Showing 75001 words to 78000 words out of 145961 words

Chapter 26 - ZUCIYA COMPLETE

kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad'a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?"

  Ashraf ya kara rike hannunta yace " Nafisa!

"

  Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace " na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawa

ra ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata."

   Idanu Ashraf ya runtse sannan ya bud'esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa k

wacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya jike shakaf.

  Kuka take sosai wanda ke taba duk wani lungu da sako na jikinsa, kanta ta kwantar a wuyansa a lokacin da ta fara tsagaitawa da kukan, jin jikinta yai ya fara d'aukan zafi ya

daure ya d'agata sannan ya riko hannunta ya shiga hura hannunta da bakinsa yana murzasu, kallansa kawai takeyi tanajin wani irin sabon kaunarsa na ratsata, Why?? Meyasa ita da takesan ta daina sanshi amma takejin haka.

   Ya kalleta yace " zazzabi ke ne

man kamaki, me yasa bazaki min magana ba kika shiga ruwa?"

  Ta kifta ido sannan tace " yaya ka tab'a tunanin ya nakeji inkamin zancen saki bayan ban tabbatar da matsayin aurena ba ma? "

 

  Ashraf ya kalli yanda jikinta yai sharaf sannan ya kalli id

anunta cikin dan fada fada yace " ina miki zancen jikinki kinamin zancen abinda ba shiba?"

   Idanu ta kafeshi dashi, ya kalleta shima, kallan juna suka shigayi dukansu wani abu na ratsasu, Nafi ta daure ta d'auke idanta ta juyar da kanta jikin window,

Ashraf ya sa hannu ya rikota tare da jawota kusa dashi.

  Idanun Nafi ne suka fifito ya kalleta yace " kalleni.!

 A hankali ta d'ago tana kallanshi ta maida kanta kasa, jikinta ne ya mutu ganin ya sa kanta akan kafadarsa yace " ki zauna a haka na yan m

intina."

   Why? Tafad'a a hankali yai gyaran murya yace " zai taimakawa jikinki dake neman kamuwa da zazzabi."

  Tai murmushi batace komai ba, ya sake gyaran murya yace " ba kuma cewa nai kiyi hakan ba da wani."

  Tace " me yasa? Naga taimako ne."

 

Ya harareta yace " ni ai haryanzu akwai aurena akanki."

Tad'an tab'e baki tace " auren da ni kaina ban tabatar ba."

 

Me kikeso ki tabbatar? Idanu ta rufe kamar mai bacci dan batada amsa.

Ya kalleta sannan yai murmushi.

  Ganin ruwa ya fara d'aukewa

yasa ya gyara mata kwanciya zuwa kujerarta duk da yasan ba Bacci take ba, sannan ya tada mota ya jata a hankali.

   Nafi kam juyawa tai tana murmushi lalai wannan rana ta shiga cikin tarihin rayuwarta ba wai cewa yai yana santa ba sai dai ta rasa dalil

in farincikin nata.

  Sun isa gida sannan yai parking yasa hannu a wuyanta yaji dumin kadan ne sannan ya kalleta yace " mai baccin karya ki tashi ki shiga ciki ki dan zuba ruwan zafi a jikinki kisa kaya mai dan nauyi."

  Kai ta d'aga ba tare da ya ju

yo ba, sannan tai sumsum tai waje ya bita da murmushi.

 Yasa ankai mata kayanta sannan ya wuce b'angarensa yai wanka shima da ruwan zafi sannan yasa kaya ya kwanta akan gado tare da dora hannunsa akan goshinsa, meke damunshi? Me yasa yake abu kamar ba shi

ba, me yasa yake yawan murmushi tare da yin abubuwan da bai saba ba in yana tare da yarinyar nan?

   Wata zuciyar tace badai kamuwa kafarayi da santa ba? Kai ya girgiza da sauri yace " No way, how can i...."

