Showing 108001 words to 111000 words out of 145961 words

Chapter 37 - ZUCIYA COMPLETE

inhar bazai taimaki mahaifinki dake kwance a gadan asibiti ba sabo

da wani shirme can da zuciyarsa ke sanar dashi ba."

Nan yai waje Ruma tabi bayanshi.

Abbas yai shiru yana mamakin wannan al'amari, sai dai tabbas in har zai taimaki Hashim to lalai sai ya yi nadamar abinda ya aikata."

Ashraf ya kalli Salim ji

n yayi shiru, yace " Uncle sai akai yaya?"

Salim ya goge gomin daya keto mai yace " anyi haka da kwana d'aya Allah ya dauki ran mahaifin Ruma, wanda kuma shock din mutuwarta ya kwantar da mahaifiyarta ta samu ciwon paralyze."

Idanu Ashraf ya zaro

tsananin tsoro ya kamashi, Salim yai ajiyar zuciya yace " Abbas yayi dana sani sosai nakin taimaka musu da wuri, shi kuma yana ganin dolene Hashim yayi nadama saboda gaba.

Sai dai faruwar wannan mumunan al'amari ya tada hankalin kowa, yayi nadama tak

in karawa gani yake daya taimaka da wuri Abban Ruma bazai rasu ba, haka ma Mahaifiyarta bazata kwanta rashin lafiya ba.

Sanda Abbas yaje gaisuwa Hashim ya sanar dashi kada ya kuskura yasa a saki kayan basa so sun kuma fahimci abinda yake nufi."

Y

ai dan hucci sannan yace kaji abinda ya faro.

Ashraf banda Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un ba abinda yakeyi.

Can ya daure yace " Nagode Uncle."

Salim har ya bud'e kofa zai fita Ashraf yace " Maganae wasiyae Abba ta matata ta farko fa? Kasan d

alilin sa nayin hakan?"

Salim ya girgiza kai yace " bansani ba gaskiya sai dai nasan ana gobe zaiyi hatsari kunyi tafiya dakai dashi da malam kunje kauyuka bada taimako, yana dawowa a daren ya bani wannan takardar."

Ashraf yai ajiyar zuciya sanna

n ya kara cewa Nagode.

Salim har ya fita ya dawo yace " karfa ka kawo komai a ranka, kasan Hashim na sanka."

Ashraf ya daga kai alamar to, Uncle na tafiya ya kwantar da kansa a jikin kujera yana fitar da numfashi sama sama.......

*#A

SHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡



*65*

A hankali yaja mota ya nufi office ji yake numfashinsa na fita da sauri da sauri dole y

ai parking a gefen titi tare da kwantar da kansa kan kujera, waya ya dauka yama Dan Litti text din inda yake sannan ya maida kansa jikin kujerar.

Nafi kam karfe 7 ta tashi saboda tanasan Ashraf yai break kafin ya fita, sai dai me? Bataga kowa a kusa

da ita ba hakan yasa ta fito falo da sauri, nan ma ba Ashraf, ta zauna akan kujera tare da kiran numbersa, sai data kusa katsewa sannan taji ya daga cikin wata irin murya mai tsoratar da mai sauraro yace " Hello!"

Mikewa tai a tsorace tace " Yaya menen

e? Me ya sameka?"

Sama sama takejin numfashinsa ganin yanda ta rikice yasa yai saurin katse wayar.

Zubewa tai a kasa tanajin zuciyarta tana kuna, hawaye ne ya zubo mata ta dafa kanta tace " wannan wani irin masifa ce? Ya Allah ka dubi wannan bawa

n naka ka sassautamai ka agazamai."

Kara kiran wayar sa tai saima tajita a kashe.

Mikewa tai da sauri ta nufi bangaren Mumy ba tare da tunanin komai ba.

Mumy kam tana zaune kan sallaya tana kallan su Afra sun gama shiryawa zasu tafi makaranta

, ta musu sallama sukai waje suna fita ita kuma Nafi tana shiga, Mumy cikin mamaki ta kalleta.

