Showing 39001 words to 42000 words out of 124905 words

Chapter 14 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

38

na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar ?wa?wawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane.

"Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaSe ki da Wana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu Wora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci"

"Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka.

Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haWe bakinsa da Nana.

Babu tsammani aka banko ?ofar Wakin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni.
Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaWa mata gangi.
Ba ta taSa tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taSa hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta ba?ar fata da ba ?abilarsu ba.
"Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faWa cikin wani irin ?araji mai razanarwa.

Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba Waya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana.
Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu Wa, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali.
Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya Waga mata hankali ba.
Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san ala?arsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai.

"Kar ka taSa ni, kar ka ?araso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi ?arya ka ke yi? Ka haWa kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan ?as?antacciyar ?azamar matar? Na zaSo ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka Soye ta ku ke lalata."

Cikin azama Hammad, ya dan?o hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna ?ofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cheri? zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba"
Cike da ba?in ciki take kokowar fizgewa cikin ?araji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daWin halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na ?asa?antar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza"

Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu,? kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi"
Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali"

AREWABOOKS

Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba Waya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna.

"Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai Wauke da nannauyan ba?in ciki da tashin hankali.
Dam?ar hannun Asal ya yi, ya buWe ?ofar suka fita tare.

Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge.

"Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana"

"Ba zan saurare ka ba, ba na bu?atar duk wasu kalaman yaudara da ?arya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka Soye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daWin halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haWiye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini ?azafi"

Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya ?ware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da ?o?arin fizgewa, amma ya ri?e ta gam.

"Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun Wa ana yi, an ce ka na da Wa da a ?alla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana i?rarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka Wauki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita"

"Ban taSa cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faWa kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan Win ki ji komai daga bakinsa.

Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banWakin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta ?ura wa kanta ido a mudubin banWakin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon ?as?anci, da bautar da ita ta ?arfi da yaji, saboda tana da kuWi da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haWiye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru.
A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga Wan jaririn Wa na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi ?arfina. Allah idan sun fi ?arfina ba su fi ?arfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini Wauki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da Wa na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini Wana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. ?aisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da Wa na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faWa ai Allahan yana ji yana gani.
'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma ?ara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa.

Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai.

Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba Waya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara.
Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faWin gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaWai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da ala?a da samun sau?insa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba Waya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki.
Gaba Waya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana ?o?arin goyon bayan Wansa ne.
Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faWin "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai.

Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba.

Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha Waya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau Waya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba.

Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a ?asa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger.
Ta fara ?o?arin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faWo daga aljihun rigar. Ta Wauki takardar ta yi shiru tana kallon takardar.
Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leSensa yana jujjuya kansa.

"Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai Wauke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi"

Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?"

"Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya ?arasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. ?wan?wasa ?ofar Wakin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirri?eta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje.

Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ?ofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu.
A rikice suka ?arasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?"

"Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ?wa?walwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a"

Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka"

Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?"

Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce"

Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne"

Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam"

"Hamud, dan Allah ka Wauke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba."

Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daWe, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa.

A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lan?wasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ?arasa da sauri yana faWin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taSa jikin Nana garin ?o?arin SanSare shi daga jikinta.

Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi.

"Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ?arfin hali.

"Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a"

Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa"

A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah"

Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ?aramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga Wan nasa a cikin wannan yanayin.

Sai kusan ?arfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba Waya. Ya yin?ura ya tashi zaune yana kallon Nana.

Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji Win?"

Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini"

Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi ha?uri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta.

Ta Wago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba"

Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ?ofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?"

"Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye.

"Ina bu?atar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane Wan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina bu?atar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buWe ?ofar nan, suka ?ara ratsa duhu suka fita wannan corridor.

Yau ma saharar ta gani, gurin ya Wauki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce.

"Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani"

Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su"

Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku"

"Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daWi"

Ta Wan shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare.

Ta Waga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaWaituwa da son sanin abin da gidan ?unsa.

Tana jin kewar ?aisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko ?asa ta daina ganinsa.

Ta lumshe idanunta ta buWe, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matu?ar fargaba a kan irin karSar da za a yi mata idan ta koma.

"Ma viee"

"Na'am Shugabana"

"Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba"

Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?"

"Sai an wa Muhsin ?ani"

Ta ce "Babu rana kenan"

"Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana ?ara ?an?ameta.

Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faWa suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata.
Ta kira Hasna a waya, Hasna ta Waga tana "FaWin Gimbiya Asal, kwana biyu"

Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faWi ta ce "Meyafaru?"

"Hasna wai Hammad yana da Wa"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Wa kuma kamar yaya?"

Cikin kuka ta ce"?a dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini ?arya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta"

Hasna ta ce "Eh haka ne"

"Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taSa cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana ?ara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta.

Hasna ta Wan yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi ha?uri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri Waya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na Wauka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki"

"Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taSa kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan ba?ar yarinyar.

Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba Wayansu, mai maganin ya ?araso.

Hammad ya ce "Waye mai maganin?"

Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai sa?on da ya bani kenan"

"Ni fa ba na bu?atar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido.

Ta basar da shi, ta Wan yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga Wakin da suke. Sai dai wani sur?u?in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login