Showing 24001 words to 27000 words out of 124905 words

Chapter 9 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

21

Ba zai yiwu na Waukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da Soyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ?arshe ya rasa ransa gaba Waya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar.
Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faWa, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi.
Akwai abokan hulaWarmu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaWina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa.
Haka na Sad da kamanni da Soye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba Waya.
Sai dai aka Soye lambar asusu, aka din ga turo mini kuWi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taSa kuWin da ake turo mini saboda ban san na waye ba.
Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi ha?uri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez.
Na samu wani gida da abokan hulWata suke gadi, muka shiga cikinsu.
Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba Waya al'amuransa sun ?ara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ?ure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taSa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi.
Tsawon wannan lokacin ban taSa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi.
Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin Wakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a Wakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan Soye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ?aramin ?arfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaSawa ina bayar da ha?uri, amma ya ce na biya masa sadakin.
Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka Waura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad.
Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan.
Na sani akwai abin da ta din ga Soye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka Wauke mu daga Nigeria bata taSa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi."

Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daWi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raSa Wa na da wanda zai cutar da shi"

"Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an Wauke mu daga Nigeria"

Sultan ya jinjina kai ya ce
"Kuma haryanzu baka san waye ya Soye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karSi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba"
Sultan ya Wan yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan"
Mahmoudu ya Wan yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta Wauke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faWi cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi.
Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ?ara rincaSewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad Win ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya.

*****

"Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai"

Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuWin ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci."

"Ni k ?yale masa kuWinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani Wa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi"

Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karSi Muhsin, ki koma Wakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana"

Nana ta Sata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaWan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension Win da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake bu?ata"

Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taSa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaSa abin da ya fi alkhairi ".

Nana ta yi shiru, gaba Waya magungunan da Nene take bata, bata taSa kawo na mene ne ba.
Gaba Waya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ?ara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaSa rayuwarta take yi a hankali.
Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba.
Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ?amshin na Wakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta.
"Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buWe idonta, kamar yadda ta yi tsammani a Wakin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai.

Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?"

"Lafiyata ?alau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame"
Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin ha?ura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaWarta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake ri?o hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daWi mana"

"Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar Wa mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa"
"Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka Waga ni"

Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaSa ni ki ke yi. Asmy"

"Na'am"

"Yanayin akwai zafi sosai, ina bu?atar sanyi"

"Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi"
Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaSa Nana, da daWaWan kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba.
Ta daWe ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan Wakin.
Mararta ta ?ulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa.
Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. ?arshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin ?aisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba.

Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da Wuminsu sai ?amshi suke yi.
Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?.
Tana cikin Waki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya.
Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa"

"Dan Allah Umma ki yi ha?uri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi"

"Su neme ta, me ta yi musu?"

"Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta"

"Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini Win ne?"

"A'a Umma dan Allah ki yi ha?uri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba Waya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?"
Gaban Nana ya yi wata irin faWuwa, ta mi?e tsaye tana sauraren me Nene za ta ce.

"Zan neme ka zuwa anjima, sai na yi magana da ita, idan ta kama sai dai ku bi ta can Nigeria gurin iyayenta, ku ro?o alfarmarsu, ku Waukko ta"

"Umma, Nigeria kuma ta koma? Shikenan mun kaWe."

Ta ce "Ka dai saurare ni na ce" Ta kashe wayar. Tana shiga Wakin ta ga Nana a tsaye.
Nene ta ce "Za ki je kenan?" Nana ta yi shiru tana kallon idon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Ai ba zan hana ki ba. Ban sani ba ko daga nan ki karSo takardar sakin naki. Ki haWa abin da ki ke bu?ata, zan kira shi na gaya masa su zo su Wauke ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kina ganin idan na je, ban yi wauta ba ko kuma tarko suka yi mini ba?"

Nene ta ce "Sam, ba na tunanin hakan, ba za a haWa kai da Mahmoudu a yi miki haka ba. Ina yi miki fatan nasara."

Nana ta ce "Nene mu tafi tare mana"

Nene ta girgiza kai ta ce "A'a wace ni, ni da mijina bawa ne, ba sa ?aunata ba sa son ganina. Ai ke ciwon ido ce, babu yadda suka iya da ke. Mussaman da yake Muhsin a tsakanin ku."

Nene ta yi ba ta ?warin gwiwa, Nana kuwa addu'a take yi, da fatan Allah ya sanya ba Giyaz ne ya ci gaba da azabtar da shi ba.

Bayan la'asar sai ga Mahmoudu a wata hamsha?iyar mota zai Wauki Nana. Nene ta yi masa kashedi sosai da sosai a kan ya ji tsoron Allah, kar a haWa kai da shi, a cutar da Nana. Ya yi wa Nene al?awarin hakan. Nana ta Wauki kayanta Nene ta raka su har bakin ?ofa, tare da yi wa Nana fatan alkhairi.
A motar Mahmoudu ya ci gaba da ba wa Nana ha?uri ya ce "Idan mun je, kar ki nuna musu fusata ko jin haushin sun ?wace miki Wa sun kore ki, bamu san abin da Allah zai yi ba idan mun je tare da ke. Wata?ila rashinki ne a kusa da shi da abin da aka yi miki ya sanya shi a wannan halin. Nana kwanan Hammad takwas ko ruwa bai shiga bakinsa ba, yana sume kawai. Ki yi ha?uri da abubuwan da suke faruwa mu je mu gani ko Allah zai sanya a dace." Nana ta jinjina masa kai, ?asan zuciyarta tana addu'a.
Ta wata hanya da bata taSa sanin da ita ba, duk da gidan ba ?aramin gida ba ne, suka bi. Ya yi parking gurin babu kowa an ?awata shi da wasu irin dakakkun kujeru na gini da fulawoyi.

