Showing 42001 words to 45000 words out of 48142 words

Chapter 15 - DIJEN KAUYE COMPLETE

29 Aug 2026

23

karata rabonta ne ta samu, domin da wani gidan taje kuma su fahimci wacece rufe get zasuyi su lakata mata dukan tsiya su watsota wajen get yana ihun ta boni ta lalace, don haka ki saka a ranki wannan dukan ne ta samu ta hanyar shemeta da kikayi."

Nan suka shiga wata hirar amma mubinan bata gaya mata zancen Abdulhakim da akace za.ai mata aure dashi ba.

********

Na'ima ce suka kule a daki itada Zannura Suna hira suna shewa da tafawa Na'ima,ima tace, "Walh bakiga yanda ta rudeba da na tsoratata

dayake jahilar kauyece ta yadda akan dukan datayi matan zata mutu a kamata a kaita prison."

Zannura ta sheke da dariya tace "Kice kinrikitata da kalamai? Lallai nasan yanzu hakan tana can da tunani da zullumi, ko kuma ince tana can tana zaryar toilet, c

iki ya rudi ruwa."

Na'ima tace, "Ni bansan ma ya akayi shegiyar karuwar ta nemi gidan ba tazo kinganta kuwa?ai da alamar yana sonta sosai duk fa yakidime da yaga halin da take cikin."

Zannura tace, "Ai gara da akai mata hakan, maganin ƴan iska masu

bin mazajen wasu gida ai gashinan ƴar kauye ta nuna mata halin nasu, wata qila kishine yasa ta rafketa."

Suka sheke da dariya harda tafawa.

Na'ima tace, "Ayyiriri ahayye nanaye, ni yau raina fess daga wancen ƴar kauyen har wannan kedarar sun kidime..

. ke nifa so nakema mu koma wajen mallamin nan a domin in gaya masa abu ya fara ci baki ga ba walh yadda ya kidime a kaina yau har yawo muka fita yana ta nan-nan dani."

Zannura tace, "Nima idan munje zaiyi min aiki akan yaya Abdulhakim domin bazan iya b

ari ya Auri kanwata ina ji ina ganiba."

Ni'ima tace, "Kamar yaya me kike nufi?mubinan yake so?"

Zannura tace, "Walh su dady ne suke son su hadasu wai don sunga tasu taxo daya and the fact that ba ya da budurwa shine zasu hadasu dan karin zumunci ni

kuma aka sakani a gaba wai infito da miji nanda shekara daya kokuma ya tsaidamin nima a cikin dangi nikuma walh naci Alwashin inban Auri yaya Abdulhakim ba babu wacce zanbari ta aureshi koda kanwar tawa ce sainayi abinda zai illata mace."

Na'ima ta kwa

lo ido tace, "Ke yanzu in yace mubinan yake so saikiyi mata wani abun na mugunta?"

Zannura tace, "Kina wasa dani kawata kinsan kuwa irin son da nake mishi kuwa, to walh babu ruwana da cikinmu guda da mubina akan yaya Abdul zan iya halakata inhar zan mal

lakeshi."

Na'ima ta gyada kanta tace, "Abun babban ne wai loma ta tokare a makoshi taki gaba taki baya koda yake banga laifinki ba kawata don nasan zafin so, sai yanzu hankalina ya kwanta tunda nasami rangwame akan So."

Nan suka shiga sak'awa da dink

ewa da yanda zasu bullowa lamarin suka kuma tsaida ranar da zasuje wajen bokan nasu.

A wani private hospital aka kwantar da lowerst inda aka rinka bata kulawar gaggawa

Sai cikin dare ta farka sbd Allurar baccin da akayi mata saboda yadda kanta ya r

inƙa wani mugun ciwo da akai treating goshin nata.

Koda ta farka ta ganta kwance akan gadon Abdallah yana zaune akan wata kujera daken kusada gadon yahada kansa da jikin gadon yana bacci sama sama

Ta kokarta ta tashi zaune tana kuka taga bai tashi b

a, haushi ya turnuketa ta

ɗ

age ta kai mashi duka hannu.

