Showing 78001 words to 81000 words out of 145961 words

Chapter 27 - ZUCIYA COMPLETE

A

shraf yace " Nima zani dan ina ganin bai kamata har ta gama skul banje ba."

Habib yai dariya yace " ashe kasan abinda ya dace, na tabbata da Little ce acan da kaje yafi a irga."

Ashraf bai amsa mai ba ya tashi ya shiga d'aki, bayan ya shirya ya fito

, kallan d'aki Anisa yai wanda ya tabbata bacci take har lokacin aya zari key yai waje.

Sun tsaya gun ajiye motoci Ashraf yace "ku tafi da motar ku dan ni tawa tafiyar daban sannan banaji zanyi hour d'aya ma acan.

Sun fito suka fara tafiya, Habib

na gaba shi yana baya, a hankali yake tuki yana tunanin me zai ce mata in sun had'u? Wata zuciyar tace " Sannu? Congrat? Hi? 'yan Mata? 'yan makaranta?"

Kansa ya shafa yace " ke zai sa in fara mata magana? Ita zata gaida ni ai nasan ni kuma sai na am

sa."

Yai murmushi ganin komai yazo da sauki.

Har suka isa yana ta 'yan tunane tunanensa.

A makaranta kuwa lokacin har an fara programs, su Nafi anshirya cikin kayan 'yan mata atamfa da siket ansha d'auri zasuyi drama ne itace lead, alokacin das

u Ashraf da habib suka iso, daidai nan an fara gabatar da drama din kenan.

Nafi sam bata kula sun iso ba ta zake sosai tana gudanar da scene dinta na star din cikin dramar, kowa ya nutsu yana kallo Nafi sai burge mutane takeyi da turanci ga iya actin

g, bawai dan tafi kowa bane aka sata a'a sai dan yanayin yarinyar yanayin Nafine.

Su Little sai fara'a akeyi, Habib kam kallan Nafi kawai yake yana tsananin mamakin yarinyar da batai primary ba itace take turanci haka??

Shi kuwa gogan ya kafe

kaf, shi bawai turancin bane yafi tada mai hankali ba, yanda ta girma ne yafi bashi mamaki, bawai wani kiba tai ba sai dai cikar mace kam Nafi tayishi a wannan lokacin, ta kara gogewa.

Sam ya sha'afa cikin tunanin yarinyar jiyai Little na tab'ashi,

ya kalleta fuskan nan a d'aure.

Little tace " Yaya kaga Feena? Dan Allah bata burgeba?"

Ya harareta sannan yace " ina wani abun birgewa ta fito kandar kandar ko mayafi?"

Ya fad'a tare da juya kai, Little ta d'an turo baki sannan ta kalli inda Na

fi take.

An gama drama Nafi tun anayi ta hangosu, aikam ana gamawa ta taho gunsu, little ta rike hannunta cikin tsananin farin cikin ganin junansu, Nafi tace " Little!"

Little ta saki murmushi tare da kara rike hannun Nafi tace " Yar Uwa Congra

ts."

Nafi tai murmushi sannan ta kalli Habib tace "Ya Habib."

Habib yai murmushi cikin kulawa yace " Princess Congrats tun dazu naketa kallanki sai birgeni kike sake yi."

Nafi ta maida kallanta kan Ashraf wanda shima kallanta yake tun da tazo gun

, kallan sa kawai tai tace " yaya sannu." tana fada ta maida kallanta kan Little.

Kallan mamaki ya bita dashi, is that all? Abinda ya fad'a kenan a ransa Cikin mamaki, yaya sannu? Ya kara kallanta gani yai sam ma hankalinta baya kansa ransa yakai kolo

luwar baci.

Nafi kam hannun Little taja tace " ya Habib muna zuwa."

Sukai gaba, kallo Ashraf ya bita dashi.

Sukam gun su Ferry suka nufa nan suka cigaba da hira ita kuma Nafi taje ta canza kaya zuwa kayan makaranta tare da sa graduation gown din

ta.

An gama taro suka fito tare da su Habib jikin wata bishiya suka zauna babbar sallaya irin manyan nan suka shimfida suka zauna, Ashraf da Habib kuma suka zauna a kan wani benci dake gun.

Ashraf ya d'au waya yana dannawa sai dai jefi jefi yan

a kallan Nafi, haushi duk ya isheshi ganin yanda sam ta d'auke kai daga kansa ko gaidashi batai ba balle ma yasa ran zasu danyi magana.

Had'e ransa yai tamau ya rike wayarsa kawai yana dannawa, Su Ferry ne suka iso suka.

Nafi ta kallesu tace " wanna

n Yayana ne Ya Habib." ta fada tare da nuna Habib, yai murmushi.

