Showing 21001 words to 24000 words out of 145961 words
yasa ta d'au kayan tare da rufemai mota tai gaba.
Tana isa
d'aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune, gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai.
A hankali cikin tsoro ta shiga d'akin, tare da ajiye kayan, Umma tace " Yauwa Ke muga ledar nan. "
Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya, U
mma ta kalli Aneesa tace " wanene lace d'in? "
Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske.
Little ta kalli Umma tace " Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?"
Umma tai murmushi tace " Little kenan
bakiji me nace ba? Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. "ta fada tana nuna Nafi.
D'aukan lace din sukai suka tafi, little ta shiga toilet ranta duk a b'ace.
Nafi kam ko ajikinta dan
batasan darajarsu ba, itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi?
*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*I Sincerely Dedicated This Page
To All Masoyan Xuciya, Nagode Kwarai da san da kuke mai.... *
😍
*ILYSM*
😍
1
⃣
3
⃣
Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad'ai tace " Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? "
Cikin
rashin kulawa da abin tace " name fa? "
Little ta zauna a gaban madubi tace " kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? "
Nafi ta kalleta tace " lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d'au
ka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? "
Little tai d'an karamin tsaki tace "Wlh ba wani kayansu, sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d'au abinda ba nata ba? "
Nafi ta mike tace " kafin ki shirya bari na anso miki abinci. "
Bat
a jira amsarta ba tai waje da sauri, Little ta bita da kallo a fili tace " lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? "
Nafi kam tana fita tai murmushi tace " ni da naga kaya daga sama? Dan an d'au d'aya menene? "
Kitchen ta wuce, ta ams
o abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance "Ke!"
Juyawa tai dan tasan Umma ce, Umma tace " zo nan. "
Ajiye tiren tai sannan ta karasa gunta, Aneesa ta maka mata hararra tare da juya kai gefe.
Nafi ta karasa tare da rusunawa tace "ga
ni. "
Umma ta mata wani kallo tace " munafuka kinje gun aikin ko kuwa? "
Da sauri Nafi tace "Naje wlh. "
Duk da dama Umman ta riga ta tambaya ankuma shaida mata taje amma sai cewa tai "in kika min karya na tambaya wlh kinji na fad'a miki jikinki
sai ya fad'a miki. "
Nafi tai kasa dakai ba tare da ta sake magana ba, Umma ta kara kallanta sannan ta ce " me Little tace bayan mun fita? " dama wannan shine dalilin kiran wancan burga ne so take taji me akace bayan sun fita.
Nafi da mamaki
ta kalleta tace " Bangane ba. "
Da kuwa Umma ta mata ta kara da kinci gidanku, ni zaki kalla kicewa baki gane ba?
Nafi tai kasa da kanta a hankali tace "kiyi hakuri. "
Cikin takaici Aneesa tace "Dalla malama kara gaba. "
Nafi wacce bata fah
imci me ake nufi da kara gaba ba tace "Naam? "
Cikin kuluwa Umma takaimata wani wawan mari wanda sai da Nafi tai baya tare da rike kuncinta.
Umma ta nunata da yatsa tace " kin bar nan ko sai na karya ki? Shigeya wacce asalinta bashida tabbas.
"
Nafi ta juya ta fara tafiya sai dai tana tafe hawaye nabin kuncinta, haka ta d'au tiren tare da goge hawayenta ta shiga.
Little har tana shirin fita sai ga Nafi ta kalleta tace " lalai Nafi sannu da zaman hira. "
Nafi tai murmushi kawa
i batace komai ba sai hanyar toilet data nufa.
Tana shiga ta tsugunna sai kuka, itakam Little abincinta taci ganin Nafi bata fito ba yasa taje bakin kofar toilet d'in tace " Nafi na tafi. "
Da kyar ta daure tace "To. "
Sai dataji alamun fita
rta sannan ta dawo ciki, ta dade kafin hawayen su tsagaita taci abinci sannan ta fara gyara d'akin.
_A Company_
Kawu zaune a kan kujerar dake tsakiyar dogon tabirin, gefe da gefe mutane ne kowa zaune akan kujerar sa, Wanda ke
daga b'angaren hagu na kusa da kawu ya kalleshi yace " A gaskiya Chairman mun gaji da abinda Chief Director(Asim) yake mana, a duk sanda muka bukaci sa hannunsa akan wani aiki ko meeting a b'angaren mu ya dinga mana wala wala kenan, sam baya yin aikins
a na Chief Director."
Kawu ya kalli Asim wanda yaketa juyi a kujera cikin rashin damuwar abinda ake kararsa dashi, ran kawu ya kai koluluwar b'aci ya kallu wanda yai maganar yace " kar ka damu Director idan har Asim bai canza halayensa ba nan da one
month ni a matsayina na shugaban wannan company d'in zan saukeshi daga matsayinsa. "
A zabure Asim ya kalli mahaifinsa wanda yana gama magana ya mike yai waje, Asim cikin tsagali da raini ya kalli mutanen gun yace " ni kuka had'a da mahaifina? Lalai
ran kowa in yayi dubu sai ya b'aci. " shima yabi bayan mahaifinsa.
