Showing 48001 words to 51000 words out of 59970 words
ɗ
in da suka zube ita ma Malama Sharly ta mayar mata da nata sai dai fa ba su da amfani.
Tsaye ta yi gaban Koojal ta yi wani furicin a take ita kuma ta bu
ɗ
e idon ta yi tozali da ƙawarta wacce tun tana makauniya take yawan sh
afar fuskarta sannan wani sa'in EZRA
ɗ
in da kanta take siffanta mata yadda take wannan yasa ba ta yi mamakin ganin fuskarta fara ƙal ba irin ta Albino.
“EZ..RA! ” ta furta murmushi mai ha
ɗ
e da kuka yana kubce mata,rungume juna suka yi cike da murna kafi
n ta shiga yi mata godiya.
“Ina Malama Sharly?” Koojal ta tambaya.
EZRA ta ce“an mayar da ita makaranta” Koojal ta fara dube-dube ta ga manyan duwatsu ne ta ko ina ta ce “nan kuma ina ne?”
“Farfajiyar Mermaid ce,an ke
ɓ
ance wannan wurin ne domin h
alittun ruwa masu rayuwa a doron duniyar bil'adama” EZRA ta bata amsa.
Koojal ta ce “ko za ki iya zagayawa da ni? ”
“A'a ba dai yau ba sai dai wani lokacin,yanzu za mu koma makaranta ne kafin a farga ba mu nan” ta fa
ɗ
i haka tana mai kamo hannun ƙawa
rta,kamar tuntu
ɓ
e haka suka tsinci kansu a makaranta cikin kuma ajinsu.Wannan lamari ba ƙaramin
burge Koojal ya yi ba,don ita a duniya tana son abin almara sai kuma Allah ya ha
ɗ
a ta da matsafiya.
Cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce “yanzu da nake gani mutane s
una iya ganewa ?”
EZRA ta girgiza mata kai,daidai nan malaminsu ya shigo ajin wanda yana
ɗ
aya daga cikin wa
ɗ
anda suka yi gulmarta.
Darasi ya fara yana tambayoyi amma babu wanda ya sani sai EZRA,duk da ya ga tana
ɗ
aga hannu amma ƙin saka ta yayi ya ju
ya ya ci gaba da rubutunsa.
Koojal ta dubi littafinta irin wanda makafi ke aiki da shi mai kamar na'ura,shafa shi ta fara yi tana mai kallon rubutun sai ta ji tamkar wata murya na karanto mata abin da ke rubuce ba tare da ta san idanuwanta ke karatun ba
.
“Koojal?” malamin ya kira sunanta,cikin sauri ta ce “na'am malam”
“In kin ga matsafi a gabanki mene ne farkon abin da za ki? Shin za ki guduwa ne ko yaya?” ita ce tambayar da malam ya jefo mata.
Koojal ta basa amsa da “zan gaishe shi cike da g
irmamawa saboda babu abin da ya fi burge ni a duniya kamar tsafi da matsafi”
Duk da ya ji haushin amsar haka ya ƙara jefo mata wata tambayar,“in ya yi ƙoƙarin cutar da ke fa wane mataki za ki
ɗ
auka?”
“Zan karanto addu'o'in kongosa na neman kariya Yes
u ya taimake ni ” ta basa amsa.Sai ya saki murmushin jin da
ɗ
i ya ce “ta ya ake gane matsafi? Ina tambaya ne ga duk ƴan aji”
Duk kowa shiru ya yi,can ya ci gaba da cewa “Maraton babban malamin Kiristanci ya ce duk wani matsafi ya tsani Bible da kuma C
ross wannan ne yasa za ku ga da yawan mabiya addinin ke maƙale da Cross ko kuma
ɗ
an ƙaramin icce mai hoton inda aka maƙala abin bauta Yesu Almasihu wannan babbar kariya ce.Sannan ya ƙara da cewa addu'ar Yesu Almasihu ka cece mu ta yi nauyi a bakin matsafi.
