Showing 69001 words to 72000 words out of 145961 words

Chapter 24 - ZUCIYA COMPLETE

a maiduguri aka d'aura auren g

idan yayan babanta, dan dama mahaifinta ne kawai a kano da iyalansa.

Mansir kam ya isa kila sai dai yayi dana sai,babu inda zai zauna kakaninsu sun rasu, mahaifiyarsa kuma tana aure a wani gidan tare da yaranta.

Haka aka wuce da Abbas kano ya

na cikin tsananin tashin hankali, a ranar aka kai Ruma sai dai ganin halin da yake ciki yasa itama hankalinta ya tashi,Abbas ya sanar da ita akan gobe dole zaije Kila neman kaninsa, ba tantama ta amince.

Abbas ya isa kila yaje gidan mahaifiyar Mansir n

an aka kirashi, da kyar Abbas ya shawo kansa ya yarda suka taho, wannan ma sai da Mahaifiyarsa tasa baki,ganin in ya zauna a garin ma a ina zai zauna yasa ya amince suka koma,Abbas ya dage yanata tambayarsa akan menene matsalarsa sai dai Mansir yaki fad'am

ai, kano suka wuce,Abbas ya roki mahaifin Ruma akan subar Mansir ya zauna a b'angaren baki dake gidan,Abbas ya naimomai Buk.

Haka rayuwa ta cigaba, sam Mansir baya sh ga harkar yayansa, har ya gama karatu shima yai aure, a lokacin Abbas ya kara samu

n matsayi saboda kwazonsa.

Ruma har Mansir yai aure ko b'atan wata batai ba wannan abu na tsananin damunta, har matar Mansir ta haihu ta haifi namiji aka samai Asim, shekarar Asim 3 Allah ya ba Ruma ciki, farin ciki kamar suyi ka ka,a kuma wannan lokaci

n ne Abbas ya Fahimci ashe Mansir matarsa yakeso tun yana Js1, hakan ya faro ne sanda yaji Mansir suna hira da abokinshi wanda suke a maiduguri sai dai yana gama aji uku aka kaishi makarantar kwana, tundaga nan suka rabu sai yau suka had'u shine yake tsoka

narsa ina Ruma kuwa? Dafatan ya aureta.

Hankalin Abbas ya tashi ya tausayama kaninsa wanda yake gani kamar shine sanadiyar durkushewar farin cikin kanin nasa.

Daga sanda Ruma ta haihu alheruruka sukai ta faruwa da Abbas, ansama d'anta suna Muhammad

Ashraf.

Dukiyar Abbas tayi yawa a lokacin da Ashraf yakai shekara 8 yanzu company ne nasa na kansa, sanda ya gina tafkekn gidan wanda zai ishesu rayuwa duk yawan 'yayan da zasu tara shi da kaninsa.

Ashraf ya taso mai tsananin san mahaifinsa, sun

shaku sosai, alokacin ne kuma Abbas yake yawan zancen had'in aure tsakanin Ashrafda Anisa wacce take shekara biyu."

" Abbas ya sanar da Ruma akan lalai ko bayan ransa karta kuskura tabar gidan nan sanda ta taimakeshi ya cika alkawari na ganin gidan

nan ya zauna lafiya."

Mansir kam yana kishin yayansa ta harkar komai ganin duk abinda yakeso aduniya daga arziki, ilimi,mata da sauransu Allah yabad'aj uwansa ba shi ba."

Little tai ajiyar zuciya tare da share kwallarta tace "a lokacin Yaya na sheka

ra 9 ne Mahaifinsa ya rasu,hatsarin mota yai, sannan Mumy na gama Takaba aka d'aura mata aure da Mansir wanda kowa bai san dalilin amincewarta ba.

Har Baban Yaya ya rasu bayan an kaishi asibiti zancenshi d'aya ne akan Mansir ya yafemai.

