Showing 84001 words to 87000 words out of 124905 words

Chapter 29 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

45

bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ?ara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai haya?i yake yi ya zubo mata ido.
Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa Wan uwanka ne, ya ?i magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau Waya bai yi magana ba.
Imam Zahradeen ya haWiye wani abu mai Waci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani.
Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala"
Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?"
"Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa"
Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan Waukko wayarsa ya Wan daddana, Hammad dai bai ce komai ba.

Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faWa, kuma ina neman afuwa da ni da waWanda zan faWa a cikin maganata.
Na ji daWi sosai da sosai da ka neme mu a keSantaccen guri kamar haka, ina ro?on ku rufa mana wannan asirin dan Allah"
Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan"
Ya ?arasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaWai ya shigo"
Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana.
Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?"
Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?"
"?aisar ya ce mini faWa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin"

Sultan ya ce "Waye Giyaz Win ne?"

Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daWe"

Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karSa"

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haWa baki da Wan uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haWa shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba Waya.
Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daWina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na Soye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar ?asar ba, abin dai ya fara taSa shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba"
Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka Soye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu ?iyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini Wa ya bar gida?"

Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi ha?uri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger"

Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri Waya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji ?amshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan ?amshin turaren ta, na ji ?amshin turaren wani ma.
Gaba Waya suka Waga kai, su na kallon Nana.
"Duk wanda yake ?amshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi.

A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye.
Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taSa shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke"
Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa.
Daga bisani ya Waga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka ?yale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda ?aisar ya yi maka"
Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin ?aisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka.
Ya kalli Nana ya ce "A gurin ?amshin turaren wa ki ke ji?"
Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen.
"Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta ?i magana tana jinjina yadda za su Wauki abin.
Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da ?arfin ikon Allah"
Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaWu da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya.
Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?"
N
Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai"
Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai"

"Bana bu?ata" Sultan ya faWa fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba.

Ya dubi Hammad da ya buWe idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba.
Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai.
"Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai.
"Ka na nan mu je mu dawo?" Ya Waga masa kai alamar eh.
Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi"
Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya Saci, ya yi mamaki ya kaWu matu?a da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a Satar masa da Wansa.
Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daWi ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo"
Tiryan-tiryan suka bi ta Wakin da su Nana suke zaune, suka buWe wannan ?ofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin.
Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a ?asa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba Waya ya rikice da ganin Sarkin baka.
Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana ?are wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo.
Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na ?waci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai ta?ama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga ?afarsa Waya ya ce "Uwar gijiyata, ?amshin turaren wa ki ka ce kina ji?"
Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "FaWi kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba"
Ta Wan sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal"
"?amshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin za?uwa.
Ta ce "Ni tsoron faWa nake, ba na son haWa husuma ne"

Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haWa husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba"

Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi Win, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuWin rawani, bayan ?amshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, ?amshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daWe da tafiya ba"
A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, ?amshin turarensa ne"
BuWe baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen ?arfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin ?aisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da Wakin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan"
Sarkin baka kawai ya nufi ?ofar Wakin, da Nana ta yi ta nacin a buWe ta, yana zuwa ya jijjiga ?ofar, amma ya ga ?aton mukulli a jiki.
A nutse ya ?are wa sauran ?ofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke.
Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?"

"Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa.

Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?"

Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa"

"Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki"

"Ni ba ni da wani aiki bayan buWewa da rufewa, da kula da ababen tarihi"

"Ka tabattar?"

Ya ce "Eh"

Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar ?aisar ta farko, Lanti ta haWa, da gudunmawar uban du?usa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da ba?a?en aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki Waya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka ba?in aljanin kanka, na haWa ka faWa da Giyaz, sannan na kashe ka?"
Ya din ga kallon Sarkin baka, ya?i magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata.
Mai gadin ya Wan ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga ?aisar a gurin.
Jikinsa na rawa ya nufi ?ofar Wakin, ya ciro wani mukulli ya buWe, yana buWewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya.
Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin.
Sarkin baka ya tankaWa ?eyar mai gadin nan, suka shiga Wakin. ?akin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye Wakin.
Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga.
Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana ?ara cika musu hanci.
?akin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake ha?owa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya.
Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaWan.
Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani.
?warangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin ?warangwal Win, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin ?aisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro.
Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro.
Sarkin baka ya ?arasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin ?warangwal Win nan, ya yi ba?i?irin saboda azabar wuta.
"Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido.
Ya yi shiru.
"Wallahi idan baka faWa ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar"
Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faWi wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin ?ara ta din ga tashi a cikin Wakin. Nana ta toshe kunnenta, ta dur?ushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa.
Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?"
Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni.
Nana ta fara neman ta burkice musu gaba Waya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi.
A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta.
Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani.

*****
Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi ?asa da murya sai magiya take yi masa.
Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki"
Cikin damuwa ta ce "Likita ka san Wan yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta ?i, shi ne aka gaya mini wata ?waya na je na karSo aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita."
Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?"
"Dan Allah likita ka yi ha?uri,? ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faWa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila.
Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba Waya, komai sai an yi mata. ?arshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya.

*****

Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga.
Sultan ya ?i kallon inda Zahradeen yake, zai Wauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taSa shi.

Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse.
Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi.
"Ranka ya daWe, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun Wazu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon.
Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taSa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?"

"Fita ki bani guri"

Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?"

"Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ?aunar ganinki, ki fita kafin na Wauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin Sacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?.
*****
Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a Wakin nan da suke, ta samu nutsuwa.
Da kyar ta samu ta iya yin salla.
Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buWe ?ofar Wakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaWan. Ta mi?e tsaye ya ?araso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya Wago ya kwantar da kansa a jikinta.
Nana ta ?ara janyo shi jikinta, ta ?an?ame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta.
"Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ?ara shigewa jikinta.
"Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ?an?ame shi.
"Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini"
"Ba komai Sayyid"
"To idan dai kina so na sosai, Wan bani sanyin mana" Yayi maganar yana Wan shafa jikinta yana murmushi.
Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya Wago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ?wari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?"
"A'a"
"Mene ne?"
"Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi ha?uri ka yafe mata"
Ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login