Showing 15001 words to 18000 words out of 124905 words

Chapter 6 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

26

daddare?"

Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haWe rai.
Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi ha?uri"
Ya mi?e ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.

Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya Wauki wayarsa ya kira Tafawa.
Tafawa ya Waga tare da yin sallama.
Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daWe"

"Barka dai" Ya amsa a ta?aice.

"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"

"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"

"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba Waya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.

A zaune ya tarar da Nana a Wakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu Wan kwali. Ta yi parking Win black natural hair Win ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa ri?e da ledoji, ya ?arasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaWai ko?"

"Dama can ai nikaWai Win nake rayuwata"

Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni Win ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta Wauki Wan kwalin kayan, za ga Waure kanta. Ya janye Wan kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"

"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taSa tasiri a kaina ba, ka bani Wana kawai na kama gabana"

"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci"

Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni Wa na?"

"Kin ci, amma ba kamar yadda nake bu?ata ba, sonake ki ?ara ?iba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ?oshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."

Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ?irjinta na bugawa da sauri da sauri.
Ya zauna a kusa da ita ta Wago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya Wago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.

Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"

"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daWi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taSa aikata shi sai ni."

Ayshercool.
08081012143
81
Nana ta taSe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haWa ni da masarautarku, kawai a bani Wa na na tafi"

Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"

"Eh" ta faWa tana kawar da kanta gefe.

"Shikenan, zan ?ara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu Satawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan ban?ara na aikata, domin ganin ba ki suSuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata Win na nufin ?ara miki ?iyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguWa baki ta sake kawar da kanta gefe.
Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau Waya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da ro?onsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wula?anci ne aka yi masa.
Ganin ya ?i tashi ya bata guri, ya sanya ta Wago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta.
Ta sake kai hannu ta Wauki Wankwalinta, amma ya jefa shi bayansa.
Wannan kallon da yake ?an?ance ido ya fara yi mata, ta ?ara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi.
Ba?i ?irin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma ya?i barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi.
Duk wani abu da Nana za ta yi ta ba?anta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.

Sai da ya bar Wakin ta samu ta ci abinci, ta tura ?ofar Wakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ?ofar dan kar ya shigo mata.
Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.

*****
Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharSeSiyar wu?a tana, ya ba ta jaririnta.
Ya din ga gudu yana ihu, ya Wan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wu?ar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faWin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na Wauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haWa uban gumi.
Ya kalli agogon Wakinsa ya ga ?arfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haWa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya sha?a masa kuWi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin.

****
Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango ?aisar, lulluSe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ?asan mayafin yana rubutu a kan wani littafi.

Ya Wago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa.

"?aisar"

"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?"

"A ina?"

"Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluSe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?"

"Na san shikaWai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye.

"In ji wa? Akwai Aljanu masu ?arfi da suka fi ni ?arfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daWin rayuwar kaWaicina da litattafaina da haWa magunguna na"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?"

"Sai na girma"

"Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?"

Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki Wakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki Waukko ki kawo mini"
Nana ta ce "To" Ta nufi Wakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa.
Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai.
Ta ga wanda ya ce ta Waukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta.

"A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta.

Ya buWe baki ya ce "Ban taSa ganin halittar da na tsana a doron ?asa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ?arar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi.
Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ?ona ta, amma ta ji shiru. Ta buWe idanunta a hankali ta ga ?aisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ?ona shi, ya faWi a gefe jikinsa yana haya?i.
Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "?aisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ?onewar da ya yi yanzu.
Giyaz ya ?araso kan ?aisar da sauri, ya saka hannunsa ya Wago shi, amma ya ga jikinsa ya saki.

"Wallahi muddin Wa na ya mutu sai na kashe ki har lahira"

Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da Wansa da ?o?arin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ?o?arin cutar da shi ka ke. ?aisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ?o?arin taSa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta.
Ta buWe idanunta a hankali cikin sheshshe?ar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya ri?e ta gam yana kallonta cikin tausayawa.
Ta yin?ura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki Wan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na Wauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina ba?in ciki da hakan"

"Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba"

Ya Wan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa.
Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata Wakin, dama kukanta da sheshshe?arta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je Wakin nata.
Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita.
Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki Soye musu komai saboda makomarmu"

"Ni ba wata makomarmu, kawai Wa na za a bani na tafi"

Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karSa ba, sai kuma ta karSa ta ce "Na gode"

Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a Wakina, akwai mayukan shafawa"

"A'a ina da man da zan shafa"

"To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ?auna" Ta murguWa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez".

"Sai ka je gurin Gimbiya hamsha?iya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba.
Ko da ta yi yin?urin juyowa, sai jikinsu ya haWu, sam ba ta san ya ?araso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ?araso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina.
Ya saka hannunsa ya zagaye ?ugunta, ?irjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ?arara a fuskarta.

"Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sar?e ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina Waga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna.
Yana murmushi ya ce "Na taSa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.
"Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma"

"Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai Wauke.

Ya cika ta ya bar Wakin, ta zauna tana sauke numfashi.

*****

"Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai"
"Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya ?i ci ya ?i cinyewa mene ne yake faruwa ki ke Soye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita.
Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi ha?uri ki ?yale ni, ni babu abin da yake damuna"

"Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?"

"Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai ?ona zuciya.

"Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana ?ara zazzare wa Jamila ido.

Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshshe?ar kuka.

"Za ki gaya mini ko sai na sha?e ki?"

Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni"

Wata irin mummunar faWuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ?irjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro.

"Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshshe?ar kuka ba ta yi magana ba.

Mama ta sha?e Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya"

"Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ?unar rai. Ta yi ?wafa ta fito daga Wakin su Jamila.

"Me yake faruwa ne?"

"Babu komai, jikinta na shiga na duba"

Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken haya?in da ki ke yi mata duk ba ne ba"

Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ?i ci ya ?i cinyewa, amma za mu koma"

*****
Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ?andagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba.
Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta.

Ya ?araso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ?uri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta.
A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji"
Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ?are mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai ba?ar fata ce.
Idanunta manya sexy eyes, farare ?al da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta.

Ya numfasa ya ce "Ina ?ara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki"

"Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?"

"Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaSar ba". Ya ciro ni?ab ya saka mata.
Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa.

Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka Wauka?"

"Eh ni na Wauka, kin ?i saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya.
Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki.

Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karSar Wanta, dan ko kaWan ba ta sha'awar gidan nan, Wan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan.

Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faWuwa, haka kurum take jin ba ta ?aunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da ?aisar yake ciki.

Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana Waga musu hannu. Ya ri?e hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba Waya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya ri?o hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar ni?ab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba.

Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga Wakin zama na musamman na cikin fadar Sultan.
A can suka tarar da Sultan Win, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu.
Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ?afafuwanta, gabanta ya din ga faWuwa. Duk ta kowacwa kusurwar Wakin, akaai na'urar sanyaya Waki, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login