Showing 132001 words to 135000 words out of 145961 words
kusa da Asim ya kalleshi yace " wlh kaji na rant
sema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba."
Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa.
Kawu yace " to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma......"
Da sauri
Asim yace " Sata nai a d'akin Ashraf."
Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace "mene?"
Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru.
Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace " bakada hankali ne? Me yasa ne nikam
kwakwalwar kifi Allah ya d'orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron,
shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d'akinsa?"
Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace " kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba."
Waje yai da sauri cikin takaici, yana fit
owa Anisa ta kirashi tace "Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?"
Cikin fada yace " kamar ya?"
Tace " a'a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya."
Cikin tashin han
kali yace " ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d'azun nan fa na barta a gida."
Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada.
Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf.
Kallansa ya di
ngayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace " ina Uwarka?"
Ashraf yai dariya yace " haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?"
Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace " no no no ai bai kamata ka
nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won't be fun."
Ya sake murmushi sannan yai ciki.
Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki
��
*#ASHRAFEENAH TEAM*
��
[17:3
2, 05/09/2017] hm: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
��
*82*
Kawu cikin tashin hankali yai gida, b'angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, ya
na zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b'angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan.
Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene
ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na 'ya'ya, shikam a yanda yakejin zuciyarsa ga
skiya bai yarda da hakan ba, kaunar Ruma da yakeyi bayaji ko tsufa yai da ita zai daina santa.
Ashraf kam gun Kb ya shiga Kb yace " kaje kuwa?"
Ashraf yace " naje sai dai abin ba dadi."
Ganin bayasan maganar yasa Kb yace " yanzu mutuminka
ya fita."
Ashraf yadan yi tsaki kadan yace " na ganshi, ya waccan fa?"
Ya fada yana kallan inda aka killace Asim."
Kb yace " yanacan."
Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje inada abinyi."
Nan ya fito, baiga kawu ba hakan yasa yai murmu
shin mugunta yace " ko kaifa, dan banaso ka badani."
"**********
Kawu kuwa gida ya taho da gudun gaske yana zuwa ya ajiye mota ya fito, ko kofar bai rufe ba saboda tsananin firgici, bangaren Mumy ya nufa, kwado kuwa ya gani daga kofar da zata sadak
a da bangarenta, kofar ya shiga jijigawa cikin wani irin kunar rai, ba shakka bazai taba yarda a dauke mai Rumansa ba, shifa a iya saninsa yaji ance in har mace da namiji sukai aure na wasu dan shekaru to fa soyayyarsu na tafiya sai dai kimma da hakuri yas
a zama ya d'ore, sai dai shikam abin ba haka yake ba, yanaji dole ne ya zauna da Ruma ko ya samu nutsuwa, kofar ya dinga jijigawa, ganin ba yanda zaiyi yasa yai b'angarensa cikin tashin hankali.
Waya ya dauka ya dinga kiran layinta sai dai duk a kashe
, tashin hankali kam ya shigeshi a wannan ranar.
********
A can bangarensu Nafi kuwa, sun isa Abuja lafiya, sai dai tun da suka sauka Nafi ke kwara amai, gashi sam ta kasa cin komai, Mumy cikin damuwa tace " Nafi anya kuwa ayi tafiyarnan dubifa y
anda kiketa amai."
Murmushin yake Nafi tai tace " Mumy karki damu, tafiyar mota ce kawai ta sani haka, kinsan mu filanuwa akwai mu da hararwar mota."
Mumy ta gamsu da zancen Nafi, a haka har suka kwanta bacci.
Da safe kuwa jirginsu ya d'aga.
Sai kasa mai tsarki.
***********
Shikam Ashraf da safe bayan ya tashi ya fito daga gidan shi da Dan Litti, wata envelope ya mikama Dan Litti yace " yaje gidan Dady kawai ya ba mai gadi yace a bashi, ya juyo karya bari Habib ko wani dag
a cikin gidan ya ganshi."