A furgice ya tashi yaga ashe itace ke kukan dan ya zaci ko a mafarkine ma

Ya kama hannuwanta yana aikin rarrashinta, tayi saurin fusgewa ranta a

ɓ

ace tana fadin, "Dena tabani mayaudari kaci ama

nata ashe dama kayi aure har biyu baka gayamin ba walh bazan yafe maka wannan cutar da kayi min ba kuma baxan...."

Ya toshe mata baki yana fadin, "Ki bari ki warke sai muyi maganar kinga kada ciwon kan naki ya dawo kuma ni ban so inga kina wahala."

T

a hau masa bore harda fuxge fusge tana fadin, "katashi kafuta bana son ganinka walh kafice ko ni infuta yanzun."

Da sauri ya saka takalmansa ya fuce daga dakin don ba xaiso tafuta a wannan tsohon daren ba domin a lokacin har karfe sha daya da rabi na da

re yayi.

Kuka kawai take tana nadamar zuwanta Nigeria tana kuma dana sanin yin soyayya da bahaushe, tana da kishi sosai shiyasa takejin a ranta sai ta koma gidan nasa ta dauki fansar wannan fashin kwakwar da aka yi mata a saman kokon kai.

Idan taji s

auki yanda yasa taji ciwon nan itama saitasa masa ciwo a ranta domin sai ta koma har gidan nasa ta illata matan nashi qonasu zatayi takona kanta kawai.

Can ta tuno da abokinsa ta ayyana cewar saita fara jonewa dashi domin ya dandani zafin da akeji in an

ci amanar mutum sbd ita ba cin amanarta kadai yayi ba harda zambatarta da ha,intarta kuma sai tayi mashi ramakon gayya wacce tafi ta gayya zafi.

A mota Abdallah ya kwana a farfajiyar asibitin ya xuge glass ya kunna ACn motar ya kwantar da kujera amma

kafin ya rintsa yafi awa biyu yana tunanin wannan halin da ya saka kanshi na ukubar soyayya, baisan yaya zaiyiba. Fa Son da yakewa lowesrt, gashi yanzun yanajin Na'ima a ransa sannan ga yanda yakejin muguwar Sha,awar Dije yana yawan tuna surorin jikinta To

waishin ina mafita...……?

*Tofa ina kuke fans saiku samo masa mafitar*

😅

_Auntyn Sayyada Da Shahidace_

👌

*DIJEN ƘAUYE.*

*True Life Story*

*Nabilancy Luv*

💘

(Auntyn S/S)

PG 85-90

Har sha biyu saura na

dare Abdallah na cikin motarsa a farfajiyar Asibitin bacci ya fara daukarsa sai ji yayi ana kwankwasa glashin motarsa.

A firgice ya farka domin wani mafarki ne naban mamaki yake na dije wai gashi nan a tsugunne a gabanta yana mata magiya akan tabashi w

ani abu amma taki bashi tana ta ja masa rai.

Murmushi ya kakaro da yaga ashe abokinsa ne Anwar.

Ya bu

ɗ

e glass din tareda futowa ya mika masa hannu suka gaisa Abdallah yace, "Abokina daga ina haka a daren nan?"

Anwar ya sosa ƙeya yana fadin, "Daga

club mana kawai dai nasan kana asibitinne tunda ka gayamin

ɗ

azu nasan ba zaka tafi kabarta ita daya ba. Ya jikin nata?"

Abdallah yace, "Da sauki tama farka daxu amma yanzun bansan kota koma ba, walh Anwar kaina ya daure akan wannan lamarin bansan ya aka

yi Lowerst ta gano gidana ba gashi taje ta janyowa kanta tsautsayi, Dijeh tayi mata fashin kwakwa a kokon kai."

Anwar yace, "hhhmmm abokina kana wasa da lamarin mata, to watakila ta taba binka a motane taga inda kake kwana kullum kuma kaga tana sonka ba

abinda baxata iya yiba."

