Showing 15001 words to 18000 words out of 59970 words
zuciya tana kallon Sheikh Rayyadeen,a cikin ƙwayar idonta yake hango wani duba wanda ba nata ba sai dai sam bai ba hakan muhimmanci ba.
Sashen Ammy aka mayar da Rashida,da lokaci yayi haka aka ha
ɗ
u wurin cin abinci a nan ne Abba ya samu labarin abin da
ke faruwa.Fa
ɗ
a ya soma yi musu me yasa ba a kira shi a waya an sanar da shi ba, Grand-Maa ta yi caraf ta ce “saboda ba kai ka haifi Rashidar ba,inda ƴarka ce akwai ƴar isk...” yadda Sheikh ya buga table da mugun ƙarfi har kwanukan sama sai da suka motsa,s
hi ya katse hanzarin Grand-Maa ta kasa ƙarasa abin da take da niyyar fa
ɗ
a.Idonsa sun ka
ɗ
a sun yi ja,duk safiyar yau in banda baƙin ciki babu abin da yake cin karo da shi,duk zafin ran sai ya soma zube shi kan Grand-Maa wacce ta yi tsuru-tsuru kamar an ruts
a kwarto.
Muryarsa har wani sarƙewa take yi wurin cewa “ ba zan ta
ɓ
a
ɗ
aukar cin mutumcin mahaifiyata ba a gurin ko ma wane ne,a kullum ina yawan nusar da kai Abih ka dinga fa
ɗ
awa Grand-Maa darajar aurenka ce da ke kan Ammy yasa take yi mata abubuwa har
nake yin shiru,amma ba ta gani.Ta yaya ne za ka bari tana zagin Ammyna a gabanka amma ba ka cewa komai?”
Ran Abba ne shi ma ya
ɓ
ace ya ce “Rayyadeen ni kake yi wa fa
ɗ
a? Ai da ha
ɗ
e mu ka yi ka yi mana duka sai mu san kana son mahaifiyarka,wato uwarka ta
fi tawa uwar kenan? Kai me yasa ba za ka yi wa mahaifiyarka magana ba? Ka fa
ɗ
a mata ta tsarkake bakinta kafin ta yi magana”
Sheikh har ya bu
ɗ
e baki amma Ammy ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa,“Deeni yi shiru” ba don ya so ba ya ja bakinsa yana
mai tsure Grand-
Maa da ido don tun da ya fito daga ƙauyen can yake jin tsanarta tun bisa hanya ba tare da ya san dalili ba.
Tsam ya tashi zai tafi amma Abba ya dakatar da shi yana mai ce masa “ka nemo malamin ruƙiya ya dinga zuwa nan gida yana yi mata ka
ratu”
Grand-Maa ta ce “da dai asibiti aka kai ta Mahmuda saboda alamomin hauka duk sun tabbata”
Mama ta kar
ɓ
e da “babu wani hauka iskokai ne ga kanta” Grand-Maa ta fiddo idonta na mugunta wanda iya Mama ce kawai ke iya ganinsu,ita kuma sam hakan bai
bata tsoro ba sai ma gefen wuyanta da ta soma shafawa inda take ajiyar nata makamin muguntar.Dole dangin naƙi yasa Grand-Maa ta tsuke shegen bakinta,shi kuwa Sheikh sashensu ya wuce sai da ya fara shiga wurin Rashida ya tofa mata“ As'alullahul azima rabal
arshil azimi an yashfiyaki ” ƙafa bakwai kamar yadda Manzon tsirai ya umarce mu da mu yi in mun je duba marar lafiya.
Daga nan
ɗ
akinsa ya wuce,wanka yayi ya canza kaya ya
ɗ
auko Alkur'ani kenan zai fara yin karatu Ammy ta yi sallama.Ya amsa,sai ta shigo
hannunta
ɗ
auke da tray, Sheikh ya wani langa
ɓ
e kai kamar ƙaramin yaro yayin da Ammy ta soma ha
ɗ
a masa abincin da bai ci ba a can.Haka ta zauna sai bayan ya gama ci sannan ta fita,shi kuma karatun yayi bayan ya gama ya yi dogayen addu'o'i yana roƙon Allah l
afiya da kuma kyautar aure da sauransu.
