Showing 87001 words to 90000 words out of 145961 words
sake hannun Anisa tai hanyar waje da gudu, jitai ta bugi mutum, ta tsaya tare da d'agowa ta kalleshi, Umma kuma wacce suka taho itada Anisa rike da bulala zata daketa itama ta tsaya cak.
Ashraf ya kallesu, yace " me kuke tunani kuke aikatawa?"
Umma ta fara hucci, Anisa kuma kallan yanda Nafi ke tsaye a jikinsa take, Ashraf ya kallesu yace "Umma me kukeyi?"
Umma tace " Kai dan marasa tarbiya,kayi kadan ka wulakantamin 'yata akan wata banza yar daji, kuma wlh kaji na fada maka ko ba ya
u ba sai na mata dukan da sai an kwantar da ita a asibiti kamar yanda aka kwantar da tawa 'yar."
Murmushi ya sakar mata wanda ya bata tsoro, yace "Umma kenan banaji ranar da zakiyi hakan 'yarki ma zata kwana a gida."
Anisa ta matso cikin takaici
tace "Yaya mai kake nufi? In umma ta daketa kana nufin nima dukana zakai ko me?"
Hannu yasa ya shafi gefen fuskar Anisa yace " No no no, kinfi kowa sanin banasan harkar duka sai dai ina nufin a ranar zamana dake ya kare."
Baya baya ta fara ja,
tana girgiza kai, wannan ba Ashraf dinta bane, Ashraf ya kalli Umma wacce ta saki baki tana mai kallan mamaki yace " i tried really hard inga na boye abinda ke raina, sai dai naga alamar bakusan wannan ba, dan haka daga yanzu i won't tolerate anyone ko da
kuwa Little ce."
Yana kai nan ya kalli Nafi yace " koma ciki ki kwanta zanga wanda zai kara gigin tabaki."
Nafi kam yau ta zama kurma, a hankali ta koma ciki, Umma ta kalleta cikin takaici, Ashraf ya kalli Little yace "kin bani kunya." ya juya za
i fita jiyai Anisa tace "Yaya karka fita."
Juyowa yai ya mata wani kallo yace " a matsayinki na wa?"
Tace "ni ai matarka ce."
Murmushi yai sannan ya tako a hankali har inda take ya rungumota jikinsa sannan yakai bakinsa kunnenta yace " mata wace t
ake shan maganin hana daukan ciki? Wacce take binciken dukiyar mijinta? Wacce take jiran mijinta ya rasu ta samu gadon sa?"
Kallan tsoro tamai, ya matso da fuskarta wajen kuncinta yace " why? Kin dauka duk ban sani ba?"
Ya kara mata murmushi san
nan ya juya yai gaba, zubewa tai a kasa tama kasa kukan sam, Umma ta matso tace "ke ya ce miki?"
Kai kawai take girgizawa, ganin haka yasa umma ta cicibeta sukai waje.
Little kam da sauri tabi yayanta.
Nafi kam ita kanta a d'aki zaka tai dab
as tana mamakin abinda Ashraf yakeyi tun jiya, ita kanta shakkarsa take taya za'ai ya dinga fadar bakar magana hankalinsa a kwance? Bata taba ganinsa a haka ba lalai kenan akwai wani hali nashi da ya boyema 'yan gidan.
Ashraf na fita bangarensa y
a nufa, yau kam gidan kamar ba safiya ba kowa ya tashi, a bakin kofarsa yaga Mumy hakan yasa ya gaidata kai tsaye ya bud'e kofarsa ya shiga.
Shigowa tai itama, guri ya samu ya zauna itama ta zauna a kujerar da ke kallansa, Little ce ta shigo ganinsu ta
re yasa ta koma gun dinning ta zauna.
Sunyi shiru kafin Mumy tace " Ashraf!"
Kallanta yai batare da ya amsa ba.
Tacigaba "me kake nufi da kalamanka na jiya?"