Nafi ta

share kwallarta cikin tausayi, chakwakiya kenan, ta fad'a a ranta..........



THE INNOCENT TEAM*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*42*

Shiru su

kai can Nafi tace " Little to ai shi Mahaifin Yaya bai sani ba na tabbata daya sani da bazai ci amanar kaninsa ba."

Little ta kalli Nafi tace " A ido Abbana yana nuna komai ya wuce sai dai daga yanda al'amura suke tafiya a gidan nan banaji har a wannan l

okacin da Mumy take matarsa ya yafema Abban Ashraf."

Cikin mamaki Nafi tace " To ita Mumy me yasa ta aureshi daga gama takaba?"

Little ta d'aga kafada tace " Allahu a'alam shiyasa sam haryanzu Yaya bai sako ba."

Nafi tai shiru tana tunani, littl

e tace " kuma kinsan ba wanda ya fad'ama yaya mumy ta auri Abba na? Shikuma a lokacin baiyi hankalin da zai kawo komai ba har sai sanda Mumy ta haifeni, lokacin shi kuma hankali ya fara zuwa mai."

Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace aikam ba'a kyauta

ba, amma meyasa Mumy tai haka?"

Little ta girgiza kai alamar bata sani ba."

Nafi ta daure tace " To naji ana zancen wasiyya har ga matarsa?"

Little ta share kwallarta tace " Feena akwai wani sirrin da Mahaifin Yaya ne kawai ya sani saboda ayan

da tarihin yazo shekarar da zai rasu lokacin yaya bai dade da shiga shekara 9 ba Abbas ya canza, shiru zaka ganshi yayi shi kad'ai sannan a wannan lokacin yana yawan zama da lawyernsa wanda yake abokinsa, hatta aiki daina zuwa yai sai dai in Ashraf ya dawo

ya sashi a gaba suyi ta hira, in baya nan kuma sai dai kaganshi da diary yana rubutu."

Nafi tai shiru, can ta ce " me yake rubutawa?"

Little tai d'an dariya kad'an sannan tace " Yaya ne kawai ya sani dan shi yakema rubutun, sai dai ganin yanda Yay

a bai tab'a nunama kowa ba sirri ne babba a ciki."

Nafi tai shiru mamaki duk ya kamata, a cikin ranta tace " ina mamakin abubuwa guda biyu zuwa uku, na farko me yasa Abbas ya barma Ashraf duk wata kadararsa bayan yana tsananin san kaninsa kamar ransa

?q

Sannan me nene dalilin yin wasiyyarsa ba rashin lafiya yake ba bare yai tunanin ya kusa rasuwa, me ya sashi yin haka? Sannan abu na uku, wato Mumy.

Wata irin ajiyar zuciya taja Little ta dafata tace " me kike tunani?" kai ta girgiza alamar ba ko

mai.

Little tai dariya tace " Feenah da alama lawyer zamuyi irin wannan tambayoyi da kikamin d'azu?

Nafi tai dariya zatai magana sukaji ana knocking, Kallan juna sukai sannan suka kalli agoggo karfe 9 waye a daren nan?

Little ta mike tare da

bud'e kofar, d'aya daga cikin mai aikinsu ta gani, yarinyar tace " Wai Nafi tazo inji Umma."

Nafi dake tsaye tace " ni kuma? A daren nan?"

Yarinyar ta daga mata kai, Nafi ta janyo mayafinta ta kalli Little wacce tai tsuru tsuru tana kallan Nafi, m

urmushi Nafi ta mata tace " karki damu ba komai."

Nafi ta wuce waje.

B'angaren Umma ta nufa batasan me yasa ba sam ba tajin tsoron ko zasu mata wani abun.

Knocking tai daga ciki akace ta shigo, nan ta tura ta shiga da sallama sai dai ba wanda y

a amsa mata.

Kallan falon tai, Umma ce a zaune ga Asim da Aneesa a gefenta.

