Showing 24001 words to 27000 words out of 59970 words
son rashin kunya da tsaurin ido,duk wanda ya yi mini
ɗ
aya daga cikinsu zane shi nake yi” ya ida furicin tare da juyowa rai
ɓ
ace hannunsa na gani riƙe da bulala.
Ko ka
ɗ
an ban ta
ɓ
a tunanin zai doke ni ba,shau
ɗ
ar da ya yi mi
ni ita ta maido ni daga duniyar mamakin da na tsunduma.Na ƙara tare da sosa wurin,cike da masifar da ban san yana da ita ba ya ce “wato don kin ma raina ni ina yi miki magana hankalinki na wani wuri ,zaunaaa ” ya ƙarashe tare da sake sha
ɗ
a mini bulalar a k
aro na biyu.Babu shiri na zube kan gwiwaina,ya
ɗ
aga zai yi mini ta uku na yi saurin kamo ƙafarsa cikin kuka na ce “don Allah Sheikh ka yi haƙuri ba zan sake ba,amma kar ka doke ni ban so” hannuwan nawa da na riƙe masa ƙafa ya sha
ɗ
e na sake shi da mugun sau
ri ina jin wani zafi yayin da shi kuma ya wani ja da baya yana jan numfashi kamar zai mutu.Ba tare da ya bani damar fita ba na tashi a guje na bar ajin na nufi namu inda muke karatu.Kamar an jefo ni haka na fa
ɗ
a ciki ina matsanancin kuka, Mujahida da ke ku
sa da ni ce take cewa “a kullum ina fa
ɗ
a miki ki rage wannan shagwa
ɓ
ar taki nan makaranta ce ba komai ne za ki nuna ke ƴar Daddy ce ba amma ba ki saurarena.Wa
ɗ
anda ke kusan window sun ga duk abin da ya faru,tun bayan fitarki ake cece-kuce don ma malam Hafi
z ya shigo ya tsawatar ne da ƙila sun ta yi miki dariya”
Kanzil ban ce mata ba don baƙin ciki,ita da ya kamata ta yi rarrashina amma ta zo tana yi mini surutu.Na
ɗ
auki kamar minti biyar kafin na ji sallamarsa,duk aka amsa masa kuwa.Gudun kar na yi wani
laifin na gyara zamana ina shafar ido,tambayoyi ya fara nan uwar iya yi Sadiya ta shaida masa ni ka
ɗ
ai ce na ƙi zuwa a koyar da ni.
Idonsa masu masifar tsoratar ni ya zubo mini,kamar daga sama na ji ya ce “zo ” kasa motsi na yi don duk a tunanina dukana
zai yi.Duk ƴan ajin suka zubo mini ido,ina jin Mujahida na salalami “innalillahi!”
Wani abin mamaki yana cewa na je
ɗ
in ya
ɗ
auke idonsa a kaina ya soma bu
ɗ
e alƙur'ani.Zuciyata na
ɗ
an dokawa na tashi ,kamar mai koyon tafiya haka na ƙarasa kusa da babban
teburin gabansa na ja na tsaya.
“Me yasa ba ki son yin karatun Alkur'ani? Ko ba ki iya komai ba kawai turo ki aka yi aji na gaba?” ya tambaye ni tare da
ɗ
ago kai,ni kuwa kayan jikinsa nake kallo yadda ya wani cire rigar sama kawai don na tofa masa
yawu.
“Kwashi kayanki ki koma tsohon ajinku ” ya fa
ɗ
a a hankali amma kana iya jin feshin wutar da zuciyarsa ke yi.
Sai a lokacin na yi magana “ka yi haƙuri na iya karatun ne”
Hannuwansa ya game wuri guda ya
ɗ
ora ha
ɓ
arsa tare da tsura mini na mujiy
a kafin ya ce “ina jinki Malama koyar da ni”
Da sauri na sunne kai ina murmushi don na fahimci me yake nufi.Ya turo mini Alkur'ani wanda shi ne da kansa ya bu
ɗ
e mini shafin,idona cikin nasa na jawo alƙur'anin tare da juyo shi gabana na soma karantawa ci
kin ƙira'ar da Daddyna ya koyar ni,sam ban ta
ɓ
a sanin ainahinta ta Sheikh Rayyadeen
ɗ
in ce ba saboda in banda cikin sallah ban ta
ɓ
a jin yana koyar da karatu ba.
