Showing 18001 words to 21000 words out of 59970 words
ɗ
an jan numfashi kafin a hankali na bu
ɗ
e idona akan gemun Sheikh suka sauka,zuciyata na
ɗ
an bugawa na soma
sassauta riƙon da na yi masa ina mai
ɗ
aga kai na dube shi.Idonsa ne na ga sun ka
ɗ
a sun yi ja,sai na ƙara ru
ɗ
e na ƙi sakin gefen cikinsa da na cikuikuye,kamar wani wanda bai da hankali haka yasa tafukan hannuwansa kan ƙirjina ya wani tura ni baya,saura ƙir
is na fa
ɗ
i amma Ammy ta tare ni.A zuciye ya fita ko sakan biyu bai ƙara ba,wani kuka ne ya zo mini wanda ban san na mene ne ba.
Ammy ta fara rarrashina sai bayan na yi shiru sannan ta kamo hannuna ta ce “zo mu je ki nuna mini daidai ina ne kika tukuny
ar ” haka na bi bayanta muka je can bayan
ɗ
akunansu na nuna mata wurin.Ta ja numfashi tana mai cewa “ Khadeejatu kin san wani mafarkin gaskiya ne,ta hanyarsa ce Allah subhanahu wata'ala yake nunawa muminai abin da ke faruwa a rayuwarsu.Ban san me
lokaci ya
tanadar muku ke da Deeni ba da har ƙaddararsa ta fa
ɗ
o a tafin hannunki,ga shi ke ce za ki zamo silar warware wani baƙin ƙulli na rayuwarsa”
Saurarenta kawai na yi amma ban ce komai ba,sai ta ci gaba da cewa “ki tsaya nan bari na je na dawo” kai na jinj
ina mata ta tafi ta bar ni nan.
Tuna wa na yi yadda hannuwan Sheikh suka sauka a ƙirjina,duk da na san a bisa kuskure ne amma haka nake jin haushi .Ina nan tsaye Ammy ta dawo da abin haka rame,da sauri na kar
ɓ
a na buga daidai wurin da aka nuna mini a
mafarki.Bugu guda ne na yi amma sai ƙasar ta soma bu
ɗ
ewa da kanta, Ammy ta duƙa ta sa hannu ta soma janye sauran ƙasar da ke bakin rame cm.Hannunta na rawa ta ciro tukunyar tana mai ambaton sunan Ubangiji ,a gabana ta bu
ɗ
e ta a ciki mun samu wandon Sheikh
tun yana
ɗ
an yaro sai kuma wani ƙwai mai kamar na jimina sai wasu tarkacen.
Ƴ
ar kallon-kallon muka soma yi ni da Ammy kafin na ji wata idea haka kawai ban san daga ina ta fito ba,“ki ƙona komai ni kuma ki bani tukunyar da kuma ƙwan na tafi da su” wani abi
n mamaki shi ne ko ka
ɗ
an Ammy ba ta yi gardama ba hakan kuwa ta yi ta miƙo mini tukunyar wacce ƙwai ke ciki na
ɓ
oye ta a hijabi ,a haka muka rabu na fita waje sai dai babu key
ɗ
in mota a hannuna kuma ban san inda yake ba.
Don dole na koma can cikin gida
,falon Ammy na shiga na kuwa same ta tuni ta zuba tarkacen a cikin kasko ta ƙyarta musu ashana.
“Ammy makullin motata” na furta,haka aka ta bincikensa amma ba a gani ba.
Ta ce “bari na kira Sheikh ya sauke ki” ba ta ma bari na furta wata kalma ba ta fi
ta.
