Showing 120001 words to 123000 words out of 145961 words
jin wannan labarin."
Ashraf
ya koma ya zauna fuskarnan a hade yace " yanzu ai kaji."
Habib ya matso cikin tsananin kishi ya kamo wuyan Ashraf yace " how can u do this to me? Kasan kuwa yada nake da burin auren yarinyar nan? Taya za'ai kac......."
Ture hannunshi Ashraf yai d
a karfi yace " kai ko kunyata ma bakayi? Taya za'ayi kazo kanamin zancen wai so bayan kasan kanwata yanda take sanka?"
Habib ya kalleshi, Ashraf yai wani murmushin yace " badai cemin zakai baka sani ba? Zan iya aminta inka fadi wani abu amma ba wannan
kalmar ba."
A hankali Habib yadanyi baya, Ashraf ya sake murmushi yace " mubar wannan maganar, ina Dady?"
Jiki a sanyaye Habib yace " yana gida."
Ashraf yace " Allah sarki Dady baka gani ya kamata a dan ko karamai girman asibitin nan ko kum
a a bud'e mai wani babba?"
Habib yai dariya yace " tab lalai, dady din?"
Wani irin kallo kasa kasa Ashraf yamai, Habib yacigaba " kabar Dady kawai sani ne bayasan ayi amma yanada kudi sosai inaj fa yanada gidajen haya manya kusan guda goma."
Ashraf yai murmushi yace " amma wannan ai mayb daga baya ya saisu."
Habib ya girgiza kai yace " a'a wlh, ni fa rannan inajinsa da Mumy yana zancen da gidajen lokacin duniya na kwance basa kawo kudi sosai amma yanzu dayake komai ya tashi kudi suke kawo
wa sosai."
Ashraf yai murmushi, kafin daga baya Habib ya tafi.
Ashraf ya d'au waya da sauri ya kira Uncle bayan sun gaisa yace " Uncle nikam kasan komai ma dukiyar Abba kuwa?" yai maganar cikin bugar ciki.
Uncle yai dariya yace " a iya sanin
a nasan komai nashi."
Ashraf yai shiru jikinsa ya fara sanyi, can ya daure yace " kasan komai nashi tun kafin ya rasu?"
Salim ya sake dariya yace " gaskiya nidai a iya sanina nasan komai."
Ashraf yai shiru can yace " shikenan na gode."
Yana kashe wayar ya mike tare da zuge glass din window yana kallan titi, a ransa addu'a kawai yake Allah yasa ba haka bane......"
*[truncated by WhatsApp]
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.c
om
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
💡
*71*
Nafi tana zaune a d'aki taji ana kwankwasa kofa, a hankali ta mike ta bud'e.
Ganin Mumy ce yasa tad'anyi baya da sauri tare da cewa " Mumy sannu da zuwa."
Mumy ta shigo ciki tare da
zama akan d'aya daga cikin kujeru biyun dake d'akin, Nafi ta zauna daga d'an nesa da ita a kasa tare da gaisheta, Mumy ta amsa sannan ta kalli Nafi tace " Zaman kadaici baya damunki?"
Nafi ta girgiza kai alamar a'a, Mumy ta dan yi shiru, kafin ta nis
a tace " Nafisa!"
Yanda ta kira sunan yasa Nafi ta d'ago a hankali tare da shan jinin jikinta, ta sani cewa zatai tabar gidan.
Mumy tacigaba " Ashraf yaro ne wanda baisan farinciki ba, bai san soyayyar iyaye ba, bai kuma san soyayyar 'yan uwansa
ba."
Nafi tai kasa da kai idanunta suka dan ciciko, Mumy tad'an yi ajiyar zuciya kafin ta cigaba " na sani i am not a good mother to him, ban taba tambayarsa ko da damuwarsa bane bare har inkai ga bin bayansa ko nunamai kulawa."
Nafi ta kalli Mum
y cikin tsananin tausayin mijinta, Mumy ta d'anyi murmushin takaici, tace " duk kuma da wannan abun danake mai ya nunamin ke a matsayin matar da yakesan zama da ita sai dai shima hakan ban bi bayansa ba."
Hawayen da ke kwance a idanta ne ya gangaro, t
ai saurin sa hannu ta goge su, Mumy ta cigaba "A nawa ganin Ashraf matar da yake bukata itace mai ilimi wacce tasan kanta wacce kuma zata kula dashi."
Nafi ta goge hawayenta sannan ta kalli Mumy jin tayi shiru, tace " na fahimceki Mumy na kuma sani
ba tun yanxu ba Yaya yafi karfina, sai dai ni na kasa fahimtar ki."
