Showing 36001 words to 39000 words out of 59970 words
irin an yi ruwa an
ɗ
auke.A kan kabarin wasu irin ƙananun baƙaƙen duwatsu ne a zube kamar shara,sai kuma wani farin kyandir daga tsakiya wanda ya fara ci da wuta da kansa,wani irin abu nake ji kamar ana fizgo ruhina t
amkar dai akwai wani
ɓ
oyayyen ruhi da ke jawo ni izuwa gare shi.Ba tare da tunanin komai ba na soma ture ƙasar kabarin ina bu
ɗ
e shi,sama da minti talatin na
ɗ
auka kafin yi nasarar bu
ɗ
e shi duka.Wani ƙyalle ne na ci karo da shi a shimfi
ɗ
e a samansa wani ƙat
on littafi ne akai,an yi masa cover da wata fatar dabba tamkar mai motsin rai,a ƙasa an yi wani rubutu wanda ba da Yaren da na ta
ɓ
a ji ko gani ba ne,amma sai na ji rubutun da kansa yana yi mini magana.
Ina sa hannu na
ɗ
auki littafin sai wani irin shock
ya ziyarci yatsun hannuna suka fitar da wani hasken wuta irin kamar waya ta ƙone.Bishiyoyin da ke zagaye da ni ne suka soma yin wata irin rawa har kana jin suna kai wa juna karo,yayin da kuma wani huci wanda kana ji ba na bil'adama ba ne ya soma karo da ju
na yana fitar da wani iska da ya saka furanni fa
ɗ
owa suna mutuwa murus.Page
ɗ
in farko na bu
ɗ
e,nan take na soma jin ana yi mini wankin ido na soma gane-gane ina ganin abubuwan da suka faru lokacin baya a cikin littafin tamkar an kunna tv.Abubuwa ne wa
ɗ
anda
hankali ba zai
ɗ
auka ba,mata da maza suna bayar da jininsu domin ƙaddamar da yarjejeniyar a tsakaninsu da Aljanai ,lamarin da muke ta tunanin tatsuniya ce ashe gaske ne an yi su a ƙarnin baya .Littafin na riƙe a hannuna yayin da kuma kukan ƙananun yaran da
aka sayar da ruhikansu
ko kuma aka bayar da jininsu matsayin hadaya na ta kawowa dodon kunnena farmaki,gefe guda kuma dubban ahali ne tsundum cikin rayuwar ƙunci saboda tun kakanni da iyaye sun yi harƙalla da Aljanu a yanzu kuma suna biyan bashin ƙarfin i
kon da aka basu.
Duk page
ɗ
in da zan bu
ɗ
a tana
ɗ
auke da wani baƙin sirri da ya gabata.Na ga ahali da dama wa
ɗ
anda suka yi ƙaurin suna a zube gaban baƙaƙen ruhikan da ido bai isa ya gani ba amma sun yi harƙalla da su don samun dau
ɗ
ar duniya ko iko.Wata p
age
ɗ
in kuma magana take yi kan ƙungiyoyin asiri wa
ɗ
anda aka ƙulla ta hanyar jini da kuma sassan jikin
ɗ
an Adam ,yayin da kuma wata ke magana kan mutanen da aka jefa wa ƙunci a zukata ta hanyar tsafi wasu kuma an haukata su ,yayin da wasu aka
ɓ
atar da su
daga duniyar bil'adama zuwa ta ruhaniya saboda sun gwada tonawa azzalumai asiri.
Numfashina ne na ji yana son
ɗ
aukewa,littafin kamar yana son koyar da ni,ya canza tunanina,ko kuma ya gwada imanina.Ji na yi ruhina yana kimsa mini wasu kalamai,yana cika
mini ƙwaƙwalwata da ilimin da aka yi hani,a kuma wannan lokacin ne na ji wani irin tsoro mai tsanani ya ya daskarar da ni,sai kuma idona suka ci karo da wani rubutun da aka yi da manyan harufa.
