Showing 141001 words to 144000 words out of 145961 words
ji da ita.
Nafi ta ba Inna labarin duk abinda ya faru wanda yasata kuka kamar ranta zai fita dan kuwa tasan laifinta ne duk abinda ya faru ba shakka itace sila sai dai tay
i farinciki na ganin yarta cikin wadata haka da farinciki.
Sun shirya tsaf Mumy ta biya kudin komawa da Inna.
Nan suka shirya suka baro kasa mai tsarki suka dawo gida Nigeria.
A ranar da zasu dawo Ashraf sam ya kasa zaune ya kasa tsaye dama t
un washegari kafin su dawo ya dau Dan Litti suka shiga manya manyan company's na yin furnitures yasa kaf kayan bangarensa aka canza ma Nafi, sannan ya sai akwatuna saiti ya zubamata kaya kala kala, dinkakune, wadanda ba'a dinka ba, dogayen riguna da Englis
h wears.
Ya dauko masu gyara aka gyara bangaren sosai kana gani kasan amarya za'a kawo.
Kayan Anisa na sawa kuwa aika mata b'angaren mahaifiyarta yai, wanda hakan ba karamin tada musu hankalu yai ba, Anisa kam ko abinci bata iya ci kullum kuka ka
wai takeyi.
Yau tun safe ya shirya dan sunyi waya da wani abokinsa da suka tafi tare ya sanar dashi yanzu zasu taho.
Bayan ya kintsa tsaf Dan Litti sai tsokanarsa yakeyi wai wannan zumudi haka? Shi bai taba ganin Ashaf a cikin wannan yanayin b
a.
Ashraf dariya kawai yakeyi, ganin akwai sauran lokaci sosai yasa kawai ya wuce police station nan yai bailing Asim bai tsaya ya ganshi ba yai gaba.
Asim yayi baki sosai kamar ba shi ba ya rame sosai, ya fito ya tari adaidaita yai gida kamar wan
i almajiri.
Airport ya wuce suka hau jirgi shida Dan Litti sukai Abuja.
Sun saita abin suna isa ba dadewa Jirginsu Nafi ya iso.
Tunda Jirgin ya fara alamun sauka Ashraf ya kafe jirgin da ido, har ya sauka sannan a hankali alhazai suka far
a fitowa kallan mutane kawai yakeyi yanasan ganin matarsa.
Bayan sun sauko ne suka taho ahankali aka musu checking nan ya hango Nafi.
Wani irin sanyin dadi ne ya dinga ratsashi ba shakka bai taba tunanin akwai 'ya macen da zatasa yaji irin wannan
yanayin ba amma yanzu ya bada kai bori ya hau.
Su Nafi suna fitowa daga gun daga nesa ta fara kalla kalle, nan idanunta suka hango mata abin begenta.
Tsaya wa tai cak tana kallansa idanunta suka ciciko da kwalla, shikansa kallanta kawai yakeyi,
Mumy ganin haka yasa taja hannun Inna sukai gaba.
A hankali suka fara takowa idanunsu nakan juna, Ashraf sam bai kula da wani agabansa ba sai jiyai ya bige wani, ya d'ago ya kalleta dariya ta sakar mai shima yai dariya sannan ya cigaba da takowa, sai
da suka zo daf da juna ya kai hannu da niyyar rungumota, ta matsa da sauri tare da cemai "yaya mutane."
Kallan mutanen gun yai sannan yadan sauke fuska alamar takaici, tai murmushin farinciki ya matso kusa da ita yace " ni fa gaskiya so nake na jiki
a kusa dani."
Kallan mamaki tamai tace " yaushe yayana ya zama haka?ba kunya?"
Mutanen gun ya kara kalla cikin takaici yace " muje masaukin da nasa a kama mana sai yamma jirginmu zai tashi."
Nafi ta daga kai nan suka fara tafiya a jere, ganin
tana jan yar karamar trolly dinta yasa yakai hannu ya amsa.
Mamaki abin ya bata sai dai bata musa ba ta sakar mai tana murmushi.
Can inda yabar Dan Litti ya karasa nan yaga Mumy, da sauri ya mikama Nafi jakarta shifa sam idanunsa sun rufe bai ku
la da ita ba.
Nafi tai saurin matsawa daga gun jakar tai kamar bata ganshi ba.
Mumy tai dariya tace " Ashraf jakar zata fadi."
Kallan Jakar yai ya harari Nafi wacce ta matsa dan yasan da saninta, da sauri ya waske yace " Mumy lallabani tai aka
n in rike mata wai ta gaji."
Nafi ta zaro ido tace " a ina kenan akai hakan?"
Harara ya buga mata nan aka kwashe da dariya dukansu harda Inna dan ta gane lalai wannan shine sirikin nata.
Ashraf ne ya kalleta ba shakka ba sai an tambaya ba akwa
i kama sosai tsakaninta na Nafisa.
Nan ya gaida Mumy ya gaidata sannan suka shiga taxi suka nufi hotel din da suka kama.
