Showing 9001 words to 12000 words out of 124905 words

Chapter 4 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

42

na yi nadamar saninka, rayuwata da kai bai amfana mini komai ba, ban taSa zaton za ku iya haWa kai ku cutar da ni haka ba, ka bani Wa na na gaya maka"
Mahmoudu sai da ya tsure, ganin yadda kamaninta har canzawa suka yi saboda faWa, idanunta tamkar ta tauna barkono saboda ja, ga ambaliyar da hawaye suke yi a fuskarta.
A Wan iya sanin da ya yi mata, tana da sanyin hali, banda tsiwa da ta kan yi wasu lokutan, bai taSa tunanin za ta iya burkicewa haka ba.
Shi kansa Imam Hammad sai da ya tsorata, yanayin da take ciki ya tabattar masa, sai ya yi aiki tu?uru kan ma ya samu ta saurare shi.
Ya shammace ta ya dam?e ta, ya nufi wata hanya da ita, ta din ga fizge-fizge, tana ci gaba da kuka da turjewa.
"Ki nutsu, kar ki yi mini asarar cikin da yake jikinki" Wani irin burki ta ci, cike da rikicewa jikinta na tsuma, ji take tamkar ba ta ji daidai ba, sai dai kafin ta tantance, jikinta ya saki ta yi baya za ta faWi ya ri?e ta.
Jikinta ya yi sanyi ?alau, sai hawaye da yake fita daga gefen idonta.
Da haka ya yi nasarar shiga da ita Wakin, ya kwantar da ita a kan gadon. Ya zare mata hijjabin jikinta.
Ya zura mata idanunsa, a hankali yake lumshe su yana buWewa a kan ta.
Ya kamo hannayenta a cikin nasa, ya sumbaci hannayen, sannan ya ce "Duk abin da ki ka yi mini, kuma duk abin da ki ka kira ni da shi, na cancanta, ban kyauta miki ba, na sani ban kyauta ba, amma ki bani dama ko sau Waya ne ma viee, sau Waya tak, ki bani dama na ce wani abu. Na san ba halinki ba ne, wannan ba halin Husna ta ba ce, amma na karSi laifina ki yi mini afuwa. Ban yi abin da na yi domin na zalunce ki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a ?irjinta yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin matsanancin sauri.

*****

Asal ce take ta shiga tana fita cikin takaici, bayan jin Nana shiru ba ta kawo Abincin safe ba, ga babu alamar na rana, kuma ba? ta gyara sashen ba. Ita a tunaninta tuni ta dawo daga kiran da aka yi mata a can gidan Sultan.
Takaici ya ishe ta, dan ta tsani zuwa Wakin da Nana take a ganinta ?as?anci ne, amma jin shirun ya yi yawa, ta fara duba kitchen ba ta nan, ta wuce Wakin Nana, saboda ya ci a ce ta dawo, duk da ba ta san kiran me Imam ya yi wa Nana ba.
Sai dai tana zuwa ta ga wayam, hatta kayan Nana babu sai katifarta.
Cikin tashin hankali ta fito ta tara su Balaraba da sauran ma'aikatan cikin gidan.
Duk su ka taru "Wai gidan uban wa yarinyar nan, mai yi wa Imam girki ta tafi? Tun jiya ba ta gidan nan, hatta kayanta ta tattara ta tafi ta bar gidan nan."

Cikin girmamawa Balaraba ta ce "Wallahi ranki ya daWe, bamu ganta ba, kin san ta koma cikin sashenku, ba ganinta ma muke yi ba"

"A ce kaf cikinku babu wanda ya ga fitarta?" Suka yi shiru, su na sauraren jarabar Asal.
Ta ?are musu rashin mutunci, ta sallame su.
Kai komo ta din ga yi tana tunanin ina Nana ta tattara kayanta ta gudu? Haka kurum ta din ga jin kamar akwai abin da Nana take ?ullawa ta bar gidan.

Tana komawa sashenta, ta tarar da tarin missed calls Win Tafawa.
Cikin rawar jiki ta bi kiran wayar, aikuwa ya Waga hasale.
"Wace irin wawuya ce ke, ina ta kiran wayarki amma kina can kina shashashanci ba ki Waga ba?"

"Dan Allah ka yi ha?uri, ina can wani uzuri ne"

"Uzurin banza uzurin wofi? Asal kin san me yake faruwa? Yau ni mijinki ya kalla ya ce mini na bincike ki, ke ce juya shi ba juya ba ne ya na da Wa"

Wani irin dumm maganar baban nata ta daki zuciyarta, ta ji wani banbarakwai, banda ba abokin wasanta ba ne, da ta ce ?arya ya sharara mata, kuma da sai ta hukunta shi a kan hakan"

"Na ji kin yi shiru?"