   Shiru yai yana tuno sanda ta kwanta aj

ikinsa tana kuka, murmushi ya saki tare da lumshe ido......

   Nafi kam haka taitayin komai cikin farin ciki har Little ta ke tambayarta yau meya same ta haka?Nafi kawai sai dai tai dariya..

  Washegari litinin da safe Ashraf ya shirya ya tafi gun ai

ki sabosa sunada Meeting yau ranace babba agunsa don project din da yai kusan wata 6 yana planning yau zaiyi presenting dinsa a gaban directors na company din.

  Karfe goma ne presentation din dan haka ya isa gun karfe 9 da kansa ya Shiga gyara gun har

10 tai, mamaki ne ya kashi ganin har 10 da rabi ba kowa a gun sai shi kad'ai nan ya fito ya fara dan zazagawa, wani member na team dinsa ya kira yace " ya dubamai ko ancanza lokaci ne."

  Yana nan a tsaye sai ga Mansir ya taho, ya karaso inda Ashraf yak

e yace " har an fara?"

  Ashraf yai kasa dakai cikin rashin jin dadi yace " ba wanda yazo shiyasa nake tunanin ko ancanza time ne."

  Kawubya d'an nuna rashin jin dadinsa a fili sannan ya d'aga waya ya kira Secretary dinsa, ko me ya cemai ya kashe tare

da kallan Ashraf yace " Ashraf ance project dinka plagiarism ne."

 Cikin tsananin mamaki Ashraf yace " Ban gane ba?"

  Kawu yace haka aka sanar da directors din ciki kuwa harda members na team dinka sannan project din har anyi lunching dinsa ma a comapn

y din da muke rivals." yana kai nan yad'an bubuga kafadar Ashraf sannan ya juya ya tafi.

   Da kallo Ashraf ya bishi ya saki wani murmushin takaici a ransa yace " ko kuma ka d'auka ka basu ba? Kana tsoron hakan zai sa mutane suyi acknowledging dina."

  Ya runtse ido saboda wani takaici da ya kamashi, yai kwafa tare da zubar da takardun yai waje.

   Mota ya shiga ransa yakai kululuwar b'aci ya dage ya daki sityarin mota da hannunsa tare da kwantar da kanaa jikin kujera ya saki wani huccin takaici.

   Little ce ta kirashi sai data kusa katsewa ya d'aga sai dai muryar Nafi yaji tace " Yaya ina kwana?"

 Ya amsa a hankali, tace " driver din yazo zamu tafi gashi bakanan bare muyi sallama."

  Yace " da inzaki tafi makarantar sai kinyi sallama dani?"

  Mamaki ya kamata tace "Yaya gani nai...."

 Katse wayar yai sannan ya kasheta gaba d'aya ya runtse idansa da karfi zuciyarsa na kara tafasa.

  Nafi kam mamaki ne ya kamata, cikin takaici ta shirya da taso in sukai waya yace ta bari ba yau ba sai dai

yanda ya amsa mata yasa taji batasan zaman gidan ma sam a wannan lokacin, ta kalli Little ta mika mata wayar Alamin sannan tace " ki bashi wayarsa kicemai na koma skul inda rabon mu sake had'uwa to inkuma babu Allah ya hada fuskokinmu a aljanna."

  Lit

tle ta kalleta fuska a hade tace " wai dan Allah bazaki hakura da tafiyar nan ba?"

  Nafi ta girgiza kai cikin takaici tace " karki damu little kwana nawa ne?"

 Little ta harareta sannan tace " wani irin sako ne wannan haka kikeso in fad'ama al'amin din?

"

 Tace "eh, bari naje nama Mumy sallama."

  Sunyi sallama da Mumy, sannam ta shiga mota ranta duk ba dadi suka tafi.....

  *ILYSM MY FANS*

[truncated by WhatsApp]*ZUCIYA*

       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

    ayushermohd.blogsp

ot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

  *46*

   Ashraf ya gyara zamansa a cikin mota sannan ya kira lawyer kuma abokin babansa, bayan sun gaisa ne yace " Uncle taimako nake san kamin."