Zubewa Nafi tai a gabanta idanunta na zubar da hawaye tace " Mumy dan Allah ki tausaya wa Yaya ki sanar dashi dalilinki nakin shiga harkarsa da kulashi da n

unamai soyayya "

Mumy ta buga mata wani kallo zatai magana Nafi ta katseta da sauri tare da hade hannayenta cikin sigar roko tana kuka sosai tace " kin taba tunanin yanda yake bacci da yanda yake rayuwarsa? A da na dauka ina cikin bayin Allah wanda s

uke bukatar a tausaya musu sai dai yanzu na fahimci cewa nice ya kamata in tausayama wasu badai a tausayamin ba, duk wahalar danasha a kauye har yaya ya tausayamin banaji nakai kashe 10 acikin 100 wanda yaya yake fuskanta"

Tadan ja hanci sannan ta cig

aba " He is so lonely, mutum ne wanda bai yarda da kowa ba sai kansa,Mumy nasan har kasan ranki kina tausayamai sai dai shi akullum kina daya daga cikin mutanen da suke bakin ciki ga rayuwarsa gani yake ba sanshi kike ba, kema kina daya daga kashe 20 bisa

100 na bakin cikin sa da damuwae dake ransa."

Nafi ta kara matsowa tana kuka tace " Na rokeki Mumy ki tausayama wannan marayan Dan naki ki sanar dashi dalilinki na mai haka ki kuma ja shi a jiki, mutum ne wanda bai san dadin uwa ba."

Idanun Mumy

ne suka ciciko, Nafi tai kasa da kanta tare da share hawaye tace "indai nice bakyaso zan bar Yaya har abada zan koma kauyenmu sai dai dan Allah ki duba darajar Allah ki sassautama wannan dan naki, maraya ne shi kice gatansa in har kika nuna bakyasan jinink

i waye zai soshi? Na rokeki Mumy dan Allah........"

Kuka ne ya kufce mata kawai ta kifa kanta akasa tana kuka, da sauri Mumy ta mike tai cikin daki, a bakin gado ta zauna itama tana kuka.

Nafi kam ta dade agun kafin ta tashi a hankali tai waje,

taje fita daga bangaren sai ga Anisa.

Sam bata kula da ita ba saboda hankalinta sam baya jikinta.

Ji tai an bangajeta da karfi har tai baya tala tala kamar zata fadi, ta dago idanunta da suka sha kuka ta kalli Anisa.

Anisa ta sa hannu ta da

ki kafadarta da karfi tace " me? Kuka kike dan ance dole ki rabu da mijina? Ko kuwa da kina tunanin banza ta shani ne?"

Ran Nafi yakai kololuwa gun b'aci, ta kafe ta da wani mugun kallo, Anisa ta matso tace " ke? Ni kike ma wannan kallon?" ta fada tan

a kallan Nafi.

Nafi ta ki dauke idanta, haushi ya kama Anisa ta daga hannu zata mari Nafi.

Nafi ta rike hannun da sauri sannan cikin dakakiyar zuciya tace " kada ki kuskura ki kara tunanin dukana, nice matar yaya ta farko, balle kiyi tunanin na m

iki kwace, sannan uban me kika tsinana ma Yaya? Bakin ciki? Ko me? Tun da kike dashi kin taba kula da halin da yake ciki? Kin damu da cinsa? Sannan sai anyi magana kice ke matarsa ce?"

Ta cillar da hannun Anisa tace " da rashin wayau ne yasa nabar Mij

ina a kulawar ki sai dai yanzu ni zan kula da abina, ni zan bashi hakkin da mace ke ba mijinta."

Tana kai nan tai waje a fusace.

Anisa kam kasa motsi tai mamaki da tsoron yanda yarinya karama ta kafeta da ido da kalamai takeyi.

Tana shiga

d'akinsu ta fada kan gado, Little ce ta shigo rike da flask na abinci a hannunta, Nafi ta kalleta haka kawai taji zafin ganin Little da kular abinci.

Ganin kallan da take mata Little tace " Feenah menene?"

Nafi ta share kwallar ta tace " Little

me yasa bakya jan dan uwanki a jiki?"

Little ta mata kallan mamaki tace " wani dan uwana kuma?"

Kai Nafi ta girgiza alamar ba komai sannan ta maida kanta kan gado, yau zafin kowa takeji har ita kanta, yanda numfashin Ashraf ke fita da sauri ya ka

sa barin kunnenta idanu ta runtse cikin kunar zuci tace " Allah ka agazama wannan bawa naka."