Cikin rashin kulawa yace "me nake nufi kuwa?abinda kikaji shine gaskiya."
Ido
ta kuramai can tace " kasan me kake fada kuwa? Kasan me ake nufi da aure?"
Dariya yai ya kalleta yace "Mumy kenan, na dauka ko dan shekara 18 yasan me ake nufi da aure, sannan banyi tunanin zaki damu ba in nayi aure ba tare da saninki be tunda kika sak
e aure ba tare da sanina ba sannan kika fita daga harkata tun ina karami."
Idanunta ne ya ciciko tace " Nasani i am a bad mother to you, sai dai Ashraf kai kanka kasan ba inda uwa zataki danta."
Idanu ya rufe yace "gashi kuwa na gani? Tunda nake
dake kin taba tambayata yaya nake?meke damuna?menene matsalata? Banaji tun mutuwar mahaifina kin kara zama dani zama na uwa da danta."
Mumy tai shiru, sai idannunta da suka ciciko, Ashraf ya dan rufe bakinsa sannan ya dan sa hannu ya shafi kansa yace
" inaji a jikina ba san mahaifina dani kike ba."
Yana kai nan ya mike zai shiga ciki, sunansa ta kira "Muhammad!"
Tsayawa yai cak jikinsa yai sanyi, tacigaba " bazaka fahimci dalilina na yin hakan ba, sai dai na sani banida wani uzuri da zan kare ka
ina tunda komai da nai is due to ky selfishness and greed."
Bai amsa ba ya shige d'akinsa, Mumy tabi bayan dakin da kallo tare da share kwalla.
Shima yana shiga ya zauna a bakin gado tare da rufe fuskarsa da hannayensa biyu.
Mikewa yai tare
da yin wanka yasa kaya ya dau jakarsa yai waje ganin lokacin aiki yayi.
Little ya gani a zaune bai kulata ba yai waje, itama kasa binsa tai dan jikinta duk ya mutu.
Ashraf a gun ajiye motoci yaga kawu shima zai fita, da saurinsa ya karasa gun kaw
un wanda har abin yaba kawu mamaki, Ashraf ya karasa tare da cewa "dama gunka zan fara isa in naje Company."
Kawu ya kalleshi yace "me? Ka bada hakurin laifin daka aikata?"
Ashraf yadan yi dariya yace " laifi? Basan na aikata laifi ba, sannan mag
ana ce ta inasan kai appointing dina a matsayin chief director a company."
Kallan mamaki kawu yamai yace " Ashraf meke damunka?"
Baki yadan motsa yace " meke damuna kuwa? So nake inyi sauri in amshi abinda yake a matsayin nawa, me? Laifi ne yin h
aka?"
Kawu ya saki baki yana kallan Ashraf, Ashraf yace "sai naga takarda." yana kai nan ya shiga mota yai gaba.
Nafi kam yau wunin daki tai da azahar Mumy ta aiko akan taje, bayan sun gaisa Mumy fuska a hade tace " Nafisa so nake ki fadamin g
askiyar meke faruwa."
Shiru Nafi tai, Mumy tace "ki fadamin ko?"
Nafi ta kalleta tace "mumy kiyi hakuri."
Mumy ta runtse ido tace "kina nufin da gaske ya aureki kenan? Tun kafin kuzo garin nan?"
Kasa Nafi tai dakai, Mumy ranta ya b'aci ta
mike tai ciki, Nafi jiki a sanyaye tai waje.
********
Ashraf ya taso daga aiki yana cikin mota a gun traffic light, an tsayar dasu, shikuma yana kan mashin ta saitin gun da Ashraf yake.
Ashraf ya leko kansa ganin mai saida ruwan faro ya amsa tare
da mikamai dari biyar, yaron yace bari na nemo cangi, kai Ashraf ya girgiza mai yamai alama da hannu akan yaje kawai.
