Showing 12001 words to 15000 words out of 59970 words
ruwa.Wallahi Daddy sai n
a ji na matsu a koma Makarantar boko don na ƙara ci gaba da karatuna daga inda na tsaya,ka ga shi kenan in Sheikh bai da lafiya ni ce zan dinga duba shi” yadda Daddy ya kafe ni da ido ko ƙyaftawa bai yi shi ya fargar da ni kan kwabsawar da na yi.
Sai na
rufe bakina da hannu ina mai waro ido.Ya ce “kafin ki amsa mini tambayoyin da zan jero miki da farko fara bani amsar me yasa yanzu kika bar saka niƙafi?”
Na
ɗ
an kwa
ɓ
e fuska kafin na ce “Daddy ta
ɓ
ata ni ma ban san inda take ba,kuma ita ka
ɗ
ai gare ni du
k na yi kyauta da sauran saboda na yi wa Momy alƙawari wacce ta saya mini kawai zan dinga sakawa”
“Na ji! Yanzu yaushe kika zama likitar malaminku?”
“Daddy ba fa abin da kake tunani ba ne,kawai mun je ganinsa ne sai likitansa ya gagara samun jijiya s
hi ne na nemo” na basa amsa ina mai sunne kai ƙasa zuciyata na dakan uku-uku saboda ganin kamar ran Daddy ya
ɓ
ace.
“Wane Sheikh ne za ki dinga yi wa magani in bai da lafiya?”
“Ƙanena wanda Momy za ta haifa mini” na basa amsa ina mai yin wani murmushi
duk a tunanina zan iya yi wa Daddy wayo,shi ma martanin murmushin ya maido mini kafin ya ce “to je ki in kin huta ki gyarawa Umma
ɗ
aki yau da maraice in sha Allah za ta zo”
Wani irin tsallen murna na yi ina mai cewa “a
ɗ
akina za ta sauka Daddy”
Ya c
e “kin sani sarai da Ummah ba ta iya hawan sama ciwon ƙafa take”
Na soma kukan sangarta kafin na ce “a'a Daddy kar ka bari ta ji haka please ka bari na sauke ta a
ɗ
akina”
Kai kawai ya girgiza,ni kuwa ina haurawa sama na ƙara gyara ko ina duk da kuwa
mai aiki ta gyara shi.Toilet na shiga,ina cire sutura ta sai na samu kaina da tsayuwa gaban mirror
ɗ
in da ke manne a bango.Na yi murmushi ina jin wata irin kunya ganin surata a ciki,sai nake ganin tamkar mirror
ɗ
in idon Sheikh ne.Da sauri na gusa na je na
yi wanka na
ɗ
aura towel na fito,kafin na kimtsa sai da na ƙara shiga shafin Sheikh Rayyadeen na yi bincike a nan ne na ga nan da sati biyu yake birthday na cika shekara arba'in da biyu.
Ina shafa mai ina tunanin irin gift
ɗ
in da zan basa,a haka har na s
hirya na sauko ƙasa.Daddy tuni ya tashi,motsin da nake ji a kitchen yasa na nufi can yau ma kamar kullum Momy ce ke a tsaye tana girki Baba Laure na taimaka mata.
Kusa da ita na ƙarasa ina mai jingina kaina a kafa
ɗ
arta tare da kallon abin da take dafawa
cikin tukunya.
“Momy kan rago za mu ci?” na fa
ɗ
a ina ha
ɗ
iyar yawu.
