Showing 108001 words to 111000 words out of 124905 words

Chapter 37 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

23

bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har ?afafuwansa. Da sauri ya fita daga Wakin ya koma falonsa yana mayar da numfashi.

****
Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi ha?uri, na daina" Ta yi maganar muryarta ?asa-?asa.
Gaba Waya zuciyarta babu daWi, har ga Allah ba ta son saSa wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?.
Ta yi shiru ta rakuSe a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya Wora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu Waya kuma yana tu?insa. Ta Waga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tu?insa.
Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa.
Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haWe take.
"Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban Sata miki rai ba"
Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai"
"A'a faWi gaskiya dai, na san ki da iyayi da ?a?ale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar"
Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai"

Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wula?anci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wula?ancinta akwai kyauta. Hannunta a buWe yake sosai da sosai gurin ungo.
Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez.
Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta ?i sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala.
"Cheri?, ba za ki ci abincin ba ne?"
Ta ce "Na ci"
"Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta ?o?arin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya.
Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raSe-raSe take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da ro?onta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haWe ta mafarki.
Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta Wan sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya mi?a mata hannunsa ya ce? "?araso mana" A hankali ta ?ara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A ?asan zuciyarsa ya din ga ro?on Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karSar ta a matsayin mata, kar ta sake yin?urin cutar da shi.
"Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya"
Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daWi da ya faru.

*****
Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar Wakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ?wallo tare dukkanin su akwai team Win da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ?o?arinta na ganin kowa ya samu abin da yake bu?ata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina.
Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaWai.
Bugun ?ofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buWe ?ofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karSa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta.
Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buWe idanunsa ya yin?ura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an WaWWaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yin?uri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daWin ji, cikin sauti mai ?arfi.
"Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo bu?atar sa, ko kuma ya yi ajalinka. ?if ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da Wanta na fari, suka fara fitowa a Wakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yin?uri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daWe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wu?a ta fara ?o?arin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ?afafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ?afa ya koma.
Sai dai ?ofar gidan a buWe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laSe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu.
Alhaji Fatuhu ya ?i sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba Waya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ?a??autawa amma ba ya iya taSuka komai, sai dai ya Suya ya yi kuka.
Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci.
Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faWa mini mene ne?"

"Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da ba?in cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba"
Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?"

"Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi ha?uri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ?yale shi.

Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata ha?uri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur.
Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata ha?uri tare da kwantar mata da hankali.

****
Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana.

Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan"

"A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini"

"Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah"

"Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka"

Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. ?an yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen Win a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma Waki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daWin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaSar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karSar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah.

Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace.
Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi Sarna a gurin yin sa ba ya ?arko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su.
Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun ri?o abin bata.
Ta fara yi wa Nene ?orafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ?arya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi ha?uri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karSa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ?ir?iro wani abu da zai amfani mata a ?asar nan, saboda tabattar da za ki iya ri?e mu?amin da aka baki"

Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba"

"Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba Win ba, dole a saba yanzu"

Haka Nana ta din ga jin tamkar an WaWWaure ta saboda takura.

Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata Wanta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana.

Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?"

Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu Wanmu. 'yan biyu sai kuka suke yi."

Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da Wayanku kamar raba ni da rayuwata ne"
Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?"

Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saSa Wanta ta yi Waki.

Baba gaba Waya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta Sata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba Waya ganin da ya yi mata ya ji WanWani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuWin aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah"
"Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana"
Gaba Waya Nana ba ta jin daWin hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karSar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru.
Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba.