Lokacin da ya kwanta ƙarfe biyu saura ,hakan yasa bai wani jima ba bacci ya
ɗ
auke shi.
Washegari bayan ya dawo daga masjid ma sai da ya je ya duba Rashida ya yi mata addu'o'i sannan ya je ya fara shirin zuwa maka
ranta.
Tun da safe ya shaidawa shugaban zai zo yau , wannan ya sa aka ƙara tsabtace makarantar fiye da kullum.
Tsit kake jin
ɗ
alibai babu haniya saboda kawai an ga motarsa,shi Sheikh ya banbanta da sauran malamai duk girman
ɗ
alibi in yayi laifi tsaf za
i zane shi.Ya sha dukan ƴan mata sai su turo samarinsu wasu su yi masa kashedi wasu kuma da niyyar ramawa suka zo.Amma kuma hakan bai sa ya canza ba,kusan kuma hakan ne yasa duk ake tsoronsa don bulalarsa ma in ka kalle ta sai gabanka ya fa
ɗ
i.
Yana shig
a ajin wani ƙamshi ya bugi hancinsa,bayan sun amsa sallamar da yayi musu sai ya samu wuri ya zauna kafin ya
ɗ
ago a hankali ya maido dubansa gare su.
Kowacce ta saka uniform,nan babu matsala sai ya soma kiran sunan
ɗ
alibai bayan ya gama ne ya ce “sabbin
zuwa su koma wannan layin” ai kuwa duk tashi suka yi
ɗ
in,
ɗ
aya bayan
ɗ
aya haka yake kiran sunansu yana binciken karatunsu da ya zo kan Khadeeja sai ya lura ita sam ba ta ma yi karatun Alkur'ani ba amma aka ƙetara ta zuwa aji na gaba,ransa ne ya
ɓ
ace duk da
ya lura ta yi kaf
ɗ
aliban maki a karatun litattafai.
“Nana Khadeeja Abdullahi” ya kira sunan nata tare da
ɗ
aga kai,Mujahida ce ta basa amsa da “ba ta zo ba malam ba ta da lafiya”
“Ita ta fa
ɗ
a miki ko kuwa ƙarya kika yi don ki kare ta?” ya tambaya yan
a ha
ɗ
e rai, Mujahida ta sunne kai tare da yin shiru sai ya ji ita ma tana basa haushi.Ya ce “tashi tsaye” ai kuwa jikinta na yin rawa ta miƙe,shi kuwa babu tausayi haka yayi mata bulala uku saboda ƙaryar da ta yi sai ga Mujahida da guntuwar ƙwalla.
Baya
n ya gama bincikar karatun nasu,sai ya fara tambayar manyan ajin abubuwan da suka faru nan ne fa Sadiya uwar kau
ɗ
i ta shaida masa abin da ya faru jiya sai maƙe murya take yi tana yin ƙalƙala duk don ta burge Sheikh Rayyadeen.Sai dai bai ce komai ba ya soma
yin karatu har lokacin shan iska yayi, Mujahida yau sam ba ta da walwala haka ta yi ta jaraba kiran Khadeeja amma ba a
ɗ
auka ga kuma lambar Hamza ita ba ma ta shiga.
Bayan sun dawo aji ne ya tura sabbin
ɗ
alibai gun wa
ɗ
anda ya yarda da iliminsu domin su
sauƙaƙa musu karatun wanda kuma hakan sabon tsari ne ya
ɓ
ullo,don ya rantse dole Khadeeja wurin Sadiya zai tura ta duk ranar da ta zo.