Nafi ta karasa ta zauna a kasa tare da gaida Umma, batare da ta amsa ba tace " ke yama sunan ki?"

Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tai d'an murmushi tace " Feenah!"

Dar

iya Anisa ta saki tace " Mee? feenah? Ha ha ha."

Asim ya kalleta yace " ke dan.........Har kin kai matsayin da zaki raina Anisa a gidan nan? Ko dan kinga Ashraf na bin bayanki?"

Nafi ta d'an kalleshi ta tuna kalamansa ka d'azu da safe akan a kashe As

hraf, jitai wani irin tsanarsa ta kamata tace " banaji nayi abinda zaisa a kirani a daren nan, sannan Ya Ashraf ne ya kawoni gidan nan duk wanda abun bai mai ba sai ya sanar dashi a sallaman."

Asim a zabure ya Mike ransa yai dubu gun b'aci, Umma kam

da Anisa mamaki ne ya kamasu.

Asim ya matso a zabure ya dage ya kai mata duka, Nafi ko gezau batai ba ta d'ago ta kafe shi da ido, ranshi ya cigaba da azalzala yace "ni kike ma wannan kallan?"

Nafi ta ki sauke idanta jitai an kifa mata mari wanda

sai da falon ya d'au kara, fulani akwai taurin kai balle Nafi wacce wahala tun tana karama take shanta ganin ko gezau batai ba yasa Asim ya tafi a zuciye ya zaro wayar CD ya taho zai fara zabga mata.

Nafi ta mike tsaye tace " Ya Asim me na maka kake sh

irin duka na?"

Ya sake zabura yace " tambaya ta ma kike?"

Tace " Kanwarka itace zata gyara rayuwar auranta ni banga me nai ba balle insan dalilin dukan nan."

Asim yai wata dariyar takaici yace " Umma dama na fad'a muku yarinyar nan karuwar Ashra

f ce inba haka ba har takai matsayin da zata dinga magana haka?"

Nafi ta kalleshi cikin wani mugun tsana tace " karuwa?"

Asim ya matso yace "me? Ba haka bane?"

Idanun Nafi ne suka fara neman kawo kwalla ta d'aga kanta sama tare da maidasu sannan

ta kalli Anisa wacce itama Nafi take kallo cikin tsananin kishi, har zatai magana kawai tai waje a zuciye.

Anisa ta kalli Umma kamar karamar yarinya zatai magana Umma tace " Ai na fad'a miki ki cire Ashraf a ranki yanzu ai kingani yanzu."

Anisa ta

kalli Asim, ya karaso gunta ya zauna tare da ce mata sau nawa kikasan ina kamasu tare? Shiyasa kikaga sam banasan Ashraf dalili kuwa shine nasan komai, ai kina kallo dai bata musa ba."

Anisa ta fashe da wani irin kukan takaici, lalai Ashraf ita zai m

a haka? Asim yace " kada ki kuskura ki nunamai kinsani ki cigaba da nunamai yanda kike sanshi har sai mun samu abinda mukeso."

Anisa kam kuka take sosai.

Nafi kam tana fita taja can gefe ta takure ita kad'ai ta saki wani kukan takaici, karuwa?

? Lalai mutanen nan makiyan Ashraf ne na gaske, shi me ya kaishi auren 'yarsu?? Me yasa duk da yasan basa sanshi suna neman kasheshi amma bai kai kararsu ba ko wani abun?

Kuka take sosai taga an dalleta da fitilar mota, a hankali ta d'ago jajjayen id

anunta, ganin wacece yasa aka rage hasken fitilar.

Nafi ta dan karkata ta kalli motar, motar Ashraf ce hakan yasa jiki a sanyaye ta mike ta karaso jikin motar inda yake.

Ashraf ya sauke glass d'in motar.

Me kike anan?

Ta kalleshi da idanunta

tace " Yaya gobe nake tunanin komawa skul saboda inyi karatu kafin a dawo, kasan yanzu S3 zamu shiga."

