Showing 138001 words to 141000 words out of 145961 words

Chapter 47 - ZUCIYA COMPLETE

tashi ya shiga sambatu yana cew

a a kira masa Ruma, shifa bai san me ke faruwa ba.

Sudai sukai waje dashi.

A cell aka garkama shi, sannan aka umarci Ashraf dayazo.

Bayan ya zo ne nan ya basu wayarsa sukaji duk abinda ya faru a lokacin.

Hankalin kawu ya tashi, ya dinga

musu hauka.

Nan aka shigar da kara kotu.

Kawu kam anga rayuwa, bai taba tunanin zama a cikin dan dakin nan ba duk tsawan rayuwarsa.

Duk yayi baki ya jemi, Ruma kawai yake kira, ya ma rasa inda zaisa kansa, yayi tunanin basu kudi su fitar d

ashi, sai dai inaa duk inda ya bula abin yaki yiwuwa.

Har ranar zama a kotu.



***********

Nafi sun fito daga masallaci a garin makka, suna tafe ita da Mumy, Mumy ta kalleta tace " gashi har mun kusa komawa banga ko waya kunyi da Ashr

af ba."

Nafi tai kasa dakai tace " Nasan zai nemimu in har ya nutsu."

Mumy tai murmushi tace " Nafisa kina birgeni sosai, kinama mijinki uzuri ba kamar wasu matan na zamani ba."

Nafi ta kalli takaru yanda taga anbiyosu sun smkwashi kayan da

suka baza akan titi da gudu kamar me suna zabga gudu, ta kalli Mumy tace " nikam Mumy wai haka duka takaru suke zama agarin nan sam ba daraja?"

Mumy tai murmushi tace " ba duka bane suke rayuwa haka, sai dai akasarinsu abinda suke kenan, sai dai addu'

a."

Nafi sunzo tsallakawa wata ta taho da kayan saidawarta da gudu ta bangaje ta da karfi wanda sai da ta fadi.

Matar ta tsaya tana ba Nafi hakuri, Mumy ta kalleta tace " haba baiwar Allah kudinga abu da hankali mana."

Nafi ta dago dan yima m

atar magana, mai idanunta zai gani?"

Mahaifiyarta ce sanye da wata kodadiyar doguwar riga da hijab tana rike da kayan saidaiwa a hannunta tanayi tana waigawa, ganin an biyosu yasa ta juya zata tafi.

Cikin zafin nama Nafi ta kama hijabin ta.

Ma

tarta kalleta tace " Malama kiyi hakuri nace."

Nafi ta kara kura mata ido, tace " Inna?"

Kallan mamaki matar ta mata tace " ban gane ba."

Hawaye ne ya fara zubo ma Nafi tace " Inna nice fa Nafi."

Idanu matar ta zaro cikin tsananin kid

ima tace " Nafi?"

Mumy kam ta fahimci me ke faruwa ganin an biyosu yasa tace " mu wuce d'aki kwayi magana."

Nan suka karasa hotel dinsu.

Nafi hannunta na cikin na mahaifiyarta kuka kawai takeyi, ita kanta matar kuka take.

Nafi ta daure

tace " rayuwar da kikeso kenan ki ka barni a kauye ni kadai?"

Inna ta share tata kwallar tace " Nafi ki yafemin wlh nayi dana sani sosai na barinki."

Nafi cikin kuka tace " menene abin birgewa anan?sannan ina kanina Mudan?"

Uwar ta share kwa

llarta tace " Mudan tun daya girma ya bi abokai suka shiga hidimar duniya, har abu yake sha, nayi fadan har na gaji, nayi dana sani har ba iyaka, rannan Aka zo min da labarin hadarin mota da sukai."

Hankalin Nafi ya tashi kwarai tace " meyasa baki kom

a ba bayan rasuwarsa?"

Tace " da wani idan zan koma? Bayan kayan Datti dana sata na bar iyayena sannan na barki, na kuma yi sanadiyar mutuwar dana, nikuwa mai zan koma inyi?"

Kuka sosai takeyi wanda hankalin Nafi ya kara tashi, nan suka shiga yi

n kuka sosai.

Mumy ta tausaya musu, nan taba mahaifiyar Nafi shawara akan ta dawo nan da zama tunda sun kusa tafiya kuma International ne zata biya kudi au wuce da ita.

Godiya sosai Inna ta dinga yi haka ma Nafi.

*************

Anyi za

ma a kotu inda Lawyer din Ashraf ya dinga fito da shaidu na garari ciki kuwa harda Auwal Max, Umma, Dady, Alhaji Uba sannan ga wasikar mahaifinsa ga kuma yaran da aka kama yasa wuta.