★
KHADEEJA
Sam kasa rumtsawa na yi ita kuwa Ummah sai faman shafa mini maganin aboniki take yi kafin can mu h
a
ɗ
a ido da ita.Da dafe ƙirji tana mai cewa “mu ga idonki” sai ta gwale mini su kamar wata doctor haka ta sa fitila ta duba,wani kwalli ta
ɗ
auko ta ramba
ɗ
a mini mai mugun yaji tana mai cewa “dama na san Allah ba zai
ɗ
auki raina ba har sai ya nuna mini wanda
zai gaje ni ” sai ta soma shafa mini wani maganin a goshi,sannu a hankali na soma jin bacci na surata har na tsinci kaina a duniyar MAFARKI.Yau ma kamar wancan lokacin a gidansu Sheikh na tsinci ruhina,duk abin da ya faru ga Rashida bayan tafiyata haka ak
a yi mini wahayinsa.Hatta zuwan Sheikh Rayyadeen ƙauye duk an nuna mini da kuma abin da zai faru a futur,wato ya bugi ƙawata Mujahida daga nan kuma sai aka cilla ni wani wurin.Da na ƙarewa wurin kallo sai na gano farfajiyar gidansu Sheikh ce, waige-waige
na fara yi har idona ya sauka ka wani tsohon toilet duk ya gur
ɓ
ace daga can cikin ƙasar.Da wani sauri na ƙarasa na isa wurin na zube tare da soma yin tono,na yi rame mai zurfi kafin na cimma wata baƙar tukunya mai murfi haka na ciro ta.Na bu
ɗ
e ta,hoton Sh
eikh ne a ciki yana
ɗ
an matashi bai fi shekara ashirin da bakwai ba,a hoton an zagaye wasu ga
ɓ
o
ɓ
insa,na farko idonsa,na biyu kunnuwansa,na uku bakinsa,na ƙarshe kuma al'aurarsa sam ban san me hakan ke nufi ba kawai dai na samu kaina da
ɗ
auko tukunyar na bi
ta ƙofa na fita.Tafiyar ƙasa na yi har na iso gidanmu,cikin furanni na
ɓ
oye tukunyar yayin da hotonsa kuma na riƙe shi a hannuna na zo na shiga
ɗ
akina na kwanta ina bacci,kuma duk hakan ya faru ne a MAFARKI.
Washegari da sarawar kai na tashi,idona ha
r wani zafi suke yi mini.Na tashi dakyar na zauna kan katifar,tuni gari yayi haske babu Ummah sai ƙullin kayanta.Na zira ƙafata kenan don zuwa ban
ɗ
aki na ji na taka wani abu mai sul
ɓ
i
kamar leda,amma ban wani duba ba na je na shiga toilet sai kuma na samu
baƙon watana ya zo.Wanka na yi da ruwan
ɗ
umi na fito,cak na tsaya ina kallon yadda iska ke tunku
ɗ
o wani kwali har ya iso gabana,na duƙa na
ɗ
auka ina birkito shi sai na ga hoton Sheikh a nan take kuma mafarkin da na yi ya fa
ɗ
o mini a rai sak irin hoton banb
ancinsa da na cikin MAFARKI shi ne wannan bai da zagayen nan da aka kewaye ga
ɓ
o
ɓ
insa.
Mamaki kamar zai kashe ni haka na zumbula hijabina na fita zuwa
ɗ
akina,falon tsit yake babu kowa sai masifar Ummah da nake jiyowa ita da ƴar aiki.Sama na haura ,na
ɗ
au
ki pad da pant na saka sannan na zira doguwar riga ta kanti na fesa turare na shafa mai.Kan bed na haye tare da riƙe hoton Sheikh ina kallo sai yanzu ma idea wanko hotunansa ta zo mini,tsam na manna shi a ƙirji kafin na lumshe ido zuciyata na
ɗ
an dokawa a
haka bacci
ɓ
arawo ya kwashe ni sai wuraren ƙarfe sha
ɗ
aya na rana na farka shi ma Ummah ce ta zo kaina tana balbale ni.
Na turo baki gaba ina cewa “ƙawali ya za ki tashe ni ina hutawa?”