Mumy ta kalleta, Nafi ta daure duk da tsoron da takeji tace " bakya gani Yaya na bukatar kulawarki? Ko baki nunamai ba a kalla kya sanar dashi dalilinki na kin nunamai soyayya."
Mumy ta maida kwallar ta dake neman fitowa tace " me yasa kike tunanin akwai dalilina nayin hakan?"
Nafi tai murmushi tace " Mumy ta yaya uwa zata haifi d'anta tace ba ta sansa? Ta yaya uwa tana ganin danta a cikin wani hali tace ba ta damu ba? Ta ya
ya uwa zataki d'anta wanda yake maraya ne? Duk inda nakai ga tunanin zai iya yiwuwa sam zuciyata bata yarda da hakan, ni nasan akwai dalilinki nayin haka, sai dai a gun yaya shidai rashin so ne yasa kike mai haka."
Nafi da sauri taga Mumy ta mike tayi
waje, ta bita da kallon tausayi.
Ta dade a zaune agun kafin ta d'au wayarta ta kira Ashraf, sai dai duk yanda wayar ke ringing bai d'auka ba.
Ta ajiye wayar tare da kwantar da kanta jikin kujera.
***********
A b'angaren Ashraf kuwa yan
a azahar ya wuce gidan Uncle bayan sun zauna a falo sun gaisa Ashraf ya kalli Salim yace " Uncle a labarin da ka bani kwanaki banaji kacemin an anso kayan su Dady."
Salim yai shiru yana kallan Ashraf.
Ashraf ya cigaba " nasan asibiti da makarantar s
a na Abba ne amma bansan gidajen hayansa nawaye ba."
Salim ya shafi fuskarsa da hannayensa yace " Ashraf you are very smart,ban taba tunanin zakai zargin wani abu ba game da wannan, shiyasa ma ban sanar dakai komai ba."
Ashraf ya kalli Uncle yac
e " me ke faruwa?"
Salim yaja numfashi yace " a lokacin da mahaifin Ruma ya rasu bayan an gama zaman makoki Hisham ya shiga gararin rayuwa, kaf kudinsa sun kare bayan rashin kudin ashe har loan yaci a banki wanda ya jinginar da gidansa.
Bayan a
n gama zaman makoki 'yan bankin sukazo amsar kudinsu kamar yanda ya sanar dasu lokacin dazai biyasu.
Sai dai a lokacin gidansa abincin ma dazasuci nema yake ya gagaresu.
Da yake Ruma na gidan ita ta kira Abbas ta sanar dashi halin da ake ciki nan
ya je bankin ya biyasu kudinsu sannan makarantar da yake masifar so ya mallakama Hisham duk dan ya farantamasa, sai dai kwanansa d'aya da bashi makarantar Allah ya d'auki ran Abbas."
Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " asibitin fa?"
Sali
m yai ajiyar zuciya yace " Ashraf wannan sai bayan rasuwar mahaifinka sukazo min da takarda akan Abbas ya mallakama Hisham asibitinsa da aka gama ginawa ko fara aiki ma ba'ai ba."
Ashraf cikin rashin fahimta yace " ta yaya ya bashi makaranta mai girma
irin wannan ya sai mai gida sannan ya kuma bashi asibiti?"
Salim ya kalli Ashraf yace " nima da naki yarda da bada takardun asibitin to amma abin mamaki rubutun mahaifinka ne."
Cikin fada Ashraf yace " zasu iya sa expert su kwaikwaya ai."
S
alim yace " yes shiyasa naki yarda sai dai mahaifiyarka itace tace tabbas Abbas ne ya rubuta."
Shiru Ashraf yai kafin yace " gidajensa fa?"
Salim yace " bansan wannan ba gaskiya sai dai bayan mutuwar Abbas naji jita jita akan bai daina safarar bi
ndigogi ba zai iya yiwuwa da su ya siya ko kuma gadon Ruma ne."
Cikin mamaki Ashraf yace " gadon Mumy?"
Salim yace " ban tabbatar ba amma tunda kace gidaje dayawa nasan tanadasu dan Abbas tun yana da rai yake siyan gida da sunanta sannan da ya ra
su aka bata gadon wasu."
Ashraf yai shiru baice komai ba, Salim ya dafashi yace " Ashraf mahaifinka burinshi kai rayuwa mai dadi ba wai ta wahala da kunci haka ba."
Murmushi Ashraf yai yace " Uncle kana tunanin zanyi rayuwa mai dadi bayan duk 'ya
n uwana makiyan Abba da ni suna zagaye da ni?"
Salim baice komai ba sai kallan Ashraf dayake yi.
Ashraf ya sake murmushi yace " ka binciko min inda Auwal Max din yake?"
Salim yace " eh to wanda yake binciken yace yana zariya sai dai yace in
kara mai 1day ya tabbatar da shi din ne."
Kai Ashraf ya jinjina sannan ya mike yace " kace kafin Abba ya rubutawa matata wasiya munyi tafiya zuwa wani kauye dashi ko?"
Salim ya jinjina kai yace " kwarai kuwa saboda bazan manta lokacin ba nayi mam
aki kwarai daya kawon wasiyyar da daddare."
Ashraf yace " Malam Mahmud ko?"
Salim ya daga kai alamar eh.
Ashraf yai godiya kafin yai waje.
Mota ya fad'a ya d'aga wayarsa sakon Nafi ne yaga ya shigo kamar haka " _Yaya dafatan kaci abinc
i?_"
Ya dade yana kallan sakon kafin ya ajiye wayar ba tare da ya mata reply ba.
Makaranta ya wuce, yai sa'a kuwa yana zuwa Malam na kokarin fita, nan ya ajiye mota ya karasa suka gaisa, Malam yai murmushi yace " Muhammad daga ina haka?"
A
shraf yai murmushi yace " gaisawa nazo muyi."
Malam yai dariya yace " nagode da baka manta da wannan tsohon ba."
Nan sukai dariya, Malam yace " Ina Matar taka?"
Ashraf yace " tana nan."
Malam yace " yarinyar fa nake nufi."
Ashraf y
adan sosa keya.
Malam yai murmushi yace " da alama tana nan."
Ashraf ya kalleshi yace " malam tambaya nazo da ita."
Malam yace " Allah g yasa na sani."
Ashraf ya nisa sannan yace " kafin Abba ya rasu munyi tafiya ni da kai da shi ko?"
Malam yace " Hakkun."
Ashraf yace " Malam zaka iya tuna abinda ya faru a lokacin?"
Malam yai murmushi yace " shekarun da yawa na dai san munje zagaye da taimakon bayin Allah dake da bukata, wannan shine tafiyarsa ta karshe."
Ashraf ya jinjin
a kai yace " ba wani abu na mamaki da ya faru game da ni?"
Malam yai shiru kafin yace " tabbas akwai na tuna, abinda ya dade yana bani mamaki."
Ashraf ya kalleshi cikin zakuwa da sanjin menene.
Malam yace " mu shiga ciki."
Nan suka n
ufi makarantar.
**********
Yau Datti yana tsakiyar bacci ya tashi cikin firgice tare da kwallama Nafi kira, sai kuma ya saki wani irin kuka mai ban tausayi.
Yayansa ya shigo d'akin a tsorace ganin tsakar dare ne gashi ya tashi mutane da da
ma.
Datti yana kuka yana cewa " a kiramin Nafi dan Allah ku taimaken ku kiramin Nafi."
Yayansa ya shiga lalabashi yana cewa kai shiru Datti da alama ka samu lafiya tunda ka fara magana.
Sai dai ina Datti kam abin ya canza salo daga kuka sa
i a kira masa Nafi kawai yake cewa.
Nan suka shiga tambayarsa a wani gari Nafin take a kirata?"
Kai kawai ya girgixawa alamar bai sani ba.
Mamaki da tsoro ya kamasu.
Mahaifiyarsa dake kwance ba lafiya tace "kila saidata yai saboda tsaba
r san kudinsa nikam na shiga uku na."
Datti kam cewa yake a kira masa Nafi......
Nace ta yaya kenan?
🤔
[truncated by WhatsApp]
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*HASKE WR
ITERS ASSOCIATION*
💡
*73*
Little ta kalli Habin tace " Yaya sai yau fa naganka!" cikin shagwaba tai maganar, ya kalli kofar da Nafi ta shiga yace " Princess nazo ai bamu hadu bane ba kawai."
Ta dan turo baki tace "na kiraka ma bak
a dauka ba."
Ya hada hannayensa biyu yace " sry mayb ban kula bane."
Ta kalleshi tace " naga sako na gode."
Kallan mamaki ya mata yace " sako?"
Kai ta daga alamar eh tace " eh mana wanda kaba Feenah ta bani."
Shiru yai a ransa yace
" au kayan dana bata ma Little taba?"
Bai dawo daga tunaninsa ba Little tace " yaya, bari inje inga Feenah da alama yaya ne ya b'ata mata rai, nayi mamakin ganin ta haka."