 Yace "me kakeso Ashraf kasan saboda kai nake ta d'aga time

din retire dina."

 Ashraf yai murmushi sannan yace " Nasani Uncle please so nake kaje Slc company kace ina tuhumarsu da satarmin project ka basu takardar shaidar sammaci a kotu."

  Lawyer yai murmushi yace " da alama yanzu ka shirya fito na fito da s

u."

 Ashraf yai dan kwafa yace " Uncle a duk sanda sukamin abu kalaman Abba daya rubutamin shi ke fad'omin sai dai inaji ajikina yanzu shima Abban bazaiso in barsu su kara b'ata ba."

  Lawyer yai dariya sannan yace " Hakane, dama ance Eye for eye, tooth

for tooth."

 Sunyi sallama Ashraf ya bud'e mota ya fito, Asim ya gani ya nufoshi yana wata tafiyar kasaita.

  Ashraf yaja tsaki yace " The biggest fool is here."

  Asim ya karaso cikin isa sannan ya shiga tafama Ashraf, kallansa Ashraf yai yace " ka

i kuma me ke damunka?"

  Asim ya saki dariya sannan yace " Ashraf shi yasa nace maka ka kiyayeni ni ba sa'an yin ka bane."

  Kallan sa Ashraf yai yace " kana tunanin kaika aikata hakan?"

 Asim ya jinjina kai yace " sosai ma tunda ninasa aka sace project

din."

 Kai Ashraf ya jijiga alamar tausayawa sannan ya matso yad'an bigi kafadar Asim da hannu yace " u are such a big fool, ka daiyi tunani dakyau amma ninasan kanka bashida wannan basirar, kaidai basirarka d'aya ka turo a kasheni."

Yana kai nan ya juy

a yai gaba.

  Asim yabishi da kallo cikin kuluwa yace " me? Yasan Abbanane yasani ko me?"kai ya jijiga alamar a'a sannan yace " ai ba yanda zaiyi ya zargi mijin mahaifiyarsa.

  Ashraf kam office ya koma ya cigaba da aikinsa, wanda akasa ya saci takar

dun a cikin members dinsa sai b'uya yake yi, sam Ashraf bai kulashi ba sai ma wani abu dake mai yawo a zuciya, wato kawu abin tsoro ne na gaske, ya tura d'ansa yayi abu yanzu in asiri ya tuno fa? Lalai mutumin nan wato akan abinda yakeso he can use anyone.

"

 Yaja tsakin takaici inya tuna uwarsa ma amfani yake da ita.

  Sai yamma ya tashi nan lawyer ya sanar dashi yace Slc ya sanar musu sai dai sunce a jira director ya shigo gobe dan shine yai proposing din project din.

  Gida Ashraf ya wuce, yana shi

ga yai parking sannan ya kira Little a waya, bayan ta d'aga ne yace " turomin kawarki."

 Little tace " wa kenan?"

  Ashraf ya had'e fuska yace " wace kawa zance ki turon bayan Nafisa."

 Da mamaki tace " naga kunyi sallama d'azu ta tafi ai."

Da sauri

taji yace " bangane ba? Ina ta tafi?"

 Little tace "Skul ba ta kiraka ba?"

Katse wayar yai sannan yai wirgi da ita gefen kujera sai a lokacin ya tuno mai sukai, yai hucci sannan yace " waya bata permission?"

  Kansa ya shafa sannan ya fito ransa duk a

jagule, b'angarensa ya nufa ya bud'e kofa ya shiga, kamshin turaren daya jine yasa ya d'ago dan ganin meke faruwa? Anisa ya gani sanye da wasu 'yan iskan kaya riga ce iya cibiya sai wani mini siket a jikinta tayi kyau sosai sannan kwalliyace ta tada hanka

lin duk wani namiji indai yanada lafiya, duk da shigar ta daki Ashraf matuka gashi dama ya dade rabonsa da ita dan dama ko da tana gidan haushin abinda takemai yasa yake kin kusantarta.