“Na Ummah ne” ta bani amsa tana yin murmushi mai sauti,na ce “to ai tare za mu ci”
“Na sani! Je ki ma ki dama fura na can kan dinning ”
“Momy na gaji please ki saka Baba Laure
” na fa
ɗ
a a shagwa
ɓ
e ashe rabon a yi mini fa
ɗ
a ne,nan ta soma balbale ni da masifa har da su cewa “wato duk yadda na tsaya kai da fata ina yi wa ahalina hidima ke ba za ki iya yin koyi da ni ba? Dama furar shi ne kin gaji? An fa
ɗ
a miki zama mace raggonci y
ake nufi? To gara ma ki jajirce don in kin yi aure babu wanda zai yi miki aikin gida ke za ki yi abinki ”
Ina turo baki ina ƙari na fita na je na
ɗ
auki furar na dama,bayan na gama na saka ta a frigo don ta yi sanyi.Sai kuma na koma kitchen na soma kama
mata aikin,ina kallon yadda Ammy ke sakin murmushi.Bayan mun gama komai muka jera a dinning kafin mu yi sallah,duk yadda Momy ta matsa mini kan na ci abinci ƙin ci na yi don na yi alƙawari tare da Kakata za mu ci.
Sai yamma lis sannan Ummah ta zo,tuni
lokacin yunwa ta gama galabaitar da ni amma ina ganinta na neme ta na rasa na je da guduna na rungume ta.
“Haba Deeje ya isa haka kar ki kayar da ni ” Ummah ta fa
ɗ
a tana dariya,na yi baya ina turo baki ina mai cewa “ni dai wallahi ba Deeje ba ke dai ce
sunanki ke haka”
Ta yi dariya ta ce “ ai sunan dai nawa ne ubanki ya ara ya maƙala miki”duk aka yi dariya,bayan gaishe-gaishensu ita da Momy aka gabatar da abinci har za ta je ta yi wanka amma na hana ta ina mai cewa “ƙawali wallahi in har sai kin yi w
anka mutuwa zan yi kafin ki fito” na fa
ɗ
i haka ina mai riƙe ciki.
Da sauri kuwa ta zauna muka ci abinci,sai dai kamar abin tsiya ina ci zazza
ɓ
i ya rufe ni saboda jimawar da na yi ban ci ba haka na yi ta yin amai wanda hakan ya galabaitar da ni sosai.Ni
da na so na sauke Ummah a
ɗ
akina a ƙarshe dai can sashen da ake sauke ta kullum in ta zo muka tare ni da ita.
★
SHEIKH RAYYADEEN
Yana cikin mazan da ba kasafai sha'awarsu ke motsawa ba,amma in abin ya taso masa kamar zai yi hauka.A daren da Ammy ta
barsa bayan ya fa
ɗ
a mata sunan Khadeeja ikon Allah ne kawai da kuma sauran shan ruwa gaba yasa bai mutu ba.Kamar yadda in gobara ta kama take ci bal-bal haka dukkanin illahirin ga
ɓ
ansa ke kukan a kawo musu
ɗ
auki.Bai da wani buri in banda ya samu mace a
ga
donsa sai dai hakan ba mai yiyuwa ba ne saboda bai ta
ɓ
a yin aure ba.Ƴan matan da ma aka ta
ɓ
a yunƙurin aura masa su ko da shi bai so to
ɗ
aya bayan
ɗ
aya haka suke mutuwa ba tare da ya san dalili ba.
Muguwar kasala ce ta ci karo baƙin cikin da ya da
ɗ
e yana
cin ransa har suka yi galabar kwantar da shi jinya.A ranar da ya je makaranta domin saka hannu a takardar da za ta bada damar turo sabbin
ɗ
alibai ajinsa jikinsa yayi
ɗ
an dama-dama sai kuma aka yi rashin sa'a ya ci karo da Khadeeja tana gudu a filin makara
nta dukkan jikinta na motsawa duk da kuwa tana sanye da hijabi.Ba tare da yayi abin da ya kawo shi ba ya juya ya koma,nan ne ciwon ya ƙara rikice masa.
Yau kuma da suka zo duba shi yadda ta ta
ɓ
a hannunsa sai da ya shiga wani yanayi,dauriya kawai yayi sa
boda a gaban
ɗ
alibansa ne.
