Showing 9001 words to 12000 words out of 59970 words

Chapter 4 - MAFARKI COMPLETE

wanda alamu ya nuna ƙawayen Aliyar ne suka hau kujeru.

Babu jimawa ta sa aka fara kawo mana lemu mai sanyi,kafin ta ce “bari na je na kira shi” wani irin dam na ji zuciyata ta buga .

Can kuma ta dawo ita da wata mata wacce kallo

ɗ

aya na yi mat

a na gano inda Sheikh ya samo kyawunsa,wato daga gare ta ne.Cike da girmamawa duk muka shiga gaishe ta,ita kuma tana amsawa cikin kulawa kafin ta ce “ku taso ku ƙaraso” haka duk muka miƙe muka take mata baya,wani falon muka ƙara ratsawa kafin kuma ta ƙara

kai mu can cikin wani.Ido na lumshe jin yadda duk ƙamshinsa ya cika

ɗ

akin,sai da Mujahida ta

ɗ

an bangaje ni sannan na bu

ɗ

e idona sai na ga tuni har sun zauna sai ni ce a tsaye kamar haure .Jikina ne ya hau rawa saura ƙiris na fa

ɗ

i Allah ya gyara na samu wu

ri na zauna, Ammy

ɗ

in ce ta kira sunansa “Sheikh Rayyadeen? Tashi ga su nan sun shigo”

Ta ƙasan ido na kalle shi,yana kwance kan kujera mai zaman mutum uku ya lulu

ɓ

e da blanket.A hankali ya tashi ya zauna yana mai yi mana sallama,ni dai ban amsa ba sa

i

ɗ

an kallon fuskarsa da na yi wacce ta ƙara yin haske .

Ƴ

ar rige-rigen yi masa ya jiki suke yi shi kuma yana amsawa,tare da tambayar sabbin fuskokin da bai sani ba su kuma suna yi masa bayani

ɗ

aliban da aka kawo ne sabbin zuwa.

A bisa tsautsa yi n

a

ɗ

aga kai da niyyar satar kallonsa,karaf idonmu ya sarƙe cikin na juna da wani irin mugun sauri na sunne kai ina mai kama yatsuna ina wasa da zobena.

Ammy wacce ke tsaye duk tana kallon komai,dama burinta bai wuce ta ga wacce ta jefa

ɗ

anta cikin wann

an halin ba.Amma don sake tabbatarwa sai cewa ta yi “ma sha Allah nan dukkanku ajinsa kuke ?”

Cikin murna suka amsa da eh,Ammy ta ce “ina ga dai tun da shi malamin naku bai da lafiya ni zan je na ci gaba da koyar da ku” duk sai aka soma murna tare da nu

nawa eh ana so ta koya

ɗ

in,ita kuwa Ammy sai cewa yi“ke ya sunanki?”

“Sadiya” ta bata amsa tana wani sunne kai,na dube ta ina mai cewa a zuci ‘ kina da kunya amma shi ne kika haye kujera daga zuwa gidan mutane’ haka Ammy ta dinga tambayar sunaye har ta

kawo kaina ta ce “ke kuma me sunanki?”

Na

ɗ

an dubi Sheikh kamar ba zan yi magana ba sai kuma na ce “Nana Khadeejatu” ina ganin lokacin da ya kawar da kai kamar na ambaci sunan kashi.Bayan ta gama jin sunayenmu cikin tsokana ta cewa Aliya “ke kuma fa?”

duk sai aka sa dariya,nan dai ta fita Aliyar na take mata baya.

Sheikh Rayyadeen kuwa tambayoyi ya soma yi wa

ɗ

aliban nasa suna basa amsa yadda ajin ya kasance bayan tafiyarsa .Duk da kaina na sunkuye amma lokaci zuwa lokaci ina jin kaifin idonsa a k

aina,a hankali na kai hannu na ta

ɓ

a Mujahida ta juyo ta dube ni tana mai tambayar “ya dai?”