Su Ferry suka gaisheshi, ta kalli Ashraf tace " wannan ma yayanane sunanshi Ya Ashraf." tafad'a tare da nuna Ashraf, Ashraf ya sake hade fuska wato shi da Habib duk matsayinsu d'aya take n

ufi ko me? Yayana? Ya Habib? Ya Ashraf?"

Wani mugun kallo ya bita dashi, Nafi kam d'auke kai tai tare da kallan Ferry.

Yana kallo suka zauna suna hira sam ma ko kallan inda yake batayi.

Ashraf kam ya cika fam ko hira da Habib yake neman jansa

dashi ya kasa biyemai.

Suna nan a zaune suna hira sai ga wani saurayi nan ya iso kana ganinsa kasan yayan Ferry ne dan suna kama sosai, yana isowa ya kalli Nafi sannan yasa hannu a saitin inda zuciyarsa take yace " Feenah zuciyata za za za......"

Ya

i kamar irin numfashin na neman yankewa, Ferry da Nafi sukai dariya, Nafi tace " Ya Nabil zaka fara ko?"

Little ta kallesu tace au wasa yake?"

Nabil yai murmushi sannan ya kalli Little yace " Yar uwar mu."

Little ta zaro ido dan mamaki, yacigaba "

ke yar uwar Feena ce kinga kuwa yar uwa tace."

Habib yai dariya yace " Lalai guy din nan kana da abin dariya."

Nabil ya cigana da magana yana kallan Little yace " Little in baki taimaken ba kinsa kanwarki ta soni ba inaji zakuzo jana'iza ta."

N

afi da Ferry suka sake dariya, Ashraf ransa ya kara b'aci a zuciye ya mike ya karasa gun motarsa ya shiga, kansa ya kwantar akan kujera zuciyarsa duk ta gama kuluwa haka take ma maza dariya?"

Kallan gun yai ya d'auka zai ga tana ko kallan inda yake sai d

ai abin haushi hira suke cikin annashuwa da Nabil.

Motarsa ya tada, Nafi ta kalli gun da sauri zuciyarta duk ta fara sanyi anya kuwa wannan hanyar itace? Ferry ce ta mintsineta a cinya wanda hakan yasa ta daina kallan motar sai dai zuciyarta duk ta karay

a.

Little ce ta kalli Habib tace " Ya Habib ina yaya zaije?"

Habib ya girgiza kai sannan yace "wlh bansani ba nima."

Ashraf har ya fara tafiya yaga bazai iya jurewa ba a zuciye ya fito inda suke hannu yasa ya fizgo Nafi dake zaune suna barkwanci

da Nabil.

Nafi ta kalleshi, fuskar sa a had'e yace " mike."

A hankali ta mike, yai gaba ta bi bayansa, jikin mota ta tsaya, ya kalleta yace " shiga."



Fuska itama ta had'e tace " ina?"

Yace " za ki shiga ko na shigar dake da kaina?

Kalla

n mutanen gun tai ta had'e rai sannan ta shiga fuska a hade.

Shima ya shiga, glass din motar ya zuge, ya maida kallansa kanta yace " i am a joke?"

Ta kalleshi itama tace " me nai kuma?"

Me kikai?tambaya ta ma kike?

Ta turo baki tace " to n

i menai? Ka fad'amin"

Ashraf ya kura mata ido cikin takaici yace " kinasan kice min bakisan me kika min ba? Sannan ko kunya ma ki fito gaban maza kadar kadar ko mayafi wai ke a dole kina drama ko?"

Nafi bata amsa ba sai baki data turo ya kara cew

a " shi kuma wancan waye? Meye hadinki dashi zaki zauna kina washe mai baki?"

Nafi ta kalleshi sannan tace " Mun saba dashi ne fa."

What?kun saba? Meye shi a gunki?"

Nafi ta juya kai tare da yin dan yin kunkuni, yace "me kike cewa?"

Kallansa tai

tace "jirana akeyi nabar mutane."

Zai sake magana yaga ta bud'e kofa kallan mamaki ya bita dashi......

A zuciye yaja motarsa da gudu yai waje, Nafi tabi bayan motar da kallo jikinta duk yai sanyi, idanunta suka ciciko, Ferry ce ta matso ta dafata s

uka kalli juna sukai murmushi.



*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

{ *48*}

Ganin yanda jikin Nafi yai sanyi yasa L

ittle tace " Me ya ce miki?"

Nafi tai murmushi tace " tambaya ta yai kawai yaushe zamu dawo nace wasu yau mukuma sai gobe."

Little ta dan tab'e baki tace " akan haka ne naga ya zuciya?ni wlh na d'aukama ko laifi kikai."

Habib yai dariya yace "

kinsan yayan naki ai Gimbiya."

