Showing 39001 words to 42000 words out of 59970 words
jikinsa”
Sake da baki Abba ke kallona kafin
ya ce “wane irin sassan jiki kuma? Ciwon ciki ne fa ya kashe shi ko?”
Ni ma da mamakin na dube shi,kafin na yi wa kaina tambayar ‘ kenan shi Abba bai ga gawar Joy an cire mata ido ba?’ amma don sake tabbatarwa haka na buƙaci mu koma can mutuware.
Da muka je muka shiga ciki na bu
ɗ
e gawar Joy tare da tsure Abba da ido kafin na ce “ka gani ko?”
“Me?” ya tambaye ni,“ba ka ga komai ba?” na tambaye shi ni ma.Ya ce “ka ga David mu je gida” ba tare da na ce komai ba na rufe gawar muka fito.Ko da muka da
wo gida mun tarar da Joyel na yin kuka kamar ranta zai fita ,tana ganina ta zo ta fa
ɗ
a jikina.Ban iya rarrashinta ba kawai na bar ta tana ta yin kukan har ta gaji don kanta ta je ta zube kan tabarma.Mutane sai shigowa suke yi suna taya mu jaje har cikin da
re kuwa,sai da daren ya tsananta sannan ƙafa ta
ɗ
aga.Na je na rufe
ɗ
aki tare da shiga
ɗ
akinsu Ummah na yi zaune kamar yadda su ma
ɗ
in suke zaune in aka cire Joyel da ke bacci.
So nake mu ha
ɗ
a ido da Ummah amma ta ƙi yarda da hakan,da na gaji don kaina n
a miƙe na fita.Sai da na watsa ruwa na
ɗ
an ji sanyi kafin na shige
ɗ
akina,bayan na rufe ƙofa na
ɗ
auko littafin sirri na ajiye kan table.
A hankali ya soma bu
ɗ
e kansa har aka zo a page
ɗ
in da na tsaya,idona ya sauka kan rubutun da ya shafi nasabata.
“BABU WANDA ZAI IYA MALLAKAR LITTAFIN NAN SAI SARKI KO KUMA MAI SHIRIN ZAMA SARKI! DOMIN SANIN DALILI KA BUƊE PAGE TA GABA” shi ne abin da yake a rubuce, wannan karon da kaina na bu
ɗ
e page
ɗ
in ta gaba sai dai wayam take babu rubutun komai a cikinta haushi
na ji kawai na rufe shi na mayar.
Na ja tsuki kafin na kwanta ina shirin lumshe idona na soma jin yanayin iskan
ɗ
akin na canzawa.A nan take na fahimci ta zo,babu jimawa kuwa na soma jin ana shafar jikina tare da sarrafa ni kafin ta mu'amulance ni bayan
nan sai na ji wata irin gajiya da ciwon jiki amma ban iya ko da motsi ba ne a haka bacci ya
ɗ
auke ni.
Wannan karon a wata unguwar nakassu duniyar mafarkin tawa ta kai ni,ko ta ina makafi ne da kurame da guragu da duk wata irin nakasa.Cike da ƙyanƙyami
nake ratsa wurin wanda yake cike da datti da ƙanzata iri-iri,daga bayana na ji an dafa ni.Na juyo da sauri nan na yi arba da wata yarinya wacce ba za ta wuce shekara goma ba a duniya ,fara ce tasss ban ta
ɓ
a ganin mutum mai irin farinta ba.Gashin kanta kuma
wani iri ne kamar na gingiya,idanuwanta blue ne masu
ɗ
an girma duk da kuwa yadda take ta ƙoƙarin ƙanƙantar da su,la
ɓ
anta jajaye ne sirara.
“Ina ne nan?” na tambaye ta.