Ammy na shiga
ɗ
akinsa ta same shi a kwance gorar ruwan sanyi a hannunsa,yana jan numfashi duk da ta san abin da ke saka shi a wannan halin amma wannan karon sai ta ƙi nuna damuwarta ta ce “ka taso ka sauke Khadeejatu gida”
Ya
ɗ
ago da sauri yana kal
lon Ammyn wacce ta ha
ɗ
e rai ,kamar wani maraya cike da tausayin kansa ya ce “to”
Sai ta fita ta barsa yana jin kamar ya kama da wuta ko kuma ya fasa ihu ƙila zai ji sassauci.Ya miƙe yana masifa yana cewa “ke
ɗ
in ba masifa ba ce a gare ni a'a ke kanki ma
tsala ce,a kullum banda fitina babu abin da kike kawowa a rayuwata duk in mun ha
ɗ
u daga kina gudu sai kin fa
ɗ
o jikina mtswww!” ya ja dogon tsaki kafin ya ci gaba da cewa “na tsane ki!” haka ya fita can farfajiya ya bu
ɗ
e motarsa ya shiga yana jiran fitowart
a.
Ina nan tsaye Ammy ta shigo ta kama hannuna muka fito,sai ta sa key ta rufe
ɗ
akinta kafin mu fito babban falo.Karo muka ci da Grand-Maa,cike da girmamawa Ammy ta gaishe ta amma tsabar munafurci irin nata sai cewa ta yi “Khadi wannan fa wace ce?”
“Ƴata ce Maa ta kawo mini ziyara ne za ta koma gida” Ammy ta bata amsa.
“Amma kamar na ganta a jiya”
Ammy ta dube ni kafin ta ce “eh ta zo”
“Tun da ta zo jiya ,yanzu kuma me ya maido ta? Munafurci ko me?” Ammy na jin haka ba ta ƙara tankata ba ta
ja ni zuwa waje,idon Grand-Maa ƙur kaina tana kallon hijabina da dukkan alamu so take yi ta san mene ne ciki.
Muna zuwa kusan motarsa Ammy ta bu
ɗ
e mini gidan gaba,kasa shiga na yi na girgiza mata kai tare da bu
ɗ
e baya na zauna.Ta yi murmushi ta ce “sai
da safe Deejar Ammy ki gaishe mini da mamarki”
A hankali na ce “to Ammyna” wata irin waigowa Sheikh yayi da sauri yana yi mini kallon mamaki mai cike da tsana kafin ya soma jan motar.
Sai da muka hau kan titi ya ce “wace unguwa?” maimakon na basa
amsa sai na soma leƙen fuskarsa,rai a
ɗ
an
ɓ
ace ya sake tambayata sai a lokacin na shaida masa.Da muka shigo layin kuma na soma nuna masa har muka iso ƙofar gida,gabana ne ya fa
ɗ
i rasss ganin duk ahalin gidan a waje har da masu gadi.
Murya na rawa na cew
a Sheikh “don girman Allah ka fita ka yi wa Daddyna bayani ko ƙarya ce ka yi masa ka ce daga makaranta nake motata ce ta lalace shi yasa ka
ɗ
auko mu ni da Mujahida ”
Wani irin rumtse ido Sheikh yayi yana jin zuciyarsa na azalzala,shi da yake hukunta
ɗ
al
ibai akan in sun yi ƙarya amma yau shi ne
ɗ
alibarsa ke son ya yi ƙarya.Fita ya yi ya je ya gaishe da su Daddy,ban san me ya fa
ɗ
a musu ba sai na ga duk sun shiga cikin gida.Sai a lokacin ya bu
ɗ
e mini na fito,na yi tsaye ina kallonsa yadda haiba da ƙwarjinin
sa suka fito.Motarsa ya rufe sannan ya yi gaba na dinga take masa baya,cike da mamaki nake kallon yadda yake sa kai ciki.Muna shiga falo sai na ga Momy har wani rawar jiki take yi wurin kawo ruwan sha,yayin da shi kuma Daddy ya nunawa Sheikh wurin zama .Ba
n wani jinkirta ba na haura can sama inda
ɗ
akina yake,ƙarƙashin bed na ajiye tukunyar kafin na cire hijabina.Toilet na shiga na ha
ɗ
a ruwan
ɗ
umi na yi wanka na canza pad,yunwa nake ji amma kasa fita na yi ƙasa don na san bai tafi ba,har yanzu kuma ban bar m
amakin dalilin da yasa Daddy bai ce mini komai ba alhalin yana da zafi sosai.
