Showing 54001 words to 57000 words out of 124905 words

Chapter 19 - Buzu Book 3 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

30

'ya ta ce na isa da ita"

"Amma rayuwarta fa? Ta yaya za ta zauna da mutumin da ba ta so?"

"Ta zauna da shi koma ta yaya ne"

Asal ta din ga bori a kan ba ta son Hammad, ba za ta aure shi ba, dan sam ba ta shiryawa aure a lokacin ba, duk da tana da ?arancin shekaru amma yadda take tsara wa kanta rayuwa sai ta ci Duniyarta da tsinke sannan za ta yi aure.

Can kuma Sultan ya saka Hammad a gaba a kan lalai ya je su gaisa da Asal, duk da sun san juna akwai bu?atar su ?ara samun sha?uwa a kuma tsara yadda biki zai gudana. Da to kawai Hammad yake amsa wa Sultan.
Tare da Mahmoudu suka je gurin Asal, sai dai a ?alla sun shafe awa Waya da rabi, Asal ba ta fito ba. Idan ya yi niyyar tafiya, sai Mahmoudu ya hana shi.
Daga ?arshe shi kansa Mahmoudu gajiya ya yi, suka tafi gaba Waya.
Sai dai washegari, Sultan ya kira Hammad, ya ci masa mutunci abin da bai taSa yi ba, wai girman kansa zai sanya ya lalata musu zumunci da Wan uwansa. Yarinya ta gama shiri tana jiransa yana zuwa ya yi tafiyarsa. Abin ya yi wa Hammad ciwo, amma ya daure ya bawa Sultan ha?uri, ya tashi ya tafi. Sai da ya yi zuwa uku, sannan Asal ta zo. Kallo Waya ya yi mata ya tuna abin da Sultan ya yi masa saboda ita, ransa ya ?ara Saci ya ji wata irin tsanarta ta mamaye shi. Sam Asal ba ta da Wa'a. Duk da kasancewarsa yaro ?arami girman sarautarsa ya sanya yana da kamewa da son girma. Amma bai ga hakan a tattare da Asal ba, sai harare-harare da take yi. Ga shi a lokacin shi har cikin zuciyarsa yana son mace mai mamora, Asal kuwa ga yarinta ga babu alamar wani abin kirki a tattare da ita.
Haka Tafawa ya din ga haWa shi da Sultan a kan Asal. Tafawa ya lura idan bai yi a hankali ba, Asal za ta ji?a masa aiki, ga mahaifiyarta sai bala'i take yi ba za a yi wa 'yarta auren dole ba.
Ya same ta da daddare a Wakinta, ya kifa mata wani uban mari, da sai da ta ga taurari ya ce "Ke kalle ni da kyau, idan ma babarki ce take ziga ki, to ki shiga hankalinki tun da wuri. Ban haWa auren nan dan ki so ko kar ki so ba. Na haWa auren nan ne domin cikar muradina. Za ki taimaka mini ne, ina son Wan uwanki ya gaji karagar mulkin Sultan, dan ba zan bari sarauta ta dauwwama a gidansu ba. Dan haka dole ki ha?ura da duk wani abu da ki ke so, domin cikar nawa muradin. Zan aura miki Hammad ne, na wani Wan lokaci na samu cikar burina, daga nan ki yi duk abin da ki ka ga dama." Asal ta sha kuka sosai da sosai. Ita ta san Hammad ba shi da wata makusa ko kaWan da za ta nuna a matsayin aibun da za ta ce ba ta son shi, kawai gani take auren kashe mata rayuwa ne. Mussaman yadda Allah ya yi mata kyakykywar halitta.
Ko da ta gaya wa mahaifiyarta abin da Tafawa ya ce, zuwa ta yi ta same shi, tana faWan ya za a yi ita ba da haifar Wa ba, a tursasa wa 'yarta saboda cikar muradin wani, tun da yana da ?anne mata a aura wa Hammad Win ?annen Asadullah.
Gudun kar ta Sata masa aiki, ya sanya ya yi mata bayanin ai idan ya aura masa a ?annen Asad, nan da nan za a gano shi, amma wanda suke ba ciki Waya ba, babu wanda zai kawo wani abu. Ya din ga kwaWai mata abubuwan da za su samu idan Asad ya zama Sultan.
Gimbiya Bilkisu ma har gida ta zo ta samu Tafawa, ta ce "Na ji labarin za ka aura wa Hammad Wanka, duk da na san inda ka dosa, na san dalilinka na yin haka, amma kar ka manta da sauran rina a kaba, tun da Zahradeen ma Imam ne, kuma Wan Sultan"

Tafawa ya ce "Haba Gimbiya Bilkisu, ai ke 'yar uwata ce, ki zo mu haWa ?arfi da ?arfe mu yi nasarar ganin Hammad bai mulki Agadez ba. Kuma kema kanki kin san alamu sun nuna Hammad yake son ya dam?awa mulkin"

Ta ce "Mu haWa hannu, ka yi mini irin yadda ka yi wa wadancan mutanen da suka haWa kai da kai. Kuma idan na haWa kai da kai, waye zai ha?ura ya bar wa wani tsakanin Asadullah da Zahradeen iya ruwa fid da kai kawai" Ta ?arasa maganar tana dariya.

