Showing 114001 words to 117000 words out of 124905 words

Chapter 39 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

18

babu ita, Allah ya ?addara ba rayayye bane ba. Kuma da na san Jamila zata faWa ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi ha?uri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki Waga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya Soye miki. Kina kallo ya rasa Wansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun ba?in sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah"

Ayshercool
08081012143
Littafin kuWi ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic

103

Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa.
Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faWi tashin da ta din ga yi bayan auren ta.
A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaWu sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faWawa ita ma.
Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin Win" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu.
Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?"
Nana ta ce "?warai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar Win Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba Waya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi"

Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin ?oshin lafiya shi"

Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki ha?uri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a ?ungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin Win, Wan Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya"

Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na ?i yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. Wata?ila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa.
Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a ?irga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa Wana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya ?ara musu da Allah ya isa ba.
Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa.
Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matu?ar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taSa gani, sai ta nutsu sai ta tuna ?aisar ne ya nuna mata.
Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi.
Ummi ta kaWu ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har ?ungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba.
Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali.
Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos.
Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba Waya.
Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuWi masu tsoka, ya ce ta Wauki nata ta tura wa Uwani sauran.
Nana ta ce "Ni bai taSa gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki"
Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daWi a duniya"
Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taSa tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu Wan Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya ?ara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai.
Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faWan Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje.
Ta idar da sallar isha'i, tana ?are wa Wakinsu kallo, Wakin da ta din ga shan azabar a ?aisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, ?wa?walwarta ta taSu sosai da sosai.
Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade.
Da kanta ta Wauki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa.
Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani ?asan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon.
Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria.
Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a.
Yaya Atine da kanta ta wanko ?afa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba.
Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faWin "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faWa me ya kawo gaba Nana?"
"To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faWa"
Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faWa haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce"
"Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan"
Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita.
Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karSa a gurin Alhaji Fatuhu.
Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar.
Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta.
Ta yi murmushi ta Waga ta ce "Masoyi"

Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina ro?on Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya"

"Amin ya hayyu ya ?ayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana"

Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta"

Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen Win wayar, ya kwaSe fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo"

Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai.
"Wai zuwa ka yi ka Waukko shi?"

"Eh mana, karSo shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina"

Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata Wanki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta ?aunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wata?ila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haWu a can"
"To ai saura kwana uku na taho"

"Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria."

Nana ta Wan langaSar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?"

Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba Sata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke"

Sun daWe su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har ma?wabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma ba?in ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba.
Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt.

Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta Wauki wata ?ungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba.
Su na ta sallama a falo babu kowa, can ?asa-?asa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar.
Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruWe ta tafi ta rungume ta, "?awata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faWa".

Cikin mamaki Nana ta ce "?awata me ki ke yi a gidan nan kuma?"

Cikin za?uwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni"

"Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?"
"Su na Abuja"

"?awata kin canza kamanni, kin yi kyau kin ?ara ?iba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?"

"Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki"

"To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu Waya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma"

Ta juya ta nufi wata ?ofa, Nana ta din ga mamaki.

Jamila ta ce "Ita wannan Win a ina ki ka santa?"

"Gidan da muka yi gadi, a gidan suke"

Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya ri?o Shukura tana takowa a hankali.

Nana ta mi?e tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "FaWin Subhanallah"

"Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da Wana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba"

Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki Soye ba?"

"Babu abin da zan Soye, Nana ta riga ta san komai"

Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne"

Tamkar za ta shiWe ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna"

Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna ?aisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa? mutum abu a mafarki saboda su haWa faWa. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura?
Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta ha?uri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daWewarsa a duniya, duk tara kuWin da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan ?arshe, waWanda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a.

Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?"

Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce"

Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?"

Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da ?irjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa Wana sai Yusra. Da fari na Wauki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya"


AREWABOOKS



Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?"

Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah"

Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?"

"Na Maman Haidar ne"

"Ma sha Allah"

Kawai Yausra ta mi?a wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi.

"Haula" Ta furta a hankali.

"Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai Wauke da abin al'ajabi"

Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?"

"Ke kin sanmu akwai al?awari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana.
Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?"

Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita"

Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma"

Nan ma Nana ta daWe tare da su, sosai Shukura ta ji daWin zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daWin zuwan nasu.
Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi.

Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba Waya?"

Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya"

"To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke bu?ata muddin bai fi ?arfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya ?ara Waukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana ha?urin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya.

"Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba".

Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaSe baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba Winke-Winke.

Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin ?arfe goma za ki bi, zuwa can Egypt Win"

Nana ta ce "Kai da wuri haka, na Wauka za a kai irin kwanakin nan"

Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama"

Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, ba?in ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku ba?in ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaSe baki ko ki kushe"

"Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata ba?in ciki?"

Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login