D'aki uku yasa aka kama d'aya shida matarsa, daya Dan Litti dayan kuwa Mumy.
Sanda zasu kama D'an Litti har tsokanarsa ya
i yace "amma dai Mumy da Nafi ka kamama d'aya ko."
Harara ya bugamai yace " to wa ya sani?"
Ana zuwa Mumy ta kama hannun Inna sukai d'akinsu dan tasan da alama Ashraf ba kara a harkarsa ta yau.
Shikam ko a jikinsa ya kalli Nafi yace muje.
Tsayawa tai tace " ina zamu? Yaya tarefa muke da mumy?"
Ya hade rai yace " to ko gabanta zamu in jawoki jikina?"
Idanu ta zaro tace " ba kace yau zamu koma ba?"
Yace " dan yau zamu koma sai aka ce a hanani jin dimin matata?"
Zatai magana
taji ya ja hannunta ya turata d'akin ya rufe.
Ita dariya ma abin ya bata tace " yaya wai yaushe ka zama haka?sam ka manta da wata kalma a hausa wai kunya."
Rungumeta yai ya saki numfashi yace " Ahh lalai nayi missing matarnan tawa."
Jiki
mta tadan janye kadan tace " nifa yaya a gajiye nake sannan wanka nakesan yi."
Zama yai akan kujera tare da juya kai gefe.
Nafi ta dauke kai itama ta dau towel ta cire kayanta ta d'aura sannan ta matso kusa dashi ta manna mai light kiss a lab'ans
a tace " is that okay?"
Juyawa tai zatai gaba da sauri yasa hannu ya kamota ta fada kan cinyarsa ya kalleta ido cikin ido yace " Are u kidding me?"
Zatai magana taji bakinta a cikin nasa, wani salo yake mata wanda yasa itama dole ta fara bashi mu
rtani, nan fa ya rabata da towel dinta ya shiga sarrafata ta nayanda yakeso, sai numfashi yake fitarwa itakanta tasan yayi missing dinta........
Sai da suka gama tukunna ya jawota jikinsa ya rungume yace " I really Miss u Feenah."
Yanda taji ya f
adi sunan sai da tsikar jikinta ta tashi, idanu ta kafeshi dashi, baki yasa ya hura mata iska a idanun yace " kallanfa?"
Bata dauke idanunta ba tace " yayan dan kara fada."
Ya kalleta yace "mene? I miss u?"
Kai ta girgiza tace "a'a d'ayan."
Kallan mamaki ya mata yace " to mene?"
Tace " d'ayan please."
Yace " wai Feenah?"
Kai ta daga da sauri tace "bantabajin dadin sunan ba a bakin wani ba kamar kai."
Idanu ya kanne yace " badai so kike kicemin haka kikesan indinga ce miki
ba?"
Shiru tai sannan tana wasa da gashin kirjinsa tace "mene? Bazan iya ba?"
Yace " sosai, dan ni Baby nake san cemiki dan haryanzu u are a baby."
Baki ta turo tace " salan ka faracemin baby daga na haihu ka koma cemin Nafisa?"
Cikin
mamaki yace " saboda kin haihu sai kawai na daina cemiki?"
Tace " sosai ma dan nasan abinda na haifa zaka koma cema Baby, haka kawai a fara cemin suna ba wani dadewa a canza."
Kallanta yai yace " to amma?" Sai kuma yai shiru kafin da sauri ya kall
eta yace " ba wani dadewa? Ya akai kika san haka?"
Kanta ta cusa cikin kirjinsa tace " ya za'ai bazan sani ba bayan lokaci kawai suke jira?"
Idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya d'agota shima ya zauna akan gadon, ya rike hannayenta yace " Bab
y me kike nufi?"
Harararsa tai tace " sai nayi dala dala? Agunka fa na koyi murda magana."
Yawu ya hadiya sannan ya kalleta cikin wani yanayi yace " Nafisa bana san........."
Kiss tamai a kunci sannan ta kai hannunsa na dama kan cikinta bat
ace mai komai ba.
Kallanta kawai yake kamar a mafarku yakejin abun, da sauri ya jawota ya rungume tsam yace "Nafisa yaushe?"
Tace "sai da mukai tafiya sannan na sani."
Wani irin tsantsar farinciki ne ke ratsashi ya kara kankameta, cikin zolaya
tace " kaga banshirya ba na samu ciki sannan gashi ance a satin nan zafa a kafe mana list na makaranta."
Ashraf ya dagota yace " makaranta?"
Kai ta daga da sauri.
Fuska taga ya canza yace " da babyn nawa za'a dinga zirga zirga?salan karatu yasa
a ki kulamin da babyna?"
Cikin mamaki ta kalleshi tace " ban gane ba?"
Yace " ki bari dai sai kin haihu."
Kallan tsantsan mamaki tamai tace "yaya mai kake fada haka?"
Dariya taga yasa yace " me? Kinji haushi? Nima ramawa nai ina murnar
zanyi d'a ko 'ya amma kidinga min zancen wai karatu? Nima shiyasa na rama."