Ta shiga gurin mahaifiyar Asal da niyyar su gaisa, amma ta ce mata "Ina fatan idanunki a buWe suke,a kan auren nan da z a a yi wa 'yarki? Idan burinsa ya cika Asadullah ya zama Sultan Asal ba ta da wata makoma. Ita dai mace ce ba sarauta za ta yi ba. Ki bar ganin shi ya haife ta, bu?atarsa na biya zai ajiye ku gefe"
Haka aka din ga Wauki ba daWi a kan auren nan, Hammad ya din ga fuskantar kalubale daga Sultan saboda yadda Tafawa yake haWa su, har sai da Matawallen Agadez mahafin su Hasna da Al-Husssain ya ankarar da shi, Tafawa haWa shi kawai yake yi da Hammad.

Haka Sultan ya saka Hammad haWawa Asal lefe, na ban mamaki, lefe na 'yar gata. Aka yi gagarumin biki da ya tara manyan mutane, ana ta jinjina yarintar amarya da ango, dan ma dai Hammad a nutse yake sosai.
Bayan an yi aure, Hammad ya tsallaka ya tafi karatu tare da Mahmoudu, ba tare da ya sake bi ta kan Asal ba. Bayan ya zo hutu, Tafawa ya dage sai ta tare. Haka aka ginawa Hammad dan?areren gida a cikin gidan sarautar aka saka Asal a ciki.
Tun da Asal ta tare, bai taSa gigin zuwa inda take ba, ta din ga yi masa alwashin tun da ya aure ta, sai ya ga tashin hankali da bala'i. Ta din ga surfa masa rashin mutunci da tijara iri-iri, tun yana jurewa har ya fara gaya wa Mahmoudu zai Wauki mataki, amma ya din ga rarrashin sa yana ba shi ha?uri.
Bayan sun koma makaranta, ita ma Asal aka mayar da ita makaranta, sai dai aka kama mata gida, saboda makarantar nesa ce da Agadez. Idan ya tafi ko son tuna Asal baya yi. Saboda tashin hankali da rashin biyayya, ango na ?iba shi kuwa ya yi uwar rama.
Tafawa kuma ya din ga nanata mata, duk wani motsi na Hammad, ta din ga sanar da shi. A haka aka shafe shekaru uku da aure, ya mayar da hankali a kan karatunsa, da ginin katafaren gurin cin abincinsa a Agadez.
Ita kuma mahaifiyar Asal ta fara saduda, tare da kwaWaitawa Asal ta kwantar da hankalinta, idan Allah ya sanya ta haifi namiji, babu lallai Asadullah ya yi mulki.
Ko da suka kammala degree na farko, suka dawo Niger, Asal babu abin da ya yi mata zafi da shi, shi ma bu kula ta yake yi ba, duk inda za ta fita yawonta babu ruwanta da neman izininsa.
Wataran da daddare yana zaune a turakarsa, yana duba wasu litattafai ta yi sallama hannunta da tray. Ya amsa mata ta shiga ta ajiye masa ta ce "Ga shayi na dafa maka" Cikin mamaki ya din ga bin ta da kallo. Ya gyaWa kai ya ce "To na gode" Ta na Wan murmushi ta tashi ta fita.
Bayan fitarta ya din ga kallon flask Win shayin, ya murza zoben hannunsa, sannan ya kalli kofin a take sai ga wani irin ba?in haya?i yana fitowa daga cikin kofin, shayin ya koma ba?i ?irin mai kauri. Ya yi shiru yana mamakin yadda ?iyayyar da take yi masa za ta sanya ta iya cutar da shi, dan tun da ya ga hakan ya san akwai wani abu a cikin shayin.
Har ta fara shirin kwanciya, ya shiga Wakin hannunsa ri?e da kofin. Bai ce mata komai ba ya zauna a kusa da ita ya mi?a mata kofin ya ce "Sha" ta dube shi ta ce "Ai na sha"

"So nake ki sake sha ai". Ta girgiza masa kai tana kallon sa.

Ya murza zoben hannunsa ya shafi saman kofin da yatsunsa, sai ga Asal ta ga abin da ya gani a cikin kofin.

Ya sake kallon ta ya ce "Ki sha, ba za ki kashe ni nikaWai ba" Ya yi maganar cikin tsawa. Ba ta taSa tunanin zai yi mata kwarjini haka ba, gaba Waya ta rikice ta hau kuka.