Abin da ya
ɗ
an mantar da shi wannan yanayi shi ne shigowar Rashida cikin mawuyacin hali.
Ko da ya dawo daga
ɗ
aukar habbatu sauda sai ya biyo da gawayin zamanin nan da ake kunna shi da ashana.Hannunsa har rawa yake yi ya kunna
tare da zuba ta ciki,nan fa Rashida ta soma yin tari yayin da shi kuma ya soma yi mata karatu.Dakyar aka samu ta dawo hayyacinta,Ammy ta ƙanƙame tana wani irin kuka kafin ta ce “don Allah ki yafe mini”
“Laifin me kika yi mini da za ki nemi yafiyata? Ai
ko ma kin ta
ɓ
a yi na yafe miki ” Ammy ta fa
ɗ
a .
Rashida ta girgiza kai tana mai cewa “a'a na yi miki laifi mai girma Ammy,na ci amanarki na rogaza tarbiyyar da kika yi mini”jikin Ammy ya yi sanyi sosai ta ƙara rungume Rashida tana kallo Sheikh wanda ha
ka kawai ya ji zuciyarsa na bugawa.
Rashida ta bu
ɗ
e baki za ta yi wa Ammy bayanin dalilin ciwonta amma Sheikh ya dakatar da ita yana mai cewa “Ammy tana buƙatar hutu don haka a bata magani ta sha”
Ammy ta jinjina kai ta ja ta zuwa can sashenta ,garin
tafarnuwa na habbatu sauda da zuma ta ha
ɗ
a ta bata ta sha babu jimawa kuwa ta soma yin bacci wanda ba a
ɗ
auki lokaci ba ta tsinci kanta wani wurin sai dai kuma ta shaida
ɗ
akin da take ba kowane ne ba sai na Grand-Maa.
Babu jimawa fuskarta ta bayyana a
gare ta tana mai cewa “wato kin zo ki sanarwa da Ammynki abin da ke damunki? Wato asirina za ki tona? To ki sani wannan baccin shi ne za ki yi ta yi har ƙarshen rayuwarki don ba zan bari ki farka ba” Grand-Maa ta fa
ɗ
a tana mai bu
ɗ
e bakin Rashida ta zuba ma
ta wani rubuta da aka rubuta kalmomin tsafi,tana gama zuba mata shi kuwa Rashida ta soma fizge-fizge wanda hakan ya jawo hankalin Ammy ita kuma ta kira Sheikh.Babu jimawa suka kwashe ta zuwa asibiti ba tare da sun san cewa ba a uƙuba suka jefa ta ba.......
[13/12 09:05] MRS SADAUKI: *MAFARKI*
👁
️
🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar :
🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI
💫
✍
️
```
05
An kwantar da Rashida kan ga
don asibiti da tunanin za ta samu lafiya sai dai abin da Ammy ba ta sani asibitin cike take da miyagu don kusan maguna/ƙuliyoyin da ke yawo mutane ne a cikin siffar mage.Sheikh bai wani jima ba wannan yasa lokacin da wata mage ta shigo sam babu wani mai ja
rumtar da zai hana ta,ita Ammy ta yi tunanin normal mage ce har da cilla mata guntun burodi amma maimakon ta ci a'a sai suka da ta yi ta haye gadon da Rashida ke kwance tana mai yagarta a fuska har sai sawun akaifunta suka fito ra
ɗ
au tare da jini.