Nima nace Amin.

Ashraf nanan a zaune Dan litti ya iso akan babur.

Nan Ashraf ya mike ya matsa daya bangaren shikuma ya shiga.

Kallansa Dan l

itti yai cikin kulawa yace " me ya faru?"

Kai Ashraf ya girgiza akan ba komai sannan yace " mu tafi office."

Sun isa Ashraf ya shiga office dinsa ya kule kofar tare da ba secretary dinsa umarnin kar abar kowa ya shigo.

Takarda ya d'ako babba y

a rubuta.

ABBAS

/ | \

Muktar. | Hashim

\ | /

Rumah

Auwal Mask???

Shiru yai yana kallab takardar kafin yace " komai yayi connecting da Mumy, yayanta, mijinta nada, mijinta

na yanzu."

Itama da ita aka dau fansa saboda suna ganin Abba ne sanadiyar mutuwar mahaifinta??

Da sauri ya girgiza kai yace " it can't be, mijinta ne Abba ai."

Shiru yai yana tunani kafin ya mike ya dauko ruwa a fridge a kafa kai, sai daya s

hanye robar ruwan tas sannan yace " cikin d'ayan biyu, ko da ita akai ko kuma ba a san ranta akai ba."

Waya ya dauka da sauri ya kira Dan litti yace " inaso kamin bincike akan dukiyar Alhaji Hashim inda mukaje rannan."

Dan litti yace " amma tayaya

?"

Ashraf yace " zan turo maka number wani dan sanda kaje gunsa zai taimaka ma."

Yana kai nan ya kashe, sai yanzu wani abu ya fado mai, in har dukiyar Dady gaba daya ya sata a cikin wannan dealer din da sukai tayaya ya farfado cikin kankanin loka

ci?

A iya saninsa ko makarantar da yake da ita tun daya taso ya santa, sannan tun da ya taso yasan Dady mai kudi ne.

Hmmm Babbar magana.

*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.bl

ogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡



*Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku My Asmy, My Asy Khaleel da Autar Hajiya, May Almighty Allah always guide u through the right path (Ameen)*

*66*

Nafi ganin tana ta kiran number

Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah?

Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata dog

uwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai.

Little kam mamaki take tace " ina zaki wai?"

Nafi tace " dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya."

Idanu Littl

e ta zaro tace " kije kiyi me?"

Tace " gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki."

Little ta rike baki cikin mamaki tace " lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika

je?ki kirashi a waya tukunna."

Nafi tai ajiyar zuciya tace " da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba."

Little ta jinjina kai tace " lalai Feenah wai a 'ya

n kwanakin nan ne kika mato haka akan san yaya ko kuwa dama can b'oyewa kike?"

Nafi ta mike tare da rataya jaka karama mai dogon hannu tace " Little muje please kafin hankali na ya nemi goshewa."

Tare suka fito Nafi ta d'auko abincin daga kitchen

suka tafi.

A hanya ko magana batayi fatanta kawai ta samu Ashraf lafiya, ganin batasan magana yasa Little ma tai shiru.

A bakin company din ta ajiye ta tace " ko inzo in rakaki?"

Nafi ta girgiza kai alamar a'a tace " zanyi tambaya."

Nan

Little tai gaba ita kuma ta nufi kofar shiga.

Taje shiga taga wani wanda ba tantama tasan fuskar sai dai a ina?? Shi kam Dan litti kallanta yai sam amma bai ganeta ba, to dama ta ina zai gane Nafi kucaka da wannan?

Tambayar sa tai tace " bawan A

llah."

Dan litti har yayi gaba ya dawo, tace " dan Allah office din Ashraf nake nema."

Kallan mamaki ya mata lalai gata kamar mutuniyar arzuki ashe neman mijin wata tazo yi, ya had'e rai yace " ban sani ba, sannan yarinya karama bai dace da ke ba

irin wannan rayuwar."

Ya juya yai gaba, kallan mamaki ta bishi dashi bai dace da ita ba kamar ya?

Shiga ciki tai ta sami wani security ta tambayeshi, nan ya mata kwatancen office din Ashraf.