Yaran ya juya yana murna, shikuma dake kan mashin ya leko dan ganin me wannan abin arzikin.
Kallan mamaki yamai da sauri ya sauk
a daga kan mashin din ya matso inda Ashraf yake yace " Wazob main ba kai bane Ashaf?"
Ashraf yamai kallan mamaki yace " Kamar nasan......"
Dariya yasa yace " bari nama inkiya ta, Do you went?
🤔
"
*#ASHRAFEENAH TEAM**ZUCIYA*
_ĸow
a da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*53*
*Wannan shafin naki ne Billy Galadanci*......
😍😍😍
Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace "Dan Littin Gayu?"
Key
a d'an Litti ya sosa yace " Ashaf nine dai kam." yai maganar yana washe baki.
Dariya sukama juna ganin za'a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje.
Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa.
Gefen titi suka gangara Ashraf yai par
king tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace "Dan Littin Gayu."
Dan Litti yai dariya yace "inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison."
Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace " Ah haba? Ni ai ba
ntaba tsammanin ganinka a nan ba."
Nan D'an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai.
Ashraf yai murmushi yace " Gaskiya kasha wahala gun nemana,
ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza."
Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba " Shi kuma wannan mahaifin Nafin....."
Sai kuma yai shiru.
Dan litti yace " Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba."
Shiru A
shraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi.
Ya juyo ya kalli Dan Litti yace " yanzu ina zaka?"
Dan Litti yace "mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina."
Ashraf yai murmushi yace " Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turan
ci."
Kansa ya kara sosa wa yace " inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin."
Sukai dariya a tare, Ashraf yace "ba matsala mu tafi gidan mu."
Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf.
Nafi kam yau gidan duk ya ish
eta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita.
Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d'ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidans
u Ferry.
Tai sa'a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu.
Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda za
suyi.
*********
Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa.
Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai fi
rgigitbya kalleshi.
Fito mu shiga ko?"
A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle.
Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud'e ya kalli Dan Litti yace 'shiga muje ko?"
Kai dan litti ya girgiza yace "a'a kadai fara shiga."
Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace " Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko
motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu."
Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace " Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci."
Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma
yai ciki.
Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace " ya akai?"
Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace "lalai Datti zai ci Kw*******"
Ya karasa ya
na dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace "KAI! Kai jama'a." da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace " ya akai?"
Dan
litti yace " Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?."
Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa " lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan."
ya kara kwashewa da dariya.
Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace " ki sa Nafisa ta kawo min abinci."
Little wacce tun dazu take neman Nafi tace "yaya wlh nima nemanta nakeyi."
Cikin rashin fahimta yace
"kamar ya kenan?"
Tace "wlh na dawo daga makaranta naga batannan."
Cikin fada yace "to ija taje?"
A tsorace Little tace "wlh bansani ba yaya "
Tsaki yaja sannan ya kashe wayar, ya zauna a bakin gado, haushinsa da takaicinsa d'aya da ko
waya bai sai mata ba, ya rufe ido cikin takaicin kansa yace " why?"
Yanzu tayaya zai soma nemanta?to inama ta sani da zata? Kansa ya dafe cikin takaici.
Yana fitowa sai ga Little ta shigo da tire ta kalli dan litti mamaki ya kamata bayan Habib b
a wanda yaya yake kawowa bangarensa,ina kuma ya samo wannan?"
Ashraf ne ya katseta da cewa " ko wa ya dawo?"
Kai ta daga alamar eh, fuskan nan tasa a daure yace " ki buga taro."
Ta amsa da to sannan ta fita, kallan Dan Litti yai yace " zo ka ci
abinci Gayu."
Nan ya kaishi dinning ya turamai tiren gabansa sannan shi ya fita.
Tunda ake taro agidan yauce rana ta farko da Ashraf ya fara zuwa gun taron da wuri, zuwa yai ya zauna fuskarsa a murtuke.