“Inna
lillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Ammy ta fa
ɗ
a tare da zuwa ta cabko magen,sai dai madadin ta ji tsoka a'a wani irin abu ta ji kamar lagwami kafin ta ƙyafta ido sai ga mage ta koma tsumma.Ammy ta yi wurgi da shi tare da komawa gefe tana zarar ido ha
ɗ
i da y
in duk addu'ar da ta zo bakinta.Babu jimawa wata nurse ta shigo,babbar mace ce don za ta kai sa'an Ammyn.Kicin-kicin da fuska ta shigo tare da miƙawa Ammy takarda ta ce “wannan maganin muke so ki je ki nemo”
Da
ɗ
an mamaki ta dube ta sannan ta ce “kafin
yarona ya tafi ai ya bada ku
ɗ
i masu yawa ya ce ko buƙatar wani abu ya tashi ku cire ciki”
“To ban yi niyyar cira a ciki ba,ungo ki sayo ko kuma ku fita ku bamu asibitinmu ” ta fa
ɗ
a tana wani ƙanƙance ido tana yi wa Ammy wani irin kallo wanda ba baƙo
ba ne a wurinta,kusan kullum Grand-Maa na yi mata shi,kuma sosai take tsoronsa.
Ba tare da ta ce komai ba ta jawo waya ta kira Sheikh ,sai dai har ta yanke bai
ɗ
aga ba.Sam Ammy ji ta yi ba ta iya fita ta bar ƴarta ita
ɗ
aya,kawai sai ta tura gadon da ka
nta har ta fito waje.Mai tsaron get ne ya je ya taro mata mai taxi,haka shi ya taimaka mata ta saka Rashidar.Ammy na shirin shiga taxi ya dakatar da ita tare yi mata magana can ƙasan maƙoshi “ciwonta ba na asibiti ba ne Hajiya,in son samu ne ki mayar da it
a gida don ina mai baki tabbaci kusan duk asibitocin yanzu irin wannan ce duk miyagu sun fi yawa.Da zarar kuma kun shiga akwai wani dafi a cikin ruhinta da zai jawo hankalin sauran miyagun zuwa gare ta”
Ammy na jin haka ta yi masa godiya har da basa ku
ɗ
i kafin ta shiga,har sun
ɗ
auki titin wata asibiti amma ta ce ya kai ta can gida,ta kwatanta masa unguwar.Tun kafin su isa ta kira Mama a waya ta shaida mata, wannan yasa taxi na tsayawa ta zo ita da Aliya suka kama mata suka shigar da Rashida ciki.Baiwar
Allah numfashi ma dakyar take yinsa,kallo
ɗ
aya Mama ta yi mata ta fahimci damuwar hakan yasa cikin dauriyar zuciya ta ce “Khadi ina neman alfarma ki kai Rashida
ɗ
akina na yi jinyarta”
Zaman amana suke yi da kwanciyar hankali wannan yasa Ammy ko tunani b
a ta yi ba ta amince suka kai ta can.Mama ba ta
ɓ
ata lokaci ba ta soma yi wa Rashidar hayaƙin turaren Mayu,duk
ɗ
akin ya turniƙe da hayaƙi.A hankali ta soma yin tari alamun ta sake dawowa duniya a karo na biyu,ta bu
ɗ
e idonta wasu hawaye na yi mata zuba.Maƙo
shinta take jin an riƙe shi gam an yi masa mugun ƙulli wanda ba ta
ɓ
atawa kanta lokaci wurin gwada yin magana ba tuni ta fahimci abin da ke faruwa da ita,babban tashin hankalinta kuma bai wuce sanin ashe Grand-Maa ce wannan tsohuwar da ta ta
ɓ
a bayyana a ga
bansu ga shi kuma ba ta da bakin da za ta iya yin bayani.
Ɗ
akin ne ya dawo normal duk hayaƙin ya
ɓ
ace,sai a lokacin Mama ta ga idon Rashidar a bu
ɗ
e sosai ta ji da
ɗ
i duk da dama ta san da wuya mutum ya shaƙi turaren nan bai farfa
ɗ
o ba.
“Ya jikin nak
i?” ta tambaye ta ,da kai ta amsa mata kafin ta ja fatun idonta ta rufe tana tunanin duk wannan tashin hankalin ya faru ne silar binciken wayar miji.