  Idanu ya kankance yace " ke kuma me kikeyi anan?"

 Cikin takun j

an hankali ta taso ta fara tahowa tana tuno shawarar Umma ki maidashi naki, zuciya da gangan jiki bayan mun gama amfani dashi sai mu munamai yayi kuskuren fifita kucakar yarinyarcan akanki."

  Ta karaso tare da zura hannayenta ta wuyansa ta kwanto a jik

insa sannan ta saki ajiyar zuciya tace " Hubby do u know how much i miss u?"

 Ashraf ya d'agota sannan yace " me kikeyi anan......."

  Bakinta ta saka a nashi nan fa kaji tsit malam....Duk yanda yaso ya daure ya ture Anisa ya kasa dan kuwa in zuciyarsa

bataso to fa jikinsa naso.

  Nan ya sungumeta sukai d'aki........Ni kuma da jawo musu kofa nai gaba.

  Bayan sun gama ne sunyi wanka sannan Ashraf ya had'e fuska tamau, ta matso kusa dashi tare da daura kanta akan kirjinsa Tace " Hubby bazaka yafemi

n ba?"

 Kallanta yai sannan yace " Anisa sam ni na rasa mai ke damunki."

 Ta cusa kanta a kirjinsa tare da sakala hannunta ta bayansa tace " tuba nake dear, kaji? Bazan sake ba."

  Yai shiru hakan yasa ta cigaba " Bakasan yanda nakeji ba in ina zaune

a gun Umma."

   D'agota yai zaiyi magana Nafi ta fad'o mai a rai, jiya ya tuno sanda ya rungumeta a jikinsa me yasa bayajin irin wannan yanayin inyana tare da Anisa?

  Mikewa yai tsaye ya wuce toilet tabi bayanshi da kallo sannan ta tuno sanda tagans

u sun shiga mota da Nafi.

  Ashraf kam a toilet ruwa kawai ya sakar ma kansa a ya sa hannunsa ya rike bango ruwa na dukansa a bayansa, idanu ya runtse sai dai abin takaici Nafi ya hango sanda ta shiga cikin ruwa, ya bud'e idanunsa tare da kallan madubin

dake toilet din mamakin kansa yakeyi ace kamar shi yazauna yana tunanin wata 'yar karamar yarinya?"

  **********

   Nafi kam tun bayan isarta makaranta sam ta rage ko magana dan daba ba kawar da zatai hira da ita, karatunta kawai takeyi sai dai a '

yan kwanakin nan har rama tai saboda ko abinci takeci tunanin Ashraf takeyi wannan abun duk ya isheta ta kosa su Ferry su dawo ko dan ta samu damuwar dake damunta ta ragu.

  ******

   Scl hankalinsu ya tashi jin gaskiyar al'amari agun director cewars

a abokinsa ne ya bashi, wannan dalili yasa suka rubuta takardar hakuri suka aika company din su Ashraf wanda hakan ya sa ma'aikatan company d'in suka tausaya ma Ashraf sannan sukai dana sanin abinda suka aikata a gareshi,  matsayinsa ya d'aukaka dan su cew

a sukai a bashi matsayi babba wanda ya dace dashi.

 Kawu kam duk yanda kaso kasan bakin cikin dake ransa bazaka taba sani ba a fili yafi kowa farin ciki dan har murna aka dinga tayashi ganin yanda yake ta farin ciki kamar me.

   Sai dai Ashraf kam kall

ansa kawai yakeyi dan yasan sarai yafi kowa bakin ciki.

  *********

Sati biyu da komawar Nafi makaranta 'yan skul suka dawo, farin ciki agunta kuwa ba'a magana, nan suka had'u da Ferry da Ferry da Jibiya, sai dai Ferry na ganinta tasan akwai abinda k

e damunta.