Abdallah yaciji yatsa yace, "Ni yanzu bansan yadda zanyi in shawo kan wannan lamarinba domin tayi fushi dani sosai, kuma suma can gida nasan

sun shiga zargi a kaina tunda sun ganta gasu munafukai tsaf zasu iya gayawa dady komai

, fatana dai yanzu in shawo kan lowerst bana jin tasu."

Anwar ya murmusa yana kitsa wata gadar zaren a ransa sannan yace, "Ka da ka ji komai zan tayaka da ƙoƙari ta bangaren lowerst din, kawai ka tafiyarka gida wajen iyalanka tun kafin rashin kwanan nak

a a gidan ya ƙara tada tashin-tashina, sbd kaga idan suka gayawa dadyn kuma yaji yau din ka kwana a waje zasu gaskata komai a kanka a gidanku don haka ka tafi kawai ni zan kwana a wajenta idan yaso sai in shawo maka kanta."

Abdallah ya gamsu da zancensa

don dadin hakan ma yaji ya bashi hannu suka sake musabiha ta sallama da jin dadi.

Abdallah ya shige motar yace, "Na tafi ka kula min da ita zan dawo da safe."

Anwar ya saki wani shegen murmushi yana kitsa yadda zai sheke ayarsa da Lowerst sannan yac

e, "Kada kaji komai abokina zan kular maka da ita sosai wanda saika gode mini, ka saka a ranka komai zanyi yiwa kaine."

Abdallah bai fahimci nufin anwar ba dan maganar yayi ta ne kamar da harshen damo sai ya juyar da ita bai bai wanda koni da nake rub

uta muku da ankare nufinsa saida na dara

😅

wato yiwa kaine

🤣🤣🤣

Lokacin da Anwar ya shiga dakin a kwance ya hango lowerst akan gadon goshinta yasha bandage.

Tana ganinsa ta hau kuka tana fadin, "Anwar abokinka yaci amanata ya yaudareni kuma walh ba

xan yardaba sai na dauki fansa, duba kaga abun da matarsa tayi min, plz katayani daukar fansa kaji."

Anwar makiri sai yahau lallabata yana fadin, "Kwantar da hankalinki fine baby zan share maki hawayenki ckn sauki domin nima saina tayaki daukar fansar.

Ina sonki har ckn raina wanda duk ya ta

ɓ

a ki kamar ni ya ta

ɓ

a, nidai fatana kawai ki yarda ki amince dani muji dadin rayuwarmu kawai."

Jikin lowesrt a sanyaye tace, "Na amince da kai amma kada ka cuceni plz karikeni amana da kyau domin mu baiwa mara

ɗ

a kunya."

Makirin sai ya hau gyada kansa yana mai rike da hannunta yana mata tafiyar tsutsa tana lumshe idanu har ya hau yi mata k'asss!k'asss!! Da yatsu bata bude idon ba saida ya kwanta a bayanta kana tayi saurin budewa tana fa

ɗ

in, "nan fa asibitin

e kabari gobe in nemi sallama muje gidanka mana."

Yana bin surarta da wani mayen kallo yace, "kada ki damu dare ne babu me shigowa, shi kuma Abdallah ya tafi gidansa, likitoci sunyi bacci saida safe zasu shigo don haka kibarni inji duminki kawai sassaf

e sai in sauka a gadon."

Ya hau mata tausa yana manna jikinsa a jikinta ai tuni ya kashe mata jiki tahau lumshe idanu jin wani maganad'isu a kwanyarta.

A bangaren Abdallah koda ya koma gidan cikin daren nan yana parking mota kai tsaye sashen Na'ima

ya shige duk da kuwa ya gama yi mata kwana biyunta tun jiya amma sbd yana ra,ayin yaji dadinta a yau shiyasa baibi takan dijeba.

Aiko taji dadin ganinsa don batayi bacci ba dama chatting take tayi da kawaye da class mate maza tanajin dirin motarsa kuwa

ta dawo falo ta baje kafar ta akan 3 siter dama kayan baccin jikinta sharara suke wanda sunansu dasu gara babu.

Yana shigowa ta tashi ta shige jikinsa da sassarfa tana fa

ɗ

in, "I miss you my love."