“DUK WANDA YA TAƁA WANNAN LITTAFI SHI NE SHAIDAR INUWARMU.
WANDA YA KARANTA SHI KUMA YA ZAMA *INUWAR ALJAN*” kalmar ƙarshe ta inuwar aljan wacce rubutunta yake da jan jini na ƙara maimaita a zuci,sai kuma na fahimci cewa wannan littafi ba wai iya kundi ne mai
ɗ
auke da sirri ba,a'a shi kansa yana rayuwa ne yana tat
tare da motsin rai.Yana ankare da ni tun tuni,ko kuma dai yana amayar da wani sirrina da nake
ɗ
auke da shi tun tuni.Ji nake ana kallona,ana ankare da ni ana kuma gwada ni da kuma tsare ni da ido wa
ɗ
anda ba a iya gani.A nan take kuma na fahimci wani abu ,na
canza har abada kuma ba zan dawo yadda nake ba tun farko .......
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*
👻
```LoVe aNd HoRrOr story```
👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI
💫
✍
️
}
*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴa
n biyu, alherin Allah ya lulu
ɓ
e ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki
👏🏻
*FCWA*
☀
️
________________________
02
Banda wani za
ɓ
i wanda ya wuce na taho gida da wannan littafin sirrin wanda nake jinsa tamkar wani jigo na rayuwata.Wuri mai
kyau na yi masa a cikin akwatin kayana na ajiye shi,abincin dare sam ban ma yi tunanin ci ba don dama duk wunin yau ba zan ce ga abin da na ci ba.
A wannan daren sam ban yi baccin kirki ba,da zarar na samu na
ɗ
an tsunduma cikin bacci sai na soma ganin ba
ƙ
aƙen inuwoyi masu jajayen idanuwa suna ambaton sunana suna kuma nuna mini yadda ake gudanar da baƙin tsafi da wasu dangin asirai.Yadda ake yin hadaya da jinin bil'adama,da kuma yadda ake ƙulla harƙalla tsakanin jinsi biyu.Cikin firgici na farka jikina duk
ya jiƙe da gumi,idona kan littafin da na
ɓ
oye a cikin kayana ya sauka amma a yanzu kan table na gansa kuma a bu
ɗ
e.Da na
ɗ
auke shi sai na ga sak irin abin da na gani cikin mafarki ne,wato ya bu
ɗ
e kansa da kansa yana karanto mini labarin da ke ƙumshe a ciki
ne.Waje na fita na yi rame can bayan
ɗ
aki na binne shi da tunanin hakan shi ne kawai mafita,ina komawa
ɗ
aki na sake tarar da littafin ya bu
ɗ
e shafi na gaba.Zaman ƴan bori na yi tare da yin tagumi,wata murya na ji tana cewa “littafi ya za
ɓ
i wanda zai karan
ta shi,tun da kuma ya za
ɓ
e ka to har abada ba zai ta
ɓ
a barinka ba” kamar wani mahaukaci haka na matsa kusa da shi na ce “to na ji ni ne ka za
ɓ
a amma sai ka bari har lokacin da na buƙaci karanta ka ni ne da kaina zan
ɗ
auko ka na karanta don haka yanzu ka ko
ma ma'ajiyarka ta farko” abin mamaki ina gama rufe bakina na ga ya
ɓ
ata kamar walƙiya yayin da kuma jakar kayana ta yi wani motsi tana rawa alamun dai ya shiga ciki ya zauna.
Kan shimfi
ɗ
ata na kwanta na shiga yin wasiƙar jaki,ƴan magana na cewa bacci
ɓ
a
rawo ne to shi ne yayi nasara sace ni a karo na biyu sai dai sam ban yi mugayen mafarkai ba a wannan karon.
Ina tsaka da yin baccin da ban samu na yi ba na ji muryar Abba kaina yana kuma jijiga ni alamun na tashi,ina bu
ɗ
e ido na ga sai yaƙar haƙora yake k
amar gonar auduga.