Su na bin wata ?ofa suka shiga, sai ga su a sashen Sultan. Nana ta yi shiru ta ga yadda aka yi wa ?asa ado da dukiya, kamar ba za a mutu a bar ta ba.
Tsahirtawa ta yi da tunanin nata, bayan ganin mutanen da a yanzu ta tsani ganinsu, tun bayan yin ?arfa-?arfar rabata da Wanta. Sun kame a kan kujeru cikin manyan kayansu da rawani, sai dai sun sauke rawanin fuskarsu tana iya gane kowanne a cikin su. Tuna abin da Mahmoudu ya gaya mata, ya sanya ta daidaita nutsuwarta, ta tsuguna a gabansu ta ce "Ina wuninku" Suka yi shiru ba su amsa mata ba.

Mahmoudu ya ce "Barka da yammaci za ki ce musu"

Ta ce "Barkanku da yammaci, na same ku lafiya?"
Matawalle ya ce "Alhamdillah, sai ki ka ji mun sake neman ki ko?"

Ta ce "Eh, ina fatan ba wani laifin na sake yi ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ki yi laifi ba. Alfarma ma muke nema a gurinki"

Ta risuna ta ce "To, Allah ya bani ikon yi"

Ya ce "Kafin nan zan tambaye ki. Ke ce ki ka rayu da shi a Nigeria a matsayin matarsa bayan barinsa Agadez. Shin ko yana yin rashin lafiya mai kama da taSin hankali, bayan larurar da ya yi na manta ko shi waye?" Nana ta Wan Waga kai sannan ta mayar ta sunkuyar. Ta girgiza ta ce "A'a bai taSa yi ba" Gaba Waya sai suka yi shiru su na kallon ta.

Sardauna ya ce "Ki na nufin bai taSa wani na larurar rashin lafiyar ?wa?walwa ba?"

Nana ta ce "Eh sai matsalar zuciya da ya yi fama da ita"

Sardauna ya ce "To idan haka ne, babu amfani kawo ta kenan, tun da babu wani haske da za ta iya bamu, ko wani abu da za ta iya yi"

Nana ta risuna ta ce "Dan Allah ina son a bani dama, ko sau Waya na gan shi, dan Allah"

Sardauna ya ce "A'a, babu bu?atar hakan"

Sultan ya yi shiru yana nazarin fuskar Nana, daga bisani ya ce "Duk da haka, mu je ta gan shi, ko da wani abu da za ta iya yi a kai, ko abinci a samu ya ci"

Matawalle ya ce "Gimbiya Asal ma ta gaza yin wani abu, balle ita?"

Sultan ya mi?e sannan suka tashi. Su na gaba Nana da Mahmoudu su na baya.
?akin kansa an rage hasken fitilun cikinsa, hanyar da suka bi zuwa Wakin ba zaka taSa cewa akwai wani Waki a gurin ba.

Daga nesa Nana ta hango shi, yana kwance a dun?ule guri Waya. Gashin kansa ya baje a ?asa. Sardauna ya kunna fitilun Wakin haske ya gauraye Wakin.
Ziiiiiiiiii ta fara jin wannan sautun, na turnu?ewar ?urar sahara. Ta tattare nutsuwarta guri guda, ta din ga ambaton Allah. Kawai ta nufe shi. Sardauna zai yi magana Sultan ya hana shi, dan ba a yi wa Nana iznin zuwa inda yake ba.
Ta dur?usa a kansa, ta ga an Waure masa hannayensa, jikinsa ya yi jawurr ga wannan hucin zafin da take iya ji, fiye da yadda sauran mutane idan sun raSe shi suke ji.
Ta hau kiciniyar kwance masa hannunsa. Wata irin mi?a ya yi tana gama kwance masa hannun. Ya mi?a hannunsa wuyanta, da wannan kalar idanun nasa mai ban tsoro. Cikin jarumta da dakiya, ta ri?e hannun nasa ta ce "Sayyid, nice. Ka saurari sautin muryar. Asmy ce ka ayyana addu'a a cikin ranka ko ba zaka iya furtawa ba." Bakinsa ne yake karkarwa yana son ya yi magana.

Ta ce "Ka yi shiru, kar ka yi magana" Ya yi wani yin?uri ya fizgota jikinsa da ?arfi.

Ayshercool
08081012143

84
LITTAFIN KU?I NE, KI BIYA KU?IN KARATU KAN KI KARANTA. VIA 0069685771.AISHA ADAM STANBIC
08081012143


Gaba Waya suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Tamkar matafiyin da ya shafe tsawon lokaci yana tafiya a sahara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login