Showing 3001 words to 6000 words out of 124905 words

Chapter 2 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

16

da suka kama ni"

"To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba Waya"

"Ki ?yale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin ?osawa da maganganun Mama.

Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba.

Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?"

Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban le?o ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?"

"Eh ya fita baya nan"

"Ita kuma wannan fa?"

Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta ?i yarda, ga na Asibitin an yi ya ?i jiki kullum ?ara rikicewa yake yi"
"To me yake damunta ne har haka?"
Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaSi ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya ?i yi mata, mu koma na gargajiya ta ?i"

Yaya Atine ta Wan zura wa Jamila ido, har sai da haushi ya kama Jamila, ta tashi ta bar gurin. Yaya Atine ta ce "Mhmm" Ta Waukko wata hirar daban.

Ba ta wani jima ba ta yi wa Mama sallama ta tafi, sai dai cikin sa'a ta haWu da Baba a ?arshen layin, dan haka ta zauna suka dasa hira a hanya.
Ta ce "Ashe Jamila babu lafiya?"
"Eh wallahi ana ta fama, an kasa gane abin da yake damun ta"

"Lallai, to gaskiya yakamata ku zurfafa bincike dan kuwa Wan yau ka haife shi ne, amma ba ka haifi halinsa ba"
Cikin rashin fahimta ya ce "Me ki ke nufi?"

"Ni babu abin da nake nufi, balle a ce na ce, ni dai kawai na ce a zurfafa bincike ka ga tafiyata" Ya yi shiru yana nazarin maganganun 'yar uwattasa.

****

Cikin fushi Sultan yake kallon Imam Hammad, ji yake yi tamkar ya kwaWa masa mari ko ya huce.
"Sai yanzu ka ga damar amsa kiran nawa?"

Ya girgiza kai ya ce "A yi mini afuwa, jikina ne ya so motsa mini shi ya sanya ban samu fitowa ba"

Sai kuma ya sassauta murya ya ce "Wani abin ne ya faru da kai bayan tafiyar taka?" Ya girgiza wa Sultan kai.

Cikin rarrashi ya ce "Hammad, ba a cin nasara da karaya da kuma mi?a wuya farat Waya. Kuma Tafawa Maleeka bai yi ?arya ba, ina son ka gaje kujerar Sultan ba dan komai ba sai domin ina buri da fatan ka gyara kura-kuran da na aikata a baya. Ni ba ina burin ka zama Sultan domin son zuciya ko wani abu ba, ko iya haka Allah ya yi maka mai kyau a duniya, ina yi maka fatan mai kyau a Lahira. Ka ma da ilimi, ka na da dukiya, ka na da mulki iko ka ke bu?ata gurin aiwatar da wasu abubuwan.
Kai kaWai ne kujerata ba ta gabanka, kuma ka fi ni jajircewa da tsayawa a kan ra'ayinka da a?idarka, burikanka a kan Agadez da ?udure-?udirenka abubuwa ne da za su sauya rayuwar mutane da dama, saSanin sauran da hawan kujerar ne kawai a gaban su, ba ?alubale da abubuwan da suka kamata ba. Dan Allah ka yi ha?uri ka jure kar ka watsa mini ?asa a ido. Wannan nagartar taka ya sanya manyan nan na majalissata suka ?ara tsanarka ba wani abu ba"

Imam Hammad ya numfasa ya ce "Abie na ji duk bayananka. Amma ka yi ha?uri na riga na karaya, kalaman da ake jifa na da su sun yi tsauri da muni, su na taSa zuciyata da yawa"

"Na sani, ba na bu?atar ka musanta abin da na zo da shi, ka yi mini biyayya kawai. Kuma majalisa sun zartar da hukunci a kan Tafawa bisa abin da ya aikata"

Hammad ya kalli Sultan ya ce "Ina fatan ba wani abin mai tsauri suka yanke a kansa ba, kar ala?a tsakanina da shi ta ?ara yin tsami, ga 'yar sa ina aure. Ko ba komai uba ne a gare ni, kuma Asal ?anwata ce kuma matata"

Sultan ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu, hukuncin ba zai shafi nasaba da dangantaka ba, ka je ka samu ka huta" Ya risuna cikin girmamawa ya yi godiya ya fita.

Bayan fitarsa Sultan ya zauna, zuciyarsa cunkushe da damuwa, tunani yake yi yaya aka yi Tafawa ya san batun larurar Hammad.
Ya yi tunanin ko Asal ce ta gaya masa, amma ko Asal ba ta san taSin hankali Hammad ya yi ba, kawai dai ciwo ne yake kama shi, gangar jikinsa ta sauya, ya din ga wannan jijjigar da kakarin.
*****
Kaiwa da komowa Tafawa yake yi a cikin falonsa, zuciyarsa a cunkushe da ba?in ciki, bayan tuna yadda wasu daga cikin majalisar Sultan suka ?aryata shi, bayan da ya faWi cewa Hammad yana da taSin hankali.
Ya yi ?wafa ya ce "Da ni ku ke zancen, sai na tabattar wa da Duniya Wan ka mahaukaci ne, sai ya yi hauka tuburan Duniya ta gani ta shaida, kujerar da ka ke ?o?arin cusa shi ya hau, sai ta zama haramiyarsa ta har gaban Abada. Mulkin ai ba da shi aka haifoka ba, da za ka ce lallai ka yi shi ma sai ya yi ba. A wancan karon mu na ji mu na gani, aka Wora ka aka ce bamu cancanta ba, a wannan karon dole sarauta ta bar gidanka ta dawo gidana, Asadullah sai ya hau kujerar Sultan, ko ka na raye ko ka mutu".