Ku maimaita YESU KA CECE MU!” duk ƴan ajin suka furta amma banda EZRA sai kuma ya ci gaba da kawo wasu addu'o'in wa
ɗ
anda suka saka kanta fara juyawa tana jin tamkar suna ƙona ta ne.
Daga nan inda take zaune ta soma jin jijiyoyin jikinta suna wata irin k
umbura suna ƙara girma,ta ware idonta wa
ɗ
anda hucin azabar halin da take ciki ne ya haddasa suka rine suka zama kamar nunannen tumatur.Kan malam Rohan ta sauke su wanda shi kuma tsabar ka
ɗ
uwa da ganin lukutar masifa ya soma yin fitsari a wando ji kake shaa
a kamar raƙumi na fitsari.Duk ƴan aji suka sa dariya,babu wanda kuma ya lura da halin da EZRA take ciki in banda shi wanda ya yi sanadiyar shigarta.
Kamar wanda lantarki ya damƙe haka ya kasa yin motsi yana mai ci gaba da kallonta don dole don ita ce
da kanta ta hana jijiyoyin jikinsa ci gaba da aiki.Cikin ƙaraji ta yi amfani da wata guragurbin murya mai matuƙar firgitarwa ta ce “wato so kake yi a lalle dole sai ka murƙushe baiwar tsafi da ke gudana a jinina da kuma ire-irena? Ka makaro domin kuwa na d
a
ɗ
an lokaci tutar tsafi ce za ta dinga ka
ɗ
awa a kaf Daular Alfanso”
Malam Rohan wanda yake cikin halin ƙaƙanikayi ya soma motsa baki yana son yin magana amma babu dama,ta hanyar tunaninsa ta banka
ɗ
o abin da ke ƙunshe a ruhinsa.“Duk yadda kike son cikar
wannan buri naki har abada ba zai ta
ɓ
a cika ba ƙasƙantaciyar matsafiya,ba tun yau ba na da
ɗ
e da fahimtar cewa laifin ƙazamai nakassu ire-irenki ne suka hassala gimbiya Janaki ta yanke wa iyayenmu hukuncin mayar da su a ke
ɓ
a
ɓ
en wuri ”
Ambaton sunan gimb
iya Janaki shi ya ƙara tunzura EZRA ,saboda duk wani mai rai da ke rayuwa a Daular Alfanso ya tsane ta saboda silarta ne suke a bayan gari ba tare da an basu damar cu
ɗ
anya da sauran al'ummar yankin Uganda ba .
Daidai saitin zuciyar malam Rohan EZRA ta a
ika masa da wata kibiyar tsafi ta cake shi nan take ya saki wata irin razananiyar ƙara wacce ta jawo hankulan mutane da dama ciki kuwa har da shugaban makaranta.
Duk students
ɗ
in suka miƙe tsaye cike da tsoro ganin malaminsu yashe a ƙasa yana fitar da wan
i baƙin hayaƙi kamar tsohon batiri haka fatarsa ke zagwanyewa.Shigowar shugaban makaranta ya yi daidai da dawowar EZRA normal,ita ma sai ta miƙe tsaye kamar sauran
ɗ
aliban tana waro idonta da suke sak irin na mage don ita madadin baƙi wani blue mai ratsin
kore ke juya duniyar ganinta.
Kallon tsaf shugaban ya soma yi wa students yayin da sauran malaman da suka samu damar zuwa nan
ɗ
in suka fara ƙoƙarin ceton
ɗ
an uwansu sai dai sun kasa saboda lamari ne na tsafi.
“Kowa ya tafi gida an tashi!” shi ne
kawai abin da ya fa
ɗ
a kowa ya soma fita.EZRA na riƙe da hannun Koojal suka fito,direct kuma can wajen ban
ɗ
akunan makaranta ta kai ta.