A hankali kowa ya fara shigowa duk
wanda ya shigo sai yayi mamakin zuwan Ashraf da wuri.
Bayan kowa ya hallara ne Ashraf ya mike yace " bayan fitata waye ya kira matata Nafisa?"
Cikin mamaki kowa ya kalleshi, Kawu yace " dalilin taramun da kai kenan?"
Ashraf yadan motsa baki s
annan yai murmushi yace " matata bayan fitatavna tabbata wani ya kirata, in kuwa ba'a kirata ba anje har inda take anci zarafinta, dan a yanzu haka bata gidan nan, ban kuma san inda ta shiga ba."
Umma tace " to menene namu a ciki? Banaji wannan damuwa
r mu ce, kila ta tafi yawon karuwancinta ne."
Ashraf yq shafa goshinsa yace " menene naku a ciki? Ina tunatarwa ne da in ban ganta ba ni kaina bansan me zan aikata ba."
Asim ya mike rai a bace yace " kai! Kayi kadan ka taramu akan wata banzar
yarinyar da mu bamu san matsayinta ma a gunka ba, wanda babu shaidar ita matarka ce."
Ashraf yadan yi murmuhsin da har hakoransa suka fito yace " Little kiramin bakon nan."
Nan ta mike tai waje, Ashraf ya cigaba " wlh in har wani abu ya samu Nafi
sa bani da guarantee din abinda zan iya aikatawa."
Mumy ta kalleshi zatai magana kawu yai saurin cewa "nina kiranta bayan ni kuma banaji akwai wanda ya kirata, inka tashi hukuncin sai kamin, tunda yanzu idanka ya rufe akan karamar yarinya sam baka tun
anin kowa."
Ashraf ya kalleshi sai dai baiyi magana ba, ya gane Mumy ce ta kirata kenan, tunda yasan ai kawu suna tare gun aiki.
Kallan Mumy ya shigayi, ta had'e fuska tace "eh nice na kirata, Ashraf wai meke damunka ne kwana biyi?"
Idanunsa ne suka fara canza kala, a hankali ya ke fitar da wani hucci dan kar a gane ransa yakai kololuwa gun tashi.
Shigowar Dan Litti ne ya taimakeshi da yayi barna dan tibiren dake gabansa mai dauke da cups na tangaran kawai yake kallo.
Dan li
tti ya tsaya daga nesa cikin tsoro ganin duk an zubomai ido, kuma kallan tsana ake mai.
Ashraf ya kalleshi yace " karka damu mutumina gani nan anan."
Kallan Ashraf yai sannan hankalinsa yadan kwanta, Ashraf ya kalli Kawu yace "to ga shaida na n
an na sanda aka daura auren, banaji daga wannan shaidar kuma kuna bukatar wata."
Kawu ya Mike ya kalli Dan Litti yace " daga ina kake?"
Dan litti yace " kauyen gwaram."
Kawu yace " menene hadinka da Nafisa?"
Kauyensu na kusa da tamu."
Menene ita kuma tsakaninta da Ashraf?
Matarsa ce.
Wannan kalma ta rikita kowa, Ashraf yama Dan litti alama akan ya koma.
Yana fita Ashraf yace " zan nemo matata da kaina, sai dai bazan yafema wanda ya kuskura ya kara shiga harkarta ba."
Yana kai nan yai waje......
_Ina mika ta'aziyata ga Aisha Y. Kura na rashin mahaifinta datai, Allah ubangiji ya jikansa, yasa aljanna ce makomarsa ya kuma kai haske kabarinsa (Ameen)_
*#ASHRAFEENAH TEAM*
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*ASMY I Sincerely dedicated this page to u may Allah help and guide u through the right path always....(Ameen)......*
😍😍😍
{54}
Ashraf ya fita da
ga gun taron rai a b'ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace " muje inkaika b'angaren baki ka huta ina da gun zuwa."
Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da
kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu.
Ta ina zai soma nemanta???
Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai,