Showing 48001 words to 51000 words out of 145961 words

Chapter 17 - ZUCIYA COMPLETE

Little wacce kawayenta sukazo sunata shiri.

Kallanta Little tai tace " Nafi wai meye hakan? "

Tace " name?"

"kina ganin kowa yana

shiryawa amma ke kina zaune sannan ga kayanki nan na fito dasu banga alamar kinada niyar sa wa ba. "

Nafi ta kalli kayan, riga ce da wando sai doguwar riga ce baka (after dress) sai dai an bita da kwalliyar duwatso rigar tayi kyau sosai.

Nafi c

ikin mamaki ta kallesu, kowa riga da wando yasa yanata kwalliya, tace " Little kinsan dai bazan iya fita a haka ba. "

Little tai dariya tace " muma ce miki mukai a haka zamu fita? "

Ta fad'a tare da ware mata after dress d'in tace "wannan zamusa.

"

Nafi tai ajiyar zuciya tace " zakuyi kyau nikam ba dani ba. "

Little ta d'aga wayarta tace " shikenan bari na kira yaya nacemai kince wai ke bazaki iya zuwa gun bikinsa ba. "

Da sauri Nafi ta mike ta kwace wayar, kawayen suka sa dariya.

Nafi tai ajiyar zuciya tace " naji zan saka kuma zani sai dai ina gefe.

Little ta d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanki.

Little da kanta ta zauna ta shiga yima Nafi kwalliya, itakam Nafi bataso gani take kamar ba mai bukatatarta a guri

meye nata na wani kwalliya? Nafi tayi kyau sosai, dan zan iya cewa tun datazo birni bata taba yin kyau irin na yau ba, mayafin abayar Little ta nata rolling dashi, tayi kyau sosai da sosai, ba wani kwalliya na kuzo mu gani bane sai dai inkaga Little lal

ai bazaka tab'a cewa ba a birni take ba.

Dukansu wando Ja suka saka, hakan yasa suka sai takalmi ja flat, sannan yar karamar jakar dake rataye a kafad'arsu ma jaa ce, sunyi kyau sosai dan ankon shigar su kad'ai sukai.

Sun fita reras dasu, L

ittle na rike da hannun Nafi, tun a gida ma duk wanda ya kallesu sai ya yaba musu, nan suka shiga d'aya daga cikin motocin da aka kawo na d'aukar mutane zuwa gun da za'ai event d'in.

¤¤¤¤¤

A can b'angaren Aneesa kam tana can gidan Aminiyarta

ankira mai kwalliya tana tsantasara mata, ganin an kusa gamawa yasa ta d'au waya ta kira Ashraf.

Sai data kusa katsewa ya d'aga, cikin salon jan hankali tace " Hubby ka shirya? "

Yace " ku mata ai kune aka sani da shiryawa ni wani shiri zanyi? "

Tai murmushi sannan tace " ka taho ta gidan su Abida sai mu tafi.

Cikin mamaki yace " ban gane ba? "

Ta kara shagwab'e murya tace " ba dama kai zaka kaine ba? Ai tare zamuje gun. "

Yace " So? "

Tace " so shine nake fad'ama ina gidan Abida k

azo mu tafi tare. "

Yace " ni na kasa fahimtarki, meye zaisa sai nazo mun tafi tare? "

Mikewa tai ganin yana neman disgata a gaban kawayenta tai d'aki tace " yaya haka fa akeyi. "

Yai d'an tsaki yace " in haka akeyi sai akace dole sai nayi?

"

Mamaki ya kamata tace "Yaya ka tab'a ganin Amarya taje gun biki daban ba tare da ango ba? "

Yace " sai a fara a kanki dan ni kam ba driver bane babu kuma dalilin dazai sa inzo in d'aukeki keda kawayen ki bayan inada abinyi. "

Idanun Anisa

ne suka canza kala tace "yanzu dai kana nufin bazaka zo ba kenan Yaya? "

Yace " ba wai bazan zo ba gaba d'aya, sai dai zaki iya zab'a in har nazo na kaiki to kuwa ina ajiyeki zanyi tafiyata. "

Aneesa ta furzar da wani iska ta bakin ciki tace " sh

ikenan zamuzo a motar Abida. "

Bai amsa ba ya kashe wayar, bin wayar tai da kallo ranta a b'ace sai dai dan karsu gane yasa ta fito tana zumbure zumbure.

Abida tace " Neesa ya akai? Ko keda Angon ne?"

Ta kara tab'e fuska tace " wai suna tare d

a abokansa su kuma shine sukace wai inyi hakuri mu tafi dake akwai abinda zasu bashine da bazai samu damar zuwa d'aukana ba. "

Sukasa mata dariya, Abida tace "sai kiyi hakuri ai uzuri ne. "

Aneesa ta harareta sannan ta zauna akacigaba da kwalliya

.

An gama kwalliya suka taso suka taho, Amarya tayi kyau sosai da sosai dan maganar gaskiya Aneesa dama kyakyawace.

A gun event kuwa, Amarya ta iso sai dai ango shiru, gashi ba dama ta shiga ta zauna ita kad'ai.

Duk yanda Aneesa ke kira

n layin sa san bai d'aga ba.

Little ta taho rai a b'ace ta zauna kusa da Nafi tace " Nafi wlh yaya nema yake ya ja mana magana."

Nafi tace " name? "

Little tai ajiyan zuciya tace " an nemeshi an rasa kuma Habib yace " wlh yana cikin gun nan dan

tare suka shigo. "

Nafi da mamaki tace "an kirashi a waya? "

"tun d'azu ake kiranshi amma shiru bai d'aga ba, gasu Mumy can da Umma kamar zasuyi fad'a. "

Nafi wacce duk jikinta yai sanyi tace " a nemeshi mana to ko wani abun ne ya sameshi."



Harararta Little tai tace " yaro ne shi? "

Nafi ta mike da sauri bata ce komai ba kawai tai baya da sauri.

Sauri takeyi tana tafe tana addu'a Allah yasa ba abu ne ya sameshi ba, duk ta gama rikicewa, sai kutsawa cikin kuryar gun ga gun ba kowa

sai dai akwai fitilo suma masu d'an duhu.

Nafi tana tafe tana waigewaige, saura kiris ta fa d'a kwata, Allah ya taimaketa sai dai takalminta d'aya ya fad'a, zare d'ayan tai ta rike a hannu.

Ko kulawa batai ba haka taketa tafiya, yanzu kam ha

r gudu take had'awa d'ashi jikake tim.

Kafarta ta bige wani dutse ta fa d'i, mikewa tai batare data dubaba ko kula da kafarta wacce taji ciwo sai jini yake batai ba.

Daga can bakin wani pool ta hango mutum a tsaye ya kurawa ruwan ido, tana gani

nshi ta baya tasan shine, da gudu ta karasa inda yake.

Ta tsaya kawai tana hakki, Ashraf ya juyo gabansa jin alamun mutum, Mamaki ne ya kamashi yake kallan Nafi.

Idanun ta suka zubo da hawaye, tasa hannu ta share da sauri tare da cewa " ba ab

inda ya same ka? "

Kallanta yai daga sama har kasa, kayanta duk sun b'aci, yabi kafar ta yabi da kallo duk jini ya b'ata kafar.

A hankali ya matso daf da ita har tanajin numfashinsa, yasa hannu kamar zai rankwasheta a kai, da sauri ta runtse

idanta kam.

Ya girgiza kai batai auni ba taji ya sureta.

Idanu ta bud'e cikin mamaki da tsoro, a can kan kujera wacce ake hutawa in anyi wanka ya ajiyeta sannan ya karasa bakin ruwan ya debo ruwa a hannayensa ya fara zuba mata a kafa.

*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

*Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra, Mom Farhan, Agra, Mom Farouk and Fresh LUSM*

{ *30*}

Gab

a d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi, har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke, sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin, hannu yas

a a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi.

Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? "

Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru, ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara

saboda azaba, baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta, idanunsu ne suka had'u da juna, Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? "

Kallansa tai batare da ta amsa ba, ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har

kiji irin wannan ciwon? "

Kasa tai da idanunta, saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike.

Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? "

Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina."

Ta d'au

ka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya, amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba, kallansa tai idanunta suka ciciko, ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi.

Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud

'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. "

Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? "

Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka."

Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa

ta miki duka."

Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please."

Bai kulata ba ya cigaba da tafiya, sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf.

Daga d'an nesa kad'an Little taga

alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri.

Kallan mamaki ta musu, Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? "

Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? "

Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita ya

ce " event d'in auranka fa akeyi? "

Yace " ehen sai me? Abun haramun nai ko me? "

Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana, Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? "

Zaiyi mag

ana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu.

Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki.

Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya, sannan

ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? "

"Kan jakar uba, abinda za ka tambayemu kenan? "

Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. "

A zuciye Umma ta matso

tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? "

Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce? Waccan yarinyar? "

Umma ta kumbura kam, yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shi

ne na taimaka mata."

Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka? Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? "

Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa da take kuka, mat

sowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. "

Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? "

Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi? Dan na

ga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan."

Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi, tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito, kun tabbatar ba wani a

bu na masha'a tsakaninsu? "

Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa, zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi.

Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. "

Hannunsa

ya fizge sannan yace " zamanta nake? Ita har takai in mata magana taki tahowa? "

Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... "

Cikin fada yace " amma me? Ba ki yadda dani ba ko me? "

Kai ta girgiza sannan tace " ba haka n

ake nufi ba. "

Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?"

Tace " ba komai kawai dai dama. "

Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to, in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. "

Nan ya fara tafiya, Umma ta maka mata harara alamar k

ar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri.

Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba.

Kan Naf

i suka dawo a zuciye, gashi Habib ya tafi, duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi.

Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan.

Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me?

Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi, Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. "

Ji

sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. "

Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka, jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take? Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? "

L

ittle ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa, Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. "

Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy.

A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta

karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya, ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. "

Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu m

ata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. "

Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai, sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki.

¤¤¤¤¤¤¤¤

A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin

sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi, fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.b

logspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

*Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi...

.lol*

{ *31*}

Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu.

A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bi

kin nan."

Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba."

Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata.

Little ta d'au waya ta kira Ashraf, sai da ta ku

sa katsewa sannan ya d'aga tace " Yaya."

Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? "

Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf, Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy."

D'agow

a Nafi tai ta kalli Little, jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye."

Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?"

A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login