Showing 117001 words to 120000 words out of 124905 words

Chapter 40 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

46

ba?in ciki"

Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin.

****
Nana tamkar idanunta su faWo, saboda rarraba idon neman Sayyid. Sai kalle-kalle take yi kamar ma dai a tsorace take.
Fararen fata da ba?a?e, sai kai wa suke yi suna komowa.
"Kamo ta nan" Yayi maganar yana rungumota, ta zabura a tsorace.
Ya yi dariya ya ce "Matsaoraciya kawai, sai rarraba ido ki ke yi"

"Shi ne zaka tsorata ni, da na yi ihu fa?"

"Sai a yi miki dariya" Yayi maganar yana jan karan hancinta.

Ya mi?a mata hannu suka gaisa, ya ce "Ya mutanen Nigeria su na lafiya?"

Ya ce "Lafiya ?alau Alhamdillah, su na gaishe ka"

Ya ce "Ma sha Allah, in sha Allah da mun dawo, zamu sake zuwa tare, na gaishe su"

Ya ri?e hannunta, suka shiga taxi suka tafi.

Katafaren Hotel ne, suka sauka a ciki, gaba Waya Nana jin ta take yi, kamar ba ita ba, kamar mafarki take yi.
Ya yi order Abinci, aka kawo mata, ta yi wanka tayi salla.
Abinci kawai ya iya bari ta ci, ba tare da bata damar hutawa ba, ya ce sai ta biya shi kwanakin da ta yi a Nigeria ba ta nan.
Nana dai da ya ishe ta, kawai ta hau kuka, ya lumshe idanu yana ?are mata kallo.
Ya yi murmushi ya ce "Ke yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba abin da ki ke yi mini?"
"Kai dai za ka ji kunya, haba daga zuwana?" Ta yi maganar tana hawaye.

Ya tashi zaune yana le?a fuskarta, fafur ta?i kallonsa, ?o?arin kare fuskarta take yi, amma ya?i bata damar hakan. Ya ce "Ni fa zuwan nan namu da biyu, honeymoon muka zo"
"Wane honeymoon, wanda ka yi a Agadez bai ishe ka ba, sai ka dame ni, daga zuwana ni dama ban zo ba"

Hammad ya ce "Gaskiya na Agadez bai ishe ni ba, na fuskanci ?anin Yarima da rigima ya zo, lokacin Yarima ai ni ake lallaSawa ina jan aji. Idan kuma ba haka ba, mutum ya musa na tuno wa mutum abin da ya aikata" MurguWa masa baki ta yi, tana goge hawayen fuskarta. Shi kuwa ya saka ta a gaba, ya din ga yi mata dariya.
Sai da suka shafe kwana uku, da zuwa, har sai da Nana ta manta da abin da ya kawo su, sai dai ta ci abinci Hammad ya yi rigimarsa.
Kwana na huWu suka bar garin da suka sauka, suka tafi garin da malamin yake. Kafin su bar garin, sai da ya zagaya da ita ta ga gari sosai da sosai.
A can garin ma da suka je, a Hotel suka sauka, sai dai a wannan karon ta tarar da Sultan da Matawalle su ma duk su na Hotel Win kowanne Wakinsa daban amma.
Sultan kamar ya ga 'yar cikinsa, ya din ga tambayarta ya ta baro 'yan uwanta da iyayenta.
Washegari da safe suka hau mota, suka tafi gidan mutumin.
Balarabe ne, sai dai yana jin turanci, tun da suka je gaban Nana ya tsananta faWuwa.
Ya yi musu kyakykyawar tarba, sai dai Nana ko buWe bakinta ta kasa yi, balle ta gaishe shi.
Ya kalli Nana cikin harshen turanci, ya ce "Sannu da zuwa"
Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ta Sangaren Hammad ma, jikinsa sai tsuma yake yi.

Da larabci suka din ga tattaunawa, Sultan da mutumin, tana iya fahimtar abin da suke faWa amma ba duka ba.

Ya mi?e tsaye ya kalli Hammad, ya ce ya biyo shi, da shi da Sultan.

