Showing 1 words to 3000 words out of 59970 words

Chapter 1 - MAFARKI COMPLETE

[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*

🦋🦋🦋



🦋🦋🦋



🦋🦋

Mallakar :

🦋

Chamsiya Laouali Rabo

```MRS SADAUKI

💫





```

SADAUKARWA: Ga mata ma'abotan saka hijabi

.

🤗

01

Yau ma kamar kullum tun safe na yi wanka na shirya cikin uniform

ɗ

in makaranta,na fesa turare marar ƙamshi kafin na

ɗ

auki jakata mai

ɗ

auke da Alkur'ani da sauran littafai da ake koya mana.Cike da nutsuwa na sauko ƙasa,da Momy idona ya yi tozal

i matar kirki wacce daular da muke ciki ba ta saka ta zama raguwa ko mai ƙiwar aiki ba kullum a tsaye take domin farin cikin ahalinta.

Duk wata sangartata ce na ji ta motsa,na tattare zumbulelen hijabina wanda tsabar girmansa har jan ƙasa yake yi.Da

ɗ

an

guduna kamar zan fa

ɗ

i na je na rungume ta ina mai yi mata sallama madadin na ce ina kwana,saboda haka Daddynmu ya koyar da mu yin sallama kafin kowacce gaisuwa.

“Wa'aleyki salam autar Momy” ta amsa mini.

Na turo baki don na tsani a ce mini auta ina

mugun ƙaunar yara wannan yasa kullum fatana Momy ta haihu.Na ce “ni dai ba auta ba Momy,kin ga Mamarsu Mujahida ma ta haihu”

Ta yi

ɗ

an murmushi mai sauti kafin ta ja hancina ta ce “wuce dai ki je direba na jiranki,ki aje hankalinki ki yi karatu banda su

rutu”

Na ce “to Momy ki ha

ɗ

a mini lemun zo

ɓ

o da kanki ,in an kusa shan ruwa kuma a yi mini salade na fruits”

“In sha Allah auta, Allah ya tsare ki ya maido mini ke lafiya”

“Amin Momy ” na amsa ina mai

ɗ

aura niƙaf a fuskata kafin na fita harabar gi

danmu wacce take

ɗ

auke da shuke-shuke gwanin sha'awa.Da sallama na ƙarasa wurinsa ina mai bu

ɗ

e baya na zauna,shi kuma ya shiga ya yi wa motar key.

Muna hawa babban titi na ciro wayata na saka ta silence ,sai kuma na shiga gallery tare da danna kundin da n

ake ajiye hotunansa.Kamar wacce ta zauce haka nake kallon sajensa wanda ya ha

ɗ

e da dogon gemunsa mai cikar gargasa baƙa ƙirin sai

ɗ

ai

ɗ

aiku daga tsakiya da suka fitar da fari.Idona ya ciko da ruwan hawaye ina jin kuma wani murmushi na sauko mini wanda ba ko

mai ya haifar da shi ba sai zuciyata da ta raya mini ‘ saura ƙiris ki cimma burinki’

Tsayawar da motar ta yi shi ya fargar da ni mun kawo,a hankali na bu

ɗ

e murfin motar na fita wanda hakan yayi daidai da tahowar motarsa.Haka na yi tsaye ina bin motar da

ido har ta tsaya inda malamai ke ajiye motocinsu,ya

ɗ

an

ɗ

auki

lokaci kafin ya fito.Kamar kullum yau ma sanye yake cikin fararen kaya sai ya

ɗ

ora alkyabar nan da malaman Saudiya ke sakawa,ita kuma baƙa ce haka ma hiramin kansa baƙi ne yayin da gilashinsa k

uma ya kasance fari.Da sauri na

ɗ

auke dubana daga gare shi na tunkari ajinmu zuciyata na dokawa,ina yin sallama ƴan matan ajin wa

ɗ

anda suka zo duk suka juyo yayin da Mujahida ta wani zo da sauri ta rungume ni tare da yi mini ra

ɗ

a a kunne wacce ta ƙara tsan

anta bugun zuciyata.