“David tashi! Tashi ka ga wa
ɗ
anda suka zo gidanmu.Taso suna son ganinka” Abba ya fa
ɗ
a cikin murna,yadda ya riƙe mini hannu gam shi ya sa na tashi don dole na biyo bayansa.A cikin rumfarmu ta kara na hangi dattawan garinmu a zaune ko w
annensu ya ƙure ƙofar
ɗ
akina da kallo,cike da mamakin abin da ya kawo su na ƙarasa na gaishe su.Bakunansu har rawa suke wurin amsawa kafin
ɗ
aya daga cikinsu ya ce “Jakob ka
ɗ
an bamu wuri muna son yin magana da
ɗ
anmu” Abba ya washe baki yana kallona kafin y
a ce “David wannan shi ne pasto
ɗ
in Cochinmu ka saurare shi da kyau,su kuma wa
ɗ
annan ai ka san su tun da kana shiga gari” yana gama fa
ɗ
a ya tafi.
Tambayoyi ne suka fara yi mini wa
ɗ
anda sam ban san mene ne alaƙata da su ba,amma da na ajiye hankali sai na
ke ganin kamar sun san na ta
ɓ
a littafin nan na sirri.Shiru kawai na yi ban iya ce musu komai ba,da suka gaji don kansu suka yi wa Abba sallama suka yi tafiyarsu.
Ina shirin shiga
ɗ
aki Ummah ta fito kamar wata munafuka ta ce “Davido wacce maganar ce
wa
ɗ
an can mutanen suka yi da kai?” kallonta na yi da kyau,sai na ga duk wasu alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta.
“Babu komai Ummah” na bata amsa tare da yin gaba.A tsakiyar
ɗ
akina na yi tsaye ina kallon akwatin kayana ina son
ɗ
auko littafin
sirri ina kuma jin tsoron kar wani ya shigo ya ganni da shi.
Daga nan inda nake a tsaye na soma jin wani irin yanayi kamar kasala kamar gajiya,idona na
ɗ
an rufewa na soma jan ƙafata na je na kwanta kan shimfi
ɗ
ata.Ba bacci nake ba kuma ba idona biyu ba,ina
cikin wani lamari ne mai wuyar fassarawa.Adaidai nan wata kyakkyawar mace ta bayyana a gare ni cikin shigar fararen kaya,tsawon lokaci tana yi mini wani kallo kafin ta zumbule suturarta nan siffar jikinta ta bayyana a gare ni,haka na ci gaba da kallonta k
afin ta tako zuwa gare ni.Abubuwan da suka faru a tsakaninmu,ba zan iya furta su ba saboda yadda ta shagaltar da ni ta saka ni cikin wani hali da babu shi a duniyata ta zahiri.Sai bayan ta gama mu'amalantata sannan ta bi ta jikin bango ta fice daidai nan k
uma control
ɗ
in kaina ya dawo.Yadda na samu duk na
ɓ
ata jikina shi ya tursasa mini zuwa na cika bokiti na yi wanka,bayan na fito na
ɗ
auki tsintsiya na share
ɗ
akina wanda kuma hakan sam ba tabi'ata ba ce Jowel ce ke yi mini gyaran
ɗ
aki amma yau dai haka na
ji ina ra'ayin yin kayana.
Ba tare da na yi wa kowa sallama ba na fice,wurin da muke ha
ɗ
uwa na je a yau ni ne na zauna domin jiransu.Ina nan zaune sai ga wata tsohuwa ta zo wucewa,sunana ta ambata wanda kuma ba iyayena ne suka ra
ɗ
a mini shi ba a'a has
ali ma ba na wannan duniyar ne ba amma a hakan na fahimci sunana ne.
“Mikiya!” ta sake furtawa a karo na biyu,sai a lokacin kuma na saka idona cikin nata wanda hakan ya bani damar yin kutse a cikin ruhinta.Babbar matsafiya ce wacce ta laƙanci aikinta
na bokanci da tsafi,ta kwashe kusan ƙarni biyu a doron duniya tana rayuwa ta hanyar fatalwar ruhinta.