Ga maganar Kawu wanda Ashraf ya dauka, hankalin Lawyer din Kawu ya t

ashi ganin ba wata mafita, nan fa kowa ya san abinda kawu yai ma Abbas da d'ansa.

Kotu ta umarci dole ne ayima Dady da Mumy hukunci sannan Umma ma.

Kawu an yanke mai hukuncin daurin rai da rai, saboda ya kashe Abbas sannan ya nemi kashe Ashraf ban

da dukiyar maraya dayake amfani da ita.

Dady kuma an yanke mai hukuncin shekara 10 saboda shima dashi aka hada baki gunyin kisa, sannan shima yaci kudin maraya.

Mumy kuna an yanke mata hukunci kala biyu, ko ta je gidan yari ta zauna na shekara 2 s

aboda karyar da tai akan gadon maraya duk da kuwa danta ne, ko kuma ta biya kudi million 30.

Umma kuma an yanke mata hukuncin biyan kudi dubu 200 saboda kin fadar gaskiya datai.

Auwal Max ma an mai hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 sabod

a yayi laifin taimako gunyin kisa.

An sanar da Mumy bata kasar sai dai ana sa ran nan da kwana 3 zata dawo.

Alkali yace tana dawowa a killaceta.

Da wannan zaman kotu ya tashi.

Littke tayi kuka kamar ranta zai fita jin wannan sabon al'am

ari, hankalinta ya tashi, labari kuwa ya bazu a gari ko ina ka zaka abinda ake fada kenan.

Su Ferry ma Nabil yazo ya basu labari, hankalin kowa ya tashi na mamakin wannan al'amarin, anyi bikin jibiya waccan satin.

Shikam kawu maganarsa daya sh

ifa Ashraf ya cuceshi akuma kiramai Rumarsa.

Hmmmm nace su kawu sai ai zaman yari lafiya.....lol

��



*#ASHRAFEENAH TEAM*

��

_Barkanmu da shan ruwa, Allah ya bamu ladan ibadar amin_

[17:32, 05/09/2017] hm: *ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn т

aѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

��



*85*

Bayan Ashraf ya farfado 'yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kan

warsa tamai ya kuma nuna musu sakon.

Nan suka bukaci anuna musu kanwar.

Ya sanar dasu tana gida.

Kb ya jasu suka nufi gidan.

********

A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa 'yan sanda sunzo hankalinsa yai

kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi.

'yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little.

Ba'a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa 'yan sanda su nemeta.

Bay

an ta iso ogan cikinsu ya kalleta fuskarnan a hade rike da littafi yace "Ke kika turama Yayanki sako akan kina san ganinsa?"

Cikin mamaki tace " a'a."

Yace " ina wayarki?"

Hankalinta a kwance ta mikamai, ya duba wayar babu sakon, ya kalleta

yace " ki tuna sosai ina kika ajiye wayarki? Ko kuma wa kika ba?"

Tace " ni ban ajiyeta a ko ina ba, mahaifina dai ya amsh wayar dazu."

Kallan juna sukai, yace " mahaifin naki yana nan?"

Tace " eh."

Yace " kira mana shi."

Nan ta taf

i bangaren Abba.

Yana zaune duk hankalinsa a tashe yaji kwankwasa kofa.

Hankali a tashe ya bud'e kofar.

Little ta kalleshi tace " Abba ana nemanka."

Yace " su waye?"

Tace " yan sanda ne, ni kaina bansan me ke faruwa ba."

Cikin tas

hin hankali yace " me kika ce musu?"

Tace " tambaya ta sukai a ina na ajiye wayata ko wa naba shine nace kai naba kawai."

Hankali Kawu ya kara tashi cikin fada ya kalleta yace " bakida hankaline??me yasa zakice ni kika ba? Ko kema kin hada baki d

a yayanki ne???"

Cikin mamaki tace " me ya faru?"

Tureta yai ya wuce cikin takaici yana tunanin me zaice? In ya gudu kuma tabbas yasan zasuyi zargin wani abu.

Fitowa yai ya isa gunsu, tare da mikamusu hannu alamar gaisawa.

Bayan sun g

aisa wannan officer din na dazu ya kalli Mansir yace " bincike mukazo yi."

Mansir ya kalleshi, Officer yace " kaine ka amsh wayar 'yarka wato Maryam dazu?"

Kawu ya danne tsoro yace " nine, amma menene dan uba ya amshi wayar 'yarsa?"

Officer

ya kuramai ido kafin yace " kaine ka turama Ashraf sako ta wayar?"