Dan Litti ya amsa da to, sannan ya ja mota yai gaba, yana zuwa kofar gidan kuwa yai sa'a ba kowa a gun sai mai gadi, hakan yasa ya mai horn, mai gadi ya taso da sauri, Dan Litti ya kwama sunglasses tare da kallansa ya mikamai
envelope din nan yace " kaga mai gidan."
Mai gadi ya amsa yana kokarin tambayarsa inji wa, yaga Dan litti ya ja mota yai gaba.
Cikin rashin kulawa ya koma ciki ya nufi ban garen Dady, Dady lokacin yana kishingide a falo abin duniya duk ya taru y
amai yawa yaji kwankwasa kofa, nan yace a Shigo.
Mai gadi ya shiga a hankali ya gaidashi tare da mikamai sakon, Dady yace " inji wa kenan?"
Mai gadi ya dan sosa keya yace " wlh ni kaina ban sani ba."
Dady ya sallameshi sannan ya bude wannan
envelope din wata karamar Mp3 ce ta fado tare da yar karamai takarda.
Fuskarsa dauke da mamaki ya sa earphone din a kunnensa tare da danna play.
Kallo d'aya zakamai kasan yana cikin tsananin tashin hankali da jin abinda ake fada, mikewa yai tsaye
cikin tashin hankali idanunsa suka kada sukai jaa, mamaki tare da firgice ne suka kamashi, takardar ya sunkuya ya dauka a kasa bayan ya gamajin sharhi daga bakin Alhaji Uba, address ne kawai rubuce a jiki na asibiti tare da number d'aki.
Makullin mot
a kawai ya dauka ya fito da sauri tare da fadawa cikin motarsa, ya ja ta da gudu yai waje.
Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin Nassarawa.
Nan yabi address har zuwa inda ya isa number d'akin, jikinsa ne yai sanyi ya kasa bude dakin, ba shakka in
har abinda yaji gaskiya ne shikam rayuwarsa ta kare, kenan ya zalinci Abbas akan hakkin da ba ruwansa, kenan duk yanda ya dauki Mansir ashe shi ne babban soko yana zaune ana amfani dashi.
Dashi Mansir yai amfani yai achieving din duk abinda yakeso a
duniya.
Yana tsaye rike da kofar yaji an bude kofar daga ciki, wata nurse ce ta fito, kallansa tai ta gaisheshi sannan tai gaba.
Kofar a bude take hakan yasa daga waje yana kallan Uba wanda ke kwance duk ya tsome, shikanshi Uban kallansa yake d
an tabbas bazai iya manta fuskar Hisham ba.
A hankali Hisham ya fara takawa zuwa ciki har ya isa kusa da gadon ya kalli Uba zaiyi magana Uba yai saurin katseshi da cewa " Hisham na gode da ka ziyarceni kafin rayuwata ta kare, ka yafemin abinda ya fa
ru."
Dady kallansa yai cikin wani yanayi yace " me nakeji game da Mansir....."
Uba ya kamo hannunsa hakan yasa Dady ya zauna kusa dashi, Uba ya kara zayyanamai komai daya faru tare da doramai " nayi babban laifi, sai dai ba'a maida hannun agogo ba
ya, Ka yafemin Hisham."
Hankalin Dady yayi mugun tashi, ya mike jiki a sanyaye ba tare da yace komai ba yai waje.
Tafiya yake kamar mara laka a jiki, har ya isa motarsa, ya shiga ciki ya zauna tare da dora kansa akan sityarin motar, me na aika
ta?
Abinda zuciyarsa ke tambayarsa kenan, waya ya dauka dan kiran kanwarsa, sai dai a kashe ya jita, haka nan ya tada mota cikin karyewar zuciya yai gidansa.
Yanzu kam ya gane komai daya faru dama trap ne da Mansir ya shirya.
*********
Ashraf bayan ya ga Dady ya koma gida dan yana biye dashi shima ya nufi gun aiki."
Bayan azahar suka shiga meeting, sai 4 suka fito, sun fito dukansu Kawu na tsakiyar mutane suka dan tattaunawa, Hisham ya karaso gun.