Ta janye daga jikina tana dariya,na riƙo hannunta ina mai cewa “wai da gaske? ”

“Wallahi kuwa ni ma yanzu da na je can ofishin shugaban makaranta na ji ana zancen” ta bani amsa.

Na ce “amma kuma ba a yi sanarwa ba”

Ta ce

“ƙila sun canza tsari”

Daga haka na je na zauna ,kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na yi sukuku duk hirar da Mujahida ke yi mini ta yadda bikin gidansu zai kasance haka-haka nake jin ta a haka har ajin ya cika.Ƙarfe takwas na bugawa kuma malami

nmu ya shigo da sallama,bayan mun amsa sai ya zauna yana fuskantarmu kafin ya fara da cewa “yau za a fara zana jarabawa, binciken karatun Alkur'ani shi ne farko wa

ɗ

anda ba su da gyara da yawa iya su ka

ɗ

ai ne za su tafi aji na gaba wanda ya kasance ajin ƙar

she”

Malam na gama wannan jawabin Mujahida ta kalle ni tana murmushi ta ce “yanzu kin yarda?”

Na ce “ƙawata tsoro nake ji”

Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa kafin ta ce “na me kuma? Bayan duk lokacin da kika

ɗ

auka kina burin ganin wannan lokacin? Ko dai kin d

aina sonsa?”

Na dube ta da sauri ina mai cewa “na daina? Kuma kika ganni a raye”

Ta

ɗ

an bangaje ni tana dariya,kafin kuma duk mu nutsu saboda buga teburi da malam ya yi alamun a nutsu.Bai wani

ɓ

ata lokaci ba kuwa ya soma binciken karatun,kasancewar d

a tsarin ABCD aka bi wannan yasa har aka fita shan iska ba a kawo sunana ba.

Muna fitowa Mujahida ta ce “ni kam Khadeeja na tambaye ki,yanzu in mun gama jarabawa muka shiga ajin ƙarshe wace kalma ce ta farko da za ki furtawa Sheikh Rayyadeen?”

Na yi

ɗ

an murmushi kafin na ce “to ai kin bari ki ga in mun ci exam

ɗ

in ko?”

Ta ce “na ma san za mu ci ai”

“To Allah yasa”

“Amin! Ina jinki me za ki ce masa?”

“Zan fa

ɗ

a masa ina sonsa fiye da rayuw...” sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi sakamak

on ido hu

ɗ

u da muka yi da Sheikh Rayyadeen duk da yana

ɗ

an nesa da ni amma kallon da ya yi mini kamar mai nuni ne da ya ji abin da na furta,wani abin mamaki kuma sai na kasa

ɗ

auke idona daga cikin nasa

ɗ

in yayin da shi kuma ya fara tunkaro inda muke.Yana d

ab da isowa na ji Mujahida na cewa “kamar fa wurinmu zai zo” furicinta ya ida hautsana cikina kawai na yi baya da mugun sauri na koma cikin aji.

“Khadeeja” na ji Malam Ibrahim ya furta,na juyo da sauri ina mai cewa “ka yi haƙuri malam ”

“Bai komai ki

n ga dama ina ta son yi miki magana,har yanzu ba ki gama tunanin ba ?”

Cike da kunyar abin da zan fa

ɗ

a masa na

ɗ

an kawar da kai gefe na ce “shi so abu ne da ke da alaƙa da zuciya...” shiru na yi saboda lura da inuwar mutum a bakin ƙofa.

“Sheikh !”mal

am Ibrahim ya fa

ɗ

a da ƙarfi muryarsa na fitar da amon tsoro.Kamar wacce aka yi wa allurar hauka haka na ruga a guje domin na fita,ina dab na kai gare shi na ji wani abu lummm ya disashe ganina.Kan ƙirjinsa na tsinci kaina wanda hakan ya yi daidai da tsayaw

ar bugun zuciyata,ban sani ba suma ne na yi ko kuwa mene ne oho abin da na sani shi ne kawai bayan na dawo hayyacina na samu kaina a can wani wuri da aka ware domin malamai su huta.

