannan soson banzan da wannan ruwa mai kama da ruwan wanki ba damunta sukayi ba.
Mubina tana kallonta tana murmusawa itakam taji Ƙaunar dije ta burgeta
Dije takalleta tace, "Ke ba zakici bane?"
Mubina tace, "A'a na koshi matar yaya n
aci nawa
ɗ
azu."
Dije ta gyada kai tace, "Amma kinsan sunana kuwa?"
Mubina ta gyada kai tace, "Na sani mana."
Dije ta washe baki tace, "To ai naji kinata cewa matar yaya, in har kinsan sunana to fadi inji."
Mubina tayi dariyar wautar dijeh k
afin tace "Khadija sunanki, kin gani nasan sunanki kamar yadda nace."
Dije ta girgixa kai tace "A'a, aradu a ƙauyenmu kaf babu wanda yake khadijah, Kawai kice min Dijen kauye yafi don kada sunan nawa ya bace
🤔😂
inzo in boni in lalace inyi ta yawo babu
suna." (Yoh Dijeh tamu ta gargajiya
🤣🤣🤣
)
Mubina ta tintsire da dariya tace "Ai Dijeh ba suna bane mai dadi ba kuma kema kince ta kauye kinga kenan khadija sai ya zama na birni tunda a birnin kike ko?"
Dije ta dire kofin ta dawo kusa da mubina
tace "To kuma in dijen ya bace fa. Shikenan idan na koma kauye in rasa suna."
Mubina tace, "Ai gara ya
ɓ
ace tunda ko Nana khadija matar manzon Allah S.A.W ba dije ake ce mata ba kuma kema ai yafi miki aji ace maki khadija ko?"
Dije cikin sokonci
ta kama ha
ɓ
a tana fa
ɗ
in, "Tab! Ni dijengala ta mai gari ina naga wani aji, bara kiji in gaya maki gaskiya nifa ko makaranta ban yi ba, don haka daina
ɓ
arnar kalaman bakinki kina kira min aji."
Mubina ta sheke da dariya har da tuntsurawa tace, "Ke aji
n makarantar boko nike nufi ba, ba ajin da ake shiga ayi karatu nike nufi ba, ajin haduwa da kamun kai nike nufi."
Dije tayi dariya tace, "Aww na fahimta."
Mubina tace, "Aunty khadija kina da kyau don wallahi kinfi Aunty Ni'ima kyau nesa ba kusa
ba."
Dije tace, "Wacece Ni'ima kuma?"
Mubina tace, "Kishiyarki mana matar yayan namu Ai gunta Zannura ta tafi yanzu."
Dije tace, "Kinga gani ban
ɓ
oye-
ɓ
oye, kada kiji haushina mubina yayarki batayi min ba sam saboda naga kamar yar wulakanci ce
, naga sai wani gani gani take min amma dai ba momy ce ta haifeta ba ko?"
Mubina tayi dariya tace, "Momy ce ta haifeta mana kawai dai ita halinta ne haka injinin ku bai haduba to bata nunawa mutum kauna karara dan haka sai kinyi hakuri da ita, kada ma k
iga ta nuna tafi son Aunty Na'ima kiji haushi, dama can ƙawartace kuma jininsu ya hadu da Yaya Abdallah zasu iya nuna miki kishinsu afili dan haka ka da ki damu da wannan abun, kinga ni ina sonki sannan suma momy da dady sum suna sonki ga kuma Yaya Abdulha
kim
ko?" Ta fadi tana ƙaryar da kai tana kallon Dije da tayi sakato da kai tana jinta.
"Na sani mubina nakuma ji dadi, Yanzu ina yaya Abdulhakim din yake?" Dijeh ta tambaya da zaƙuwa.
Mubina tace, "Kafin mu fito suka fita da dady zasuje can wani k
amfanin da dadyn ya bude musu."
Dije ta gyada kanta tace, "To in kinje ki gaidamin shi kinji."
Mubina tace "Zaiji insha Allahu."
Dije ta kwashe kayan ta kai kicin ta dawo ta zauna kusa da mubina tana fadin, "Amma dai ba yanzu zaki tafiba ko."