"To ai na kasa ganewa ne, wai wane Imam Win ne yake da Wan?"

"Wanne ki ke aure? Kuma kaf cikinsu waye ba shi da Wa ban da mijinki?"

Cikin kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace. Abba ya zan yi, ni Hammad zai yi wa haka? A ina yake da Wan?"

"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faWa kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji ?arshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?"
Ba ta iya tantance sauran abin da yake faWa ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taSa zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali.
Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya ?i.

Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla.

Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da Wa, Wan ma ba da buzuwa ba, 'yar wata ?asar bayan ya san me hakan yake nufi.
Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu Wan ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi"

Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu bu?atar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma"

Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo? wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru"

"Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taSa ganinta, a ina aka samo ta ne?"

Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waWanda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta"

"Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari.

Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau Waya wayar ba ta shiga ba.
Hakan ya ?ara jefa su a tashin hankali.

A hankali Nana ta yi mi?a, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin ?ara, saboda azabar yunwar da take ji.
Ta yin?ura da ?yar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata.

"Kin tashi?"

"Ina Wa na yake? Kuma waye ya ce ka taSa ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?"

"Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba Waya ya canza mata.

"Na haWa ka da girman Allah, ka bani Wa na, ka bani Wa na, ni ban sanka ba, Wana kuma ba Wan ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karSi yarona na koma ?asata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta.

Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?"

"Ni ban sanka ba"

"Haba?" Yayi maganar yana ?an?ance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya ?ule Nana.

"Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani"

"Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taSa yarda da shi ba. Ka bani Wa na na tafi"

Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi"

Daina ganewa Nana ta yi na wani Wan lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana Wauke da juna biyu ma Wazu. Ta kalli cikinta, ta Wago ta kalle shi, ya Wage mata girarsa Waya.

Ayshercool
08081012143
80
Gaba Waya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur.

A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?"

Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba Waya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta Wauki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta.

Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?"

"Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matu?ar zafafe.

Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta ri?e shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yin?ura da kyar, jikinsa babu ?wari, ya Wauki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar Wakin.
A Waya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin za?uwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?"

Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta ?i saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, ta?i saurarta kawai na ba ta Wan ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti Waya ta saurare ni. Babban abin da yake Waga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na"

Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi ha?uri, Sacin rai ne kawai ya sanya ta faWar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba"
Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?"

"Sosai ma, yanzun ma Sacin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce"

Ya koma ya kashingiWa yana kaWa ?afafuwansa.

Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa"

Ya Wan kwaSe baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta ha?ura ta yafe mini ta saurare ni."

"Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?"

"Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus Win da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe"

Mahmoudu ya ce "Tur?ashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?"

Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa.

"Au dariya ma na baka?"

"Eh mana, ni fa duk wannan masu sau?i ne, ban Wauke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya ?arasa maganar cikin damuwa.

"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta Wauki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka"

*****

Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi.
A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati Waya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka.
Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?"

Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki"
Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe"
"Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah"

"Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daWi sam"

"Na sani, ki yi ha?uri sai ki kwanta a side Win hannunki na hagu ko na dama"

Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana ?arami ya zo da tangarWa yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba.

Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sau?i sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu.
Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya ?wace masa.

****

Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na ?o?arin hana ta sukuni.
Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta.
"Me ki ke nema ne?"

Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake ?are mata kallo ne, ya sanya ta haWe rai.
"Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina"

"Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?"

Ya yi murmushi ya ce "Ki ci Win tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban.

HaWaWen bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon Wakin, ta Waga kai ta kalli agogon Wakin, ?arfe Waya da rabi na dare.

"Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa.

"Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado.
Ta yi ?yam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ?ara ?arewa Wakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake Wakin ya fara damunta.
Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa.

"Me yasa ki ka fito?"

"Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a ta?aice.

"Ohh yi ha?uri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haWe rai.

"Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman.

Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faWo ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu.

Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?"

Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?"

"?akin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki.

"To mu je can Win, nima ban ci komai ba, wata?ila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin"

Nana ta ?ara haWe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana bu?atar duk wani abu da zai ?ara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai".

"Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, Wauki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon.
Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi Wakin da aka ajiye ta.
Sosai ta fara ?o?arin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin.
Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta.
Har za ta yin?ura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ?ule ta, ta ?uduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan.
To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta.
Gaba Waya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta ha?ura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta.

Sai dai ta ?i yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yin?urin yi mata wani abin.

Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn ?aisar.

Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluSa da wani ba?in mayafi.

Ya kalli fuskarta da ke Wauke da damuwa ya ce "Ya dai?"

Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?"

"Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?"

Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login