“Daular Alfanso !” ta bani amsa tare da miƙo mini wani
ɗ
an itaciya wanda shi ma b
an ta
ɓ
a ganinsa ba,hannunta na bi da kallo wanda yake da datti duk laka ta
ɓ
ata shi .Na girgiza mata kai na ce “a'a ban ci”
“Ka kar
ɓ
a dai za ka ji da
ɗ
insa” ta fa
ɗ
a tana yi mini dariya wacce ta bank damar ganin haƙoranta wa
ɗ
anda suka sha banban da na mut
ane don kuwa ba farare ba ne a'a kamar chocolat haka suke da duhu amma wani abin mamaki sosai suka yi mata kyau ƙila don saboda kalar fatarta.Na kai hannu kenan zan kar
ɓ
a na ji muryar Ummah “Davido?” kamar tsawa haka na ji sautin,da mugun sauri na tashi in
a ware ido a kallon farko sai na ga Ummah da wata siffa kanta kamar na Tinkiya amma da na murje idona sai na ga ta dawo normal.
Kafin na kai ga cewa wani abu ta ce “ka tashi ka yi mini rakiya can mutuware ina son ganin gawar
ɗ
ana kafin a rufe shi”
Na ce “an samo ku
ɗ
in bikin jana'izar ne? ”
“Ka same ni a ƙofar gida” ta fa
ɗ
a tare da ficewa,a dole na fita na yi wanka na zo na shirya.Sai da na shiga
ɗ
akinsu,a zaune na hango Joyel ta raku
ɓ
e kamar wata
marainiya,tausayinta ne na ji ya ratsa ni amma ba
n iya yi mata magana ba na fice na samu Ummah a ƙofar gida.Gaishe ta na yi amma ba ta amsa ba,taxi na samo mana muka shiga.Har muka isa babu wanda ya yi magana,sai da na nuna takardar shaida sannan aka bu
ɗ
e mana mutuwaren.Wani irin iska ne mai ha
ɗ
e da huci
n ruhika ya tarbe mu,da sauri muka kalli juna ni da Ummah kafin kuma mu ida shiga.
Gawar Joy na nuna mata,ta bu
ɗ
e tana shafar fuskarsa.A yanayinta kawai na fahimci ita idonta suna gane mata abin da ni ma na gani a tattare da gawar sa
ɓ
anin Abba.
“Je k
a biya ku
ɗ
in wanka a zo a yi masa mu wuce da shi,ba zan bari ya ƙara kwana
ɗ
aya ba a nan” Ummah ta fa
ɗ
a .
Na ce “akwatin gawa fa? Ina za a samu?”
“Ka yi abin da na ce” ta fa
ɗ
a cikin ƙaraji,wani irin tsoron Ummah ne na ji ya
ɗ
arsar mini a ƙahon zuciya
wanda ban ta
ɓ
a jin makamancinsa ba,da sauri kuwa na je na nemi mai gadi na sanar da shi tare kuma da biyan ku
ɗ
i.
Wani matashin saurayi ne aka turo domin yi masa wankan,Ummah ta fita yayin da ni kuma na tsaya.Almakashi yasa ya yage suturar Joy sannan ya
lulu
ɓ
a masa wani zanen,ya
ɗ
ago da niyyar yi mini magana sai kuma na ga ya yi shiru tare da kafe ni da ido har sai da na tsargu na ce “Me?”
“Babu komai! Ammm.. na ce ka ta
ɓ
a ganin an yi wankan gawa irin wannan ko kuwa yau ne farko?” ya fa
ɗ
a .
Na ce “
ban gane irin wannan ba?”
Sai da ya sake dubana da kyau kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake nufi ba, alhalin ga alamun baiwar da ke tattare da kai nan a bayyane”
Na ja ajiyar zuciya don na fahimci abin da yake nufi, wannan yasa na b
asa amsar tambayar tasa na ce “yau ne farko”
Ina fa
ɗ
ar haka sai ya miƙo mini auduga ya ce “ka cusa wannan a ƙofofin hancinka ” na dube shi har zan yi tambaya amma kuma sai na kar
ɓ
a tare da yin yadda ya ce
ɗ
in ,yana fara zuba ruwa a gawar Joy sai na ga g
awar ta yi motsi.Murya na
ɗ
an rawa na ce “kamar fa ya motsa” ya ce “ba kama ba ce motsin ne ya yi” sai kuma ya ci gaba da yin wankan,can sai ga gawar Joy ta tashi zaune kan ƙugunsa.Matashin sai ya ciro wani abu daga aljihunsa ya shayar da Joy,nan take sai
ya soma aman wani baƙin abu ana cikin haka sai kuwa wasu baƙaƙen inuwoyi suka fara bayyana a cikin gidan gawar.....
