Showing 33001 words to 36000 words out of 124905 words

Chapter 12 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

36

samu lafiya haka har yake iya takawa?

"Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka.

Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi ha?uri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka Waukko, ba mai Sullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan ?warin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba Waya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin.

*****

Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna.

Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki Waya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi i?irarin yana da Wa, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan mu?aminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken i?irarin da ya yi na yana da Wa zai fito. Idan kuma shaci faWi ne abin da ya faWa ta tabatta yana da matsalar ?wa?walwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa.

86
A SAUKE HAKKI, A BIYA KU?IN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143
Gaba Waya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai Waci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa Wan uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi ?asa-?asa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai"
?aya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'ala??a da waWannan Imam da aka naWa, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarWa kuma ba a Wauki wani mataki ba, to yana nufin goben ?asar nan yana cikin hakin da ba a sani ba"

Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taSin hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaWa wannan zancen, za a Wauki ?wa??waran mataki a kansa."
Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata ?wa?w?warar magana. Sultan ya san tabbas tun da? Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji ?wal uwar daka.

*****

Shukura ce a kwance a ?asa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buWe ?ofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe Wakin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta Waga kanta a mugun galabaice ta kalli ?ofar ta ga kamar ?ofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buWe ?ofar ko a buWe take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma ?ofar a rufe take. Ta ji ciwon na ?ara tsananta, yayin da wani abu mai Wumi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin ?afarta.
Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a dur?ushe ta ?arasa gaban ?ofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga ?ofar ta buWe. Ta zura kanta ta lelle?a ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi Wakin a cikinsa.
Tana faWin "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan ?afafuwanta tana takawa a hankali.
Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haWe da jini a jikin ?afafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saSi hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar Wan cikinta zai faWo saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuSutar da ita.

Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raWaWin mutuwar nan"

Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin Wina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji"

Ya tsuke fuska ya ce "A ta?aice dai, gaya mini magana ki ke yi"

Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daWe yana yi mini zafi"

"To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wata?ila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaWaici"
Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?"

Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka Waga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaWo da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da Wan abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko Waki uku ne mu koma"

Ya waro ido ya ce "?aki kuma? Ina Waki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki Wakuna huWu ne da falo biyu, ya yi mana kaWan"

Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai Waki biyu ne ni da Umma"

Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da ?yale-?yale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina ?ara yi muku godiya sosai da sosai"

Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa"

Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana ?aunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?"
Ta ce "A'a sai ka faWa Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta Waga masa gira tana murmushi. Ya Wan ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba ?aramin daWi nake ji ba. Ha?i?a larurar nan ta ?ara mini tsoron Allah da imani, ya ?ara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo ?arshe. SaSanin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na ?ara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah"

Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu"

Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaWi.

*****

Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ?alau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ?o?arinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ?asa suke kwana, ba ta taSa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ?an?ameta idan ciwon ya motsa
Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta ri?i karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ?arshe da ta yi wa ?aisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba Waya ta rikice, a kwana Wayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. ?ari ko na haila.
Tuni aka ?ara ?awata Wakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su bu?ata.
Yana banWaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ?oshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banWakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da Wakin ?ato ne sosai da sosai amma duk ?an?antar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba.
Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta.
Ya Wan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake Wakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ?ame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ?wace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta.
Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaSa ta Wauki fulo ta ajiye a ?asa ta kwanta.
Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin Wakin. Hayaniyar? halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin ya?i. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ?ofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ?ofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaWa shi. Sai dai wannan sautin ?arar ya hana ta ci gaba da bin sa.
Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta Waga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ?ofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya Wan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buWe ?ofar. Ya ri?o hannunta suka ratsa hanyar da take ba?i?irin mai Wauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren Wakin mai Wauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun Sullo wani guri kamar corridor.
ShimfaWaWWen yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya Waya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen.
Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba.
Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka"

"Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haWe yake? ?aya ba zai iya rayuwa babu Waya ba"

"Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa Soyayyu da ban gama fahimta game da kai ba"

"Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai."

Ta buWe idanunta tana ?arasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ?ara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiWe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu ?aisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ?ara hargitsa mata tunaninta.
Ta? tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata.

"Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta.
Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ?an?ame jikinta.

AREWABOOKS

?an?ance idanun ya yi, kasancewar fitilar Wakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta.

"Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba Waya babu daWi, ta kalle shi a tsorace.

"Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ?o?arin matsawa kaWan.

"Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?"

Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaWai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa"

Ya Wan fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya ri?o hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai"

A Wan ?ufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda ba?i da muni" Ta ?arasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faWi haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaSa ki. Dan Allah ni dai ki yi ha?uri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba ?aramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri Waya" Baki buWe take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi.

Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wula?anta ni. Ba ?aramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar Soye ba"

Ya ce "Haka ki ka ce?"

"Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata ?ara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login