Daga can baya na ji muryar A'isha tana cewa “ma sha Allah! Yau dai mun ji wacce ta iya bin
ƙira'ar Sheikh ” duk sai wasu suka shiga yin murmushi mai sauti.
Ni kuwa shi na kalla sai na ga ya ƙara ha
ɗ
e rai kuma ko arzikin kallo ban ƙara samu ba haka ya dinga yi mini binciken karatun kamar wani makaho har ya kammala ya ce na je na zauna.
Ƙ
in tafiya na yi na sake cewa “don Allah malam ka yi haƙuri ka bar fushi da ni, wallahi muddin ka ci gaba da yi to ba zan samu sukuni ba har abinci ba zan ci ba”
Yadda duk mutane suka zubo masa ido suna kallo yasa shi cewa “na ji to tafi ki zauna”
Na
ɗ
an yi murmushi na ce “da gaske ka haƙura?” ya jinjina mini kai cike da murna na je na koma wurina na ci gaba da kallonsa cike da so.Shi kuwa Sheikh Rayyadeen karatu ya soma koyar mana, lokaci zuwa lokaci haka nake tsintar idonsa cikin nawa a haka har aka
fita shan iska.
Muna fita na rungume Mujahida tare da bata labarin yadda muka kwashi adashen tsiya ni da Sheikh bayan na tofa masa yawu daga ƙarshe na ƙara da cewa “wannan dukan da ya yi mini sosai na ji da
ɗ
insa,kin ga yau zai wuni da tunanin abin”
T
a ja tsuki tana mai cewa “ni dai wuce mu tafi mu yi sauri mu dawo kar lokacin dawowa aji ya yi mu kuma muna can”
“Ina za mu tafi?” na tambaye ta,sai ta waro ido tana mai cewa “asibitin mahaukata ko kin manta?” ina shirin yin magana wani abu ya
ɗ
auki han
kalina yadda Sadiya da ƙawayenta suka tunkari aji alhalin Sheikh na ciki.
Da wani mugun sauri na ja hannun Mujahida muka zagaya bayan aji don ta can ne zan fi jin abin da za su yi wurin nasa.
Kunne na kasa ina saurare,ina jin lokacin da Sheikh ya ce “i
na jinku me kuka zo yi?”
Kame-kame suka fara kafin
ɗ
aya ta ce “dama...dama mun zo ne mu sanar da kai
ɗ
aya daga cikinmu ce ke sonka shi ne kawai”
Na yi tunanin zai balbale su da masifa,zuciyata har wani bugawa ta yi jin ya ce “ita wacce ke son nawa ba
ta da baki ne sai ke? ”
“A'a malam ba haka ba ne kunya take ji”
“To ku fita ku bani wuri” ya fa
ɗ
a .
“Sadiya ki fa
ɗ
a masa mana” na ƙara jin wata ta fa
ɗ
a ,ƙiri-ƙiri Sadiya ta canza harshe zuwa larabci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen tana sonsa har da
su cewa in bai aure ta ba mutuwa za ta yi.
Ban san matakin fushi da kuma tashin hankalin da na tsinci kaina ba,sai da na ji ƙusoshin kaina na kwancewa yayin da wani abu ya soma yi mini motsi da mugun ƙarfi na ƙwala wata razananiyar ƙara wacce ta kara
ɗ
e dukkan makarantar.Duk wata bishiya da ke da kwai sai da ta ka
ɗ
a cike da razani, wannan karon hankalina bai gushe ba duka ina jin lokacin da Sheikh ya leƙo ta window yana tambayar Mujahida wacce ke faman riƙona.