Kallan idanunta yai ba tantama yasa kuka tai yace " Wani abun aka miki?"

Kai ta girgiza alamar a'a ya juya kai yace " amma me kike anan? Ba dai

jirana kike ba?"

Ta d'an bata fuska tace " ni a suwa? Akan me zan jiraka?"

Yai ajiyar zuciya yace " good daya kasance ba haka ba."

Nafi tad'an juya kai sannan tace " Amma yaya daga ina kake a daren nan?"

Yace " Ko Mumy inta ganni na dawo a wanna

n time din banaji zatamin wannan tambayar."

Baki ta d'an turo batace komai ba.

Ya kalleta yace " ki wuce ki kwanta gobe kizo da safe muyi maganar makarantar."

Ta jinjijina kai alamar to, sannan ta juya.

Kallanta ya tsaya yi baisan s

anda ya saki murmushi ba can yace " me aka mata? Wata zuciyar tace kasan su ai."

Tsaki yaja sannan yai 'yar kwafa.

B'angarensa ya nufa yana shiga ya shirya tare da kwanciya ya d'auko diary din Abbansa shafin tsakiya ya bud'e.

" Ashraf ban tab

a tunanin abinda naji da kunena ba har kuma a wannan lokacin ina fatan abinda naji ya zama karya ba gaskiya ba, don't ever trust anyone except ur self."

Ajiyar zuciya yai yace " Abba me kaji? Me yasa baka rubuta ba?"

Idanu ya lumshe zuciyarsa na

zafi, a haka bacci yai gaba dashi.......

*Fatan Alkairi gareku Masoyana, Allah ubangiji ya barmu tare (Ameen)*



*THE INNOCENT TEAM*

[7/10, 7:20 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*

       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

    ayushermohd.blog

spot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

  *Wannan shafin sadaukarwace gareki yar uwar arziki Lubbabatu Maitafsir, Allah ubangiji ya kareki daga sharrin mutane, yasa ki gama da duniya lafiya....Ameen suma Ameen*

  *43*

    Da safe bayan nafi ta

tashi daga bacci tai wanka sannan ta fita zuwa kitchen, da kanta ta shiryama Ashraf abinci sannan ta d'auka tai b'angarensa.

   Tsayawa tai tana mamakin ganin taje kwankwasawa taga kofar a bud'e, shiga tai tare da sallama sai dai jin shiru ba'a amsa ma

ta ba yasa tai tunanin ko wanka yakeyi.

  Shiga tai ta ajiye tiren a kan dinning sannan ta karasa cikin falon da niyyar zama, a kwance ta ganshi akan duguwar kujera yana bacci, ta saki murmushi sannan ta karasa gun.

   Tsugunnawa tai a saitin fuskars

a ta kuramai ido bacci yakeyi sosai, a hankali tace "Handsome." sannan ta kalli kirjinsa littafine wanda bangonsa ke da kauri kana gani kasan ba irin littafan yanzu bane, hannu tasa ta d'aga littafin, jitai an rike hannunta.

  Da sauri ta kalleshi har a

lokacin idanunsa a rufe suke, ta sake littafin tare da neman tashi, jawo ta yai wanda hakan yasa ta fad'a kan kirjinsa, idanu ta shiga kiftawa tana kallansa, idanunsa a rufe yace " ina zaki?"

   Kallan mamaki tamai ya akai yasan itace? Ko ya d'auka mat

arsa ce? Katseta yai da cewa " kin gama kallan nawa? Me kika gano?"

  D'agashi tai kad'an sannan tace " yaushe na kalleka?"

 Murmushi yai sannan ya bud'e idansa a hankali ta d'auka zaiyi mamakin ganinta sai taji yace " kin tabbatar ba kallona kike ba

?"

 Kai ta d'aga tare da d'an juya kai, ya d'an had'e rai yace " to amma ya akai nakeji kamar anata kallona?"