****
Kwanaki huWu kenan, Alhaji Zailani kamar wanda aka yi wa asiri, ya kasa barin gidan, ga shi dare da rana tsorata shi kawai ake yi a gidan nan. Banda ihu marasa daWin ji, a Wauke shi a yi ta bugawa da ?asa.
Ko ya yi ta ma?abarta waWanda ya bayar a ?ungiyar asiri, suna ta kokowa da shi za su danna shi a cikin kabari su rufe, yana ihu yana ?o?arin fitowa, ko kuma ya ga su na ?o?arin kashe shi. Duk yadda ya so sarrafa tunaninsa domin ya je gurin Malam Gambo neman mafita, amma ya kasa jin sa kawai yake yi a wata Duniyar daban.
Tsawon kwanakin nan ya galabaita, ba ci ba sha, ba wanka ga kufcewar hankali. Yaje kitchen ya Waukko wu?a ya ri?e yana zazzare ido, da nufin yana ganin sun fito masa ya caka musu.
Sai dai Shukura ta bayyana, da wu?ar nan a hannunta, su na ta kokowa da shi, yana ?o?arin kar ya caka mata, saboda zuciyarsa na raya masa, itakaWai ta rage masa yanzu. Kawai ya hango Alhaji Fatuhu na ?ya?ayata masa dariya yana faWin "Yanzu wa ya yi nasara? Ka rasa komai Zailani. Ba ka da kowa, ka kashe kowa naka, dukiyar kuma ba zata amfane ka ba. Ni kuma da ka yi niyyar hallakawa, komai nawa ya dawo, ga shi kuma dole mutuwa zaka yi" Ya saki Shukura ya nufi Alhaji Fatuhu yana faWin "Na tsane ka, ba na ?aunarka. Ba zan taSa sonka ba kuma sai ka mutu, sai ka riga ni barin duniyar nan, na yi yadda nake so". Ya yi maganar yana cakawa Alhaji Fatuhu da yake gani wu?ar nan a cikin sa.
Jini ne ya fara fitowa ta bakin Alhaji Fatuhu,? ya ce "Zailani wannan shi ne ?arshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon ?yashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, ?eta na bushe na yi ba?i, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini bu?atar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka bu?atuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka ?i kulawa ka bani magani. Ga shi biyan bu?atuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga ?arshe mara kyau"
Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raWaWi ya ratsa cikinsa.
Abin da bai sani ba, da ya Wauki wu?ar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaWi, yana faWin "Na kashe ku Win, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma ?o?arina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faWar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi ?o?arin ?wace wu?ar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faWi ?asa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faWuwa bakinsa a buWe, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa.

(Ya hayyu ya ?ayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan ?arshe, Allah ka raba mu da mummunan ?arshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowa=?O?=?O?=?O?=?-?)

Abin ka da zamani na amfani da social media, a lokacin da Alhaji Zailani yake wannan tamSelen, aka samu masu ciro waya suka Wauki abin da ya din ga yi, suka sanya a shafukan sada zumunta, duk wasu shafukan an sauke videos Win, saboda abin da yake ciki na tashin hankali.
Tuni aka nemo jami'an tsaro, suka Wauki gawar Alhaji Zailani. Sagir ne ya fara gani a social media ya tashi hankalinsa a dugunzume, ya tafi gidan Alhaji Fatuhu ya yi sallama da shi.
Ya kalli Sagir ya ce "Lafiya kuwa? Ko Shukuran ce babu lafiya, na ganka kamar ba a nutse ba?"
Ya ciro wayarsa ya nuna wa Alhaji Fatuhu abin da yake faruwa. Sai da ya jingina da bango sannan ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ya daWe cikin mawuyacin hali, kafin ya daidaita nutsuwarsa ya dubi Sagir ya ce "Shukura ta gani?"
Sagir ya ce "A'a, ai babu waya a hannunta ma"
"To ka yi duk yadda za ka yi, kar waya ta shiga hannunta. Tun da Allah ya riga ya yi masa rasuwa, komai ya ?are. Yanzu muje gurin 'yansanda mu ro?e su a ta?aita lamarin binciken nan, a yi masa sutura a binne shi" Sagir ya sara wa zuciya irin ta Alhaji Fatuhu, a irin abin da Alhaji Zailani ya yi masa, yake cewa su je su karSi gawarsa a binne shi.
Sun sha fama da 'yan sanda, dan hana gawarsa suka yi, sai da aka je gidansa, domin zurfafa bincike. Sai dai da bincike yayi bincike aka din ga gano, abubuwa na tsaface-tsaface da suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login