Kawu yai alamar mamaki yace " ban gane in turama Ashraf sako ba? Akan me zanyi hakan?"

Officer yace " zaka biyomin office da kai da 'yarka dan tsananta bincike."

Kawu zai yi

magana officer din yace " in har kana san kar a zargeka kenan, in kuma har da abinda kake b'oyewa to."

Kawu yace " muje, bari na canza kaya."

Nan ya koma bangarensa, ya canza kaya cikin tsananin firgice, tsoro ne fal a cikin zuciyarsa, nan suka t

aho da Little suka shiga mota suka bisu a baya.

Ashraf kam ya ware sai dai yaki yarda a sallameshi, sun hada baki da likitan akan yace har yanzu bashida lafiya.

Su Little zaune a station duk tayi tsuru tsuru, shikansa Officer din yasan ba ita b

ace dan dai ya zama dole ne ayi tambayar nan da ita.

Wayarta ta karba ta kira Habib.

Ta dade tana ringing kafin ya daga, tace " yaya kana ina?"

Yace " ina gida ya akai?"

Tace " dan Allah kazo ina police station tsoro nakeji."

Mikewa

yai daga kwanciyar da yake cikin rikecewa yace " ban gane ba me kikeyi acan?"

Alama aka mata akan ta miko wayar hakan yasa tai saurin mai kwatance ta mika musu.

Kan kace me sai ga habib ya danno mota a guje da gudu ya shigo cikin station din, sam

bai kula da Kawu ba gunta ya nufa da saurinsa ya rike hannayenta yace " Little are u alright?"

Kai ta girgiza mai hawaye suka zubo mata tace " yaya ka kira ya Ashraf kaji ko yana lafiya naji ance yana asibiti."

Cikin mamaki yace " asibiti kuma?"

Kai ta d'aga mai, zaiyi magana suka hada ido da Kawu, wani irin kalli yamai cikin takaici baisan sanda yace " ka gama lalata rayuwar wasu yanzu ta 'yarka kake san lalatawa?"

Cikin mamaki Little ta kalleshi, kawu ma kallan mamaki yake mai.

Ha

bib ya dauke kai sannan ya matsa gun officer dan jin abinda ke faruwa.

Sosai officer yamai bayani, ran Habib ya baci cikin fada yace " Ai ba sai kunyi wani bincike akan wannan baiwar Allahr ba tayayya ma yarinya karama zatai tunanin yin haka? Sannan y

ayanta ne fa ubansu d'aya banda yanda suke tsananin san juna, shi kuma waccan mahaifinta ne sai dai im shine."

Little cikin mamaki ta kalli Habib tace " Yaya ya zaka ce Abba ne? Mai zaisa Abba ya cutar da Yaya?"

Habib bai amsa mata ba ya kalli Of

ficer.

Kawu kam ya ma rasa mai zaice, aransa yace "like father like son dukansu sai zuciya basu iya controlling din fishinsu ba sam.

Sai yamma wanda yaje bincike ya dawo dauke da doguwar takarda, duk abinda ya faru a wayarta ne da wanda aka kira

da time din kiran da kuma texts.

Kawu kam yana zaune ne kawai.

Bayan an kawu ne aka ga tabbas an kira Ashraf bayan kuma texts da akamai.

Mamaki ya kama Little duk da Yaya ne yace taba Abbanta wayarta inya tambayeta bata kawo komai a ranta ba

.

Officer ya kalli Little yace " me zaki iya cewa gameda sako da kuma waya da akai da layinki?"

Abbanta ta kalla sannan ta daure tace " nidai wlh ban kira Yaya ba."

Officer yace " mahaifinki fa?"

Tace " shima nasan bai kira yaya ba, sab

oda me zaisa ya kira yaya a wayata bayan ga wayarsa? In ma ya kira wani to sai dai in Nafisa ya kira."

Officer yai murmushi yace " hakane abinda kika fada me zaisa ya kira yayanki a wayarki bayan ga wayarsa? Wannan itace kalma ta farko da take bukatar

bincike."

Kawu kam gabansa sai faduwa kawai yakeyi.

Officer yace " kuje gida zamuyi bincike zuwa gobe."

Habib ya jata suka shiga motarsa sukai gaba.

Kawu ya shiga tashi cikin tashin hankali.

*************

Datti kam jiki

ba dadi da kanshi yake bi gari gari kauye kauye kauye sai dai ba Nafi ba labarinta ba kuma Dan Litti.

Hankalin Datti ya kara tashi nan ya fara zuwa gun malamai akan amai addu'a akan yarsa ta fito.