Nana ta koma gefe ta rakuSe, ta din ga tunane-tunanen da ita kanta ba ta san daga ina take yin su ba.
Gaba Waya ba ta cikin nustuwarta, ba ta kuma iya tantance abin da take ji. Wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, sannu a hankali ta din ga jin wani irin ihu mara daWin ji.
Ta saka hannu biyu ta toshe kunnuwanta, ta din ga jin tamkar ana Sarar da kaya, ko ana kokowa da wani irin abu mai nauyi.
Har azahar ta yi, Nana ba ta ga fitowar Hammad ba. Aka bata ruwa ta yi alwala ta yi salla, aka kawo mata abinci, amma ta kasa ci, hankalinta a tashe ba ta ga Hammad ba, ga kuma yanayin da take ji a jikinta mara daWi.
Sai wajen la'asar, sannan aka fito da Hammad, Sultan ya ri?o shi idanunsa a lumshe.
Hankalin Nana ya tashi, ta mi?e tsaye tana faWin "Lafiya meya same shi?"
Sultan ya ce "Babu abin da ya faru, ki kwantar da hankalinki zai wartsake in sha Allah"
Dattijon nan shi ne mai maganin, ya fito ya jagorance su har wani Waki.
A ciki aka kwantar da Hammad, sai ajiyar zuciya yake yi, jikinsa yayi jawur hatta gashin kansa a hargiste, rawaninsa ma da babbar rigarsa a hannu Matawalle ya fito da ita. Ta din ga mamakin, yaya aka yi haka? Me aka yi masa ya fita daga hayyacinsa haka. Sai warin wasu mayuka yake yi, da ta gaza gane kowane iri ne.
Su Sultan suka fita yin salla, Nana ta ?arasa kusa da Hammad, ta taSa shi, ta shafa gashin kansa ta ce "Sayyid, Sayyid ka na ji na kuwa?"

"Mmm" ya amsa da kyar.

"Mene ne, me ya yi maka?"

Ya girgiza kai ba tare da ya buWe idanunsa ba.
Da su Sultan suka dawo, suka tarar da ita hankali a tashe.
Matawalle ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zai wartsake a hankali in sha Allah. Ya ce sai dai mu kwana a nan, mu ga yanayin jikin nasa tukuna, sannan kema ya duba ki"
Kasancewar mutumin babban malamin ru?iyya ne, da magungunan musulunci yana da gurin saukar ba?i, saboda yadda ake zuwa daga garuruwa gurinsa.
Sannu a hankali Hammad ya dawo hayyacinsa, har ya yi salla ya ci abinci, amma kana kallonsa zaka gane ba ya jin daWi. Nana dai ba ta iya tambayarsa komai ba.
Sultan ya tambaye ta, za ta iya kwana da shi, ko a bata wani Wakin, ta ce zata iya zama tare da shi.
Ba da wani shiri suka taho ba, kasancewar ba su san za su kwana a gidan ba. Gidan Sarkin baka ne ya faWo mata, da irin gane-ganen da ta yi a gidan.
Ta nemi guri ta kwanta a kusa da Hammad, ta ji ya matso da ita jikinsa, ya ?an?ame ta.
Kamar wadda ta farka daga bacci, haka ta ganta a Libraryn ?aisar.
Sai dai gurin ya Wan yi duhu, sheshshe?a ta din ga jiyowa daga wani guri, ta tafi a hankali tana sanWa. Tana buWe ?ofar da take jiyo sautin ta ga wani irin ?aton guri, ?aisar na dur?ushe a kan gwiwoyinsa, ya saka wani abu dogo da ba ta san ko menene ba a gabansa, yana wani irin kuka. Da sauri ta ?arasa gabansa, ta gefen mayafin take hango wani abu ba?i ?irin kamar an ?ona itace.
Sandar Giyaz ta gani kwance a gefen abin da yake gaban ?aisar Win, a razane Nana ta ce "Giyaz ne ya mutu?"

Kawai ?aisar ya sake fashewa da kuka, yana yaye mayafin da ya rufe Giyaz. Ya yi wani irin ba?i kamar dutse yayi gobara. Ga wani irin tsawo mara misali da yayi, sai gemunsa da ya ?ara wani irin tsawo. Nana ta ja da baya a razane. ?aisar ya kifa a kansa yana wani irin kuka.
Ji ta yi an girgiza ta, ta buWe idonta, ta ga Hammad ya tsare ta da ido ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Kasa magana ta yi, sai ajiyar zuciya da take yi kamar za ta shiWe. Duk da jikinsa babu ?wari haka ya din ga rarrashinta, yana tambayarta mene ne, amma ta?i magana. Da kyar ta tashi ta yi sallar asuba. Aka kawo musu abin karyawa, amma ta ?i ko kallon abincin. Da ta tuno yadda ?aisar ya rungume Giyaz yana kuka, sai ta hawaye yana zubo mata.
Hammad ya fita daga Wakin, bayan mintuna kaWan, ya dawo ya ce ta taso. Jikinta gaba Waya babu ?wari, ta tashi ta bi bayansa.
Ko su Sultan kasa gaisar da su ta yi, tana ganin Hammad ya nufi hanyar da aka bi da shi jiya, ta ja ta tsaya.
Ya ce "Meya faru ne? Mu ?arasa mana" Ta girgiza kai ta ce "Kai dai ka je, ni ba zani ba"

"Saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

"Ma viee, ki yi ha?uri babu abin da zai faru in sha Allah, magani za a yi mana mu rabu da wannan larurar, mu samu kwanciyar hankali mu zauna lafiya mu rayu kamar sauran mutane"

Ta ce "Ni ba na so" Ta yi maganar tana kuka.
Sultan ya ?araso ya ce "Meyafaru ne?"