A can falo kuwa cike da mutunta wa suke kula da Sheikh Rayyadeen,wanda shi
ɗ
in ba
ɓ
oyayye ba ne a wurinsu musamman ma Daddy wanda suke cikin association Islamic ta ƙasar Nij
ar shi da Sheikh
ɗ
in.Ammy ita kuwa ta san shi a tv da kuma bakin mijinta in yana yi mata hirar addini,ko ka
ɗ
an Daddy hankalinsa bai tashi ba da Sheikh Rayyadeen ya fito ya shaida musu cewa ya kawo Khadeejatu ne gida a bisa umarnin mahaifiyarsa,sai dai yana
mamakin meke ha
ɗ
in Deejar da Ammy
ɗ
in.
Ummah dai na zaune tana kallon Sheikh Rayyadeen don ita ba ta san shi ba,amma sosai take mamakin ta ya babban malami kamar shi yake
ɗ
auke da ƙulli-ƙulli na asiri a jikinsa.Hirar addini kawai suke yi kafin ya miƙ
e ya ce “ni zan koma” Daddy ne ya yi masa rakiya har zuwa ƙofar gida sannan ya dawo ciki, ya dubi Momy ya ce “je ki kirawo mini Ummita”
Ina kwance ina wasiƙar jaki Momy ta shigo,da sauri na sunne kai ina jin gabana na fa
ɗ
uwa.“Ki taso Daddynki na kir
a” shi ne kawai abin da ta fa
ɗ
a ta fice,jiki babu ƙwari na zumbula hijabi na sauka.Kusa da Ummah na zauna ina mai kwantawa a jikinta,“daga ina kike? ” Daddy ya watso mini tambayar da ta tabbatar mini cewa Sheikh bai sanar da su komai ba.Wannan yasa na gyar
a zama na shararo ƙarya,“daga makaranta muke Daddy,motar da na
ɗ
auka ce ta lalace ka san an kai mu ajin ƙarshe shi ne Mujahida ta zo muka tafi can don mu yi exercises ”
“Amma shi Sheikh ce mini yayi Ammynsa tasa ya kawo ki gida”
“Eh suna tare ne
lokacin da suka ha
ɗ
u da mu a hanya,ka san wani abu Daddy Ammynsa nada kirki sosai ” na fa
ɗ
a ina murmushin ƙarfin hali don zuciyata cike take da fargaba.
“Ina motar take yanzu?”
“An kira mai gyara ya tafi da ita ,Ammy ta ce in an gyara za a kawo mini
har gida” na basa amsa.A yadda na ga Daddy ya gamsu da hujjojina shi ya kwantar mini da hankali har na nemi abinci na ci.
Ummah ta miƙe ta nufi
ɗ
akinta tana mai cewa “ƙawali ki zo ki yi mini tausar ƙafa”
Sarai na san halin Ummah babu wata tausa da za
n yi mata ,tambayoyi ne za ta yi mini amma saboda ban jin tsoro ko shakkar sanar da ita sirrina kawai na miƙe na bi bayanta.
Ina shiga kuwa ta jawo ni ta zaunar tare da tsura mini ido,na ja
ɗ
an numfashi kafin na ce “gidansu ne na tafi Ummah ,kin san kusan
shekara uku kenan nake ciwon son Sheikh Rayyadeen amma ban ta
ɓ
a furta masa ba.Jiya kuma na yi wani mafarki da ya tsorata ni shi ne na je na shaidawa Ammynsa ”
Ta ja numfashi kafin ta ce “ƙawali ba ki ganin mutumin nan yayi miki girma? Dube shi fa gud
an dattijo da me Daddynki ya girme masa?”
Na turo baki na ce “to ni ina ruwana da girmansa tun da ba goya shi zan yi ba na yi yawo?”