Can kuma suka zagayo su duka hu
ɗ
un,cikin
bayar da umarni yasa aka kai ni ajin malamai.Karatu ya soma yi mini su kuma suna tsaye a kaina, Mujahida kawai ce ta riƙe ni.Kamar zan mutuwa haka nake ji,shigowar malam Ibrahim ce yasa sauran suka fita iya ƙawata ce kawai ta tsaya.
Wani abu ya shaƙa m
ini a hanci wanda ya kusa kai ni lahira ban shirya ba,wani irin ƙarfi ne ya zo mini na turo Mujahida zan gudu.Sheikh Rayyadeen ya riƙo ni da hannu
ɗ
aya tare da mini wani riƙaƙen kamu wanda na kasa kubcewa,ci gaba yayi da karatun yana bugun tsakiyar bayana
da hannunsa.
Kamar ana ruwa haka na soma jin wani sanyi na rufe ni,yayin da wani abu mai zafi da ke cikin jikina ke yin ƙasa.Kamar wata ƴarsa haka yake ganin Khadeeja,shi sam bai ma ta
ɓ
a ganinta matsayin cikakkiyar budurwa ba duk in Ammy na yi masa zan
cen ya aure ta har mamaki yake ji.
“Khadeejatu?” muryar malam Ibrahim ta daki kunnena, lokacin tuni na ida samun cikakken hankalina.A hankali na sa hannuna kan na Sheikh Rayyadeen don cire nasa da yayi mini mugun riƙo don har wani zafi nake ji.Sai da
ya kalli tsakiyar idona kafin ya sake ni,a hankali na miƙe kamar zan fa
ɗ
i Mujahida ma ta tashi tana mai kamo hannuna.
“Ya jikin naki?” ya sake tambaya ta,ban basa amsa ba sai ma ƙeya da na sa na fice.
Sheikh Rayyadeen ji ya yi kamar ya ha
ɗ
iye zuciy
a ya mutu don takaicin abin da ta yi wa malam Ibrahim shi kuwa da wani irin kallon so ya bi bayanta har ta fice.
Yana maido hankalinsa ga Sheikh ya sha jinin jikinsa saboda irin mugun kallon da ya ga yana yi masa.
“Khadeeja har yanzu yarinya ce,sai a
hankali ” ya furta don ya ga da alamu ran Sheikh
ɗ
in ya
ɓ
ace yadda ta tafi ba ta yi musu sallama ba haka kuma babu godiya.
“Kana iya tafiya” Sheikh ya fa
ɗ
a a takaice.
Malam Ibrahim ya ce “don Allah ina neman alfarma ne,a yi haƙuri da ni son Khadeeja
ya da
ɗ
e a zuciyata ne shi yasa na kasa controling kaina,na san haramun ne a bisa dokar makaranta yin soyayya da
ɗ
aliba muddin dai ba a wajen nan ba ne za ku yi ta.Amma ina so ni dai a bani wannan damar zan dinga koyawa Khadeeja karatu duk in lokacin shan
iska ya yi ta haka ne ƙila za ta yarda da ina sonta”
Tun da ya fara zuba Sheikh ya tsura masa na mujiya har ya dire,da sauri ya juyar da kai yana mai cewa “ka tambayi mahaifinta ni malaminta ne kawai,sannan wurin shugaban makaranta ya kamata ka nemi i
zini ba wurina ba”
Jikin malam Ibrahim ya yi sanyi kafin ya ce “to in sha Allah! ” sai ya juya ya fita, Sheikh ya bisa da wani mugun kallo kafin shi ma ya fita don lokaci ma tuni yayi.
Muna fita direct aji muka nufa,yau
ɗ
in ma haka mutane suka yi m
ini caaa suna kallo yayin da Sadiya ke hararena kamar idonta za su fa
ɗ
o.Samun kaina na yi da mayar mata da martani tare da jan tsuki,na furta “marar aji kawai” yadda ta waro ido shi ya tabbatar mini ta canki abin da bakina ya furta.Ni kuma raina sai yayi f
ari ƙal kafin na
ɗ
auki ruwa na leƙa ta window na wanke fuskata juyowar ga da zan yi muka yi ido hu
ɗ
u da Sheikh.Da wani mugun sauri na je wurina na
zauna,shi kuma rubutu ya soma yi jikin babban allon aji kafin ya soma yi mana bayani kan tarihin rayuwar Anna
bi.Tsawon lokaci kafin ya tsaya a wani wurin sakamakon lokacin tashi da ya yi,haka aka fara fita amma ni da ke a gaba ko motsi ban yi ba.