Sai dai haryanzu ba labari, Datti duk ya canza

magana ma ba damunsa tai ba, ba dukiya, ba 'yarsa dama wadancan sun gudu, duk ya zama abin tausayi.

*#ASHRAFEENAH TEAM*

[03:10, 06/09/2017] hm: *ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRI

TERS ASSOCIATION*

��



*87*

Little tayi kuka kamar ranta zai fita, Anisa ma haka, haka suka rungume juna itada Little a kotu suna kuka, Ashraf daga gefe yana zaune yana kallansu, shikansa abinda yake tausayi da tsoro kenan bayasan Little

tasan abinda ke faruwa sai dai ba yanda zaiyi.

Habib wanda ke zaune kusa dashi idanunsa sun kada sunyi jaa kamar goro, yasa hannu ya buga kafadar Ashraf baice komai ba ya mike zai fita, hannu Ashraf yasa yamaidashi ya zauna sannan a hankali yace " in

a zaka?"

Duk yanda Habib yaso ya b'oye hawayensa kasawa yai tun balle daya kalli Little yaga yanda take wani irin kuka, a hankali hawayensa suka ziraro ya kalli Ashraf kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa.

Ashraf ya mai murmushi yace "karkace koma

i Buddy nasan abinda ke ranka, so stop feeling guilty, ba laifinka bane haka fatanmu dai Allah ya yafe mana kurakuranmu."

Rungumeshi Habib yai alokacin hawaye ya fara zubomai sosai, cikin takaici da tsantsan tausayi yace "Ashraf na na......."

Ka

sa karasawa yai dan kukan yamai karfi, Ashraf ya bubuga bayansa a hankalu yace " karka damu abokina in har zuciyarka ta karye haka, Little fa?"

A hankali Habib ya d'ago ya kalleta sannan ya kalli Ashraf.

Murmushi Ashraf ya sakar mai sannan yace "

kalli Dady ka gani shikanshi murmushi yakema."

Nan Habib ya kalli mahaifinsa wanda za'ai waje dasu, da sauri ya dauke kansa yace " ni ai bansanshi ba."

Ashraf ya hade fuska yace " ka tashi kaje kamai sallama, ko kamanta mahaifinka ne?"

Habi

b ya kalli Ashraf yace " Haba Ashraf kisa fa?"

Sosai Ashraf ya tamke fuska yace " ka tashi ko kuwa?"

Jiki a sanyaye Habib ya mike ya karasa gun mahaifinsa.

Yana matsowa Dady ya kama hannunsa yace " Habib kayi hakuri."

Habib ya kalleshi c

ikin takaici yace " Dady ban taba tunanin haka halayenka b'oyayyu suke ba."

Dady ya daure yace " Ni kaina bansan me ya sameni ba, sa dai fatana kada kasa wannan abun a ranka harya xamemaka wani abun, sannan duk da abinda ke tsakanina da mahaifin Littl

e bazai hanani yimaka sha'awar auranta ba."

Habib ya dago cikin mamaki yace " Kanaso kace in auri Little bayan abinda kukama mahaifin Ashraf?ai ba Little ba banaji ma zan iya auran wata a duniya."

Yana kainan yai waje da sauri, Dady ya bishi da k

allo hawaye suka zubomai.

Nan akai gaba dashi, kawu kam ba wanda yaje gunsa haka aka fita dasu aka sasu a mota Sai gidan yari.

Anisa kam tana isa gida ta rufe kanta a d'aki banda kuka ba abinda takeyi, tayaya mahaifinta zai kashe mahaifin Ashraf

? Itakam ba wani uzuri da zatama mahaifinta ace d'an uwanka?duk da ba uwarsu d'aya ba ai jini jini ne, itakam bataji zata iya ko da cutar da Little ne bari har akai ga kisa.

Duk yanda Umma ke buga mata d'aki taki bud'ewa, a yanzu kam ta tabbatar da au

renta da Ashraf ya kare haka kuma tasan rayuwarta tazo karshe ba tantama.

Ganin taki bud'ewa yasa Umma ta koma falo ta baza tagumi tana kallan tsakar falon, lalai ba shakka duniya abin tsoro ce, itakam komai da yake faruwa jinsa take kamar a wani mu

munan mafarki ne da takeyi.

Little kam zazzabi ne mai zafi ya rufeta wanda sai dayakaita ga kwana a asibiti.

************

Mumy da kanta ta nemi mahaifiyar Nafi akan ta zauna da su sannan su tafi tare, Inna kam ta amince da hakan dan bat

ada wani uzuri sai mamakin yanda 'yarta ta zama takeyi balle yanda taga Mumy na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login