“Ki tashi mu tafi” na furta kamar zan yi kuka,don wani irin yanayi ne nake ji yana ratsa ni ga kuma kallon Sheikh da nake ji a jikina.Hararar wasa ta yi mini tan

a shirin juyawa na ce “please ki zo mu fita waje to” kanzil ba ta ce mini ba sai ma yadda kusan kowa ya maido dubansa kaina sai na ji duk na tsargu,cikin ikon Allah Aliya ta sake shigo wa hannunta riƙe da faranti an yanka ƴaƴan fruits sai ta soma tsokanars

u tana cewa “yau dai za ku ci abinci a gidan malaminku duk wacce ta ƙi ci kuma bulala goma” hakan da ta yi ne yasa sai hankalinsu ya koma can.

Uwar iya yi Sadiya wacce na lura kamar kanta na rawa sai cewa ta yi “duk wanda ya yi habaici dai a kasuwa ya s

an da wanda yake”

ɗ

ayar ce wacce suka hau kujera a

ɗ

azu ta kar

ɓ

e da cewa “ai ban so kika kula ta ba Diya ”

Yadda suke raha a gabansa abin yayi matuƙar bani mamaki,ko da yake kawar da kai yayi gefe yana latsa waya.Ko kunya ba su ji haka wasu daga cikinsu

suka sa hannu a faranti suna

ɗ

auko fruit suna ci.

Aka yi sallama, Ammy ce da tare da wani mai farar rigar likitoci.Gaishe shi aka fara yi kafin shi kuma ya tambayi jikin Sheikh

ɗ

in kamar wanda bai son yin magana ya ce “alhamdullah!”

Hannunsa ya kama

don saka masa sabon tiyon ƙarin ruwa amma samun jijiya ya gagara sai sokarsa yake yi jini na zuba.Duk in ya tsake shi sai na rumtse ido don takaici,da na ji na kasa haƙuri ban san ina na samo jarumtar miƙewa ba na ce “kawo ka gani”

Ba Sheikh ba alamu

n mamaki ne ya bayyana a fuskokin kowa,duk yadda kuwa Mujahida ta so riƙe mini ƙafa ina tuni har na isa gabansa na kar

ɓ

e allurar .Sai kuma a lokacin na dawo hayyacina,yadda Sheikh Rayyadeen ya kafe ni da ido shi ya saka jikina soma rawa.

Mahaifiyarsa ce

ta matso tana cewa “bari kallonsa yi aikinki” sai da na ƙara kallon tsakiyar idonsa kafin na sunne kai,a cikin ledar magunguna na zaro safar hannu kafin a hankali hannu na yi mini rawa na soma jan hannun jallabiyarsa sama.Ɗaure damtsensa na yi gam ba a

ɗ

a

uki lokaci ba kuwa jijiyarsa kore ta bayyana,da Bismillah na soka allurar ina mai

ɗ

an

ɗ

agowa na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna kafin kuma ya kawar da kai gefe.Na ja numfashi ina mai kwance

ɗ

aurin da na yi masa tare da cewa likitan “na nemo jijiyar”

Ya saki

ɗ

an murmushi kafin ya zo ya ƙarasa aikinsa,ni kuwa ji na yi ban iya zama cikin

ɗ

akin na nufi ƙofar fita ina shirin ficewa muka yi kaure ni da wata,da sauri ta yi baya ni ma haka kafin kuma mu

ɗ

ago muna kallon juna.Zuciyata ce ta wani buga daram

mm sakamakon ganin fuskarta,ba kowa ba ce sai matar da ta zo mini jiya cikin mafarki.....