Office d'in kawu ya shiga, yana shiga yaganshi a tsaye kusa dashi ya karasa yace "Abba.... "
Littafin dake hannun kawu ya makamai iya karfinsa, Asim ya fad'a kan kujera cikin
tsoro yace " Yahkuri Abba amma sharri suke...... "
Yatsa kawu ya nunamai idanunsa sunyi jaa yace "kai dakikin ina ne? Meyasa sam kwakwalwarka bata aiki? "
Yai wani hucci sannan ya cigaba "Company d'in nan na Waye? Kana tunanin dan na rike s
hi na shekara ashirin yana nufin ya zama nawa? "
Kai ya jijiga sannan ya cigaba " A'a, da zarar Ashraf yaso zai zo ya amshi matsayinsa ne babu kuma yanda zamuyi. "
Asim cikin b'acin rai yace " ta ina zamu barshi? "
Tsaki kawu yai yace " 50% d'
in yaya(mahaifin Ashraf) gaba d'aya a gunsa yake, kai kasan duk karshen wata kud'in dake shiga account d'insa ya ninka nawa mai 20%?"
Asim wanda ya fara huccin takaici ya kalli Mahaifinsa, kawu yacigaba "In baka rike matsayin ka ba ka nuna ma mutan
e zaka iya kana tunanin Ashraf mai taurin kai zai bakka ka cigaba da abinda kaga dama in har ya fara aiki anan? "
Asim ya mike cikin takaici yace " shiyasa duk duniya ba wanda na tsana irin yaron nan, mahaifinsa kaf arzikinshi sunan sa yasa, kai da
ka wahala gurin taimakama uban sanda yana da rai bai ma kara ya barma ko da wannan companyn ba. "
Kawu ya zauna kan kujera cikin b'acin rai shima ya kalli Asim yace " Ka kula sannan ka dinga kokarin b'oye tsanar da kakema Ashraf dan naga kamar kanka
na rawa baka kunyar nuna mai. "
Shiru Asim yai baice komai ba.......
_A Gida_
Nafi bayan ta gama komai tai wanka dama Little ta fito mata da kaya hakan yasa ta saka ta fito domin zuwa kitchen yin aiki.
Ta d'anyi tafiya
kad'an taji ance "Ina Zaki? "
Tsayawa tai cak ta kasa juyowa, shima bai sake magana ba hakan yasa ta daure ta juya a hankali, daga gefe ta ganshi zaune akan d'aya daga cikin kujerun gun, gani tai ba kallanta yake ba hakan yasa tad'an kuramai ido,
duk da bai kalleta ba jitai yace " Kallan fa? "
Da sauri ta d'auke idanta tace " na fito ne kawai"
Ya kalleta sannan ya mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta karasa inda yake, ya kalleta yace " So nake kimin wani abu. "
Cikin mamaki
ta kalleshi tace " Me kakeso yaya? "
Ya bud'e baki zai magana sai ga Aneesa ta karaso cikin salon tafiya da yanga, tana zuwa ta shagwab'e murya tace " Cwt Yaya kaifa nake nema. "
Ashraf ya kalli Nafi sannan ya kalleta yace " Anie ya akai?"
Baki ta turo tace "ni dai banasan Anie kacemin Neesah na. "
Kunne yad'an sosa sannan ya kalli Nafi wanda da alama zaman gun ya isheta yace " Nafeesa jeki kawai. "
Wani kasalalen kallo tamai wanda ita kanta batasan ta iya ba, so take ta tambaye
shi me yakeso tamai? Ga Aneesa agun ita kuma duk ta rasa mai zatace, Aneesa ta maka mata harara sannan tace " Nafi yace kije zamuyi magana ne. "
Kamar tai kuka haka ta juya ta fara tafiya, me yake so? Abinda ke mata yawo kenan.
Itakam Anees
a zama tai ta shiga mai salo, wani abun ya biyeta wani kuwa ya juya kai kawai.
Nafi kam duk aiki take amma hankalinta nakan Ashraf har suka kammala girki, nan Goggo tace "A d'au na Ashraf akai mai. "
Da sauri Nafi ta amshi tiren tace "bari na k
aimai. "
Goggo ta kalleta tace " kinsan b'angarensa ne? "
Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani.
Nan Goggo ta bata.
Fitowa tai tana ta kalle kalle, nan Allah ya had'ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace "Amra ina
ne b'angaren Yaya? "
Nan Amrah ta nuna mata, karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan.
Knocking tai a hankali, Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace "in abinci ne ajiye zan d'auka."
Nafi ta
kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa.
Shikam ya dade kafin ya taso ya bud'e kofar, mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace "lafiya? "
Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi, ka
llan mamaki ya mata yace " kece? "
Kai ta d'aga kawai, yace " D'auko abincin ki shigo. "
D'auka tai sannan tabi bayansa, tana shiga ta tsaya a bakin kofar, ya karasa kan kujera yace " turamin kofar. "
Rufe kofar tai sannan ta kalleshi, da
hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning, nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta, ya kwanta ba tare da yace mata komai ba, itama shiru tai dan batasan me zatace ba.
Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana, sun d
ade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi.
Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa, a hankali ta d'an matso kad'an cikin in ina tace "dama d'azu ne.... "
Sai kuma tai shiru, Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace "
naji kace zan ma abu? "
Nan ma shiru, lekashi tai kad'an, gani tai bacci yake, a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido, a ranta tace "na sashi yai bacci baici abinci ba. "
Kallansa ta karayi, itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takes
an taga tana kallanshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje.
*THE INNOCENT TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
1
⃣
4
⃣
Sai yamma Little ta da
wo, abinci kawai taci suka shiga bubud'a kaya nan Little ta ware mayafai da jaka suka had'a kayan da za'a kai d'inki.
Nafi sai murna take a ranta zataga cikin gari.
Driver d'in mumy ne ya d'aukesu, a hanya Nafi sai kalle kalle take can ta tuno t
ahowarsu a mota itada Ashraf murmushi ta saki wanda Little ta kula dashi.
Little ta d'an harareta tace "Nafi na kula yau dai a farin ciki kikeyi."
Murmushi ta sake sannan ta kalli Little tace "Little dan Allah tambaya. "
Inaji kawai little tac
e sai dai ta maida hankalinta kan Nafi, Nafi tai kasa dakai cikin alamun kunya tace " in mutum yace yanaso kamai wani abu, me zai kasance? "
Dariya sosai Little tai ta dade kafin ta tsagaita tace "Hala Ya Ashraf ne ya fad'a? "
Nafi ta d'an turo
baki kadan tace "shine to menene kike dariya ?"
Little tai d'an karamin tsaki tace "in kikaji yaya ya fad'i haka wallahi aiki yakesan saki. "
Nafi ta kalleta tace "aiki shine yanasan inmai wani abu? "
Little ta girgiza kai tace "Tab bakisa
n mutumin nan ba, amma duk da haka nayi mamaki dan ni kad'ai yake sawa aiki ni kuma ba abinda na tsana a rayuwa irin inji yaya yace zan mai wani abu. "
Nafi ta d'an jujuya kai sannan tace " Meye abin tsana? Nikam dadi zanji inya sani aiki ma. "
Little ta mata wani kallo na yarinya da sauranki tace "Nafi bakisan waye Ya Ashraf ba, duk aikin da zakimai bazai tab'a burgeshi ba sannan bazai tab'a cemiki ko sannu ba. "
Nafi ta d'an tabe baki tace " to mezai sa sai yayi miki sannu bayan ke kanwa
rsa ce? "
Kallan mamaki Little take ma Nafi itakam Nafi ina ta sani cigaba tai da cewa " Sanna? N da alama ba a mai aikin yanda yake so ne. "
Duka little ta kai mata,Nafi tai saurin sa hannu agun, Little ta rike hab'a tace "Lalai ashe kina magan
a haka? "
Nafi tai murmushi batace komai ba, Little ta kalleta tace "Naji ni kanwarsa ce sannan naji d'in bana mai yanda yakeso, ke tunda kinanan sai ki mai yanda yakeso ki kuka tabbatar yacemiki sannu. "
Nafi murmushi kawai tai batace komai b
a, Little tace "Kinga da Ya Habib ne? Wayyo Allah na. "
Da mamaki Nafi ta kalleta tace "Ya Habib? "
Little ta saki wani fara'a yacigaba "D'an yayan mumy ne yanazuwa gida sosai ya dad'e yanzu ma na tabbata kila karshen satin nan ki ganshi. "
Nafi ta maida kanta titi kawai, Hannu little tasa ta juyo da ita tace " Nafi kinsan me? "
Kai Nafi ta girgiza alamar a'a, Little ta cigaba cikin zakuwa "Ya Habib ko Opposite d'in Ya Ashraf ne. "
Nafi da mamaki tace "Oppo? "
Little ta daf
a goshi tace " Kinsan me? Kinga Ya Ashraf bai da san magana shi kuma ya Habib akwai surutu, sannan Ya Ashraf akwai zafin rai shikuma Ya Habib Saukin kai gareshi. "
Nafi ta d'an bata fuska tace "Zafin rai? "
Little tace " naji ba zafin rai ba,
sannan kinga Ya Habib akwai san wasa da mutane, ga mutunci. "
Nafi wanda ta rasa dalilin jin haushi Little datai tace "Little da wa kuka fi kusa? "
Cikin rashin kulawa tace "Ya Ashraf. "
Nafi tai shiru batace komai ba jitai Little tace "Amma
Ya Habib zan aura. "
Juyowa tai cikin tsananin mamaki ta kalleta, Little ta harari Nafi ta juya.
Nafi kam ta kasa magana sai shiru tai.
Tanaji Little ta d'aga waya suna hira da wata kawarta akan Lesson d'in da suke zuwa, saboda shirye s
hiryen Exam d'in Qualifying da zasuyi, ga makarantarsu anyi hutu kuma suna komawa za'a fara jarabawa.
Nafi kam sai kallan sha'awa take mata, har suka isa gun d'inkin.
An gwadata