Ta yi ƴar dariya kafin ta ce “lokaci yayi za ki fahimci abin da nake nufi.Matansa nawa?”
“Bai ta
ɓ
a aure ba” na bat
a amsa,ta ce “amma hotonsa ne na gani a hannunki ko?” na jinjina mata kai,ba ta ce komai ba sai jakarta da ta jawo.Magani ta ka
ɗ
a mini ta bani na sha,kafin na fita na koma
ɗ
akina.Wayata na
ɗ
auka na kira Mujahida,tana
ɗ
auka na soma yi mata masifa.Ta sheƙe d
a dariya ta ce “ke ba fa zan tsaya ba Sheikh yayi dambuna ah to,kin ga yadda yake hararenmu kuwa?”
Na ja tsuki ina mai cewa “to ai shi ya kawo ni gida” cike da mamaki ta ce “da gaske?” nan fa na bata labarin duk abin da ya faru.
Ta ja numfashi ta ce
“yanzu tukunyar na nan wurinki?”
“Eh bari duk ranar da kika zo zan nuna miki ” na fa
ɗ
a ina mai jingina jikin pilowe da na
ɗ
ora a baya,haka muka yi waya sosai ni da ita kafin mu yi sallama.Na cije le
ɓ
ena na ƙasa ina mamakin maganar da na furtawa babban m
alami kamar Sheikh Rayyadeen,sai yanzu ma na ji kunya na rufe fuskata da tafin hannu ina mai cewa “ oh Khadeeja me ya shiga kanki da har za ki cewa Sheikh ya furta kalaman ƙarya?” sai kuma na ji tsoro kar ya
ɗ
auke ni wata iri wacce ba ta da tarbiyya.Karon
farko da na ji cewa ya zama dole na samu lambarsa,sai dai duk iya binciken shafinsa ban ga inda ya ta
ɓ
a
ɗ
ora lambar ba a dole na haƙura na shiga rungume pilow ban san lokacin da bacci ya
ɗ
auke ni ba ya kai ni duniyata ta MAFARKI.
Yau kuma cikin wata a
sibiti ce na tsinci ruhina,ina tafe ina dube-dube kamar wacce ta
ɓ
ata kafin kuma na soma shiga
ɗ
aki bayan
ɗ
aki har na isa wani mai lamba uku.A can ƙarshen gado na hango ta tana kuka,gashin kanta duk ya cunkushe haka ma kayan jikinta duk sun yage,yayin da f
atarta ke fitar da jini saboda yagar kanta da take yi da manyan akaifunta.
Ina yin tsaye bakin ƙofar ta tsaya cak da kukan da take yi tana kallona,a zahiri mahaukaciya ce amma a ba
ɗ
ini da hankalinta rasss.
“Me yasa ki ke zaune a asibitin mahaukata alha
lin da hankalinki?” ita ce tambayar da na jefo mata.
Jikinta ta ƙanƙame tana mai cewa “alhaki ne! ” tako biyu na yi kawai amma na ganni a gabanta,hannunta na kama na jimƙe sosai sai ta soma magana kamar an kunna rediyo.
“Ƴar talakawa ce ni,na auri ta
laka na rayu da shi na tsawon shekaru har na haifa masa ƴan mata biyu.Amma rayuwarmu na nan a talauce,ƙarfin babu ta sa na soma yin aikatau don ciyar da yarana saboda mijina ya koma cima zaune.Yawan aikin da nake yi yasa cikina
ɓ
arewa ina tsaka da gugar ti
les,nan na zube jini na bin ƙafafuna ina murƙususu.Na
ɗ
an fita hayyacina na wani lokaci kafin na dawo normal,nan na yi tozali da abu ma fi girman
ɗ
aga hankali.Uwar mai gidan da nake yi wa aiki ce na yi tozali da ita ta kwashe
ɓ
arin da na yi ta saka shi a k
walba tana si
ɗ
ar yatsunta da suka yi kace-kace da jini.Ƙwala-ƙwalan idonta kuma suna juyawa babu sirki kamar na ƴar tsanar roba,wagegen bakinta ta bu
ɗ
e mini tana
wani irin murmushin ajali kafin ta ce “ni da mai ciki ba mu iya zama wuri guda,yawuna tsinkewa
suke yi ” wani tashin hankalin ne ya sake rufe ni,don kuwa na fahimci ita
ɗ
in mayya ce na yunƙura da niyyar maƙure mata wuya shi ne ta cire igiyar da ke saita tunanina ta ha
ɗ
iye a bakinta,kin ji dalilin zuwana a nan
ɗ
in ” ta ƙarashe fa
ɗ
a tana mai janye ha
nnunta yayin da kuma idonta suke canza kala zuwa kore kamar dai na Rashida.