[12/12 18:35] MRS SADAUKI: *MAFARKI*

👁



🦋🦋🦋



🦋🦋🦋



🦋🦋

Mallakar :

🦋

Chamsiya Laouali Ra

bo

```MRS SADAUKI

💫





```

04

Da wani sauri na ƙara ja da baya ina mai ci gaba da kallon matar wacce idon nata suka ke kore kamar dai yadda na gani a mafarki.Ita kuwa ban sani ba ko ba ta gane ni ba ne oho,haka ta bi ta gaban

a ta ƙarasa shiga falon.Na bi bayanta da kallo sai dai kafin ta ida sa wurin Ammy ta zube nan tana wani abu kamar wacce ta aka yi wa allurar hauka.Duk aka kwashi salalami kafin Ammy ta zo tana kiran sunanta ha

ɗ

i da jijiga ta,“Rashida? Rashida?” sai dai bab

u wani canji zai ma ƙara hauhawa ciwon yake,tuni

ɗ

aliban suka fara fita a bisa umarnin Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye kamar ba shi ne ke yin ciwo ba.Duk kowa ya fita hatta likitan da ya zo yi masa magani,Mujahida ta zo ta kama hannuna amma kamar gunki h

aka na ƙi motsawa.Sheikh wanda ke tsaye ya zubo mini idonsa kafin cikin wata murya ya ce “fita”

Na

ɗ

an girgiza masa kai saboda wani furici da zuciyata ke jadadda mini ‘ Khadeeja ba banza ba ne Allah ya nuna miki matar nan a cikin mafarki ƙila ke ce za k

i cece ta’ haka Mujahida ta fita ta bar ni saboda yadda Sheikh ke banko mana wani mugun kallo kamar idonsa za su fa

ɗ

o.

Daga nan inda nake tsaye na ce “a yi mata turaren habbatu sauda ” Ammy ta

ɗ

ago ta dube ni kafin ta cewa Sheikh “je ka

ɗ

auko,ke kuma

je ki nemo garwashi ” sai a lokacin kawai na fita zuwa can falo,babu kowa da dukkan alamu

ɗ

aliban sun tafi.

Waige-waige na fara don duba ina ne kitchen,kwatsam idona ya sauka kan hoton ahali shi ma sak irin yadda na gansa a mafarki ne.A hankali na som

a takawa na isa gare shi,abu biyu ne suka

ɗ

aure mini kai yadda na ga kaf mutanen cikin hoton an yi musu wani mugun

ɗ

auri daidai wuyansu in aka cire Sheikh da kuma wata tsohuwa wacce nake kyautata zaton kakarsa ce.

Hannu na kai na shafi hotonsa,ina ta

ɓ

a na tsohuwar na ji wata murya a bayana.

“Wace ce ke?” ita ce tambayar da aka yi mini cikin wata baƙar murya mai tarwatsa hankali.Da mugun sauri na juyo nan na yi arba da tsohuwar,ina shirin yin magana sai ga Aliya tana mai cewa “Grand-Maa tun

ɗ

azu fa k

e nake nema kin Rashida can ta zo babu lafiya” ta fa

ɗ

a tana mai kama hannun wacce na ji ta kira Grand-Maa.Take musu baya na yi,su ke gaba wannan yasa suka rige ni shiga da wani mugun sauri na ga Grand-Maa ta fito tana tari kamar ranta zai fita.

Wani kal

lo da ta yi mini da jajayen idonta kamar na tsohuwar mayya shi ya tsorata ni ,da gudu na baro wurin na kama hanyar fita daga gidan gaba

ɗ

aya.Ko da na fito ƙofar gida sai na hangi Mujahida can gaba tana zaune kan dakali tana waya.Na ƙarasa ina mai zama kusa

da ita,da sauri ta yi sallama ta kashe wayar kafin ta zuba mini na mujiya.

“Me?” na tambaye ta.

Ta waro ido ta ce “yaushe kika koyi ƙarfin hali Khadeeja? Kin ga kuwa yadda ran Sheikh ya

ɓ

ace amma ke oho ko a kwalar rigarki,kuma a haka ne kike so y

a amince ya kar

ɓ

i soyayyarki”

Na ce “ni fa ban ga abin laifi ba”

“To a wane dalili za ki tsaya alhalin kowa ya fita?”