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*
👻
```LoVe aNd HoRrOr story```
👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SAD
AUKI
💫
✍
️
}
*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya lulu
ɓ
e ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki
👏🏻
*FCWA*
☀
️
________________________
03
Yadda baƙaƙen inuwoyin suka zagaye wurin shi ya haifar da dissashewar ƙwan la
ntarkin mutuwaren.A daidai wannan lokacin ne matashin mai wankan gawa wanda har zuwa yanzu ban san sunansa ba ya soma yin magana.
“Kar ku yi kuskuren ta
ɓ
a patient
ɗ
ina,kun yi naku aikin kun kashe shi yanzu kuma ku bari na yi nawa aikin” ya fa
ɗ
a cikin mu
ryar garga
ɗ
i.Sai kuma na ga duk sun nutsu sun bar motsi,wani abu ya ƙara cirowa daga aljihu ya shafa a goshin Joy nan take gurbin idonsa wanda babu komai a ciki ya soma
ɓ
ul
ɓ
ulowa da jini can sai ga dukkan idanuwansa biyu sun dawo.Kamar yadda mutum mai rai
ke kallo haka Joy ya dube ni da idonsa kafin ya yi baya ya kwanta ya lumshe ido,gefen wuyansa wanda yake a
ɓ
urme nan ma sai da ya zuba maganin da ban san na mine ne ba shi ma ya dawo daidai .
Inuwoyin da suka kawo mana caffa? Tuni sun
ɓ
ace kamar walƙiya
.Na ja ajiyar zuciya na dubi matashin na ce “kana da baiwa ! Haifarka aka yi da ita ?”
“Sunana Nelson
ɗ
a ga Sarkin yaƙin Daular Uganda ” ya bani amsar da ba ita na tambaye shi ba yana mai ci gaba da gyara gawar Joy har ya kammala.
Ƙ
ofa aka bu
ɗ
e,mai g
adi ne da wani suka shigo suka kawo akwatin gawa sai muka ha
ɗ
u mu duka hu
ɗ
un muka saka gawar a ciki. Tare da fito da ita aka saka a mota,Ummah na duba sai na ga tana kallon Nelson na
ɗ
an matsa kusa da ita na ce “ko kin san shi ne?”
“Mutane na can gida s
una jiranmu mu je” shi ne abin da ta fa
ɗ
a tare da yin gaba,na juya na kalli Nelson wanda shi ma na ga yana kallon Ummah wani iri.Na ce “na gode ” ya jinjina kai.Sai na wuce na shiga mota,kusa da ita na zauna kafin na ce “a ina kika samu ku
ɗ
i?”
Ko kallon
a ba ta yi ba,a haka muka ƙarasa gida.Tun da muka shigo layinmu na soma jin ƙarar sautin ganguna ana ki
ɗ
e-ki
ɗ
e,muna isa aka zo aka sauke gawa aka ajiye ta a wurin da aka yi mata tanadi aka ci gaba da yin ki
ɗ
a da rawa da waƙe-waƙe.
Hannuwana na har
ɗ
e ina
kallon akwatin da ke
ɗ
auke da Joy,duk wasu tsoffin moments
ɗ
inmu ne suka ta kawowa ƙwaƙwalwata ziyara ina tuna yadda yake mugun sona da girmama ni.Wasu hawaye masu
ɗ
umi ne suka zubo mini,daga bayana na ji muryar Isa yana cewa “David ashe rasuwa ƙanenmu ya
yi? To Allah ya jiƙansa ya yi masa gafara,yanzun nan muka dawo daga wurin interview tun jiya da muka tafi”
Na ida juyowa ina kallonsu,tsabar yadda hankalina ya
ɗ
an gushe sam ban san mene ne shi Abdul ke fa
ɗ
a ba kawai dai na ga bakinsa na yin motsi.