Ina gama jin labarinta na fito daga cikin
ɗ
akin,cikin wani lungu mai tsananin duhu wata mata ta bayyana a gare ni tana mai yi mini wani jawabi mai kamar bushara.“Duk wasu matsal
olin da muke fa
ɗ
a miki a MAFARKI don su nusar da ke ne gidan da kike son kutsa kanki ciki.Hadiza(cewa da Ummah mahaifiyar Daddy) ta yi wa duniyarmu hidima wannan yasa muka yi alƙawarin kare bayanta, wannan
ɗ
in haƙinmu ne.Ungo wannan ruwan ki zuba su a ciki
n baƙar tukunyar da kika
ɓ
oye a ƙarƙashin gado” ta ƙarashe tare da miƙo mini wata ƴar mitsitsiyar kwalba na kar
ɓ
a tare da jimƙe ta gam cikin tafin hannuna.Daidai nan na farka,wata irin ƙirshiwa ce nake ji ina shirin dirowa daga kan gado na ji wani abu ciki
n hannuna ko da na duba sai na yi tozali da kwalba.Nan take kuma mafarkin da na yi ya dawo mini cikin kai,sauka na yi na jawo tukunyar na bu
ɗ
e ta tare da zuba ruwan ciki wani abin mamaki shi ne yadda
ɗ
igon ruwan da ba su wuce biyar ba amma suka kusan cika
tukunyar .A sannu a hankali na ga ƙwan na ƙara girma yana yin motsi,kafin kuma ya soma tsagewa .Ido kawai na zuba ina kallo har ida bu
ɗ
ewa duka,wata ƴar jaririyar halitta ta fito mai kamar mutum kamar kuma aljana,tana da manyan ido da kunnuwa faka-faka sai
ɗ
an ƙaramin hanci.Wani tsalle ta yi tare da yin suka kan jikina,na bu
ɗ
e murya cincin ƙarfina na ƙwala razananiyar ƙara da mugun sauri ta sauka daga gare ni ta yi suka ta haye gadona tana mai zubo mini idonta da suke wasar canza launi....
Normal group
300, VIP 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[15/12 09:13] MRS SADAUKI: *MAFARKI*
👁
️
🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar :
🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI
💫
✍
️
```
07
Ban ta
ɓ
a shiga tashin hankali ba irin na yanzu,kuka nake yi na rashin mafita.Ga shi dai ni ce da kaina na binciko wannan baƙin sirri amma kuma sam ban ji zan iya zama tare da aljana ba a
ɗ
aki guda,ita kuwa shegiyar
halittar sai ci gaba take da kallona tana juya ido kafin ta ce “ sunana Nina halittar prophecy,na rayu a wasu ƙarnikan baya,yanzu kuma kin sake haifata kin raya ni ”
Jikin ƙofar toilet na ƙara matsawa na riƙe ta gam,jin kuma wata lukutar masifa wai ni
na haife ta.Wani tsallen ta sake ta diro ƙasa kafin ta ci gaba da cewa “kar
ki ji tsorona,aikina shi ne nusar da ke hanyar da za ki bi don cimma burinki na samu Sheikh Rayyadeen ”
Ambaton sunansa da ta