Sai da na kamo dukkan hannuwanta sannan na ce “Mujahida matar nan da ta shigo ita ce wacce nake baki labari na yi mafarki da it

a,kuma wallahi yanzu ma idonta sak irin na macijin na gansu”

Mujahida ta ƙwace hannuwanta kafin ta ce “kin ga tafiyata babu ni cikin hikayar nan,ta ya daga ganin mata yau ki ce wai ita ce ta zo miki a mafarki”

Na ce “ki yarda da ni,wallahi hatta

hoton da na ce miki na ahali to yau

ɗ

in nan ma sai da na gansa”

Shiru Mujahida ta yi kamar mai nazari kafin ta ja numfashi ta ce “ni ma na ga hoton amma sai na yi tunanin ko dai ƙila kin ta

ɓ

a ganinsa ne Sheikh ya

ɗ

ora”

Na girgiza kai kawai ina jin

wani tsoro na lulu

ɓ

e ni,haka muka rungu

ɗ

a zuwa makaranta.

Yadda ajin ya kancame da hirar Sheikh Rayyadeen ana ha

ɗ

a sunansa da na Sadiya sai abin yayi mugun

ɓ

ata mini rai.Mujahida wacce ita ka

ɗ

ai ta san sirrin da ke ƙunshe a birnin zuciyata sai cewa ta yi

“kar ki wani damu kanki wai don tana rawar kai, wallahi ina da yaƙinin ita ka

ɗ

ai ke ki

ɗ

anta take rawarta.Ke yanzu ki dube ta kin ga ta yi kama da macen da Sheikh Rayyadeen zai so?”

Idona ya ciko da wasu hawaye kafin na ce “na sha ji a labarai cewa baƙar

mace na

ɗ

auke da wata irin baiwa Mujahida,kuma malamai sun fi kowa sanin sirrikan da ke tattare da mata to ƙila ita ma Sadiyar tana da shi”

Ta ja tsaki kafin ta ce “waccan fa da kike gani tsohuwa ce don ta haura shekaru talatin da biyar yanzu kuma yayi

n ƴan shila ake yi” sai kuma ta yi shiru tare da yin wata muguwar dariya kafin ta kawo bakinta daidai kunnena ta ra

ɗ

a mini “amma fa ƙawata za a sha gwagwarmaya don an ce tuzurai sun fi kowa zalamar mata kuma alƙur'an yadda Sheikh yake da ilimi na san akwai

kallo duk ranar da kuka ke

ɓ

e”

Wani irin yammm na ji a jikina,na

ɗ

an bangaje ta tare da yi mata hararar wasa na ce “ta ya aka yi ma har tunaninki ya kai can? Ni fa ko sau

ɗ

aya ban ta

ɓ

a hango mu a wannan matakin ba”

Ta yi wani ƙayatacen murmushi k

afin ta ce “ Khadeeja ko kin san da ina sonki ne domin Allah? Ganinki cikin farin ciki shi ne abu mafi tsada a rayuwata,silar ƙaunar da nake yi miki shi ne dalilin da yasa har na kar

ɓ

i Yaya Hamza matsayin wanda zan aura amma kin san ba irin kalar namijin d

a nake so ba ne”

Na ja numfashi na ce “amma Mujahida a wane dalili ne ba ki son farin namiji?”

“Ni dai bai yi min ba” ta bani amsa a takaice.

“Yaya Hamza fa shi ya yi miki?” na jefo mata tambayar.