Ya tareta yana jin wani shaukinta ya rungumeta tsa

m a gefensa yana shinshina gashin kanta da ya ji gyara, da wata shegiyar murya yace, "I miss you too ƴan matana."

Ta janyoshi takaishi har dakinsa don yi masa abubuwan daya dace...

_To ba sai mun bisuba mundai san abinda zai iya faruwa bakyau bin kwa

kkwafi_

😜

*********

Washe gari Suka fito ckn kwalliyarsu gwanin sha'awa Abdallah yasha shadda milk gezna tasha aiki, dalilin fitowar yana da daurin aure na wani abokinsa wanda zaije tareda Abdulhakim yayinda ita kuma Na'imar ta nemi ya kaita gidan

momyn a cewarta zasuje kunshi da kitso gobe sunada bikin kawarsu itada zannura (gun bokan za.aje dai

🤔

)

Yana shirin tada mota knn yaji ana kwada masa kira.

Dijeh ce ta taho da saurinta ta iso gurinsu ta tsaya a kansa tace, "mallam zanje gidan A

unty maryam ne ya za.ayi?"

Ya kalleta sama da kasa fuskarsa ba fara.a yace, "Idan kinsan gidan saiki taka sayyadarki kije." Ya rufe glass din.

Na'ima da samun waje ita matar so sai cewa tayi, "Ke malama dalla bamu guri zamu tafi anguwa kada ki bata m

ana tym."

Dije ta kufula ta nuna ta da yatsa, "ke ciciru cici cikon banci mara zuciya gun

ɗ

a namiji rufamin baki ba da ke nakeba da mijina nake. Ke baki isa inyi dake ba domin ba kai ba, mata masu aji wanda suka san kansu sune ake yi dasu bake ba wacce

bana jin tana da ajin."

Na'ima tayi shewa tace, "Ayyiriri ahayye nanaye saniyar daji ta samu sake. To sannu me miji bora yar kauye uwar marasa hankali wacce garin katobara zatayi kisan kai sbd bakin kishi walh dai anji kunya."

Dijeh ta murmusa tace,

"To akuyar makotan kofa idan kin gama tunbelen ni ina da abun yi."

Dije tana gama fa

ɗ

in haka ta wuce abunta, ta bar Na'ima tana ciji yatsa saboda zata maida mata martani kenan taga Dijeh ta wuce.

Saida Dijeh ta matsa gefe sannan ta tsaya tana bin m

otar da harara, Tana kallo me gadi ya wangale get suka fuce abinsu suka barta da cizar yatsa na maganganun da aka ya

ɓ

a mata duk da dai ta mayar da raddi mai zafi musamman ga waccen yar iyar.

Shi ko Abdallah kalamin dijene ya tsaya masa na jin ta cewa da

Na,ima wai tayi mata shiru bada ita takeba da Minjinta take to ashe dama ta daukeshi mijin itama ashe, kenan ta sakashi a wani bangare na maxauni mai matsayi, lallai to shima zai sakata a wannan matsayin.

Dijeh tana ganin motarsu ta fice ta juya ta n

ufi hanyar bangarenta, tana shiga ta kira mubina tace maza taxo yanzun ta rakata gidan Aunty maryam domin yau tana son taga yan biyu.

Daga

ɗ

aya bangaren Mubina tace, "Kin tambayi yaya yabarki?"

"Yabari mana dan Allah kitaho yanzun suma sunfita unguwa

shida Ni,iman. Ni

ɗ

aya aka bari a gidan."

Mubina tace "To matar yaya ganinan tafowa."

Kafin mubina ta iso har ta shirya ckn wata atamfa kwaddebuwa mai tsa

ɗ

a da zanenta mekyau.

Mubina ta tsara mata kwalliya mai kyau ta yan birni wanda ya futo da t

santsar kyanta na khadijanta ba wai dijen kauye ba don fondetion ta kwanta luwai a fata.

Suka fita a

ɗ

an sahu.