“Tashi mu tafi Malama ni nan yunwa nake ji ban ci komai ba” cewar Mujahida.
Na ce “to sannu acici uwar sakawa ci
ki abinci,ni me ki ga na ci?”
“Na tafi don wallahi ba a gabana za ki sake yin wata tijarar ba” ta furta tare da ficewa,haka kowa ya fita aka bar ni a zaune ina kallon Sheikh Rayyadeen da ke faman latsa waya da dukkan alamu bai ma san ina nan ba.
Murm
ushi na ga yana yi wanda ya fito tsantsar kyawunsa,muryar Ammynsa na ji tana cewa “yau yarona ya yi kewata har haka ne shi yasa ya kira ni video call?”
A shagwa
ɓ
e ya ce “Ammy please kafin na iso a ha
ɗ
a mini ruwan wanka kuma a sake gyara
ɗ
akina don yau i
na son na huta sosai”
Ta ce “tuni fa Saude ta yi komai,sai ka zo”
Ya shafi sajensa ya ce “ina jin yunwa kuma”
“Oh! Ni Khadi Allah ya nuna mini dai ranar da za ka kawo mai yi ma girki don ni na kusa gajiya.Yawwa ka baiwa Khadeeja key
ɗ
in motarta ”
Ya dafe kai ya ce “ciwon kai dai,don Allah Ammy ki bar mini maganarta zuciyata ta tafasa take yi.Yanzu dai gani nan tafe yanzu in sha Allah ” yana gama fa
ɗ
a haka ya kashe kiran,ni kuma da mugun sauri na yi kwance jikin table ina mai rera kuka a hankali.
Inuwarsa da na gani a tsaye yasa na fahimci ya farga da mutum a ajin.“Ke?” ya furta,a hankali na
ɗ
an
ɗ
ago kai na dube shi.Ya ha
ɗ
e fuska tamau kamar ba shi ba ne ya gama zuba shagwa
ɓ
a,“me kike yi nan?”
Ya tambaye ni,wani haushi ya rufe ni wato ba
i ma ga kukan da nake yi ba ballantana ya rarrashe ni.Ban ce masa komai ba,shi ma bai ƙara ba sai key
ɗ
in motata da ya ajiye mini ya fice na bi bayansa da kallon mamaki kafin na tashi da mugun sauri na fita.
Sadiya na tsinkayo can nesa kusan inda yake
ajiye mota,da sauri na ga ta nufe shi tare da kar
ɓ
ar jakarsa ta kai masa har mota.Bayan ya bu
ɗ
e ya shiga ya zauna,ita ta yi tsaye ta riƙe murfi yayin da kuma suke yin maganar da ban san me suke cewa ba.Gudun kar baƙin ciki ya kashe ni na nufi masjid
ɗ
in m
ata,ai kuwa a can na samu Mujahida tana waya ita da Yaya Hamza ko da muka ha
ɗ
a ido ta
ɓ
e baki ta yi tare da juya mini baya.
“Taso mu tafi ga key
ɗ
in motata ya bani” na furta,ta juyo da sauri kafin ta kashe wayar ta ce “ da gaske?”
Nuna mata na yi,sa
i ta miƙe da sauri tana murmushi muka fito.Bakin hanya muka tsaya muka samu abin hawa ,duk da babu nisa haka muka je a taxi
ɗ
in.Muna sauka kuwa na hangi motata,sai kuma na yi mamakin ta yaya aka yi har yanzu Sheikh bai zo ba.
Kasancewar a hanya duk na
baiwa Mujahida abin da ya faru sai cewa ta yi “ko ya tafi kai matsiyaciyar nan ?”