“Me za mu yi a nan?” Koojal ta tambaya,EZRA ta ƙara ƙanƙame ta sosai kafin ta ce “ki jira ka
ɗ
an yana zuwa” ko gama rufe
bakinta ba ta yi ba kuwa sautin iskan fukafukinsa ya soma kawo musu farmaki.Kamar saukar jirgin sama haka Jemagen ya dira a gabansu,babba ne sosai don ya fi girman Giwa wannan ya tsoratar da Koojal ta
ɓ
uya a bayan EZRA ita kuwa ce mata ta yi “kar ki ji ts
oro mana,zo mu hau ya kai mu fadar Mermaid zan nuna miki abubuwan da ban ta
ɓ
a fa
ɗ
a miki su ba”
Koojal dai a tsorace ta yarda ta hau bayan Jemagen, EZRA ke gaba ita tana baya a haka ya tashi da su sama.Cikin abin da bai fi minti biyar ba ya kai su wata d
uniya wacce ba ta bil'adama ba.
Farkon wurin ya soma ne da wani abu mai kamar bakan Gizo,yayin da hotonsa yake kamar madubi.Sauka suka yi suka ratsa ƙofar,nan suka
ɓ
ulla a daidai wurin nan da suka zo
ɗ
azu da Malama Sharly.
EZRA ta ce “nan ne tushenmu,n
i
ɗ
in jinsi biyu ce .Ba koyon tsafi na yi ba,haifata aka yi da shi sai dai ban ta
ɓ
a sanin mene ne ba sai da Ummi ta ilmantar da ni.Wannan Jemagen da kika gani shi ne abin hawata,duk inda zan je muddin yana da nisa to da shi nake amfani”
Koojal ta ja a
jiyar zuciya ta ce “amma ta ya aka kika san da zamansa?” kafin ta bata amsa wata kifanyar ruwa ta
ɓ
ullo ta cikin wani
ɗ
an ƙaramin gurbin ruwa.Ta yi ihu ta ce “ EZRA???” ambaton sunan nata yasa ruwa suka dinga
ɓ
ul
ɓ
ulowa ta ko ina kafin ƙyaftawar ido sai ga
su a ƙasan ruwa.Ido Koojal ta bu
ɗ
e tana kallon halittun ruwa,wasu rabi mutum rabi kifi ko kuma rabi mutum rabi maciji.Tsaye ta yi tana kallon ƙawarta wacce a duniya in aka cire iyayenta babu wacce take so bayan EZRA,yadda ta ga jelar kifi madadin ƙafafu ya
sa ta waro ido ta matsa da sauri don fargar da ƙawartata sai dai ita ma sai ta ashe ita ma ta zama Siren
ɗ
in.Wani irin kuka ne ya zo mata ba ta shirya ba,wanda ya jawo hankalin EZRA da sauri ta zo ta kama hannunta.Kamar ƙyaftawar ido sai ga su wajen ruwa a
saman wata ƙatuwar bishiya....
★
DAVIDO
Ruhina da ruhin Nelson ne suka
ɗ
ingiza esprit
ɗ
inmu izuwa maƙabartar da aka binne ƙanena Joy.A tsaye suke suna ta shawarar yadda za su haƙo gawar Joy,na dubi Nelson kafin na ce “mene ne zan yi a yanzu?”
“Ka yi musu magana,ka kuma basu damar ganin ruhinka ” ya bani amsa,sai dai ko ka
ɗ
an wannan karon ban tambaye shi ƙarin bayani na game da yadda zan yi hakan ta tabbata.Ƙarasawa na yi na tsaya kai ga kabarin,abu na farko da na yi shi ne bayyana musu hasken
ruhina.Sai duk suka ja baya,sai kuma na soma gagga
ɓ
a dariya kafin na soma yi musu magana cikin garga
ɗ
i “tona wannan kabarin shi ne babban kuskuren da za ku aikata a rayuwarku,ina mai baku shawara da ku juya ku koma inda kuka fito”
Ɗ
aya daga cikinsu wand
a yake da ƙarfin hali sai cewa yayi “ba za mu ta
ɓ
a matsawa daga nan ba sai mun tabbatar da abin da muke zargi,don haka kar ku wani ji tsoro ku tuna cewa littafin sirri ya fi komai muhimmanci a rayuwar kowanne daga cikinmu” ya yi furicin ne tare da duƙawa y
a soma ture ƙasar kabarin.Kamar yadda ake
ɓ
alle hannun ƴar tsanar roba haka na yi wa dukkan hannuwansa a lokaci guda suka fita suka yi sama.Cikin iya shege irin nawa na yi amfani da hannuwan na soma
ɓ
alla musu maruka ji kake fauuu,tun suna daurewa har suka
soma yin ihu sai dai babu damar guduwa na riƙe ƙafafun.
