Showing 6001 words to 9000 words out of 124905 words

Chapter 3 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

41

tashi tsaye, ya hau tattare kayan.
Rikicewa ta yi tana ?o?arin hana shi, amma ya ture ta ya Webe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buWe alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa.

Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki ro?a mini it??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a gafara, da kuma na zama ni ne mutum na ?arshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan.

Yana zuwa Wakinsa ya Wau biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta Sace daga hannunsa.
Bai razana ba, ya saka hankicin a ?asan fulonsa.
Bai yadda ya haWu da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana ?ule a Waki, ya kwana a kan fulon da jan ?yallen, wanda shi ma ya Sace daga baya.
Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faWiwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma ?ungiya sun shanye masa jini.

*****

Da ?yar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin Wa'ar da ka nuna."

"Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzu?e.

Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da Wa, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez "

Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan.

Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan i?irarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai ?arawa wuta fetur. Kaf faWin Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saWaka ne bamu sani ba".

"Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba ?arya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da Wa"

Matawalle ya ce "Wai wani irin Wa a na zaune ?alau? Yaushe Asal Win ta haihu ba mu sani ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, Wa na kuma ba shi da ala?a da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba Waya"

Sultan da ya fara harzu?a ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali"

Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daWe, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai".

Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka".

Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana.

"Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?"

"Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki"

Gaba Waya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba.

Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?"

"A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki Waga hankalinki ba, wata?ila Imam Hammad ne kawai yake neman ki"

Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?"

"Eh wata?ila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na ?warin gwiwa, da Balaraba ta faWa wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba.
Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana.

Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faWuwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin ?ofar tana rarraba idanu.

Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan.

"?araso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya.

Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie"
Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faWuwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara.

"Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro"

?o?arin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai.

Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan Win? Me ka ke ?o?arin yi ne haka?"

"Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye.

Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan Win daga ina take?"

Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taSin hankali sa saboda soki burutsun da yake yi.

Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka Waya kuwa? Ita wannan Win daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?"

Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne ala?arki da shi?"

Cikin ruWewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata ala?a tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta Waukko ni na yi mata, ni ban san shi ba"

Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah"

"Dan Allah ka yi ha?uri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai ?arfi na ?wace mata.

"Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice.

"Hammad, anya maganar Tafawa babu ?amshin gaskiya a cikin ta, na ga ba?a ce kamar ma ba 'yar ?asar nan ba ce? Meye haWin ka da ita?"

Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya ?i magana.

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi"

Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce Wakinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuWawa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taSa yi mata aka hana ta fita daga gidan.
Sai dai ba ?aramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan.
Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate.

Masu gadin ?ofar suka ?are mata kallo Wayan ya ce "MaraWi za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki"
Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba"

"Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka mi?a mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karSa suka buWe mata ?ofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan.
Ta ?udurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta Wauke Muhsin ta yi Nigeria.

Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba.
Ba ?aramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri.
Ta buWe envelope Win da aka ba ta kuWi sabbi kar a ciki.
Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaWan-kaWan.

Sun sha tafiya ba kaWan ba a hanya, kafin su isa MaraWi. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta.
Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura.
Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin ya?e.
Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta ?ara ?iba.
Nana da gabanta ke tsananta faWuwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?"

"A'a Nene kusan kwana huWu ba ta nan"

Gaban Nana ya faWi, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?"

"Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan"

"Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa.

Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta Wauka ba.
Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba Waya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama.
Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta.
Su ka kawo mata abinci, amma ta ?i ci, ta yi musu sallama ta Wauki kayanta ta fice.
Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene.
Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take.

Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira.
Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?"

Hajara ta ce "Bari na kira ta"

Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta Waga.

Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene"

"Na'am Nana, ki na lafiya?"

Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya Wagawa ina ku ka tafi?"

Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki ha?uri, baban Wan ya zo ya karSi Wan sa"

Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban Wan? Nene wa ki ka ba wa Wa na? Haka muka yi da ke Nene?"

"Dan Allah Nana ki yi ha?uri, nima fin ?arfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne"

"Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda Wa na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani Wa na"

Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karSi Wan sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga"

Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karSe shi?"

"Imam Hammad Jalaludeen Agadez "

"Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali.

AREWABOOKS

Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi ha?uri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?"

Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta ?udurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karSi Wan ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba Waya.', a kan ta tafi ta bar Wan ta, a wannan gidan.
Bugun ?ofar gidan aka din ga yi da ?arfi ana sallama.
Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da ba?i a waje"

Nana ta Wago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?"