A hankai ta murda kofar ta shiga ta gaida secreta

ry din sannan tace " gun yaya nazo."

Kallan mamaki ya mata yace " yaya wanne kenan?"

Tace " ya Ashraf kace mai kanwarsa ce."

Secretary ya mike tare da knocking din kofar Ashraf, daga ciki Ashraf yace " ka manta nace banasan ganin wani in ba

urgent bane?"

Yace " yallabai kanwarka ce tazo."

Ashraf cikin mamaki yace " Little?ba dai wani abun bane ya faru."

Da sauri yace " ta shigo."

Nan Nafi ta karasa tare da murda kofar ta shiga.

Sannan ta maida kofar ta rufe tare da jin

gina jikinta jikin kofar.

Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki, ganin Ashraf a zaune lafiya kalau.

Kallan kallo suka shiga yi mamaki yake dama Nafisa ce?

Sansanyar murmushi ta saki sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake.

Kallant

a kawai yakeyi yanajin wani sanyi naratsa shi.

Nafi sai datazo kusa da inda yake kadan sannan ta ajiye abincin akan center table cikin shagwaba tace " Nasan ba farin ciki kai da ganina ba, dama lafiyarka nazo dubawa, tunda na gani bari na juya."

T

a fada tare da juyawa, da sauri Ashraf ya taso ya kamo hannunta ya jawota jikinsa ya rungume tsam, sannan ya saki ajiyar zuciya yace " Ban kawo araina zan ganki bane sam."

Tace " A wani hali kake tunanin zaka barni bayan ka amsa waya kamar numfashinka

zai fita? Sannan daga baya ka kashe wayar ma gaba daya?"

Ashraf ya dagota tare da rike kafadunta yace " Sry Baby nasan zaki damu in ban daga ba sannan dana daga kuma sai naga kamar zan fi tada miki hankali inkikaji yanayin da nake ciki."

Ciki

n damuwa tace "mai ya faru wai?"

Murmushi ya mata sannan ya kara jawota jikinsa yace " karki damu ba wani....."

Kwace jikinta tai tace cikin dan zafin rai kadan " yaya baka yarda dani ba ko?"

Jawota ya sake yi ya rungume yace " kema kinsan b

a haka bane, kece mutum ta farko dana yarda da ita a duniyan nan."

Har kasan ranta taji dadin kalamansa.

Sake ta yai ya zauna tare da jawo kular abincin yace " Ahhh bari inga mai matata ta shiryamin."

Tai murmushi sannan ta kamar zata zauna

a dan nesa dashi.

Harararta yai sannan ya bubuga kusa dashi da hannu yace " nan."

Kallansa tai tace " in wani ya shigo fa?"

Ta fada tare da matsawa inda yake.

Hannu yasa ya jawota ta fada kan cinyarsa yace " anaso ana kaiwa kasuwa."

Baki tadan turo tace " yaushe nace inaso?"

Wani murmushi yai yace " gashi nan waya d'aya ta tada hankalinki gaba daya har kika tsiri kunyar fulani kika biyo mijinki."

Idanu ta dan murza tace " yaya wani abu ya shiga idona."

Dariya yadan yi

yace " ko? Bari in duba miki."

Neman mikewa tai tana rurufe ido, hannu yasa ya riko kugunta sukasa dariya a tare.

Kan desk dinshi ta kalla taga take-away kallansa tai tace " wancan fa?"

Yai murmushi yace " wlh abokina ko ince abokinmu ni da

ke shine ya damu wai yaga alama banci abinci ba ya kawo min."

Kallan mamaki tamai tace " abokin mu? Ni banda wani aboki namiji."

Yai dariya yace " nima ba wai ina nufin abokinki ba na abota abokinmu dai na aure."

Kallan mamaki ta sake mai, z

atai magana ya matso saitin kunnenta yace " ya? Muyi skipping din aikin yau ne?"

Hannu tasa ta rufe mai baki tace " aikin fa?"

Yadan sosa kai kadan yace " yau so nake nai spending din whole day din dake."

Tai kasa dakai tace " kar mu tafi az

o nemanka."

Yace " karki damu muje kawai."

Abincin ya dauka da kansa ta kwace tace " barshi ni zan dauka."

Yai murmushi shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login