Zaune na yi ina kallon

ɗ

akin ina jin kaina na

ɗ

an sara mini,na yi tun

anin ni

ɗ

aya ce a wurin sai da Mujahida ta shigo ne da sallama na ji an amsa mata daga can bayana.Da wani matsanancin sauri na juya idona kuwa ya sauka cikin nasa,yanzu babu gilashi a fuskarsa wanda hakan ya ƙara tona asirin kyawun manyan fararen idonsa.Wa

nnan karon kasa jurewa na yi kawai sai na yi juyo kaina tare da sunne shi, Mujahida ta ƙarasa ta miƙa masa gorar ruwa.

Murya cike da nutsuwa ya ce “kuna iya tafiya”

Sai ta zo ta kama hannuna ta miƙar da ni tsaye,sai da muka kai bakin ƙofar fita sanna

n na juyo na saci kallonsa wannan karon idonsa a lumshe suke ya

ɗ

aga gorar ruwan yana sha har suna

ɗ

iga a gemunsa wanda hakan ya nuna a matuƙar buƙace yake da su.

Muna fitowa Mujahida ke cewa “yau na ga ikon Allah kin ga yadda ki ka sandare a jikin Sh

eikh Rayyadeen? Kamar mai cutar sanƙarau,wajen mu hu

ɗ

u muka

ɗ

auke ki zuwa ajin malamai bawan Allah shi kuwa Sheikh sai hankalinsa ya tashi shi ne ya tsaya kanki yana ta yi miki karatu har sai da numfashinki ya dawo normal ”

Tun da ta fara magana nake

kallonta amma ban ce komai ba a haka muka ƙarasa can ajinmu.Yadda duk suka zubo mini idonsu ya saka na ji duk na tsargu,hatta shi kansa malam Ibrahim kallon nawa yake yi.Zaune na yi kawai,ina sauraren yadda yake bincikar karatun sauran

ɗ

alibai tuni ma an w

uce sunana.Kwance na yi jikin table na lumshe idona nan take hoton yadda na fa

ɗ

a jikin Sheikh ya shigo tunanina,yadda ya wani riƙo ni da mugun ƙarfi da hannuwansa masu taushi duk ina tune daga nan ban tuna komai ba.Ina a haka har lokacin tashi yayi muka fi

to,sai a lokacin kuma na tuna babu niƙaf a fuskata.

“Mujahida ina niƙaf

ɗ

ina?” na tambaye ta ina mai kamo hannunta.Ta ce “oho ni ma ban sani ba,ko ƙila tana can ajin malamai”

Ban ƙara ce mata komai ba haka muka nufi wurin da ake cin abinci,gefe kawai

na zauna har ta gama ci muka fito zuwa masjid na mata wanda yake babba ne akwai kuma ban

ɗ

akuna.Sai da muka yi alwala kafin mu shiga mu zauna,saboda na ture tunaninsa daga cikin kwanyata na

ɗ

auko hirar bikin gidansu nan fa muka ta zantawa muna dariya.Lokac

in sallah na gabatowa masjid

ɗ

in ya soma cika,kafin kuma mu miƙe mu fara daidaita sahu.Yau ma Sheikh Rayyadeen ne ya bamu sallah,har aka gama idona na lumshe don ji na yi ƙira'arsa ta yau ta fi ta kullum da

ɗ

i.Bayan mun gama kwantawa na yi domin na rumtsa k

afin lokacin shiga aji yayi.

Ban san iya lokacin da na

ɗ

auka ina hutawa ba amma ko da na tashi na hangi Mujahida ita ma tana baccin.Fita na yi na shiga ban

ɗ

aki bayan na yi addu'a,ko ina tsaf yake babu datti don har wanka ma wasu na yi amma ni dai ban ta

ɓ

a yi ba in ba yau da nake jin zafi na rufe ni ba.