  Da daddare bayan jibiya tayi bacci Ferry ta kalli Nafi tace " Feenah meke damunki?"

 Nafi tai yake tace " ba komai."

  Ferry tasa hannu ta dafata tace " Nafi akan yayanki ne?"

 Hawayen da ta dade tana had'iyewa ne suka zubo, Ferry ha

nkalinta ya tashi tace " Feenah menene?"

  Nafi ta goge hawayenta sannan cikin muryar tausayi da radad'in zuci tace " Ferry inaji san Yaya Ashraf shine zai zama ajalina."

  Ferry ta kalleta tace " Feena me kike fad'a haka?"

  Nafi ta kara share hawaye

nta tace " Ferry ko bacci nake da tunanin mutum nan nake kwana kullum sai nayi mafarkinsa, rashin ganinsa na hanani komai a rayuwan nan na rasa ina zansa kaina."

   Ita kanta jikin Ferry sai dayai sanyi tace " Feenah."

 Yanda ta kira sunan Nafi ne yasa

Nafi ta tattara hankalinta kanta.

 Ferry ta cigaba " Na fahimceki sai dai Feenah inaso ki koyama kanki danne so, kada ki kuskura ki bari shi wanda kikema wannan san ya fahimceki in kuwa kika bari har hakan ta faro? Maganar gaskiya ko shima yana sanki zai

dinga wulakanta ki."

  Nafi ta kalleta tace ta ya ya? Ferry tai dariya tace karki damu zan koya miki yanda zakiyi ki mamaye zuciyar wannan yayan naki, ba tare da kin wulakanta ba.

  Nafi tai murmushi tare da rungume Ferry tace " Ferry shiyasa nake m

a Allah godiya dayasa kike a matsayin Aminiyata."

  Ferry ta harareta tace " ba wani nan bayan nayi nayi kizo muje gidan mu kinki?"

  Nafi tai murmushi tace " nafisan zaman skul."

 Ferry tace " Shikenan in kinasan kisan komai na kama saurayi sai kin y

adda zaki bimu wannan hutun, Ammi nasan ta ganki kuma kinga daga wannan hutun sai extension."

 Nafi tace " I will think about it."

  Sukasa dariya dukansu.....

   ********

  A riga kuwa yayyan Datti suka matsamai sai da sukasa shi ya sake aure

, ya auri wata bazawara bafulatana, tanada 'ya'ya uku sai dai yace shi bazai rike ba, ita kadai ya d'auko sannan yamata kashedi sosai akan dabobinsa, ko garken ma ya hanata zuwa saboda bayasan ma tasan yawan dabobinsa, in zai fita kwad'o yake sawa a kofar

karken sannan ya kakara itace.

Itama sam ta nunamai ba ruwanta da shirginsa hakan yasa yakejin dadin zama da ita......

*#THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE

WRITERS ASSOCIATION*

💡

*47*

Su Nafi manya anyi hutun first term da kyar ta yarda tabi su Ferry gida tai hutu, sunyi waec sunyi neco.

Yau sun tashi suna ta shirye shiryen graduation ceremony da za'a musu.

Zuwan Little biyu d'aya da

Mumy d'aya kuma itada driver tana zuwa kawoma Nafi provision.

Sun tashi a gida ita kadai zataso dan Mumy tanada biki, hakan yasa ta kira Habib ta fad'amai da sauri ya amsa akan zaizo dan kuwa shima yana san ganin Nafi.

Bayan Habib yazo ne ya kar

asa gun abokinsa wato Ashraf nan ya sanar dashi inda zasu, shiru Ashraf yai yana tunani tabbas yanajin rashin yarinyar nan har cikin jikinsa, amma zuwansa bazai kawo masa raini ba kuwa??"

Habib ya dafashi yace " mutumin mu mun wuce."

Da sauri yaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login