"Ni ba zan je ba, a ?yale ni ba na so"

Da gaske Nana ta kafe, ta ce ba za ta shiga ba, Matawalle ya shiga ya yi wa mutumin magana. Mutumin na fitowa ta juya zata arta da gudu. Hammad ya ri?o ta, ya ce "Amsy me yake damunki ne?"

"Wallahi ba za a kashe ?aisar kamar yadda aka kashe Giyaz ba. Wallahi ba zan je ba. Da ya kashe shi gara ni ya kashe ni"

"Asma'u, kin zaSi aljani a kaina da rayuwar aurenmu kenan? Ki nutsu mana"

Hammad ya yi mata magana cikin tsawa.

Tana kuka ta ce "Wallahi ba zan tsaya ba, shi ma mai rai ne, kuma yana son rayuwarsa, ba zan tsaya a kashe ?aisar ina gani ba"

Mutumin ya tambayi Hammad, me take faWa ne.

Hammad ya yi masa bayani, cikin harshen turanci, yake gaya wa Nana, ba shi ya kashe Giyaz ba, taurin kai Giyaz yayi shi ya kashe kansa da kansa, amma ba shi ya kashe shi ba"

"Ni dai ku ?yale ni, zamu rabu a hankali, idan na bari aka kashe shi a dalilina ban yi masa adalci ba, ko ya cutar da ni ta wani bangaren bai cutar da ni ba. Ni dai kar a kashe shi dan Allah."

Sultan ya sassauta murya ya ce "Kina ji, ba kashe shi za a yi ba, za yi miki tsakani da shi ne ya rabu da ke, amma ba kashe shi za a yi ba. Wancan Win ma ba shi ya kashe shi ba, shi ne ya kashe kansa dan kawai an nemi ya musulunta ko a ?ona shi"

Nana ta girgiza kai ta ce "?aisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta ?arasa maganar har da haWa hannayenta biyu alamar magiya.
Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana Wauke da juna biyu.
Nana tana da matu?ar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba.
104


Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban ha?uri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta ?i saurararsa tana cewa ita ba za a kashe ?aisar ba.
Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita.
Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta.
Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faWa, ko kuma ya ce zai takura ta.
Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaSi sosai da sosai, ta ?i cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga ?aisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wata?ila sai ma ta'azzara wasu abubuwan.
Tun bayan tariyarsu, ba su taSa yin faWa ba sai a wannan lokacin.
Da daddare ma a ?asa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya ?i kula ta.
Gefe guda ta hango ?aisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar.
Jiki a sanyaye Nana ta ?arasa gefensa ta zauna ta ce "?aisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matu?ar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka ha?urin rashin mahaifinka da ka yi".
Ya Wan jinjina kai ya ce "Ha?i?a mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji ba?in cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na ro?a masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya ?ona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi ha?uri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka ?addarar"
Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?"
Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai ?alubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma Sata gari, kuma ku na da na kirki da Sata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faWa, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya Waya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata Wayanmu ya zamana yana cutar da Waya ba, ko amfani da Waya gurin fin ?arfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun ?irji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda Wan Adam yake yi"

?aisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Ha?i?a nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu sa?onni da yakamata bil adam ku sani. Na ?aru da abubuwa da dama ta Sangarenki. Tabbas ba na cikin ba?a?en aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba Waya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna.
Na ji daWin samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya Waya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin ?iftawar idanu zamani yake canzawa.
A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daWe da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata Sarna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci.
Rayuwa tare da ke, ya ?ara haska mini juriya a cikin ?addara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin ?addarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza Wabi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a.
Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taSa tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na Waukar fansa a kan ki.
Ha?i?a wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaSar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi ?o?arin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake Waukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika al?awarin da na Wauka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki al?awarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma Wabi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon ?arnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi ?o?arin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama.
A ?arshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wata?ila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A ?arshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada.
Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin ?addara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana ?in ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi.
A ?arshe ina ro?on dan Allah ki yafe mini,?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login