Wankan na yi na

ɗ

aura alwala na mayar da kayana kafin na fito,fitowar tawa ta yi daidai da fitowar Mujahida ita ma cikin ki

ɗ

ima take cewa “ƙarfe uku ta buga fa har da minti wajen biyar bari na yi alwala

kawai”

Na ce “da yake da na tashi ban duba lokaci ba”ciki na shiga na fiddo mai na shafa da turare sannan na

ɗ

auko jakakunanmu na fito na tsaya.Tana fitowa na miƙa mata tata kafin mu wuce aji, Allah yayi sa'a ma Malam bai shiga ba.Ko da ya shigo kuma s

ai aka raba mana takardu muka zana jarabawa wacce ta ƙunshi abubuwa da dama,ba mu yi awa

ɗ

aya ba kuma duk aka lashe amshe saboda lokacin sallah da ya yi ina ta jiran jin muryar abincin ruhi amma sai na ji ta wani malami daban.Bayan mun dawo aka ƙara bamu m

uka ƙarasa duk wanda ya ida sai ya fita wannan yasa da na gama na fito na ciro wayata na soma lalubo wayar direba amma a kashe.

Ji na yi kamar na mutu tsabar takaici,haka na yi ta tafiya har na fita daga cikin makarantar ga shi fuskata a bu

ɗ

e mutane s

ai kallona suke yi ga abin hawa ya yi wuyar samu.Abinka da ƴar Daddy kawai sai na ji hawaye sun cika mini ido,ina nan tsaye na ga motar gidanmu.A gabana ya tsaya tare fitowa ya bu

ɗ

e mini murfi yana bani haƙuri kan ya manta ne bai taho da wuri ba.Ji na yi t

akaici ya ƙara rufe ni kukan da nake ta riƙo ya kubce mini a hankali na fara magana ba cikin hayaniya ba,“ta yaya mutum zai manta da haƙin da ya rataya a wuyansa? Dama ana manta aikin wajibi ne?”

Ya ha

ɗ

e hannuwansa biyu yana bani haƙuri,ban ƙara cewa ko

mai ba na shiga na zauna ina shafar hawaye.Ina

ɗ

aga kai na hangi Sheikh Rayyadeen a tsaye kuma da dukkan alamu ya ga komai don idonsa na kan motarmu ne,zuciyata ce na ji tana bugawa a haka dai ya ja mu zuwa gida.

Ina shiga yadda na ga an cika dianing da

kayan lambu da na motsa baki na ji a raina Daddy zai dawo sai dai falon tsit yake.Ina shirin nufar

ɗ

akina na ji tambaya daga sama “ina niƙaf

ɗ

inki?” muryar Daddy ce ,cak na tsaya ina kallonsa yana cikin shiga ta manyan kaya har da hulla ya

ɗ

ora.Ban basa a

msar tambayar ba sai nufarsa na yi na je na rungume shi ina kukan farin cikin ganinsa.

Ya tallabo fuskata yana goge mini hawayen kafin ya ce “Ummita ba na hana ki fita babu niƙafi ba? ”

Na kwa

ɓ

e baki na ce “ai da zan fita na tafi da ita fa

ɗ

uwa ta yi

ban sani ba”

“Ta ya ta fa

ɗ

i har ba ki sani ba?” shiru na yi ban basa amsa ba,sai kuma can na canza akalar zancen “Daddy shi ne ba ka sanar da ni za ka dawo ba”

“Na cewa Momynki ta sanar da ke,kenan ba ta fa

ɗ

a miki ba?”

Na turo baki gaba na ce “Dad

dy ai ka san Momy na kishina so take ta fara ganinka kafin ni shi yasa ta ƙi fa

ɗ

a mini”

Yayi murmushi mai

ɗ

an sauti kafin ya ce “ƙila tana tsoron ki ƙi zuwa makaranta ne shi yasa”

“Da dukkan alamu gulmata ake yi ƴa da uba” Momy ta fa

ɗ

a tana mai fitow

a daga

ɗ

akinta ta saka wani rantsatsen less,dariya kawai na yi na wuce can

ɗ

akina da ke hawa na farko.