"Ki je ki gani, ba?inki ne dai"

Nana ta yin?ura ta tashi ta fita, tana jan ?afafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai Waya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki.
Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci"
"Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta.

"Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke"

Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je"

"Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su.

"Tafiyar da Wan nisa, ki Waukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki"
Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?"

"Tafiya zan yi"

"Ki je ina? Wai ni, me ya haWa ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan Win Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?"

"Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haWaWWiyar mota ce, ta haWu ga kyau ga wani daddaWan sanyi da take fitarwa.
Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da Wan ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta.
Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin ?aton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate Win gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sau?i ba.
Sai dai hanakalinta baki Waya ya fi karkata, ga ta yi tozali da Wanta, ta san a halin da yake ciki.
Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan.

Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banWaki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta ?arasa.
"Ki yi ha?uri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta ?ara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin.
Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai.
Gaba Waya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya ?i tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaWai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani.
Jin ana turo ?ofar falon, ya sanya ta mi?e tana ?ara le?awa ko za? ta ga Muhsin.

Sai dai ba ta ga Muhsin ba sai baban Muhsin, yana sanye cikin ba?ar jallabiya, ya yafa hirami a kansa, bayansa kuma Mahmoudu ne, wanda ta fi sani da Habu.
Razana ta yi, ta tsaya ?yam tamkar an dasa ta, ta haWiye wani abu mai masaifar zafi tamkar wuta a ma?ogwaronta zuwa ?irjinta.

Ya kalli idonta, yana ?o?arin tantance wane irin kallo take yi masa, ya rasa ta ina ma zai fara.

"Ina Wa na?" Ta jefa masa maganar a zafafe tana huci.

Habu ya matso gaba ya ce "Nana, ki yi ha?uri ki ci abinci ki huta, ki samu nutsuwa, sai mu yi miki bayani"

"Bayani? Wane bayanin nake bu?ata bayan wanda na gani? Kun cuce ni, na ?arar da lokacina ban tsinana wa rayuwata komai ba, na tsaya na yi biyayyar aure na rabauta, ashe mutumin da nake tausayawa azzalumi ne, kuma mugu ne. Kun zalunce ni kun yaudare ni, kun Soye mini abubuwa da dama, ba dan ba ni hakkinku ba Allah ya saka muka haWu ba, da shikenan haia zan ci gaba da gararamba, ba ni da makoma. Ba zan yafe muku ba. Allah ba zai bar zaluncin da ku ka yi mini ba. Ka bani Wa na dan ba Wanka ba ne, baka da hurumi da shi Muhsin ba shi da uba na zaSi ya tashi da wannan tambarin da ya san ubansa azzalumi ne da ya wofantar da rayuwar mahaifiyarsa".

Wata irin suka maganganun Nana suke yi wa zuciyarsa, amma ya san koma Nanan ta faWa a kansa, ba ta yi laifi ba, ya kuma cancanci hakan daga gare ta.

Mahmoudu ya ce "Nana, kin san wa ki ke gaya wa haka? Mijinki ne fa?"

Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Wannan ba mijina ba ne, mijina Buzu ne da bai san waye shi ba, babu kowa a duniyarsa sai matarsa da ta nuna masa ?auna saboda Allah. Ba wannan mayaudarin da ya yaudare ni da cewa ni rayuwarsa ce ba, na yi asarar lokacina a kan nemansa ba. Ka bani Wa na ka haWa mini da takardar sakina na koma ?asata na sama wa rayuwata mafita" Ta yi maganar tana ri?e rigarsa tana kuka mai fallasar da dubban damuwoyin da suke binne a ?ar?ashin zuciyarta tsawon lokaci.

"Ma vie" ya furta a kasanlance idanunsa fal hawaye, yana kallon ?wayar idonta.

"Kar ka sake kira na da wannan sunan da na fi tsanar ji a rayuwata, Ni da nake mummuna, ba?a 'yar Nigeria da ba kowa ba hadima kuma baiwar da ake ci wa mutunci a gaban wanda yake yi mini i?irarin ni rayuwarsa ce yana ji kuma yana gani. Wata?ila ma alhakin iyayena ne ya kama ni, da na baro su saboda wauta irin ta soyayya da ?o?arin sama wa Wa na mafitar rayuwa. Ka bani Wa na ka sake ni na koma inda na fito" Ta yi maganar tana zare masa ido tamkar numfashinta zai Wauke.

Ya saka hannunsa yana ?o?arin kamo ta jikinsa, amma ta yi baya tana kai masa duka ta ko ina, cikin kuka tana faWin "Na tsane ka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login