Sannan ta karasa maganar a hankali " Naga they get along with eachother v
ery well, da alama fadan masoya sukai."
Ya kalleta yace " Ai Asharaf sai a slow, amma...."
Little ta kalleshi jin yayi shiru, kallan mamaki ya mata yace " me kikace daga karshe?"
Cikin rashin damuwa ta maimaitamai tace " Allah naga tunda m
ukasan tsakaninsu kullum suke tare da juna."
Cikin tsananin mamaki yace " me kikace?"
Yanda yai maganar yasa jikinta yadanyi sanyi tace " oh bakasan fa ashe matar yaya bace fa ko?"
Gani tai yadan yi baya tare da rike kansa, cikin wani irin
yanayi yake kallan Little wanda yasa tasha jinin jikinta, yace " matar wa?"
Kasa maimaitawa tai sai kallansa kawai datakeyi, ganin tayi shiru yasa ya juya jiki a sanyaye yai gaba batare da ya kara cewa komai ba.
Little tabi bayansa da kallo me k
enan? Ko dai shock ne irin wanda sukaji da suma suka samu labarin?"
Ciki ta shiga ta samu Nafi ta sauko daga kan gado ta zauna a kasa tare da d'aura kansa a kan jikin gadon.
Little ta matsa kusa da ita tace "matar yaya da alama fada kukai ko?"
Nafi ta kalli Little sai dai batace komai ba, Little tai dariya tace " karma ki fadamin nima ba san ji nake ba, na kuma san goben nan zaku shirya."
Ta karasa maganar tare da mikewa.
Nafi da kyar ta tashi ta watsa ruwa kawai tai sallah ta kwanta
, sam ta kasa bacci ita ba wai ganin yanayin da suke ciki da Anisa bane yafi daga mata hankali, kiss din da sukai a gabanta shine ya tsaya mata a kwakwalwarta, ai karama wani abun ce, ta tuna sanda yake ce mata su zauna a shagari su biyu.
Wani dogon t
saki taja tace " kamar irin da gaske ya manta da matarsa din nan."
Sam kasa barci tai sai juyi kawai take, da kyar baccin ya d'auketa.
A b'angaren Ashraf kuwa sun zuba love shida nisa sai dai sam yaki yadda ya kusanceta, ganin ta matso da hakan ya
sa ya d'an matsa kadan, haushi ya kamata tace " Hubby meye hakan?"
Kallanta yai tare da rike hannunta yace " sry Nisa."
Ta fizge hannunta cikin fushi tace " me? Kana tunanin matarka Nafisa ne ko me?ko kuwa so kake kace baka sha'awar yi dani baya
n kayi da yarinya?"
Jawota ta yai jikinsa ya rasa me zaice, baisan sanda yace mata" ba haka bane, banajin dadi ne wanda likita ya hanani saduwa amma inani ina kin matata?"
Nisa ta kalleshi cikin zargi tace " me ya sameka? Sannan naji Umma tace ka
kwana da Nafi fa!"
Kara jawota yai yace " zargin Umma ne kawai karki wani sashi a ranki."
Da wannan yasa ta saki ranta, shikuma ya kwanta yai bacci.
Tana gani yayi bacci ta mike a hankali ta bud'e drawer din nan a hankali ta zaro takardun na
n tai falo.
Karantasu tai taga tabbas kuwa takardun filayene da wani babban gona.
Tai dariya tace " da alama zan gano komai wannan karan."
Nan ta dau hotunan a waya ta turama Asim, sadi ya kara kamashi tace " yaya in sato su?"
Yace " a'
a ki maidasu sai mungama ganin ragowar tukunna karya gane."
Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta maidasu a hankali ta koma ta kwanta.
Hankalin Ashraf a kwance ya tashi yai asuba, duk yanda yaso ta tashi tai sallah taki, dama inda sabo ta saba d
an bata sallah sai rana ta fito.
Sai daya gama shirinsa na gun aiki sannan ta farka ta kalleshi yana fesa turare.
Mikewa tai tazo ta bayansa ta rungume shi, yai murmushi yace " kun tashi My Neesa?"
Wani irin sanyi ne ya ratsata tace " eh hub
by."
Ya juyo da ita gabansa yace " da fatan kinyi bacci mai dadi."
Kai ta daga tace " sosau ma, na dade rabon danai bacci mai dadin haka."
Yai murmushi yace " gud, ni zan fita."
Kiss ta mannamai a kuncinsa tace " sai kadawo."
Kai ya d
'aga mata baice komai ba.
Yana fita waje yasa