Showing 18001 words to 21000 words out of 145961 words
ne ya fad'o mata a ranta tace " ko baffa yan
a me? "
Jitai an kwankwasa kofa hakan yasa ta mike tare da yafa d'an kwalinta ta bud'e kofar, Matar data gani d'azu itace ta gani yanzu, ko ba'a fad'a ba tasan Mahaifiyar Ashraf ce, murmushi ta mata sannan tace "fito falo muyi magana."
Tai
gaba Nafi ta bita a baya, akan kujera ta zauna hakan yasa Nafi ta zauna daga nesa kadan a kasa, Mumy ta kalleta tace " ya sunan? "
"Nafi. " ta fad'a kanta a kasa.
Mumy tace " Nafisa kenan ai."
Nafi tace " Eh." tai maganar cikin sanyin murya.
Mumy ta kalleta da gani batafi sa'ar Little ba tace " kinsan ko ni wacce? "
Nafi tad'an kalleta kad'an sannan tace " Mamar Dan Binni ko? "
Mumy tai dariya tace " Ashraf kenan? "
Kai ta d'aga itama tana murmushi, Mumy tace " Nafi iyayenki
fa? "
Kallan Mumy tai jiki a sanyaye batace komai ba, Mumy tace " Nafi karkiji komai ki sanar dani duk abinda ya faru babu wani abu, ni mahaifiyar Ashraf ce."
Nafi tai shiru me zatace? Me zatace?
Jitai Mumy tace " Nafi!! "
A hankal
i Nafi tace " Mahaifiyata ta koma saudiyya da zama, mahaifina shine yake kokarin aurar dani ga babban mutum shine Dan binni ya taho dani. "
Mumy tai shiru ba shakka yarinyar abin tausayi ce amma ita tasan Ashraf sarai shi ba mai shiga abinda bai sha
feshi bane bare har ya d'auko yarinya daga gaban mahaifinta.
Ta kalli Nafi tace " Kidinga kirana Mumy kamar yanda kowa yake cemin, sannan ki saki jikinki kamar nan ma gidanku ne. "
Nafi ta d'ago ta kalli Mumy idanunta suka ciciko, Mumy tai mu
rmushi tace " Karki damu kinji? Sannan karki kara cema Ashraf dan binni kidinga cemai Yaya kamar yanda kowa ke cemai. "
Ta d'aga kai, ba shakka yanda taga yanayin 'yan gidan lalai in tsautsayi ya sa akasan an d'aura musu aure da Ashraf to fa lalai
tanaji ko Mumy bazata sakar mata fuska ba.
Nan Mumy ta mike tace " Little ba ta dawo ba? "
Nafi tace " eh. "
Mumy ta jinjina kai sannan tai waje.
Nafi tabi bayanta da kallo sannan tai murmushi.
Mumy na fitowa daidai nan Ashraf y
a dawo daga masallaci yana shirin yima little magana, ganin Mumy ta fito yasa gabansa ya fad'i, yasan mumy da fasaha da iya bugar ciki da alama taje ta bigi cikin Nafi ta fada mata komai, Mumy na wucewa yai wuf ya shiga bangaren.
Nafi lokacin ta m
ike kenan zata shiga d'aki, jin sallamar Ashraf yasa ta tsaya cak ta kasa juyowa sai dai ta amsa, Ashraf ya shigo da hanzari yazo daf da ita yanda har numfashinsa take jiyowa hakan yasa gabanta ya shiga bugawa, juyowa tai cikin tsoro hakan yasa suka fus
kanci juna daf da daf, gabanta ne ya cigaba da fad'uwa har tanaji kamar shima yanajin bugun da zuciyarta yake.
Shikam cikin rashin damuwa yace " Nafi me kika cema Mumy?"
Kasa magana tai sai bakinta dake motsi shi kadai, Ashraf cikin takaici yace
" kin fada ko? "
Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ke nake jira me kika ce mata? "
Gaba d'aya jitai ta kasa magana, da sauri ta murda kofar d'aki ta shige tabarshi a nan, tana shiga ta sulale ta zauna a kasa, ya za'ai ya matso mata haka daf y
ace wai tai magana?