“Ba sunana Mikiya ba! David ne sunana” na fa
ɗ
a murya a
ɗ
an dake.Ta yi wani murmushi wanda ya ida fito da sauran muguntarta ta ce “sai yaushe ne za ka
yarda? Sai zuwa yaushe ne za ka
ɗ
auki ƙaddararka a hannu? Kai Mikiya ce mai yi wa dukkan abin da ya tunkaro ka dirar sauri,kar ka hana ikonka yin aiki akan nauyin da ke kanka” ba tare da na fahimci abin da take nufi ba na ce “na ji na yarda! Za ki iya taf
iya”
“Wannan salo naka ya burge ni sak irin jarumtar mahaifinka sarki Alfanso”tana gama fa
ɗ
ar haka ta
ɓ
ace cikin iska, maimakon na
ɗ
auki ƙarshen furicinta da muhimmanci sai na watsar.Ina nan zaune sai abokaina suka zo a tare lokaci guda,yanayinsu kawai
na duba na fahimci yau ba su fito da niyyar yin dako ba.
“Ina za ku je haka?” na tambaye su ba tare da na yi nauyin baki ba.
Isa ya bani amsa da “za mu je mu kai takardunmu ne ko Allah zai sa mu dace a
ɗ
auke mu aiki ka ga shikenan sai mu huta da yin
dako”
“Yaushe aka yanke wannan shawarar ba tare da sanina ba?” na fa
ɗ
a ina jin wani iri alamun babu da
ɗ
i don duk abin da
ɗ
aya zai yi to dole ya shawarci sauran.
“Saboda mun ga ba ka yi wani dogon karatu ba ne shi yasa,amma ba wai da wata manufa ba” A
bdul ya fa
ɗ
a .
“Okay!” shi ne abin da na fa
ɗ
a kafin na miƙe na kama hanyar kasuwa,tafiya nake cike da
ɓ
acin rai ina jin ya zama dole ma na yi karatun boko tun da har an fara yi mini gori sai dai ta ina zan fara ? Ban sani ba.Da isata kasuwa na soma yin
dako cikin zafin rai,wanda sam ban san na yi aikin mai yawa ba da Alhajin ya zo biyana sai ya bani ku
ɗ
i na ban mamaki.Cike da murna na koma gida,sai kuma ta koma ciki tarar da mutane da na yi a tsakar gidanmu fuskokinsu cike da alhini haka na ratsa na isa
gaban Ummah wacce ke ta gumurzun kuka.
“Ummah?” shi ne kawai abin da na iya cewa,ta
ɗ
ago kanta ta dube ni da idonta da suka yi mugun ja kafin kuma ta sake rushewa da wani kukan.
“Meke faruwa ne wai?” na sake tambaya,da hannu ta yi mini nuni da
ɗ
aki
haka na tunkari
ɗ
akin zuciyata na yi mini matsanancin bugawa.Cak na yi tsaye ina kallon tashin hankalin da na ci karo da shi,gangar jikin Joy ce a kwance cikin
ɗ
aki babu numfashi .Fuskarsa babu ido an cire su haka ma daidai wuyansa an yi masa wani rame da
dukkan alamu wani abu aka cire daga jikinsa.
