Showing 27001 words to 30000 words out of 145961 words

Chapter 10 - ZUCIYA COMPLETE

yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa

makuli ta bud'e.

Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf.

D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a h

annunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu.

Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. "

Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido ci

kin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. "

Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a.

Idanunsu ne suka

had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai.

Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! "

Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hu

bby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. "

Kallan mamaki ya mata yace "me? "

Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. "

Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out."

Mikewa tai

cikin mamaki tace "me kuma nai? "

Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. "

Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. "

Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? "

Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? "

Aneesa ta mike ta fita cikin takaici.

Tsaki yai sannan ya tuno sanda

Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai.

Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho....

Harta zauna ta mike tai kitchen.





_A Mota_

Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan m

e zaiyi da wuka? "

Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka?

Sun isa kachako anan

kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota."

D'an litti yace "nawa ne? "

"dari 700."

A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? "

Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. "

Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule.

D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. "

Nan aka fara hay

aniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? "

"I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nuf

in ba i am not ne.

Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shiri

n d'aukowa? "

Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya.

Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi

office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. "

Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu."

Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankw

a aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. "

Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? "

Mai mota yace sai sun bashi dari 1000

su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba.

Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa.

Maman hanne ta kalleshi

tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... "

Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abin

da ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? "

Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... "

Nima nace Ameen

*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayus

hermohd.blogspot.com

*_Hakika bani da bakin da zan muku godiya, nagode kwarai da so da kaunar da kuka nunamin, ina kara godiya ga masu min ta'aziya ta waya, ta text, da ta chat nagode kwarai Allah ubangiji ya barmu tare......_*



2



0





Shiru Ashraf yai a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta? A kalaa dai shekarunsu d'aya da Little banbancinsu dai Little nada d'an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi, ko alphabet bata iya ba.

Ya d'an juya kai, ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace, yai d'an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d'auramai.

Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina

zamu?

Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace "Adamu me muke jira kuma? "

Adamu ya dan saki fuska yace " tun d'azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. "

Tsaki ya kara ja sannan yace "Mu tafi gida, tunani ne suka min yawa. "



A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za'a bata, duk ta yad'ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci, anyi carko carko a waje kowa nata fada'an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani suke ai

ta cancanci abata ta gani, dan ankusa d'aura musu aure.

Mumy kam tana d'aki abin duniya ya dameta itakam ba abinda ta tsana irin taji ance Ashraf yayi abu.

Tun da suka shigo Ashraf ya fuskanci da matsala sai dai har sukai parking ya fito bai

nuna komai ba, ba kuma yasan ya san meke faruwa, direct hanyar banharensa ya nufa, suna daga tsaye ko kallan inda suke baiyi ba, Ga Aneesa da su Umma suma daga d'an gefe.

Asim ne cikin kuluwa yace " Ashraf bakaga dan kai muke tsaye ba? "

Kall

ansu yai ya saki wani mugun smiling na rainin hankali yace " Da alama tsayuwar domin ni tana muku dadi ne. "

Ya ci gaba da tafiyarsa, a xabure Asim da kannansa suka matso inda Ashraf yake, Asim ya tafi a zuciye zai shake Ashraf, saura kiris ya karaso A

shraf yace " D'an daba muka samu a gidan? Ka tabbatar kasan me kake shirin yi kafin a samu matsala. "

Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake, ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?"

Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su, cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka? Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani

bare. "

Ran Asim ne ya kara dugunzuma, yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu, Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya? Gatannan sai ka tambayeta me baren

nan ya mata. "

Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba? Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai? Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......"

Kasa karasawa yai sabo

da ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut! Dariya ma na baka? "

Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa

ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? "

Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?"

Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data

bishi da sauri, tana kiranshi.

Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? "

Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace "

wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa.

Da kallo ta bishi dashi, wani mugu

n tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje.

Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna

abinda likita yace mai.

"Ashraf a ina ka bugu haka? "

Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min."

Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? "

Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin a

ccident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. "

Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? "

Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, san

nan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. "

Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. "

Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an

gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. "

Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira.

Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan A

llah yasa ta dawo.

Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. "

Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai d

ai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo.

Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. "

Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " tay

a zan tafi in barki? "

Little tace " naji muryar yayan ma kamar......"

Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda

kawai tasa a ranta kenan.

Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne?

Nafi kam jikinta ya fara tsum

a ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. "

Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita.

Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama, jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki, baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi.

A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Na

fi ta juya baya da sauri, a hankali tace "Yaya ga...... "

Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. "

Nafi ta ju

yo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... "

"Little wuce mana"

Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake, nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin

ta fito, ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin, kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba, idanunta ne suka fara cicikowa, ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai g

un, dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an.



Kamar a jikinta takejin ciwo nan, intaga ya motsa sai ta runtse ido.

Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bay

anta a kufule.

Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki, me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai???????

Tofah! Babbar magana........

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako, kayan da maman hann

e tazo dasu suma sai siyarwa tai.

Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram.....

¤¤¤¤¤¤¤

Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi.

D'an litti yac

e " ku nemo min Ashraf. "

Officer yace " Ashraf wa? A ina yake? Meye number wayarsa? "

To fa! Da masifa D'an litti yace " nidai ba na fada muku ba? Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. "

Officer yace " me kake nufi to? So kake mu shiga kano

mu fara neman masu suna Ashraf ko me? "

D'an litti

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login