Ashraf yabi dakin da kallo cikin takaici ya juya yai waje, yana zuwa kofa Aneesa na shigowa, tana ganinshi tai murmushi tace " Yaya sry ina gun Umma ne. "
Fuskar nan a had'e dama ransa ya gama b'aci yace "Ni har zaki rainaw
a hankali muna tafiya dake ki fita ki hau adaidaita? "
Kallansa tai cikin mamaki ta d'auka hakuri yazo bata, ta daure tace " Yahkuri Yaya dazun ne raina a b'ace yake. "
"Na gane" kawai yace ya wuceta yai gaba.
Kallansa tai cikin mamaki.
Ashraf yai waje a zuciye, d'akinsa ya wuce.
Itakam Nafi anan take a zaune har Little ta dawo wajen Isha'i, ta kalleta tace " Nafi me kike a nan? "
Nafi ta mike ba tare datace komai ba ta nufi ban d'aki, sai kuma ta dawo tace " Maryam
taramin ruwa inyi alwala dan Allah. "
Little tai murmushi sannan ta ajiye takardun data amso ta tara mata.
Little ta kula da yanda Nafi take sallah tasan kuma da alama batamasan me ake cewa ba, sunci abinci wanda Little ta d'auko mus
u sannan suka zauna hira, Little tace Nafi ta bata labarin rayuwar kauye.
Nan Nafi ta fara bata labaruruka tace " ni ba shiga mutane nake ba amma fulanuwa masu tsayawa a rafi gunsu nake zama.
Little tayi dariya sosai in taji wani labarin cikin l
abarin ta bige cikinta akan sallah.
Nafi tace " Ni kawai yi nake yanda naga Innata tanayi. "
Little tace "Zan koya miki yanda akeyi. "
Nafi cikin farin ciki ta amsa da to.
Sun dade suna hira sosai kafin su kwanta.
***********
A bangaren Mumy kuwa ta sanar da mijinta abinda ya faru acan sannan ta karasa maganar da cewa " Alhaji kasan halin Ashraf tunda kaga ya d'auko yarinyar nan to tabbas tausayinta ne yamai yawa gashi ta taimakeshi. "
Kawu yai shiru can
yace " shikenan Hajiya dama ni ban ce komai ba mamaki nake yanda akai Ashraf har ya shiga abinda ba nashi ba. "
Mumy ta ce" nima wannan abun ya ban mamaki sai dai inaji a jikina akwai dalilinsa nayin haka. "
Kawu yai murmushi yace " ai dama Ashra
f baya laifi. "
Ta kalleshi kawai tai murmushi batace komai ba.
Ashraf kam ya kasa zama,yanzu in akaji ya auri wannan kucakar ai an gama zubar mai mutunci, hakan yasa ya kira wayar Mumy.
Da mamaki Mumy ta kalli mijinta sannan ta kalli
wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace "Ashraf? "
Gyaran murya yai sannan yace " Mumy dazu me Nafi ta ce miki? "
Mumy da mamaki tace " me ya faru? "
Yace " ba komai, sai da safe. "
H
Da sauri ganin zai kashe wayar tace " Ashraf!"
Naam kawai yace.
Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu.
Ashraf yabi wayar da kallo tare d
a furzar da wata iska yace " Da alama tanada wayau."
Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa.
*THE INNOCENT TEAM*
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel,
makeup and kitchen1
⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2
⃣
)
WHATSAPP NO:
+2349030159301
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
1
⃣
2
⃣
Karfe hud'u Nafi ta bud'
e idanunta kamar yanda ta saba, shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci.
Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab'a Nafi, da
karfi Nafi tace " Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. "
Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad'anyi dariya tace " Nafi nice! Da alama Baffan nan bulala yake miki. "
Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace k
omai ba.
Little tace " Tashi kiyi sallah. "
Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace "kin tarar mi..... "
Katseta Little tai tace "Na tarar miki ke da bakya mantawa. "
Nafi tai toilet tana murmushi.
Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little
wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace " Maryam naga kin kwanta?"
"Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d'aya zan fita?"
Nafi tace" nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. "
Little ta zauna tare da kallan Nafi tace " Bacci mana. "
Id
anu Nafi ta zaro tace" Bacci kuma? Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta? Tab di. "
Little tai dariya tace " Uhm hm i kam dai bacci zanyi. "tai maganar tare da kwanciya.
Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al'amari, mutum ya kwana yana bacc
i sannan ya kara kwanciya da safe? Shi ba ciwo yake ba?
Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike sanye da hijabin datai Sallah tai waje.
Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace" Masu gini
sun sha aiki. "
Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha'awa, sukam 'yan kitchen sunata hada hadar aiki, ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska, Matar jiyar nan ta kalleta tace " yanaga kinzo da wuri? "
Nafi ta dan mur
musa tace " in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. "
Kai ta jinjina, Nafi ta kallesu tace " me zan fara? "
Wata daga ciki ta kalli matar tace " Goggo me zatayi? "
Goggo tai shiru can tace " ke wani bangare kika fiso? Ak
wai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. "
Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace "Nafisan b'angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. "
Dariya suka sa mata, Goggo tace " B
angaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai, wani sa'in da rana ko dare ma haka."
Nafi tace " Bakomai."
Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za'ama kowa yau, sunyi sa'a
wasu suna zuwa iri d'aya, nan suka shiga aiki.
Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa.
An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma 'yan gida su kuma nasu aka fita dashi.
Nafi kam abin sai birgeta yake, sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi.
Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci, Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud'e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa.
Ba
cci ne yai gaba da ita, wajen 9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa, da sauri Nafi ta mike tare da bud'ewa, Wasu yarane su biyu d'auke da ledoji suka kalli Nafi sukace " Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. "
Little dake zaune akan gado tace "Am
ra ku shigo mana. "
Nan suka fara kokarin jan ledar, Nafi ta amsa ta shiga dashi, little ta kalli kayan tace " me yace?"
Wacce ta kira da Amra tace " cewa yai mukawo miki zai kiraki. "
Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf, da sauri
tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin, tace "Yaya ina kwana? "
Yace " kinga dama kin tashi? "
Kallan Nafi tai sannan tace " Yaya ba bacci nai ba. "
"Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki."
Little ta d'an turo
baki sannan tace " Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji."
Yace " Yanzu za'a kawo manyan, naga su bazasu iya d'auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. "
Little tace " to kana ina? "
Ina gun motor park, Sai Amra ta rakota. "
Little tace " to amm
a yaya kayan meye? "
Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d'au driver ya rakaki gun mai d'inkinki sai a gwadata a mata. "
Baki little ta bud'e to kawai tace tanaji ya kashe wayar.
Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiy
a daga nan duk ke ya siyowa kayan. "
Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace " eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d'an miki yawa. "
Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata.
Little ta katseta "ki tashi dan Yaya baisan j
ira. "
Nan suka mike itada Amra.
Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa.
Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi, kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace " kema daga ba
ccin kike? "
Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ki d'au kayan suna bayan mota."
Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d'auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace " Nafeesa da wani
abun ne? "
Yawo ta had'iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima.
Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana, Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace " Yaya
. "
Dasauri ya d'ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan.
Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya.
Ta kara daurewa tace " Yaya Na gode. "
Tana fada ta juya zata d'au kaya, jitai yace "
Nafisa!! "
Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro, ya kalleta kad'an sannan yace " Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?"
Kanta na kasa sai gabanta dayake fad'uwa, Ashraf yace " meye dalili? Ko raini ya fara shiga t
sa...... "
Katseshi tai da sauri da cewa " Wlh ba haka bane, matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad'uwa shiyasa na rufe. "
Da mamaki yake kallanta yace " Nafisa yaushe kika koyi karya? "
Idanu ta zaro cikin mamaki tace "Wlh ba ka
rya nakeba Yaya. "
Ya d'an kura mata ido hakan yasa tai kasa da kanta, a ransa yace " dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. "
Wani abu ya tuno ya d'auke kansa daga kanta a hankali yace " da alama sanda kika ciren riga gab
an naki bai fad'i ba "
Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya, ya kalli yanda take sauri yace " kayan fa? "
Idanu ta rufe, cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe, batasan har tazo inda yake ba, jin tayi dan tun
tube da kafa yasa ta bud'e ido da sauri, Ashraf ya kalleta yace " Toh da alama gaban naki baya fad'uwa ko? "
Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta, idanunta suka ciciko, Ashraf ya mike tare da d'anyin murmushi, ya matso
saitin kunnenta yace " in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. "
Tanaji ya tafi, ta dade kafin ta mik'e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar, jin goshinta ya fara zafi