Na yi shiru kafin na ce “ban iya na sani,amma tana yi yiwa motarsa na cikin gida”
Mujahida ta ce “to sai dai in ke
ɗ
aya za ki je amma wallahi ni ba zan shiga ba” haka
na je na gaishe da mai tsaron get na shaida masa motar da ke ƙofa tawa ce tun jiya na bar ta a nan sannan kuma ina son ganin Aliya saboda yau ba ta je makaranta ba.Ƙofar ya bu
ɗ
e mini na shiga,sai dai a farfajiyar gidan ma babu motar Sheikh.Maimakon na juyo
a'a sai wata zuciyar ta ce mini na shiga na gaida Ammy,ina dab da shiga falon na soma jin hayaniya da alamun kuma fa
ɗ
a suke yi.
“Ba zan ta
ɓ
a tafiya na maido Khadi ba saboda ba ni ne na ce ta tafi ba,
ɗ
anta ne ya kwashe ta suka koma can saboda ya nuna mi
ni isasshe ne shi sannan ya fi son mahaifiyarsa da ni.Ke kuma da ba ki kishin mijinki shi ne kike goya musu baya” murya babban mutum ce wacce nake kyautata zaton mahaifin su Sheikh ne.
“Abban yara sam wannan ba adalci ba ne,yadda Maa ke da haƙi a kanka
mu ma matanka haka.Amma babu komai ni ma gidanka zan bar maka sai uwa da
ɗ
a su zauna su ka
ɗ
ai”
“Mahmuda in dai ni na haife ka to kar ka dakatar da Ramma ta yi ta tafiya,ai ba su ka
ɗ
ai ba ne mata ni nan zan auro maka yarinyar
ɗ
anyar sharrr” wannan karon
kuma muryar wannan tsohuwar ce na ji wacce suke kira da Grand-Maa.
Da sauri na yi baya jin kamar za a taho,ina fita na bu
ɗ
e mota muka shiga ni da Mujahida sai da muka hau titi ne ta tambaye ba'asi na kuwa labarta mata kafin na ce “kakarsu Sheikh ba ƙara
mar she
ɗ
aniya ba ce”
“Yanzu asibitin za mu je?”
“Eh saboda ina son ganin mahaukaciyar nan,ina ji a raina kamar akwai abin da ta
ɓ
oye mini a cikin labarinta sannan a wajenta ne kawai za mu samu tarihin gidansu Sheikh ” haka muka ta yin hira har muka i
sa asibitin.
Kamar yadda tsarin yake sai ka je ka nemi izini sannan ka je wurin mutum,sai da muka je can muka nemi izini sunanta aka tambaye ni.
Na ce “gaskiya na manta sunanta sai dai wancan lokacin da muka zo ni da Kakata a
ɗ
aki mai lamba uku ne ta
ke”
Shiru ya yi yana kallona na wani lokaci kafin ya miƙa mini wata ƴar guntuwar takarda na kar
ɓ
a sannan muka fito.Kamar a MAFARKI haka na dinga bin hanyoyin har muka kawo
ɗ
akin,ina yin tsaye ƙofar ta bada ƙiiii tare da bu
ɗ
e kanta ban san ta ya aka yi b
a ƙafata ce ta dama ta yi mini nauyi wannan yasa a dole na shiga da ƙafar hagu,wanda ya yi daidai da tashinta tana yin ihu.Da sauri na ƙarasa na kamo hannunta,shiru ta yi tana kallona da idonta da suke son canza siffa suna
ɗ
aukar na tsohuwa kafin na kai ga
furta wani abu fuskar Grand-Maa ta bayyana madadin ta mahaukaciyar,da wata irin murya ta maƙetata take cewa “wane ruhi ne ya zo wanda idona suka kasa ganinsa?”
Shiru na yi ina nazari kafin na kai yatsana cikin idon nata na tsokane,muryar Grand-Maa na j
i tana ihu kafin kuma fuskar baiwar Allah ta dawo normal.Ƙanƙame ni ta yi tana mai cewa “ki tafi da ni don Allah kar ki bar