Ji nake yi kamar na shaƙe musu wuya na kashe su kamar yadda suka yi wa
ɗ
an uwana,amma wani sashe na zuciyata na bani wata irin shawara mai muhimmanci wacce nake ganin ita ce daidai da rayuwarsu.Rungume su na yi a tare na soma kuka biyu,
ɗ
aya na rashin ƙanen
a
ɗ
ayan kuma takaicin rungumar da na yi wa abokana kuma manyan maƙiyana.Rarrashina suka fara,ina jin yadda suke sauke ajiyar zuciya mai nuni da sun samu salamar ruhi,ƙila suna tsoron kar a ce na fahimci suna da hannu a mutuwar Joy.
Ke
ɓ
a
ɓ
en wuri muka zau
na har zuwa lokacin da manyan pastoci suka ƙaraso duk kowa ya miƙe.Addu'o'i suka fara yi kafin a bu
ɗ
e akwatin gawa aka cewa Abba da Ummah su zo su yi masa kallon ƙarshe,sai dai wani abin mamaki Isa da Abdul ƙoƙarin kutsawa suke yi ban san mene ne nufinsu b
a amma dai ina da tabbacin ba mai kyau ne ba wannan yasa na kasa na tsare na ƙi bari su gusa daga kusa da ni.
Abdul ya shiga matso ƙwallar munafurci yana mai cewa “bari na matsa na ga ƙanenmu shikenan mun rabu da shi yaro mai kirki” hannunsa na yi sauri
n riƙewa na ce “kar ka tafi” sam ban yi tunanin furicina zai yi babban tasiri ba,kamar wani dutse haka Abdul ya kasa motsi da Isa ya so matsawa kuwa iya kallo na yi masa shi ma ya kasa wani kata
ɓ
us har aka rufe akwatin gawar aka
ɗ
auke shi domin kai shi mak
wancinsa.Muna tafe ana waƙa har aka isa maƙabarta aka binne shi sannan muka dawo gida ,abinci aka rarraba da abun sha daga nan mutane suka
ɓ
age da yin hirarrakin duniya.
Su Isa kuwa kasa zama suka yi haka suka yi mini sallama suka tafi,ni ma wuraren ƙ
arfe shidda haka na silale na tafi can mutuware na kuwa ci sa'a na ga Nelson.A zaune na tarar da shi yana shayi,muna ha
ɗ
a ido ya sakar mini irin murmushin nan na dama na san za ka dawo.Gefensa na samu na zauna kan banci kafin na ce “barka da warhaka”
Ba tare da ya amsa ganuwar da na yi masa ba ya ce “ka yi nasarar hana su jefa ƙwayar cutar tsafi a cikin akwatin gawar ƙanenka amma hakan ba shi ke nufin yaƙi ya ƙare ba,akwai sauran rina a kaba”
Na dube shi da kyau na ce “me zai faru kuma?” sai da ya m
iƙo mini kofin shayi sannan ya ce “za su sake yunƙurin cikar burinsu ta hanyar farmakar kabarinsa tabbas za su je”
Hankali tashe na ce “mene ne mafita?” sai da Nelson ya yi mini wani kallon tsakiyar ido kafin ya ce “ka tambayi littafin sirrinka ”
Ƙ
ya
f-ƙyaf na yi da ido ina mamakin ta ya aka yi ya san ina da littafin sirri,amma sai kuma na ƙi yarda na nuna na san abin da ma yake nufi don ƙila shi ma aiko shi ne aka yi.Na ce “wane littafi kuma?”
Wata dariya ya yi kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka
san abin da nake magana akai ba,za ka iya yi wa kowa ƙarya amma banda ni don haka ka bar
ɓ
oye-
ɓ
oye littafin sirrin Ruhaniya yana hannunka”
“Kai ta ya aka yi ka sani?” na tambaye shi.