Haka dai sukai ta hira sama sama sannan sukai sallama tare da tafiya da kayan Nafi yanda gobe sai dai ta taho ita kad'ai.

********

Shikam Ashraf har ya isa gida zuciyarsa batai sanyi ba, sai ma kara tunano abind

a tamai kawai dayakeyi, sannu yaya? Lalai kalman nan ta bala'in b'atamai rai ya cije leb'e tare da yin kwafa lalai yarinyar shi zata dizga???

Da karfi ya shiga gidan ko mai gadin bai kalla ba ya fito tare da rufe kofar motar da karfi yai bangarensa.

A falo yaga Anisa tana ganinsa ta taso da sauri tana neman rungumeshi gocewa yai ya wuceta yai gaba.

Kallan takaici ta bishi dashi tana kallo ya shige d'aki tare da rufo kofar da karfi, wanda har sai dayasa tadan razana.

Yana shiga ya cire ka

ya ya wuce toilet, ya dade yana zuba wa kanshi ruwa kafin ya fito.

Ya kwanta akan gado tare da daura hannu akan goshinsa, Anisa ce ta shigo cikin kissa ta zauna a gefenashi tace " Dear muje kaci abinci ko?"

Juya mata baya yai yace " banasan magan

a yanzu bacci zanyi."

Kallansa tai tace " Amma......"

Wani kallo daya mata yasa ta mike tai waje.

******

Nafi ce bayan isha'i zaune a hostel itada Ferry da Jibiya suna cin abinci, sai wasa kawai take da cokalinta sam ta kasa kaiwa bakinta,

Ferry ta kalleta tace " banga laifinki ba Feena gaskiya Ashraf ya hadu karshe sannan rashin maganarsa da hade fuskarsa charm dinsa ne."

Nafi ta buga mata harara, Ferry tace " sai dai bawai ina nufin haduwarsa da charm dinsa ba ko kudinsa sune zasusa y

afi karfinki ba ko ki karaya ba, sai dai......" shiru tai batare da ta karasa ba.

Nafi jiki a sanyaye tace sai dai me??

Ferry tace " sai kinyi da gaske dan irinsu ko suna san abu in har ka nuna musu soyayya dayawa to fa zakasha wahala, kinada ky

anki ga gashi gaki 'yar chas in har kika bi yanda ya kamata Ashraf bazai miki wuyar samu ba."

Nafi ta kalleta sannan ta dan yi murmushin yake tace " Ferry ni fa ba 'yar gidan bace, na dade inaso in sanar da ku hakan."

Harararta Ferry tai tace " N

asani ai."

Mamaki ne ya bayyana a fuskar Nafi ta kalleta tace " How? When?"

Ferry tai dariya tace " kin manta nasan sunanki?sannan sanda muna Junior ai kowa yasan bafulatana ce ke kuma kema dakanki kin fada kince daga karamar hukumar gwaram kike.

"

Nafi tai dariya sannan tace " lalai Ferry."

Ferry tace " bansan matsayinki a gidan ba sai dai inaso ko ma meye matsayinki karki bari wannan ya rage miki daraja."

Nafi ta kalli jibiya tace "Jibiya lalai ki kiyaye yayan nan taki kwakwalwarta a

cike take fam da plan."

Sukasa dariya, nan suka shiga hirar bikin jibiya wanda za'ayi bayan sun koma ba da dadewa ba.

A ranar dai basuyi bacci ba dan hirar karshe a makaranta.

Washegari da safe kuwa suka shirya suka kamo hanya, Ya Nabil ne ya

zo ya d'aukesu, a hanya ma hira sukai tayi Nabil na kara sasu dariya dan mutum ne mai tsananin barkwanci.

Nafi suka fara ajiyewa sannan sukai sallama, ganin gidan yasa Nabil ya kalli Ferry bayan Nafi ta shiga ciki yace " Farida dama a gidan Marigayi A

bbas Saleh take?"

Ferry tace " ka sanshi ne?"

Nabil ya juyo yace " kin manta? Ta kalleshi tace me fa? Ya harareta yace " inda Dad yai aiki da ai company dinsa ne."

Ta mai kallan mamaki tace " haba?inda ya ajiye aikin bayan mai company din ya ra

su?"

Nabil yace "Bingo! Kinsan ai da Secretary din marigayin ya fara daga nan har ya zama Chief Director."

Jibiya tace " me yasa dan ya rasu ya ajiye aikin?"

Nabil ya girgiza kai alamar bai sani ba sannan yace " kawai dai nasan ya taba cewa

mutuwar mutumin akwai conspiracy."

Sunyi mamakin jin hakan sai dai agun suka bar maganar sukai gaba.