  Ta kalleshi cikin shagwaba tace " dama ba bacci kake ba?"

  Ya sakar mata hannu sannan ya d'auke littafinsa tare da mikewa zaune yace "

wayacemiki ba bacci nake ba?"

 Ta kalleshi idanunsa kuma sun nuna bacci yakeyi, tace " to ya akai kasan ina kallanka bayan bacci kake??"

  Ya sa diary din a gefensa sannan yace " ke zan tambaya."

Mamaki ya kamata ta kalleshi sannan ta nuna kanta

da yatsa tace " ni kuma?"

 Ya juya kai sannan yace " amma da alama in babanki ya ganki yanzu banaji zai yarda kece 'yarsa."

 "Why?"ta fad'a tana kallansa, yace " komanki ya canza kinsan me ake nufi da komai?" ya karasa maganar yana neman kare mata kall

o, mikewa tai da sauri tace " ni bansan wani komai ba sannan me yasa kabar kofarka a bud'e?"

  Yace " baki nake jira sai dai nayi mamaki danaji basuzo ba."

  Baki? Da safe?

 Kai ya d'aga sannan yace " bakin da ba'a sanin zuwansu bare tafiyarsu."

  

"B'arayi??" tafad'a cikin tsoro, wani murmushi ya saki sannan yace " just 4get,kikace me jiya?"

  Tace " cewa nai zankoma skul yau saboda karatu, na saba bana dawowa gida shiyasa yanzu nakejina daban."

  Dinning ya kalla ganin breakfast yasa ya mike

ba tare da ya bata amsa ba ya d'au diary djn nan ya shiga d'akinsa, toilet ya fad'a yai wanka sannan yai brush ya fito ya shirya.

  Nafi kam haushi duk ya isheta taya za'ai suna magana ya tashi ya barta agun ba tare Da yace mata komai ba, ta d'an harari

kofarsa kad'an sanna tace " badai bacci ya koka ba? Wata zuciyar tace zai iya kuwa dan kinsan ya tab'a tsaidake yai bacci, ta dan cije leb'e sannan ta mike da niyyar yin zuciya ta fita, har taje bakin kofa ta tuna so take fa ashe tabar gidan nan, komawa t

ai a hankali tana tafe tana zumbure zumbure, har ta shiga falon zata zauna sai kuma ta kara kallan kofar ta kalli hotonsu da Anisa ta makama hoton harara sannan ta tab'e baki tace " da alama kai kadai kake santa, dan da tana sanka da bazata yarda da sharri

n da akama ba wani ni karu.....Tsaki taja sannan ta kara hararar hoton tace " ko meye ma nasa hoto a falo? Sai kace ba'a sansu ba?"

   Ta had'e rai tare da kara hararar kofar tace " san maso wani kaima dai kakeyi kamar ni." tana cikin murg'udawa kofar b

aki Ashraf ya fito, idanu ta zaro ganin ya ganta yanda ta karkace baki, juya baya tai da sauri tare da rufe bakinta da hannu.

  Har ya karaso gunta bata sani ba sai kamshin turarensa kawai da takeji yana ratsata,har wani lumshe ido takeyi, saitin kunnen

ta ya kai bakinsa yace " badai bayan murgud'a bakinba harda zagi?"

 Daidai inda yai maganar ta juyo da fuskarta da sauri cikin tsautsayi bakinta ya tab'a nashi, jikinta ne ya hau rawa da sauri ta matsa ta fara ja da baya ta rufe bakinta da hannu tai waj

e da gudu.

  Shi kansa a kame ta barshi ganin yanda ta fita da gudu baisan sanda ya saki wani murmushi ba, da sauri ya girgiza kai yace " me ke damuna? Rainane ya kamata ya b'aci fa ganin abinda ya faru meyasa nake murmushi???"

   Kan dinning ya kara

sa ya bud'e babbar kular dankali ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login