Ta yi murmushi ta ce “jininki ne fa ai ke ma kin

san dole na so shi”

Na kama hannunta na ce “don Allah kar ki yi wasa da zuciyar

ɗ

an uwana yana mugun sonki”

“Na sani,don yana fa

ɗ

a mini kusan kullum ”

Ina shirin yin magana amma

ɗ

aya daga cikin manyan

ɗ

aliban ajinmu ta yi magana kan a yi shiru sa

i ta soma jawabi “da farko ina yi muku sallama irin ta addinin musulunci,abin da yasa na buƙaci na yi magana shi ne dama don na ce mu yi wa kanmu fa

ɗ

a .Don Sheikh bai da lafiya ba shi zai sa a ce an ƙi ci gaba da karatu ba,a cikin ajin nan akwai mahadatan

Alkur'ani har biyu Sadiya da kuma A'isha da wannan nake kira a gare su don Allah su taimaki sauran wurin koyon karatu na san in kun yi haka sosai Sheikh zai ji da

ɗ

i in ya dawo” wannan shawarar da ta bayar duk kowa sai yayi amanna da ita,yayin da kuma aka f

ara zuwa suna koyar da karatun haka kawai na ji kishin Sadiya duk da tana yin karatu mai da

ɗ

i sai dai ba ta fi ni iya ƙira'a ba.

Ko motsi ban yi ba ballantana na je ta koyar da ni kasancewar ita A'isha

ɗ

in an tsara wa

ɗ

anda suke yin hadda take yi wa gyar

a.A gabana Mujahida ta je aka koya mata tana zaunawa ita Sadiyar ta

ɗ

ago kai tana kallona,na kawar da kai gefe ina kallon Mujahida wacce zungurar mini ƙafa.

“Ke?” ta furta duk da na san da ni take amma ban ko waiga ba,“ke kin iya karatun ne?” wannan kar

on a gabana ta zo ta tsaya tare da buga table.Na

ɗ

aga kai na dube ta,a girme ta girme mini don ta kusa ninka shekaruna biyu amma da yake shi kishi babu ruwansa da shekaru sai cewa na yi “ai masu ra'ayi ne za a koyar to ni banda shi”

Tana shirin yin maga

na malam Ibrahim ya shigo da sallama,aka amsa masa cikin ladabi kafin shi kuma cike da murna ya ce “na ji da

ɗ

i sosai yadda na ga kun mayar da hankali kuna karatu masha Allah ”

“Malam ita wannan ta ce ba a isa a koyar da ita ba” cewar Sadiya tana mai n

una ni da yatsa.

Malam Ibrahim ya dube ni da kyau kafin ya ce “Khadeeja yaushe kuma kika

ɗ

auki wannan hali?”

Na turo baki gaba ina cewa “ni ban so ta koya mini ne don ban saba yin karatu wajen mace ba in ba Momyna ba”

Kusan ajin dariya aka shiga y

i mini wasu na tsokanata da sunan ƴar Momy,sai da malam ya tsawata musu kafin ya cewa Sadiya “tun da ba ta so ki bar ta kawai,ci gaba da koyar da sauran”

Sai da ta banka mini mugun kallo kafin ta gusa daga inda nake.Mujahida ta ce “ban so kika yi haka b

a yanzu sai ki sa ki yi baƙin jini wurin mutane a yi dubin girman kai ne gare ki”

“To sai me? Su suka sani” na fa

ɗ

i haka ina mai

ɗ

aukar jakata na fice daga ajin,wayata na fiddo na kira direba na ce ya zo ya

ɗ

auke ni.Kusan mintin sha biyar kafin ya iso,n

a shiga baya na zauna kafin na ci gaba da latsa wayata ina aikin da na saba.Shafinsa na facebook na shiga na duba ai kuwa na ci karo da wani sabon hotonsa da ya

ɗ

ora.Kamar wata mahaukaciya sabon kamu haka na yi ta dariya ni

ɗ

aya har sai da direba ya juyo y

a tambaye ni sai a lokacin na nutsu.

Ina isa gida na tarar Daddy na nan,sallama kawai ya amsa mini ya jefo mini tambayar “me kika dawo yi gida?”

“Malaminmu a bai da lafiya shi yasa,yau muka je ganinsa har na saka masa ƙarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login