*******

Nafi kam bangaren Mumy ta fara zuwa bayan sun gaisa ta mata murnar gama makaranta sannan tace "taje tai wanka ta kuma ci abinci."

Nan Nafi ta mike ta fito tai b'angarensu, Little ba tanan dan dama tasan nazata sameta ba sakamakon jarabawar da sukeyi a makaranta.

Wanka tai tana fitowa taga an aiko da abinci inji Mumy, sai data shirya tai sallah sannan taci abinci ta kwanta a

kan gado, ko minti goma batai ba bacci yai gaba da ita.

Ashraf wanda ya kasa samun Little yana shigowa gida yai b'angarensu, knocking yai yaji ba motsi bai kawo komai ba dan baima san Nafi ta dawo ba ya murd'a kofar dakin.

Tsayawa yai daga bakin

kofa ya kura mata ido, a hankali ya tako zuwa cikin d'akin ya tsaya tare da kallan fuskarta, bacci take sosai ba wani kwalliya tai ba, ya kalli jikinta riga ce doguwa mai ba wai ta bacci bace sai dai ta bi jikinta ga hanun rigar karami ya mata kyau sosai

'yar kanti ce.

Kansa ya girgiza yace " me kake kallo?" juyawa yai zai tafi yaga tad'anyi motsi, ya juyo ya kalleta sannan ya juya zai wuce.

Hannunsa yaji an rike, juyowa yai tare da hadiyar wani abu, Nafi tace "Yaya?"

Ta fad'a cikin muryar bacc

i, kallanta yai tare da dakewa yace "Yaushe kika dawo?"

Ta saki hannunsa sannan tace " d'azu."

Kai ya jinjina alamar to sannan ya kara kallanta, ta daure tace "me kake anan?"

"Little, little nake nema."

Batanan, abinda ta fada kenan ta juy

a mai baya tare da rufe ido, ya kalleta, is that all? Yauma? Ba ko gaisuwa?

Ya dauka ko in ya fqra tafiya zata kulashi amma sai yaji dif, ya juyo yaga har yanzu bata juyo bama, komawa yai rai a b'ace yasa hannu da karfi ya zaunar da ita.

Kallan

sa tai cikin tsoro, tace cikin tsoro mai nai kuma?"

Yatsa ya nuna mata yace " ni wanene?"

Tace "ban gane ba?"

A zuciye yace "waye ni? Just answer nake so."

Tace " Ya Ashraf mana."

Ya ce "ok good, in har zaki kirani da yaya ban isa ki ga

idani ba ko me?"

Kallansa tai sannan tadan shagwabe fuska tace "Bacci fa nakeyi ka tasheni."

What?

Tace " sannan naga kamar baka fiya san gaisuwa ba dan naga da in na gaida kai ba koda yaushe ma kake amsawa ba."

Wata irin dariya yai yace "

And so?"

Tace "nima shiyasa naga in kana cikin mood din amsawa sai inyi gaisuwar."

Kallan mamaki ya shiga yi mata, kanta ta d'auke ta juyar dashi gefe, a zuciye yasa hannu sai juyo da fuskarta ita kuma tai saurin gocewa gashi gaba dayanshi dama ya

gama sakar jiki, ya kara sa hannu ai kam ta matsa da sauri ta koma can karshen gado.

Mamaki ya kamashi yace " ni kike gudun ma?"

Ya fad'a tare da hawowa gadon yazo kamata ta tai saurin kwanciya, tare da yin rufda ciki.

Babbakewa yai ya juyo da

ita da karfi, nan shima kuwa ya fada kan gadon sukai facing din juna, kallan juna suka shiga yi, Nafi ta daure ta d'auke fuskarta, cikin wata irin murya yace "Yaushe kika zama haka?"

Ta kalleshi gabanta na fad'uwa tace " Na zama me?"

Hannunsa yakai

kan bakinta yace " fitsarariya mana."

Hannunsa ta ture tace " ni ka tashi ka tafi.........."

Bakinta taji cikin nata, gaba daya numfashinta ne ya tsaya, shikansa bai san me yakeyi ba, sai dai ya kasa daina abinda yakeyi.

Nafi anyi luf ana k

arbar sako, sai can ta farga da abinda sukeyi, tureshi tai iya karfinta, Ashraf takaicin kansa ya kamashi, da sauri suka mike zaune.

Nafi ta sauka daga kan gadon har yanzu hannunta bai bar rawa ba tace "Yaya me kake yi hakan?"

Jitai yace " wannan

ita kadai ce hanyar saita bakin da bashida kunya, ki cigaba da min fitsara ni kuma zan koya miki hankali."

Da sauri tai hanyar toilet tana 'yan kokoni."

Ya bita da kallo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login