Ta maza na yi na ƙarasa na zube gwiwaina ƙasa tare da tallabo kansa,wani abu na ji ya caki idona mai bala'in zafi da ra
ɗ
a
ɗ
i a dole ban shirya ba na rumtse ido gam.Kamar magiji haka aka nuno mini ta yadda ak
a yi abin ya faru da shi.Yana zaune cikin ajinsu aka aiko kiransa,bayan ya fito sai ya ga su Isa ne da Abdul.A mutumce suka gaisa kafin su ja hankalinsa sosai ta hanyar yi masa ƙaryar cewa ya zo ni ne ke nemansa cikin gaggawa .Suna fitowa daga cikin makara
nta wata mota suka shiga da shi suka saka shi a tsakiya,suna tsaka da yin gudu suka shaƙa masa hodar bacci a haka suka isa wani gida inda suka yi masa kisan gilla,da farko wuyansa suka caka da wuƙa wanda zafi da ra
ɗ
a
ɗ
i yasa ya dawo hayyacinsa kafin kuma su
cire masa idanuwa duka biyun. Daidai nan kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya suka shigo suka zagaye Joy,wata hoda ce
ɗ
aya daga cikinsu ya zuba a jikin Joy
ɗ
in yana yin wasu kalamai wa
ɗ
anda ba na wannan duniyar ba ne amma sarai na fahimce su.Nan take gawar
Joy ta
ɓ
ata ta zo nan inda yake kwance a tsakiyar
ɗ
aki,sai kuma na ga lokacin da Ummah ta shigo
ɗ
akin da kuma yadda ta tsorata saboda cin karo da ta yi da wannan lukutar masifar.
Idona na bu
ɗ
e wa
ɗ
anda nake jin sun yi mini wani mugun nauyi da zafi,har wa
ni yaji nake ji suna yi mini feshi. Jiki na
ɗ
an rawa na miƙe tsaye da niyyar fita sai dai wani jiri ne na ji ya soma kwasa ta,da sauri na dafa bango ina jan numfashina da ke barazanar
ɗ
aukewa gaba
ɗ
aya.Amma da yake ina da ƙarfin hali haka na ƙoƙarta na fit
o ina rangaji,wata irin runguma Ummah ta zo ta yi mini tana mai kiran sunana tashin hankalin da nake tsinkayowa a cikin amonta kamar ma ya fi na mutuwar Joy.
Damtsena na ji shigar wani abu kamar mashi,amma ba shi ne ba yatsan Ummah ne.Wani furici take
yi mai shige da wancan
ɗ
in wanda ya kasance na ƙarnin baya sai dai wannan sam ban fahimta.Kamar yadda in an zuba wa wuta ruwa take mutuwa murus,to haka na ji duk zafin kaina da
ɓ
acin raina sun sauka.Baya na
ɗ
an yi ina kallon Ummah wacce take yi mini wani
kallo ita ma,kafin cikin
ɓ
acin rai ta ce “mene ne wannan Davido? Ina za ka je da wannan
ɓ
acin ran? Wuce ka tafi
ɗ
akinka,yanzun nan Abbanku zai zo”
‘Wace ce ke?’ ita ce tambayar da zuciyata ke son yi mata amma kamar wanda aka tsafe na kasa furtawa,
ɗ
akin
a na koma na yi tsaye ina kallon akwatin kayana inda na ajiye littafin sirri.Ina son yin bincike a cikinsa sai dai shock
ɗ
in mutuwar Joy ya ƙi barina dole na haƙura,babu jimawa kuwa Abba ya shigo ya kira ni da kansa.Gawar Joy muka
ɗ
auka muka kai can gidan
gawa kafin mu fara shirya yadda jana'izar za ta kasance don sai an yi bikin binne shi,domin yin haka kuma muna buƙatar ku
ɗ
i masu
ɗ
an yawa .Na sayen akwatin gawa,da kuma abincin da mutane za su ci da kuma ku
ɗ
in da za a bai wa maka
ɗ
a da pastocin da za su yi
masa addu'o'i.
Tun a hanyar komawa gida Abba ya ce mini “ David ya kake gani game da bikin binne Joy? Ka ga dai ni banda ku
ɗ
i kai ne za ka yi komai,kana ganin sai mun yi gayyata dayawa ko kuwa?”
Na dubi Abba cike da takaici na ce “kai ba ka damu
da irin yadda ka samu gawar
ɗ
anka ba a'a ta yadda za a rufe shi kake ? Abba ka cire ran zan bari a rufe Joy ba tare da na binciko su wane ne suka yi masa wannan kisan gillar ba suka raba shi da sassan gangar