Showing 12001 words to 15000 words out of 145961 words

Chapter 5 - ZUCIYA COMPLETE

yai kamar yand

a ta taimakeshi, tana ta tunani har bacci yai awun gaba da ita.

Ashraf kam yayi shiru yana tunani, tabbas motarsa lafiya kalau ya ajiye ta, to amma mezai sa lokaci daya burkin motar yakiyi? Girgiza kai yai da sauri yace " zato zunubi, ikon All

ah ne. "



*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

8



Bakin wani katon gida Ashraf yace mai yai parking, daga bakin gate din mutane ne sosai a tsatsaye sannan

wasu dauke da speaker da cameras hakan yasa Ashraf yasan 'yan jarida ne a gun, kallan Nafi yai wacce ke zaune yace " Nafisa kin gaji ko? "

Kallansa tai sannan ta girgiza kai alamar a'a, ya dan murmusa sannan yace " mun iso. "

Ta kalli waje ganin

mutane yasa ta kalleshi, ya bud'e motar ya sauka sannan ya zaga ya bud'e mata, a hankali ta fito jikinta duk a sanyaye, ya kalli driver d'in yace " bari in kawo ma kudin ka. "

Ya amsa da to, juyawa yai ya fara tafiya, bai karasa gun mutanen ba

kawun sa wato kanin babansa ya hangoshi cikin tsananin mamaki da farinciki ya taho da saurinsa, kusa da Ashraf ya tsaya yama kasa magana sai dariya kawai da yake ya kankame hannun Ashraf, mamakin da ya kamani banga Ashraf yana farinciki sosai ba sai dai

yace " Kawu na tada muku hankali ko? "

Wanda ya kira da kawun ya gari fadada murmushinsa yace " Ashraf duk mun daga hankalinmu ganin jiya a rafin wudil muka wuni cur ana nemanka an rasaka tsoro yasa muka fara tunanin ko ka cika sai dai mahaifiyarka t

aki yarda sam tace lalai kana nan da rai. "

Yad'an yi murmushi kadan sannan yace " Bari na shiga ciki, sannan dan Allah aba mai mota kud'i."

Kai ya daga mai cikin farin ciki, Ashraf ya juya ya kalli Nafi dake tsaye yace " Mu shiga ko? "



Kallanta kawu yai saidai baice komai ba, Nafi kam a hankali ta karasa inda yake, nan suka fara tafiya, hannu kawai ya dagama 'yan jarida suka nufo inda yake, bai jirasu ba ya nufi gate, ya shige ciki.

Inalilahi abinda Nafi ta fada kenan

a fili, wani tafkeken gida ta gani, ba wai haduwaa kad'ai ba gida ne kato flat flat dayawa, in ka gani zaka dauka ko gidan hayane na masu kud'i sai dai Ina gida ne na Marigayi Alhaji Saminu wato mahaifin Ashraf, ya gina wannan tafkeken gidan ne saboda

yazauna shida d'an uwanshi sannan yayi flat dayawa ne saboda in 'ya'yansu sun taso kowa ya kama flat daya ya zauna da nasa iyalen.

Wannan kenan.

Ashraf har yad'anyi nisa ya juyo a bakin gate yaga Nafi a makalle tana ta fadin Inalilahi, a hankal

i ya tako yazo inda take, ya kalleta yaga ta runtse ido tsam, yace " Nafisa muje ko? "

Kallansa tai a tsorace tace " Muje ina? "

Ya nuna mata hanya yace " ciki mana. "

Yawu ta hadiya tace " Dan binni nan din inane? "

Ya dan canza

fuska kadan yace " badai baki yadda dani ba? "

Kai ta girgiza da sauri alamar a'a, yace" good, to in har kin yadda dani muje ko? "

Duk da tsoro bai bar ranta ba sai dai bata daina binshi a baya ba, can wani flat sukaje, suna karya kwanar flat di

n sukaga wata yarinya wacce batafi sa'ar Nafi ba rike da faranti zata shiga ciki, Ashraf yace " Little! " yafad'a tare da daga mata hannu.

Cikin mamaki ta juyo, ganin Yayanta batasan sanda ta saki farantin ba wanda ke dauke da lemon kwalli akai ba

, da gudu ta karaso gunsa ta rungumeshi, sai kuka.