“Saboda mahaifina ne mawallafin littafin ” ya bani amsa kai tsaye,n
a ce “kenan ba Aljanu ne suka rubuta shi ba?”
“Akwai wani banbanci ne tsakanin matsafi da Aljanu?”shi ma ya tambaye ni.
“Wane ne matsafi?” na sake yi masa sabuwar tambaya,ya bani amsa da “ni da kai”
“Ni ba matsafi ba ne”
“Da ace zancenka gaskiy
a ne to da littafin sirri bai za
ɓ
e ka ba matsayin wanda zai karanta shi ya kuma maido tarihin ƙarnin baya” Nelson ya fa
ɗ
a yana kallon kofin shayin da ya bani wanda har zuwa yanzu ban sha ba,saurin shanye wa na yi na miƙa masa kofin ina shirin yin magana na
ji wani irin rau da idona kamar an watsa mini yaji.Bibbiyu nake ganin Nelson wanda ya soma karanto wasu
ɗ
alasiman tsafi yana mai jimƙe hannuna,kamar wata leda haka ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka yi sama muna shawagi cikin sararin samaniya.Tun ina kallon d
uniya cikin hayyacina har na neme shi na rasa,ko da na dawo normal a wani ru
ɓ
a
ɓ
en
ɗ
aki na tsinci kaina a kwance kan gadon kara irin na ƙarnin farko.Da sauri na tashi zaune ina dafe kaina da ke mugun sara mini,daidai nan aka bu
ɗ
o ƙofa wani tsoho ne ya shigo
hannunsa riƙe da sandar tsafi sai wani sheƙin baƙar azaba take.
“Ka tashi? Barka da zuwa fadar Jacki! Ungo wannan na san ba za ka rasa jin yunwa ba” tsohon ya fa
ɗ
a yana mai miƙo mini wata guntuwar gurasa da ya ciro daga aljihunsa.
“Wane ne kai? Me
nake yi a nan?” na tambaye shi a harzuƙe ina mai miƙewa tsaye,kafin ya bani amsa Nelson ya shigo a hasale na yi cikinsa zan kai masa naushi amma abin mamaki tsohon nan na nuna sandarsa kawai na yi baya cikin iska na dawo na fa
ɗ
a kan gado.
Cikin bayar
da umarni ya ce “ka nutsu da kyau don za ka fi fahimtar dalilin zuwanka nan” nutsuwar na yi don ban ga hanyar
ɓ
ulle mini ba muddin na kawo gardama.
Ya saki
ɗ
an murmushi kafin ya ci gaba da cewa “wannan
ɗ
ana ne,na san ya baka labarin cewa ni ne Sarkin y
aƙin wannan Daular ta Uganda.Ni ne babban abokin mahaifinka,duk wata shawara da za a zartar a masarauta ni ne nan ne basa ita a ƙarshe dai ina son ka
ɗ
auki
ɗ
ana Nelson matsayin mai baka shawara”
Wata dariya na yi kafin na ce “ni kuma meke ha
ɗ
ina da Ugan
da da kuma sarauta?”
Bai ce komai ba sai sandarsa da ya nuna a kusurwar
ɗ
akin nan take wani haske ya fito mai kamar madubi kafin kuma wata madaidaiciyar ƙofa ta bayyana.Na waro ido ina mai miƙewa tsaye,a hankali na taka na isa can na yi tsaye.Wata masar
auta ce idona yayi tozali da ita,kamar dai a mafarkina kusan duk al'ummar yankin suna da nakasa
ɗ
ai
ɗ
aiku masu lafiya.Ina cikin baza ido kuwa kallona ya sauka kan yarinyar nan,tabbas ita ce na gani ko shakka babu yarinyar da ta bani ƴaƴan itaciyar.Tana tsay
e tana kallon wani gun idonta na zubar da ruwan hawaye,inda ta tsure da ido na duba sai na hangi wani babban mutum cikin na