"Gaya mini wane ne? Waye ya baki wannan abin ki bani, kuma na mene ne?" Ta hau girgiza kai tana kuka.
"Ki gaya mini kafin na Wauki matakin da ya dace" Ta kasa magana ta ci gaba da girgiza kai.

"Shikenan, tun da ba za ki faWa ba, idan na kai ki gaban Sultan kya gaya masa meyasa ki ka yi yin?urin cutar da ni" Ya fice ya bar ta a Wakin, hankalinta ya yi mummunan tashi, ta kira lambar Abbanta amma ta ?i shiga, ta karaya ajalinta ya zo a Agadez. Amma kwana uku shiru babu wanda ya kira ta, kuma ba ta sake ganinsa ba.
Kwana na huWu har ta kwanta, ta tashi ta shiga sashensa, ta gan shi a zaune yana cin dabino yana kallon labarai. Yana ganinta ya tsuke fuska ya tashi ya bar mata falon. Ta tsaya a falon tana wasi-wasi, sai dai ta shiga lissafin halin za za ga shiga idan ya tona mata asiri, ta san duk abin da za a yi mata ba za ta iya tona wa mahaifinta asiri ba. Ta daWe tana tufka da warwara ta ga dai ba ta da sauran mafita.
Dan haka kawai ta bi bayansa, gara duk wadda za a yi, a yi. Sai dai da ta shiga kawai ta tarar yana Video call da wata baturiya. Wani abu mai Waci ya tsirga mata ta tsaya tana kallon kyakykywar fuskarsa mai cike da ?uruciya yana murmushi.

Ayshercool

91

Bai daina wayar ba, kasancewar malamarsa ce a faransa. Sai dai bai bari ta fuskanci hakan ba. Ta ?arasa gabansa cikin ?unar rai da wani abu da ta kasan gano ma mene ne a ranta. Ta je ta tsaya masa a ka. Bai kula ta ba, ya ajiye system Win, ya fara ?o?arin kwanciya. Ta zauna a gefen gadon ya ce "Imam gurinka na zo"

"An sake aiko kin ne?" Ta girgiza kai cikin sanyin jiki.

"FaWi abin da ya kawo ki zan kwanta"

"Dan Allah ka yi ha?uri" shiakWai ne abin da ta iya furtawa, ta fashe da kuka.

"Na yi ha?uri da aka yi me?"

"Abin da na yi maka, wallahi ba dan san raina ne ba"

Hammad ya ce "Ba da son ranki ba? Bayan kin gaya mini ba kya so na, ba kya ?aunar zama da ni, sai na yi dana sanin aurenki, ai ba abin mamaki ba ne ba dan an haWa kai da ke an cutar da ni. Amma ko ba ki kalle ni a matsayin miji ba, yakamata ki kalle ni a Wan uwanki ki yi ha?uri mu zauna lafiya. Koma waye ya saka ki, ku sani ba zan mutu ba sai wa'adin da Allah ya Wibar mini ya yi "

Asal ta din ga kuka tana ba shi ha?uri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba.
Daga ?arshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa"

"Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah"

"To ban guri zan kwanta"
Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru.

"Mene ne kuma?"

"Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?"

Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin Wacinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta ?aunarsa.
Kasancewar ya saba baccinsa shikaWai a ?aton gadonsa, ya sanya shi ?o?arin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yin?ura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma Wakinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. ?arshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta bu?ata ba.
Tun daga lokacin Asal ta Wan nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faWi abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi ?orafi a kanta.
Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi ?o?arin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da Wansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta ji?a musu aiki.
Shi ma Sangaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya.
Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a? kansa ba, har kiran Asal yake ya ?are mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya ?ara tonuwa.
Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad ha?urinsa ya fara ?arewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam Win ?asar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaWa ya raya ta ce ba zata ba.
Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa.
Tun da ya faWi haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya ro?i Hammad kar ya yi aure, yayi ha?uri tana addu'a ta san za ta haihu wataran.
Bata taSa tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har i?irarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad.
Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai ha?ur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi ha?uri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta."

Karo na farko Hammad ya buWe baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai ha?uri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haWiye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaWai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa ?alau.
Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi ha?uri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar ?ara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a.
Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karSo ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruWewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a.
Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace"

Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba Waya hankalinta a tashe yake, amma a Wan ?ara ha?uri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya zama na surutu.
Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad Win yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da ?ananan shekaru, Hammad ya haWu da larurar hawan jini ake ta fama.
Asal ta ?ara shiga tashin hankali, ganin yadda ake ?ara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa.
Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, ba?a?en nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal.
Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu"

"Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne"

"Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da ?iba, Allah ya sauwwa?e" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai ?ara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi.
Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login