Hannu tasa tadan bigi kirjinsa tace " yaya harfa ka tsoratani."
Mikewa yai ya daga ta cak yai toilet da ita yana cewa gwara tsoron ya tsaya daga ke karki kaimin shi ciki
."
Yana ajiyeta a bathtub ta kalleshi tace " ka gani ko? Dama nasani ina haihuwa zaka daina sona."
Murmushi yai yace "sorry Feenah dan da alama zan daina kuwa."
Haushi ya kamata ta kafeshi da ido, goshinta ya matso ya sumbata yace " in band
a abin ki ai soyayyar da muke ma juna ita zamu yi karo karo mu ba babyn mu."
Ta kalleshi tace " hmm gashi nan har ka daina cemin baby, shi yasa ma nace kar a fara."
Shigayai cikin bathtub dib ya sakar musu shaya ya jawota jikinsa ya rungume a hank
ali yace " Nafisa bansan irin farincikin da nake ba yau lalai ina cikin farinciki mara misaltuwa, ji nake kamar bayani farinciki a duniyarnan."
Murmushi tai ta kara shigewa jikinsa.
Bayan sunyi wanka dakansa ya shafa mata mai sannan ta saka wata
doguwar riga baka dake cikin jakarta sannan sukai order na abinci aka kawo musu.
Shi dakansa ya dinga bata bayan ta koshi sannan shima yaci, ya koma kusa da inda take zaune ya jawota suka kwanta a kan gado, a hankali tace " yaya ya kuka kare?"
Na
n fa ya zayane mata duk abinda ya faru Nafi kam tasha kuka kankameshi tai tsam taba kuka tace " Yaya."
Murmushi yai yace " karki damu ai komai ya wuce."
Cikin kuka tace " wace irin rayuwa ce wannan ace duk mutanen dake zagaye dakai ba sanka suke
ba? Ace mutum ya fifita dukiya akan jininsa"
Ya sake murmushi yace " _zuciyar kenan ai kowa da irin tasa_, wani akan kudi ba abinda bazai iyayi ba."
Tai murmushin takaici sannan tace " yaya wato da rayuwa ta da taka is so similar inaji tamu kadda
rar kenan, bamu da kowa sai junan mu, nima daga mahaifina har mahaifiyata kowa rabuwa yai dani saboda san abin duniya."
Ashraf ya kalleta yace " ya akai naga kamar mahaifiyarki?"
Nan ta bashi labarin abinda ya faru, kai ya girgiza cikin takaici ya
ce " Kaddarar da Allah ya daura mana kenan, ikon Allah ne yankaini garinku har na hadu dake, duk da rashin mutanen da ke sona tsakani da Allah a kalla ina alfahari da matata Nafisa na sona tsakani da Allah."
Murmushi tai tare da goge hawayenta ta kai
fuskarta saitin tasa sannan tasa hannayenta ta kare bangare biyun idanunta a rufe suke sai ta bud'esu a hankali tana kallansa, shima kallanta yakeyi tace " nima ina alfaharin kasancewa dakai."
Murmushi ya Mata yace " Nafisa tnx alot 4 not living me."
Wani sansanyan murmushi ta saki sannan ta zare hannayenta ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace " zaka cigaba da sona duk da banda komai?"
Murmushi yai sannan yace " zaki cigaba da sona duk da yanda nake?"
Idanu ta lumshe tace " duk rintsi
bazaka wulakantani ba?"
Murmushi ya sake yi yace " duk rintsi bazaki gaji dani ba?"
Kallan juna sukai suka saki murmushi Nafi tace " yaya amma Little dita fa?"
Ajiyar zuciya yai yace "sai dai kinje."
Ta jinjina kai tace "yaya nisa fa?"
Kallanta yai yace "tana gun tsohuwarta."
Cikin mamaki tace " amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?"
Ya hade fuska yace " kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina."
Nafi tai
murmushi tace " amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?"
Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace " kabarta ma da abinda t
akeji plx karka saketa."
Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace " wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi."
Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace " ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya
shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba."
Kanta ta kwantar a bayansa tace" amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?"
Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru.
Dariya so
sai tai tace " amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba."
Ashraf yai dariya yace " nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shi
ne yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura."
Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace " amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka k
uwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu."
Ashraf yace " haka ne, amma bakya ganin ya ka
mata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?"
Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace " karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida."
Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar ts
oron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya.
Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kans
a yace gidajenta za'a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba.
Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da saur
i, a kwance ta ganta a d'aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri.
Little tace " Nafisa da wani id
o zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?"
Nafi ya rike hannayenta tace " Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?"
Little hawaye na zubo mata tace " ta ya zakice b
an aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?"
Kai Nafi ta girgiza mata tace " karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara."
Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta
jata bangaren Mumy.
Little na zuwa ta fada kanta tana kuka.
Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi so
sai ya tam sannan tace yaje yai wanka.
Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare.
**********
Da daddare Ashraf yana zau
ne ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace " yaya ya akai?"
Yace " wai bazaki taho gun mijinki