A Asibiti har lowesrt ta gama tsaya yadda zatayi ramuwar gayya, ta saka Anwar ya kaita gidan Abdallah.

Anwar ya ajiyeta nesa da gidan ka

ɗ

an yana jaddada mata sharadin tafuto da wuri idan ta dade zai tafi kada a ganshi da ita a harbo jirginsa.

Aiko dai Ashe bankwana sukai bada rabon tafuto su tafi taren ba.

A lokacin da ta tura get ta shiga gidan tayi magana taji shiru kasancewar

mai gadi ya zagaya bandaki, wannan ne ya bata damar shigewa gidan da

saurinta sbd tasan idan har ya ganta zai iya gano kudirinta domin kuwa jarkar feturce a hannunta da lighter wanda suka biya ta siya.

Kai tsaye part din Dije ta nufa babu tsoro alamarin

ta domin daukar fansa taxo yi, taci alwashin sai ta qona dije ayau sannan takoma bangaren Na'ima itama ta konashi idan makirin yana nan ta hada har dashi ta kona sai itama ta qona kanta.

Ta tura kofar a hankali ckn sa.a taji a bude, aiko taxura kai tas

hige

Saida taje tsakiyar dakin tahau fadin, "matar Abdallah kina ina?"

Da taji shiru na mintina saita nufi kofar data hango a bude ashe kicin ne.

Tana shiga ta hau tittila fetir akoina sannan tadawo ta yaryarfa afalon tadauko lighter da sauri ta k

unna aiko dai kaikayi koma kan masheqiya domin tuni wuta ta kama hannunta da ya jike da fetir a yayinda take tultulawa, saiga wuta ta cinye kayan jikinta, ta rinƙa ihu tana birgima a kafet wanda shima wutar yake ci

Duk iya ihunta mai gadi baijiyo taba h

ar wuta tacinyeta tafara cin silin da rufin dakin

Mai gadi bai auneba yana zaune akan benci yafito dg toilet yana daga kansa ya hango hayaqi yatirnike saman dakunan Dije ai aguje ya mike yayi gurin yana fadin "innalillahi wa,inna ilaihir rajiuna ………

*Auntyn Sayyada da Shahida ce*

👌

*DIJEN KAUYE*

🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕🏕



🏕🏕🏕



🏕🏕



🏕

*True life Story*



*N

abilancy Luv*

💘

(Auntyn S&S)



*ANA WATA GA WATA...*



PG 95-100

Abu goma da Ashirin yatararwa Abdallah domin bayan lafawar gobarar data taso a part din Dijen kuma wata daban ce ta faru domin waya aka yiwa

Dady aka gaya masa faruwar hatsarin dasu Na'ima sukayi a hanyar gidan boka, an kirasa ne kasancewar lambarce Last call a wayar Zannuran.

Ba ƙaramin tashin hankali iyalin Daddy suka shiga ba. Tun lokacin da suka isa asibitin Aminu Kano Teaching Hospital,

kowa ya shiga wani hali na damuwa da firgici.

Duk wanda ka gani daga cikin ƴan uwansu kuka yake yi. Wasu na zaune wasu suna tsaye suna masu roƙon Allah ya sauƙaƙa. Yanayin ya kasance cike da tausayi da damuwa.

Sai ga kuma labarin rasuwar Zannura da

ya iso masu a daidai wannan lokaci. Wannan labari ya sake ƙara dagula zukatan kowa. Mutane sun kasa

ɗ

aukar abin da ya faru, domin ba wanda ya ta

ɓ

a tunanin za a rasa ta cikin wannan hali.

Ga Na'ima ita ma bata cikin cikakken hayyacinta; ba ta san me ake

yi a kanta ba, sai dai ta yi ta kallon mutane cikin rashin fahimta.

Wannan rana ta zama rana mai cike da ƙunci da jarrabawa ga wadannan iyalan. Duk wanda ya halarta ba zai ta

ɓ

a mantawa da ita ba, domin ta bar tabo mai zurfi a cikin zukatansu.

Abdalla

h yana zaune nesa dasu yana kuka yaji an dafa kafadarsa ya juyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login