Koke-kokensu ya jawo hankalin mai gadin maƙabartar,shi kuma babu wani tunani ya kira jami'an tsaro.Ko da suka iso wurin tuni na canza musu kamanni.
“David? David?” na ji muryar Jami'i na tash
e ne,dakyar na fizgo ruhina daga waccan duniyar na maido shi gangar jikina.Na ware ido dakyar na sune shi,da sauri na ga ya
ɗ
an ja baya yana ha
ɗ
iyar yawu.Duk da ban san dalili ba haka na ja fatun idona na rufe,kafin can ƙasan maƙoshi na ce “har gari ya way
e ne?”
“Wai don Allah wane ne kai?” na ji ya yi mini wata tambayar rainin hankali sai ka ce ba shi ne ya je ya
ɗ
auko ni ba.
Ni ma cikin rainin wayon na ce “David Jakob,Mama kuma ta ce Davido”
Ya ja dogon tsuki kafin ta bugi gefen cinyata ya ce “
banza ba wannan nake nufi ba,a duniyar ruhaniya nake tambaya wane ne kai?”
Zumbur na miƙe tsaye ina mai yi masa wani kallo kafin ni ma na aiko masa da tawa tambayar“ wa ya aiko ka wurina ?” bai ce mini komai ba illa juya mini ƙeya da yayi ya fice.
In
a nan tsaye na ji wata irin ƙara ha
ɗ
i da buguwar abu kan madubin window.Da sauri na juya sai dai wayam babu kowa,ƙarasawa na yi na bu
ɗ
e window
ɗ
in ban ida daidaita tsayuwata ba na ji wani irin iska wanda ba zan iya kamanta shi ba ya bugi fuskata.Na lumshe
ido ina shaƙarsa ina jin wani irin yanayi kamar ana lilo da ni,ko da na bu
ɗ
e idona sai na fahimci tuni ƙafafuna sun rabu ga ƙasa wato ina tsaye ne cikin iska.Ban gama fita daga wannan mamaki ba na soma jin ƙasusuwan jikina na fitar da wata irin ƙara kafin
kuma a sannu a hankali wani gashin tsuntsuwa ya soma tsiro mini a jiki can kuma
ɓ
oyayyar siffata ta ida fito na riki
ɗ
e na zama Mikiya daidai nan kuma jami'in ya shigo idonsa ƙurrr a kaina......
Ga masu son fara payment,Wa
ɗ
anda ba su da hali su tur
a 300 ,masu shi 500, hajiyoyi kuma 1k
🌚
via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +2279505822
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*
👻
```LoVe aNd HoRrOr story```
👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI
💫
✍
️
}
*SAD
AUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya lulu
ɓ
e ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki
👏🏻
*FCWA*
☀
️
________________________
07
Cikin siffata ta tsuntsu nake kallon jami'i kamar yadda shi ma yake kallona cike da tsoro da firgi
ci.Murya na
ɗ
an rawa ,ya nuna ni da yatsa ya ce “David kai ne ka koma Mikiya?” ban basa amsa ba sai tashi da na yi sama ina ka
ɗ
a fukafukaina kafin na bugi gilashin window ya tarwatse haka na fita a guje ina shawagi a sararin samaniya.Cikin abin da bai fi m
inti biyar biyar na isa gidanmu wanda yake
ɗ
auke da masu zaman jana'izar Abba.Kan wata bishiya da ke cikin gidanmu na sauka ina kallon kowa da ke wurin kafin idona ya sauka kan Ummah wacce ita ma ban sani ba ta ji a jikinta ne da akwai idon sharri a ankare
da ita ko me,sai gani na yi ta
ɗ
ago kanta sama ta sauke idonta cikin nawa tana wani ƙanƙance su.