Hisham nada tsananin
zuciya wanda duk itace tasashi yin abubuwan da suka faru a baya, sam ransa ya gama b'aci baima kula da mutanen dake tsatsaye a gun ba, ya karaso gun Kawu.
Cikin tsananin mamaki kawu ya kalleshi yace " Yaya ya......."
Mari yaji an tsinkamai nan
fa kowa ya kallesu, kawu mamaki ya kamashi, ya rike gun yace " Hisham ba kada hankali ne?"
Dady yai wani murmushin takaici yace " au yanzu dakaji mari ka manta da yayan?"
Kawu ya kalli mutanen dake gun ciki kuwa harda Ashraf wanda takaici ya kar
a kamashi, ya daure yace " yaya muje office dina da alama ranka ne a b'ace."
Dady sai a lokacin ya kula da mutanen gun, suka hada ido da Ashraf, nan sukai office din Kawu.
Ashraf yai murmushi yace " Whoa lalai Dady ba sauki."
Nan yai nashi of
fice din hankalinsa a kwance.
Kawu kam suna shiga yasa key ya kalli Dady yace " Yaya meye hakan.....?"
Idanun Hisham sunyi jaa na takaici yace meye hakan?
Dady yace " wai me......"
Jiyai Hisham ya karamai wani marin, dady ya fusata yace
" malam meye hakan?"
Dady yace " waccan marin na farko na rainamin hankali dakai ne, wannan kuma na takaicin hada zuri'ata dakai danai ne."
Kawu ya hada rai yace " wannan wani irin banzan zance kake? Mu bayara ba ba komai ba?"
Hisham ya nun
a Kawu da dan yatsa cikin kunar rai yace " wlh kaji na rantse maka bazan yafe ma rainin hankalin daka min ba, ba zan yafema sanadin mahaifina dakai ba, bakuma zan yafema amfani dani dakai ba ka auri kanwata, ba kuma zan yafema na amfani dani dakai ba wajan
kashe Abbas ba."
Kawu kallan Hisham kawai yake, sai yanzu ya fara gane inda zancensa ya nufa, cikin rashin damuwa Kawu yace " ni ban fahimceka ba."
Hisham yace " naji komai daga Alhaji Uba, munafikin banza da wofi, wlh Mansir nayi danasanin sani
nka a rayuwa, kai kani ne ga Abbas sai dai ko kadan halayenku ba iri daya bane, shiyasa a koda yaushe kake losing akansa, dukiyar da kake takama da ita ficika ba kai ne kai wahalarta ba, tarawa akai ka kwaceta karfi da yaji, matar da kake takama da ita, ba
sanka take ba, ita ma karfi da yaji ka kwace ta, ko da wasa bazaka taba zama Abbas ba duk wannan abun daka kwata kuwa."
Idanun Kawu suka rikide babban takaicinsa a duniya ace mai daga dukiyarsa har matarsa ba nash bane, wani irin abu ya fara da fuska
rsa, hannu yasa ya shake Dady.
Cikin wani mugun yanayi yace " karyane, komai nawane, uban waye ya isa yace dukiya da Ruma ba nawa bane?"
Hisham da kyar ya fizge hannun Mansir, cikin tsananin mamaki ya kalleshi yace " kana tunanin wannan abun da k
akeyi shi zai sa su zama naka? Ruma da kake tunanin wai hakan santa kakeyi yanzu na fahimci obsession ne ke damunka, lalai kana cikin gararin rayuwa, kuma wlh ka gaggauta ba kanwata takardarta."
Yana kaiwa nan yai waje.
Wani irin ihu Kawu ya saki
yana cewa " waye ya isa yace ba nawa bane?"
Ya dade a haka kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, nan fa ya shiga tunani uban waye ya sanarma Dady abinda yake a b'oye?"
Fitowa yai ya nufi office din Ashraf.
*#ASHRAFEENAH TEAM*
��
[17:32,
05/09/2017] hm: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
��
*83*
Kofar ya bude ba tare da kwankwasawa ko sallama ba, a zaune yaga Ashraf yana aiki yana
kuma kurban tea dake gefensa, kana ganinsa kasan hankalinsa a kwance yake, jin yanda aka bude kofar ne yasa ya kalli gun, ganin kawu ne yasa ya sakar mai murmushi tare da dagamai hannu yace " Hi!"