Ya dagota kadan yace " Little kukan fa? "

Hawaye take tace " Yaya ina ka shiga? Hankalinmu ya tashi sosai. "

Kanta ya shafa sannan yace " to naji ya isa haka, ya dan juya ya kalli Naf

i yace " Little zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. "

Kallan Nafi tai sannan tace " waccece? "

Yace "Zan fada miki, Mumy fa? "

Tace " duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa

kawai tasha. "

Ya dan juya kai, little tace " Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. "

Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa y

asan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama.

Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga

nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu.

A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma'a n

oni sanda hawaye nabin kuncinta.

Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d'azu.



Turus yai agun, jikinsa duk ya

i sanyi, little ta kama hannun Nafi tace " wuce mu tafi xasu fara abin nasu. "

Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki.

Kallan fallon Nafi tai, aranta tace " lalai rayuwa t

ana wani gun. "

Sunje shiga d'aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace" Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. "

Nafi ta kalli kofar d'akin jikinta ya kara sanyi, Little tace"

karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab'a shikuma saurin b'ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. "

Nafi ta jinjina kai sannan tace " Amma kuna kama da ita. "

Little tai murmushi tare da tura kofar d'akin tace " Yaya tace

ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. "

Kallan mamaki Nafi ta mata tace " Ban gane ba. "

Dariya Little tai tace"Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. "

Nafi ta zaro ido cikin

mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d'akin, kallo tabi d'akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d'akine? Jitai Little tace " Yes. "

Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d'akin.

Ashraf kam yana tsaye gurin 'yan uwansa manyan 'ya'ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab'a Neesarsa.

Mumy ta kalleshi

tace " Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??"

Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace " Zan shiga ciki."

Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nu

fi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa.

Ashraf ha

r ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa.

Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa "Neesah?? "

Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya

dan dade yana knocking kafin yace " shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d'aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. "

Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace " Amma ya

ya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. ......."

Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace " Neesah ki bud'e inganki please...."

Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa,

murmushi ta kakaro da kyar tace " dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan."

Tanajin motsin bude kofar.

Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso so

sai saitin kanta ya kwantar da kansa yace " Ko kallo na bazakiyi ba? Na d'auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? "

Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai sauri

n rikewa, yace " ya isa to dear ai kin huce ko? "

Ya fada yana mata wani kallo.......

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*For you my dear Friend Asiya Musa (Ko

xali) luv u soooo much

😍

*

9



Little ce ta fito daga toilet ta kalli inda Nafi take tace " zo ki shiga kiyi wankan. "

Nafi ta mike jiki a sanyaye ta karbi dan towel din da little ta mika mata, kallo tabi towel din dashi tace" dan wannan ab

un zan daura? "

Little tai murmushi tace " to dame zaki daura? Ni shi kadai garen. "

Kallan zanin jikinta tai tace " na d'aura wannan. "

Little ta saki murmushi tace " ya sunan ki? "

Nafi a kasan zuciyarta so take tace Nafisa sai dai ta

rasa me yasa batasan akirata da haka tafisan tadinga jin wannan sunan daga bakin Ashraf, "Nafi. "ta fada tana Kallan little.

Tad'anyi murmushi tare da mika mata hannu alamar gaisuwa tace "ni kuma Maryam amma little ake cemin ko kice little Maryam,

mu biyu ne masu suna maryam babbar riketa akai agidan har tayi aurenta. "

Nafi ba tare data mika mata hannu ba tace" li?? Hmm nidai Maryam kawai zan dinga ce miki. "

Little tai murmushi sannan ta kara mika mata hannu tace " mu gaisa to. "

Nafi ta noke tare da girgiza kai tace " ba maza bane ke gaisawa?"

Little ta fizgo hannun Nafi tace "Mata ma nayi ai musabaha ce. "

Kai Nafi ta jinjina, little tace "shekararki fa? "

"16."

Little tad'anyi tsalle kadan tace "nima haka. "



Sukai murmushi a tare, Nafi ta daura zani ta nufi inda little ta kira da bayan gida, Da gudu Nafi ta dawo ta kalli Little tace " kina nufin anan zanyi wanka? Ta ina? Ta yaya kuma? "

Little ta kalleta tace "muje in nuna miki."

Nafi ta ja ta

tsaya, Little tace "Nafi muje mana. "

Dum Nafi ta mata itadai tsoro take ta ina zatai wanka a wannan gun?