“Me ka dawo yi?” ita ce tambayar da ta jefo mini ta ido da dukkan alamu ta gane ni,kai tsaye na bata amsa da “wurinki na zo ,ina son mu yi magana ne”
“
Ba ka ganin jama'a ne? Ka koma ka bari zuwa dare”
“Inda zan komawa can
ɗ
in yanzu dare ne,na yi tunanin nan
ɗ
in ma haka ne.A takaice dai dole ki saurare ni” na fa
ɗ
a ina mai
ɗ
aga kaina sama tare da yin wata irin cara sai ga kowa da ke wurin ya
ɓ
ingire bac
ci in ka fidda Ummah.Ban kuma
ɓ
ata lokaci ba na sauko ƙasa,direct
ɗ
akina na yi tsinke Ummah ta take mini sawu.A gabanta na canza siffata na dawo normal mutum,kamar wani ƙaramin yaro haka ta zo ta ci kwalar rigata tana cewa “Davido ba ka da hankali ne? Me y
a maido ka nan bayan ka samu ka ku
ɓ
uce?”
Na sa dukkan hannuwana na cire nata kafin na kalle ta tsakiyar ido na ce “ki fa
ɗ
a mini gaskiya wace ce ke? Mene ne dalilinki na kashe Abba?”
Cikin ƙaraji ta ce “ba Abbanka ba ne!” ni ma na tari numfashinta na
ce “ko ma dai mene ne ai shi ya raine ni ya kuma yi
ɗ
awainiya da ni”
Wani gigitacen mari ta
ɗ
auke ni da shi kafin cikin wani yare da ba na Hausa ba ta ce “ ni ce na haife ka don haka dole ka saurare ni kuma ka yi abin da na ce” tana gama fa
ɗ
ar haka t
a soma harha
ɗ
a mini kayana tana bu
ɗ
e akwatina nan ta yi kici
ɓ
is da littafin sirri ta kai hannu za ta
ɗ
auko shi amma na hana ta hanyar yin furucin tsafi littafin ya tashi sama ya zo hannuna.
Jikin Ummah na
ɗ
an rawa ta ce “tun yaushe ka samu littafin sirr
i? Davido dama kana mafarkin samun prophecy amma shi ne ba ka ta
ɓ
a sanar da ni ba? Fa
ɗ
a mini ya siffarta take?”
Ido kawai na tsurawa Ummah jin tana magana kamar dama tun can asali ta san abin da ke faruwa a rayuwata ko kuma zai faru,amma daidai
ɗ
aya ran
a ba mu ta
ɓ
a zama ni da ita mun yi maganar fahimta ba.
Ganin na yi shiru sai ta ci gaba da cewa “haukan da abokinka ke yi kenan kai ne sila? Mutuwar Joy fa?” ta ƙarashe idonta na cikowa da ruwan hawaye.
Na yi wani murmushin gefen baki kafin na ce “Umma
h me yasa kike son nuna mini kina da ƙawa zuci? Kar ki yi
ɓ
arnar hawayenki don zuwa yanzu ban san wani abu wai shi tausayi ba,zuciyata ta ida ƙeƙashe na
ɗ
auki alƙawarin yin rayuwata a salon yadda na gani ta dace da ni.Ban damu da sai kin sanar da ni wane n
e mahaifina ba saboda na riga da na san shi ” ina gama fa
ɗ
ar haka na nufi ƙofar fita ina mai rungume da littafina.
“Ka kula da kanka, sannan ka yarda cewa Ummarka na ƙaunarka fiye da komai na duniya da ta mallaka” shi ne abin da ta furta ,duk da kalam
an sun dake ni amma ban juya ba haka na fita tsakar gida a kuma take na ƙara
ɗ
aukar siffar Mikiya na yi sama ina mai sakin carar da ta dawo da kowa cikin hayyacinsa sannan na yi gaba abina.
Sai da na yi shawagi sosai wanda ya ishe ni kafin juya idona
ta hanyar tsafi na dira a Uganda wannan karon