Mubina tace, "A'a ba yanzu ba muna hirarmu me dadi ina zan tafi, momy ma cewa tayi in tsaya muyi girkin rana da dare ni dake in nuna maki abun da baki ganeba na electric.(Kayan wuta na gas)
Dije taji dadin hakan sosai barin yanzu da ta kusa zama da yun
wa akan rashin iya amfani dasu
Nan ta sake da mubina sukaita hira abinsu. Dama sa'annine baifi shekara daya ko biyu Mubinan ta baiwa dije ba
********
Sati guda da dije tayi agidan kusan kullum mubina saitazo tayata hira kuma tun zuwanta bata saka i
donta akan ango Abdallah ba hakan bai dame taba bama taso taganshi hatta Ni,ima babu abinda ya hadasu kowacce na part d'inta
Shakuwa sukai sosai da mubina da dije domin kullum intazo hirarsu suke tamkar yan,uwan juna ita mubina tayita bata labarirrikan
birni na ban al'ajabi ita kuma dije labarukan kauye na ban dariya take bata bayama labarinsu na fulani aiko mubina nashan dariya.
Domin inda Dijeh tana bata dariya har nuna yadda ake yi takeyi musamman yadda ake zuba dambe har yadda ake naushin ciki tak
e nunawa.
Ta miƙe tana mai kaiwa iska naushi tace, "In gaya maki kamar haka ne Balaraba ta kaiwa indo naushi, ina gaya maki sai gani mukayi Indo tayi warware a ƙasa, ashe kibar banza gareta, aiko daga ranar babu wanda ta ƙara yiwa burga."
Mubina ta f
ashe da dariya, "Kai, kai, kai, amma anyi badakala."
Dijeh ta sheke da dariya, "Ina gaya maki dukan tsiya mata tayi mata lulus ta barta kwance tana kuka har da majina."
Sau dayawa dije na tambayar mubina shin Ina Abdulhakim anya kuwa sakon gaisuwarta
na isar masa?
Takan gaya mata cewar tana gaya masa mana yana dai busy ne ga kuma uzuri tunda ya fara zuwa kamfani shi da Abdallahn.
A bangaren Ni,ima kuwa a kullum neman samun shiga takeyi agun Abdallah dataji yashigo part dinta zatayi saurin fitowa
daga dakinta tayi masa sannu da zuwa, wani zubin harda binsa da ruwa da lemo cikin dakinsa amma bata ta
ɓ
a ganin fara'arsa ba, a hakan bata gajiya ta saka a ranta cewar ba zata taba gajiyawa ba har sai hakanta yacimma ruwa, itafa yanxu Abdallah ne a gabant
a ba dije ba don ta dije me saukine tunda tana da labarin abin duk dayane, itada da itan babu wacce yakeso, Zannurace ta gaya mata hakan dayake zannun itace abokiyar hirar Abdallan
Itako mubina ta hannun daman Abdulhakim kullum tazo gun Dije saitayi mat
a tambayar cewa, "Shin wai wacece budurwar Yaya Abdul hakim ne? Yaushe shima zaiyi auren?"
Mubina takan tabe baki tace mata, "wuuuu!tabdijan ai yaya Abdulhakim baida budurwa bansan kuma ranar aurensa ba tunda bai tsayar ba, bai kuma kawo mana wacce zai
Aureba kinga dai nice abokiyar hirarsa da da akwai zansani nidai nasan cewar Yaya Zannurat tana sonsa sosai Amma shi baya sonta yaki kulata suyi soyayyar."
Ran dije ya
ɓ
aci da jin hakan taji ta ƙara tsanar Zannuran a ranta Amma kuma Abu dayane ya tsay
a mata arai shin ta yaya Abdulhakim da Zannura zasuyi soyayya ta yayama cikinsu daya zatace tana sonsa? To ko dai zannurar bata da sanine a addinance ya haramta ka Auri yayanka ciki daya? Lallai ta yarda zannu batada hankali bawan Allah yasan abin bame yiy
uwa bane shiyasa yaki kenan.
Tabbas tashiga duhu alamarin saidai ta kasa tambayar mubina komi wannan tambayar Abdulhakim