Ran Kawu ya kara b'aci matsowa yai gunsa ya kuramai i
do.
Ashraf ya kalleshi cikin rainin hankali yace "ya akai? Ko shayin zan hada ma?"
Kawu yanasan ya tambayeshi ko shine ya fadama Hisham sai dai yana tsoron karya buloma kansa aiki, yaje haka kawai Ashraf din bai san komai ba ya sanar dashi.
Daurewa yai ya juya, har ya kai tsakiyar gun yaji Ashraf yace " Ba tambaya kazo kayi ba?"
Kawu ya tsaya cak tare da juyowa ya kalleshi, Ashraf ya mike tare da matsowa inda kawu yake cikin gadara, ya dan tafa hannayensa biyu a hankali yace " Ohhhh kana
tsoron kar inji?"
Kawu ya buga mai wani kallo, Ashraf ya dan rike kunne yace " sry kanin Abba, sai dai ya zamuyi? Da alama Dady fa yasan komai."
Idanu kawu ya zaro cikin rawar murya yace " kai kai ne ka....."
Dariya Ashraf yasa yace "kawu
meye hakan? Kar ka badani mana, ya muryarka zatai rawa daga nan?"
Kawu ya daure ya nuna Ashraf da yatsa yace " Ashraf wannan shine last warning dina akanka, ka shiga hankalinka dani, kada kai tunanin komai yana tafiya yanda kakeso kai tunani kaci rib
a akaina, wlh kayi min kadan, tsohon ka ma bai isa yaja dani ba bare kai da aka haifeka a gabana."
Hannu Ashraf yasa ya kankame jikinsa yace " Ahh so Scary!!"
Kawu ransa ya kara baci yace " ina tausaya ma dan wlh......."
Ashraf ya hade han
nayensa biyu yace " plzz na rokeka kar ka tausayamin dan Allah, Dan Allah na rokeka kana kwafsamin in naji zancen tausaya war nan."
Zuciyar kawu ta cika taf da takaici, a zuciye yai hanyar fita, Ashraf yace " ka tabbatar kanacin abinci mai kyau kafi
n ka shiga prison dan naji labarin abincin can ba dadi."
A zuciye kawu ya bankade kofa yai waje.
Yana fita ya kara kallan kofar cikin takaici yai kwafa yace " in ni banje ba kai ka ziyarci kabarin ka ai."
Daga ciki kuwa yana fita Ashraf y
a furzar da wata iska tare da zama akan kujera Ya kira Uncle Salim.
**********
Su Nafi an isa kasa mai tsarki sai dai Nafi kam jiki yaki dadi sam, haka suka shiga d'akin da aka basu a kasar madina ita kam duk ta gama fadawa.
Mumy cikin ku
lawa tace " Nafi ya kamata muje asibiti nikam naga hararwan nan ta isa ga ba abinci kike ci ba."
Nafi ta dago tace " Mumy Allah in na huta nasan komai zai tafi."
Kallanta Mumy tai tace "kinga yanda kika rame kuwa?"
Nafi tai murmushi tace " A
llah ba komai Mumy."
Shiru Mumy tai jikinta yai sanyi.
Nafi kam gata dai a kasa mai tsarki garin da take masifar san gani amma gashi tazo a kwance ba lafiya.
**************
Da yamma Ashraf ya koma gida, yana fitowa daga mota yaga
Anisa na tahowa, hade rai yai jakarsa ya dauka yai kamar bai ganta ba, Anisa ta karaso da saurinta ta rike rigarsa ta baya.
Dole hakan yasa ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace " ya akai?"
Idanunta ne suka ciciko tace " yaya."
Kallanta yai
yace " ya akai?"
Ta share kwallarta tace " jikin Umma ba dadi, ga ya Asim har yanzu shiru."
Kallanta yai kawai baice komai ba.
Anisa ta rike hannunsa tace " yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka."
Bai musa ba nan