*****
Tun da ya koma gida Asal ta share shi, shi ya manta ma abin da ya yi mata, ya ga tana basar da shi ga damuwa da yake ciki.

"C'heri'"

Ta Wago ta kalle shi. "Me yake faruwa ne?"
Ta girgiza masa kai alamar babu komai.
"Idan na yi miki laifi ne, ki yi ha?uri, ina cikin damuwa ne kwanakin nan, ki din ga yi mini addu'a" Ya yi maganar yana hargitsa gashin kanta da ta gyara.
Ya nemi guri ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana fatan bacci ya Wauke shi, ko ya samu sau?in wannan damuwoyin.
Yana jin ta ta kashe fitilar Wakin, sai hasken fitila na gefen gado wanda ba mai takura ba ne. Ta hau kan gadon ta kwanta a bayansa, ta zura hannunta ?irjinsa.
A hankali ya juyo, ya rungumeta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, duk da ta ji haushin abun da ya yi mata Wazu, amma da yake ya ?ware a iya mantar da mutum laifin da ya aikata masa, dole ta ba da kai bori ya hau. A hankali ya ji jikinsa ya fara Waukar zafi. Ya raba Asal da jikinsa saboda yadda yake jin san tamkar an saka masa fetur an kunna wuta a jikinsa.
Ya mi?e ya din ga kaiwa yana komawa a Wakin, yana maimaita ya hayyu ya ?ayyum. Ya shiga banWaki ya haWa ruwan Wumi ya yi wanka ya fito.
Kasa jurewa ya yi jin yana neman ya fita daga hayyacinsa, ya fita falo. Yana fita ya ji wannan dadaWan sanyin ya ratsa shi. Kan sa tsaye ya nufi inda yake jin sanyin na fitowa wanda hanyar Wakin Nana ne.
A corridor din gurin ya yada zango, ya samu guri ya zauna, ya jingina da jikin bango yana numfarfashi.

*****

Kwanaki biyu a tsakani, aka kuma zama, sai dai a wannan karon ba da duka Imam Win aka zauna ba, Hammad ne kawai, sai manyan masu faWa a ji na kusa da Sultan, wanda an yi zaman ne saboda abin ya shafi Hammad Win.

Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya bu?ata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na bu?atar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan mu?amin da ka ke kai.
Abu na gaba, mu na bu?atar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya.
Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan.
Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa Waga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana Wauke da larurar ?wa?walwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi.
Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka"

Cikin fusata ya mi?e ya ce "Ai dama na sani, wata ma?ar?ashiyar da mana?isar ake ?ulla mini, saboda ba a ?aunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar Wansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka Soye amma aka ce jinya ya yi a ?asar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga mu?amina ba har abada ai.
Kuma na faWa na maimaita, Hammad ba zai taSa zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta ?wa?walwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai ba?in baya ba zai yi mulki a Agadez ba"

Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti.
Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi ?arfinka. Duk abin da za ka faWa a kaina ka faWa amma kar ka sake kira na da Juya mai ba?in baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da Wa, na haihu ba ba?in baya ne da ni ba! Zobe kuma ya Sata ban san inda yake ba" ?if gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke bu?atar fashin ba?i gwari-gwari.

*****

Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daWinta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daWin yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faWi tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba"

Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki ?yale ni da maganar sani mijin Shukura"

Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne"
Ya Wan Wago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?"

"Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya"

Ya yi guntun tsaki, yana sake mi?e ?afafuwansa a kan gadon.

*****
Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi ?urii tana kallon roofing Wakin.
Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya ?aurace wa idanunta. Idan kuwa bacci Sarawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa.
Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da Wan gidan Alhaji Fatuhu ?aninta.
Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki.
Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da ?yar.
Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya Wauke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a ?one ta yi ba?i ta biyo ta tana ?o?ari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo Wakin, kawai ta cakume shi tana ihu.

"?anwata lafiya kuwa?"
Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiWanu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji.
Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da Wan Alhaji Fatuhu.
Ta rasa abin da yake yi mata daWi, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharSeSiyar wu?a a mafarkin za ta kashe ta.
Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen ?arfe sha Waya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan.
Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa.
Ba a yi awa Waya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta Wauke ?afa da zuwa gidan.
Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi.
Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi.
Ta Webo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa.

Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?"

Ayshercool
08081012143

79
Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan Win, amma ina mai baka ha?urin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaSi ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin damuwa da ?aguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah"
Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haWuwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a ?ungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga ?ungiyar sai da ta gaya masa.

Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taSa ganin idanun Wan Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba.
Ya ?ame a guri Waya tamkar babu rai a jikinsa.

Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi ha?uri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haWa ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa Wan sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faWa dan na haWa ka da mahaifiyarka ba.

Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuWi tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana Waure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe.
Jamila na ji daWi sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daWin ?o?arin kare kisan Wan Wan uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya.
Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?"

Jamila ta jinjina masa kai tana kuka.
Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka Wau wannan Wanyen hukuncin ba, mafita zaka nemo"

Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma Wan Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuWi ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar Wan Adam ba."
"Yaya Abba to me zaka yi?"

"Ni zan zama abin sadaukarwar taku?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba"

Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa"

Cikin kuka Jamila ta ri?e hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?"

"Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo Wan uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina ro?onki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya ?arasa maganar yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login