Uniform

ɗ

in na cire na shiga wanka,a gaggauce na shirya cikin doguwar riga ta atamfa.Ko da na fito tuni Daddy na zaune yana addu'a saboda gabatowar lo

kacin shan ruwa,ni ma kujera na ja na zauna na fara nawa addu'o'in idona na lumshe nake roƙon Allah ya mallaka mini Sheikh Rayyadeen matsayin miji.



SHEIKH RAYYADEEN

Matashin malami ne wanda har yanzu yake cikin ganiyar samartaka,duk da shekarunsa

sun

ɗ

an ja amma fatar jikinsa ba ta nuna hakan ba.Shekarunsa arba'in da

ɗ

aya a duniya yana dab da cika da biyu,fari ne sol yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba.Shi

ɗ

in ya fito daga ƙabilu biyu,mahaifinsa kanuri ne

ɗ

an asalin garin Diffa da ke nan ƙasar Nijar

yayin da Mahaifiyarsa ita kuma ta kasance Balarabar Nijar ce suna rayuwa a babban birnin Yamai.

Wannan yasa kyawunsa ya fito da wani fasali na daban,wanda hatta shi da kansa ya san shi kyakkyawa ne don yana

ɗ

aya daga cikin abin da yasa mata ke

tururuwa

suna kawo masa tayin soyayya amma bai kar

ɓ

a a bisa wani dalili nasa da ya

ɓ

oyewa kansa.

Malamta kusan gadon gidansu ne don kusan kowa yana da ilimin addini,sai dai banbancinsu da shi kawai ita ce aƙida duk da tun farko karatun allo ya yi amma daga ƙarsh

e da ya canza akalarsa zuwa karatun habsi wannan kuma ya samo asali ne saboda keta ƙasashen Larabawa da ya yi ya ƙara samun gogewa ta fanni daban-daban.

Shi ne da kansa ya bu

ɗ

e makarantar NOOR-RULLAH sannan kuma ya zuba malamai daban-daban ya kuma bai

wa wani matsayin jagoranci yayin da shi kuma ya zo a matsayin malami.In banda mahaifiyarsa babu wata halitta da ta san sirrinsa,komai zai yi yana

ɓ

oyewa bai son bayyanawa.

Yana

ɗ

aya daga cikin tabi'unsa shi ne baiwa sirri da amana muhimmanci,yana son t

urare saboda mutum ne mai musulmar tsabta.Ya tsani yawan surutu,bai cika son shishigi ba wannan yasa kusan bai da abokai barkatai sai dai in na karatu wannan kenan;

Bayan ya gama ha

ɗ

a komai ya mayar da komai kan fasali sai ya

ɗ

auki key

ɗ

in motarsa ya fi

to.Kusan makarantar ta yi tsit saboda lokacin tashi tuni ya kusa,a hankali yake driving lokaci zuwa lokaci fuskarta na fa

ɗ

o masa a rai da kuma irin yadda ta yi shure-shure da yana yi mata karatu,yadda take kuka tana ƙanƙame shi gaban

ɗ

aliban da yasa suka k

ai ta can.Ya

ɗ

an ja tsuki yana jin wani irin takaicin yarinyar da ya ji suna kira da Khadeeja,kamar mahaukaci haka shi ka

ɗ

ai ya soma yin magana “ni da ba haka Ammyna take ba,ban ma san wane ne ya za

ɓ

a mata suna mafi daraja ba” ya ƙara jan wani tsaki yana m

ai karyar hancin motarsa tare da yin Horne,babu jimawa aka bu

ɗ

e ƙaton get

ɗ

in ya shiga a hankali ya je ya parker motar ya fito.

Tun kafin ya shiga falon yake jin masifar Grand-Maa ,yana yin sallama ta ja baki ta yi shiru tana mai cewa “to ga ustazu na

n” Ammy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login