“Tashi maza ki ci abinci babu ruwa da sakarci,kin ga jiya haka k
ika jigata da kika zauna da yunwa”
Tashi na yi na yi brush na wanke fuskata ko da na fito sai na samu hoton Sheikh Rayyadeen a hannun Ummah tana kallo.A kunyace na kar
ɓ
e hoton,yayin da ita kuma ta tsuro mini na mujiya kafin ta ce “wane ne?”
“Saurayin
a mana” na bata amsa ina mai fesa turare.
“A ina kika samu hoton?” ta jefo mini tambayar.
Na ce “ni da saurayina shi ne za ki tambaya ina na same shi? To shi ne ya bani da kansa”
“Ke da shi halan duk makafi ne shi yasa ba ku ga matsalolin da ke ta
ttare da hoton ba?” Ummah ta fa
ɗ
a cikin
ɗ
aga murya,da sauri na juyo ina kallonta zuciyata na
ɗ
an bugawa.Na san Ummah na bayar da magani,wani sa'in ma ba sai ka tambaye ta ba a'a haka kawai a hanya ma in ta ha
ɗ
u da kai sai ta baka magani amma ban ta
ɓ
a sanin
cewa iliminta har ya kai iya ta hoto ma tana iya hango matsala.
Na zo dab da ita ina mai cewa “halan meke da hoton ?”
“Zo mu sauka ƙasa ki ci abinci ” ta sauya zancen,haka na ajiye hoton ƙasan pilow na take mata baya.Ammy na zaune a falo,gaishe ta n
a yi sannan na zuba abinci na soma ci ta miƙo mini wayata sai na ga miss call
ɗ
in Mujahida.Sanin yanzu tana cikin aji yasa ban maida mata ba sai text na yi mata,ai kuwa ta maido mini har take shaida mini cewa Sheikh Rayyadeen ya bulalaye ta saboda ta yi ƙa
ryar banda lafiya,dariya na shiga yi kafin kuma na yi tsit sakamakon zuciyata da ta raya mini ‘ jiya ai na yi wannan mafarkin ’ babu shiri na ajiye plate
ɗ
in na haura sama,ina jin Ummah na tambayar lafiya amma ban juya ba.Zaune na yi na soma
rubutawa Mujah
ida kaf irin mafarkin da na yi a daren jiya,ita kuma ta tabbatar mini da za ta zo gidanmu in an tashi daga makaranta.
Haka kuwa aka yi,ta cika alƙawari bayan ta zo
ɗ
akina muka shige na ciro hoton Sheikh Rayyadeen na miƙa mata ina mai cewa “kin gansa”
Shiru ta yi tare da kar
ɓ
a tana dubawa kafin ta ce “kuma kin tabbata ba wani ne ya baki hoton nan ba?”
Na ce “wani wa? Mujahida ni fa na fara jin tsoro kar dai a ce ni ma Rashida ta saka ni cikin group
ɗ
insu na Mayu ”
Sai da ta sheƙe da wata dariya k
afin ta ce “ke fa matsala ta da ke hauka,yanzu dai abin da za a yi kawai mu shirya mu je gidansu Sheikh
ɗ
in sai mu kaiwa mahaifiyarsa hoton” ba tare da wani tunani ba kuwa na amince,muka fito lokacin har duhun magarib ya fara shigowa wannan yasa Ammy da Um
mah duk ba su falo.
Muna fita na kar
ɓ
i key
ɗ
in mota ga direba,haka na tuƙa mu har zuwa gidansu Sheikh Rayyadeen.A bakin ƙofa na yi parking,na cewa Mujahida “yanzu in muka shiga me za mu ce?”
“Wurin Ammy muka zo ” ta bani amsa sai muka fito,ni ke gaba
ita kuma tana baya bakin get
ɗ
in babu kowa hakan yasa muka shiga kai tsaye.Ina shirin shiga falon na ci karo da shi har kaina na dukan ƙirjinsa,ruwan gemunsa suka
ɗ
iga kan fuskata da wani matsanancin bugawar zuciya na yi baya saura ƙiris na fa
ɗ
i Mujahida
ta taro ni sai muka yi cirko-cirko muna ƴar kallon mu da Sheikh Rayyadeen.....
