Showing 105001 words to 108000 words out of 124905 words

Chapter 36 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

48

maganar, Alhaji Fatuhu ya ?araso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo"

Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa"

Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani"

Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka.
Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ?aramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuSuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta"
Gaba Waya suka kalli Yusra cike da mamaki.
Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faWa kuwa?"
Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ?arya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi ha?uri na faWa"

Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ?wa?walwa, wata?ila...

Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ?arya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ?ungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar"

Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haWa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ?azafin?"

Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ?azafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. ?ana ya Wauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haWa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna.
Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faWar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa.
Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina.
Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faWa haka ne, ko kuma Wimuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi.
Sagir ya Wan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ?arti majiya ?arfi su uku.
Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haWu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yin?urin kashe ta, ya yi amfani da ?warewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki.
Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faWi ?asa.

Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ?wa??waran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai Wauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taSa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba.
Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taSa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina.
Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaWai ba ne a ?ungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da Wanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka Wauka a kaina, sai ka haWa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!".

*****

Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta Winke da tarin jama'a.
Tun daga kan gashin kanta, lungu da sa?o na jikinta, babu inda bai ga gyara ba.
Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ?amshi take yi na musamman.
Babu babban abin da ya razana Nana, irin sar?ar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sar?ar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa"
Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ?asar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta ha?ura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar.
Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tin?aho.

?aton Wakin taro ne, ta kowane Sangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, Sangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri Waya da na mahaifinsa.
Aka buWe taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin.
Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani Wan sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta.
Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faWar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez.
Aka gabatar da ro?o ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haWu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faWaWa shi a ?awata shi, ya zamana gurin buWe idanu sosai ga ba?i. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga ba?in da za su din ga zuwa yawon buWe ido.
Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ?abilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ?asa.
Aka yi ta kaWe-kaWe ana shiga ana fita da abinci kala-kala.
Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naWi aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa.
Sai kuma abin da ba a taSa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren Waya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ?anwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haWin.
Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin Wan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naWin Imam kuma Yariman Agadez mafi ?arancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki Waya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci.
Daga bisani aka din ga koWa Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima.
Nana gaba Waya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka.
Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ?arshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ?asar Agadez.
Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guWa, suna yi mata kyaututtuka.
Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan Worewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata.
Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ?aunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taSa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba.
"Ha?i?a yau rana ce mai girima, da Wumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ?asar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ?arasa maganar a raunane.
"Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da Wan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faWa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ?asa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu.
Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ?ara sake mi?a godiya a gare ku"
Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa.
Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taSa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan Waga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ?ololuwar matsayin da zato bai taSa zata ba.
Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan ma?iya ba haka suka so ba.
Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira.
Batun sabbin naWe-naWen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu mu?amai, ya bawa 'ya'yansa.
Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so.
Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu.
Nene ta ri?e hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daWin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi"
Gaba Waya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta.
Hammad yana ta shiri a Wakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haWuwa da Hammad ba, saboda karSar ba?i.
Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ?amshi"
Ya buWe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "?an uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu bu?atar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya ri?o" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa.
"Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na...
Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu"
Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai".
"To kuma tana son ba?ar fata"
Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ?abilar buzaye, ban taSa ganin ba?i mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk ba?ar fata gaba Waya matata ta fi kowane ba?ar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ?anwata kyakykywan zaSi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha.
Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun ri?e addu'a a duk inda take.
Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad.
Daga bisani, Hammad ya Wauke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? re tare da ita da danginta kaWai, washegari kafin su wuce Nigeria.
Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirri?e Hasna.
Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan Wauka a kansu."
Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ?arshe na faWa halaka, kuma bu?atar taka bata biya ba"

"Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!"

101
Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?"

Da kyar ya harhaWo maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?"

Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka Wauki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga ?ungiya kawai"
Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa.
Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi ha?uri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar Wakin su Sagir su zo. Ya Wauki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla"

Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaWai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?"
Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taSa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ?iftawa da Bismillah. Ya Wauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ?ungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba.
Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ?afafa ta matan masu kuWi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware.
Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa.
So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ?ura mata ido daga bisani ya kai hannu ya Wauka ya duba.
Sa?o aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar.
Ya fito daga cikin sa?on, ya ga sa?on Yusuf na ?arshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga sa?ona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya.
Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daWe su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya.
"Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buWe idonsa a razane ya mi?e tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login