Little tadan had'e rai tace "Shikenan bari in je in fadama Ya Ashraf. "

Da sauri Nafi ta rike rigar Little jin an anbaci Ashraf tace "Zan

je Maryam. "

Little tadanyi dariya tace "muje to. "

Sunje toilet nan Little ta nunama Nafi yanda zatai wanka, ganin hankalin Nafi yaki kwanciya da shaya yasa little ta tararmata ruwa a baho tace hakan fa?

Nafi tai murmushi alamar gwara h

akan.

Nan little ta fita ta barta.

**********

Ashraf kam suna shiryawa da Neesah ya wuce bangarensa, ko ince bangaren mahaifinsa shikadai ne a bangaren saboda duk yanda akaso asashi cikin 'yan uwansa maza kin yarda yai ya

ce " lalai shidai a bangaren Mahaifinsa yake san zama. "

Yana shiga ya wuce toilet yai wanka ya zura doguwar riga sannan ya fara rama salolinsa.

Bayan ya idar ne yaga sakon meeting a babban falo, in kuwa za'ai wannan taron to acan ake cin abin

ci.





An sanar da kowa akan akwai meeting a babban falo saboda dawowar Ashraf.

**********

Nafi ta fito daga wanka ta shafa mai kawai littleta bata doguwar rigar atamfa tasa, saboda little ta fita

kiba hakan yasa rigar bata mata kyau ba ga wuyan rigar sai fad'owa yake, ga ta kima daurin dan kwalinta ta matse kanta tamau.

Itadai little taso mata magana sai dai tasan daga zuwan mutum gari bazai wuyo ace ya canza abinda ya saba ba, gashi tana ts

oron karsuyi latti wajen meeting.

Nafi na gamawa little ta kama hannunta tace "muje ko? "

Nafi wanda gabanta ke faduwa tace " Maryam gani nake ni bai kamata inje ba. "

Dariya Little tai tace"to yaya na kira na tambaya yace muje tare yanas

an introducing d'inki. "

Nafi ta kalleta da mamaki tace "me? Inkiro me? "

Dariya little tai tace "ke dai muje kawai. "

Nan suka fito sunyi sa'a Neesah ta riga ta fita, nan suka taho har zuwa babban falo.

Katon falo ne sosai wanda

gefe aka kawatashi da wani round din dinning table manya guda biyu, d'aya maza ne a zazzaune d'ayan kuma mata ne, sai dai duk a kusa da juna suke.

Tunda suka shigo kowa ya zubama Nafi ido yana mata kallan mamaki sai dai banda Ashraf wanda ke zaun

e fuskar nan tasa kamar yanda ya saba a murtuke, Haka little ta jata har zuwa inda zasu zauna.

Zuciyar Nafi kam kamar zata fado saboda tsananin tsoro da ganin mutane dayawa maza da mata, kanta na kasa, sunje zama kawai tai tuntube ta fad'i, kwas

hewa akai mata da dariya sai ta samu kanta cikin tsananin tsoro ta kasa mikewa, Ashraf ne ya kallesu ran nan a had'e ya kalli Nafi wanda itama shi take kallo ya mata alama data tashi.

Jiki a sanyaye ta mike little ta taimaka mata ta zauna.



Kanta ta sunkuyar, kawu yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu yace "Bismillah."

Nan kowa ya fara zubama kansa a binci, Umma kuwa mahaifiyar Aneesa da ita Aneesan sun kafe Nafi da ido.



Kowa ya fara zuba abinci, itadai Nafi a zaune ta

ke sai gabanta dake ta faduwa, ganin batada niyyar zuba abinci yasa Little ta zuba mata shinkafa da miyar carras sannan ta matso mata da papper chiken da salad, Nafi ta kalle ta sannan ta d'au chokali, ganin yanda kowa yakecin abinci yasa ta fara cin sh

inkafar a hankali, sai dai lomarta biyu taji inaa bazata iya cigaba da ci ba, gani tai kamar kowa kallanta yake, ta zaune tare da matse kafafuwanta dake rawa, little ta kalleta tace "Nafi tafiya fa kikai kici abinci mana? "

Nafi ta kakaro yake ta

ce " a koshe nake ai naci abinci a mota Yayanki yaban doya da kwai.

A hankali sukai maganar, Ashraf yadan kalli inda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login