Group biyu ne normal 300 , VIP kuma 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .Kamar tun a talla na fa
ɗ
a muku wannan sabon salo ne sabuwar sheƙa to haka t
ake,nan duk shimfi
ɗ
a ce ba mu ma fara labarin ba.
[14/12 15:15] MRS SADAUKI: *MAFARKI*
👁
️
🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar :
🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADA
UKI
💫
✍
️
```
06
Ban san me yasa yake yi mini ƙwarjini ba a duk lokacin da babu gilashi a idonsa,sai na dinga ganinsu tsirararsu girma da kyawunsu ya ƙara fitowa uwa uba wani abu da nake gani kwance a cikinsu mai
ɗ
aga mini hankali da ka
ɗ
a hantar cikina
.
Mujahida ce ta yi ƙarfin halin gaishe shi “barka da warhaka Sheikh ”
Bai amsa ba sai ni da yake kallo,ƙila gaisuwar tawa yake jira.Kai na sunne ina mai ƙara jimƙe hotonsa da ke hannuna.Bai ce mana kanzil ba saboda kiran sallar da aka ƙwala a masjid
ɗ
in gidansu,yayi gaba yana jifata da mugun kallo yayin da ni kuma na ja wata ajiyar zuciya ta murna ina mai shigewa cikin falon .
Ko ina tsaf yake sai ƙamshi ke tashi,kamar wacce ta san gidan haka na bi na tafi wancan sashen na jiya sai a lokacin ma na f
arga da Mujahida ba ta biyo ni ba.Zan juya kenan Ammy ta fito tana cewa “wa ke nan?” da sauri na juyo ina kallonta,a kunyace na gaishe ta ita kuma ta amsa mini da murmushinta tana ambaton sunana daga ƙarshe,babu wata magana don duk a daburce nake na ciro h
oton Sheikh
ɗ
in na miƙa mata.Sai ta kar
ɓ
a ta duba tare da kallona da mamaki,“ina kika samu wannan hoton?” ta jefo mini tambayar.
Shiru na yi,sai ma a wannan lokacin na ga wautata.Kame-kame na fara kafin daga ƙarshe na shaida mata mafarkin da na yi,duk i
llahirin jikinta ne na ga yana kyarma kafin ta ce “ MAFARKI?”
Na jinjina mata kai,sai ta ja hannuna ta kai ni
ɗ
akinta ta zaunar da ni tana mai cewa “zauna na yi sallah” banda wani za
ɓ
in haka na zauna,yadda ta jima a sujidar ƙarshe yasa na ji ina ƙaunart
a don na tabbata addu'a ce take yi.
“Ammy?” na ji muryar Sheikh daga can falo,bai tsaya da kiran sunan nata ba yadda na ji amon muryarsa na tunkaro nan shi yasa na tashi da mugun sauri na bu
ɗ
e wata ƙofa na shige ina dafe zuciya da tunanin na tsira sai
dai nan
ɗ
in ma wani tashin hankali na ci karo da shi .Fuskar tsohuwar nan Grand-Maa ce zaune ra
ɗ
am a mirror
ɗ
in toilet,babban tashin hankalin shi ne iya kanta ne kawai ya bayyana kuma a gundile babu gangar jiki.
“Yiiiii!” ta girgiza gashin kanta tana b
ani tsoro na fasa ihu tare da banko ƙofar na fito,sam idona sun rufe da tsoro ban gansa ba haka na je na fa
ɗ
a jikinsa tare da ƙanƙame shi gam ina kuka tare da rumtse idona ina cewa “aljana! Aljana!“
Kiciniyar hakice ni yake yi,sai dai sam na ƙi basa wan
nan damar don ba mugun riƙo na yi masa.Sai da Ammy ta yi magana ne sannan nutsuwata ta fara dawowa,“Khadeejatu?” ta furta tana mai jawo ni ta baya,na