A can
ɓ
angaren Sheikh Rayyadeen kuwa tun bayan da ya dawo daga asibiti ya shige
ɗ
akinsa,wani irin tuƙ
iƙin baƙin ciki ne ke rufe shi yadda ƙanƙanuwar yarinya ta raina shi ta nuna masa taurin kai.Ji ya yi ya matsu gobe ta yi don ya je makaranta,yana son yi mata hukunci mai tsauri domin ta shiga hayyacinta.
Zama ya yi ya
ɗ
auko system
ɗ
insa yayi bincike,yana
nan zaune Ammy ta shigo ta sanar da shi halin da ake ciki kafin ta ƙara da cewa “Sheikh ina ga lokaci ya yi da zan koma ƙauyen nan da na ta
ɓ
a fa
ɗ
a maka zan je na kar
ɓ
owa Rashida magani wurin tsohuwar nan”
Ya
ɗ
an ja numfashi kafin ya ce “amma Ammy kin t
abbata ba shirka ba ce ?”
“Magani ne kawai fa take bayarwa,ba ta yin dibo kai ne da kanka za ka fa
ɗ
a mata matsalolinka sai ta baka maganin da ya dace.Shekarun da suka shu
ɗ
e ita ce ta bani magani na sha har na samu cikinka ya tsaya ban yi
ɓ
ari ba”
“Ya
ushe za mu tafi?” yayi tambayar don ya san tun da ta ce za ta je to in ba zuwan suka yi ba to ba zai samu kanta ba.
“Yanzu!” ta basa amsa tare da miƙewa ta fita wanda tuni ya fahimci me take nufi, wannan yasa ya miƙe ya kimtsa.Ba su wani
ɗ
auki lokaci ba
suka fito ,direba ne ya ja su sannan babu wanda ya san sun fita.Tafiya ce ta awanni wajen biyar, Sheikh na baya zaune kusa da Ammynsa wacce ba sai an fa
ɗ
a maka hankalinta ba kwance yake ba.
Sallah kawai ke tsayar da su,abinci ma iya direban ne kawai ya
ci har suka isa ƙauyen wanda iya idonka kawai sun isa su yi maka fassararsa.Kirarin da suke yi wa ƙauyen BABU RABON MUGU A CIKI,ko ta ina ka duba wasu alamomi ne masu nuni da kariya a haka Ammy ta dinga nuna masa hanya har suka isa ƙofar gidan tsohuwar sa
i dai aka samu akasi a rufe yake.
Duk fitowa suka yi, Sheikh ya ce “ga shi gidan a ƙargame ba ki da lambarta?”
“A'a bani da,ga wani yaro can tambayo mana shi ka ji ƙila tana nan kusa ”
Da hannu Sheikh ya kira yaron, Ammy ta ce“ ina tsohuwa mai w
annan gidan don Allah?”
“Ta tafi birni yau
ɗ
in nan” ya bata amsa.
“Amma ko ka san yaushe za ta dawo?” kai ya girgiza,ba su da wani za
ɓ
i a dole suka koma cikin mota.Cike da takaicin rashin ganin tsohuwar suka juyo mota,ba su kawo gida ba sai cikin dar
e suna shiga suka ƙara tarar da wani tashin hankalin Rashida ta farka sai dai ba ta cikin hankalinta har yawu ke yi mata zuba.Haka Ammy ta sa kuka tana yi,yayin da Mama ke cewa “wallahi ban san abin da ya faru ba ni dai na bar ta a
ɗ
aki ta bu
ɗ
e idonta daga
in shiga kitchen in fito ne na same ta tana ƙyalƙyata dariya”
Sheikh dai bai ce komai ba sai kofi ya samu ya zuba ruwa ya yi mata addu'a,wurin fa shan ruwan ne aka yi daga don sai da aka dadanne ta aka
ɗ
ura mata su.Baiwar Allah sai ta soma jan ajiyar